Chapter 6
*Makauniyar Shari'a*
_Sai a Lahira_
*NA*
_*IKILIMA ADAM*_
_( kyauta daga Allah)_
SHAFI NA SHIDA
" Dakata." shine farkon kalmar da ya samu damar fitowa daga bakinsa.
" Mamy shin kin san maganganun da kike fade kuwa , nasan girman Allah , kuma ina tsoron haduwata da shi , abubuwan da nake miki na farillah ne bana kawo sunnah acikin al'amaruna dake Mamy , taimakon da nake yi dafatan dai ba sokike in daina yi wa addini hidima ba ? in ko hakane babu biyayya ga abokin halitta wajen sabawa Allah ." yana kai karshen zancen ya katse wayar , tare da ajiye wayar kan tabur din gabansa, hannayensa duka biyun ya sa dafe da kansa , nan take wasu hawaye masu zafi kebin kyakkyawar fuskarsa , kuka yake kamar karamin yaro , Mansur cikin kidima ya karaso gabansa hade da dafashi ta baya yana bubbuga masa baya Alamun rarrashi , hannunsa yasa ya kauda tarin file dake gaban Ridwan , kana ya dawo ta gabansa ya zauna kan tebur din , cikin muryansa me nuni alamun wanda ke shirin yin kuka ya ce , " Rid tun muna Yara muka taso sau da dama na kan ganin kamar baka jituwa da Mamynka , amma kullum inna tambayeka dalili baka gayamin , kuma na lura kuka baya maka wahala muddin Mamy ta yi maka magana akan matsalarta , shin ban canci ka gayamin damuwarka bane ? ko dai abun naka sirrine da baze iya faduwa , amma karka manta Rid , kai sirrina ne , ni kuma sirrikane , dan Allah karka bari abotanmu ya samu rauni da rashin aminci." Yakai karshen zancen yana mai tura yatsarsa daya abakinsa. Ridwan dagowa ya yi tare da kai dubansa akan Mansur dinsa , cikin azababben kuka da ya kara zuwa masa , yanda yake kuka kai kace sakon mutuwa aka aiko masa , kukan yake sosai sannan yana fesar da numfashi tare da daukan tissu ya fara goge hawayensa , hannunsa yasa still ya sa tissu ze gogewa Mansur hawayensa , ga mamakinsa sai ganin Mansur ya yi ya kauda kansa gefe hade da sauka daga kan tebur din , tafiya yake goye da hannayensa abaya har ya karaso wajen window din office din , idanunsa na kan farfajiyar ma'aikatar mai cike da haduwa , inda jerin motocin ma'aikata suke yake kallo , idanunsa na kan Motar Rid kirar Mercendenz 2022 , murmushi mai kama da ciwo yayi jin Ridwan ya dafa shi ta baya , be waigo ba amma duk hankalinsa da nutsuwarsa ya dawo akan Ridwan da ya ji ya fara magana.
" Mansur kafi Mamy daraja da kima a wajena".
Firgit Mansur ya waigo kamar an tsinkaye shi da allura , cikin rawar baki ya ce , " Ri....d...w...a.....n..... ka ko ....san abinda ka..ke ..fa..de...kuwa.....". sauran kalamansa samun makalewa su kayi jin Ridwan yana magana kamar haka.
" Eh nasan abunda nake fada kuma kai ma kasan banda Mahaifiya data wuce Mamy , karkaga laifina domin na tsani !! mata , natsani mata !! , banason Hulda da mata !! Wannan dalilin yasa ko Aure ni Ridwan bazanyi ba , ahaka zan kare rayuwata, amma ina kaunar kannena mata , mahaifiyata ban tsaneta tunda ta kawoni Duniya har nake shan iskan cikinsa , kuma abinda kake son sani akan abubuwan dana fada akan Mamy zan fada maka amma ba irin wannan lokacin ba , Mamy bata min komi ba a rayuwata ba , ni Ridwan zan baka labarin zuciyata kila muzo ra'ayi daya ni dakai." Yakai karshen zancen yana mai share kwallan daya zubo masa.
Mansur hannayensa masu taushi yasa ya soma goge masa kwallah , cikin murmushinsa wanda ta zama dabi'arsa ya ce , " Rid bansan meye dalilin da yasa ka tsani Mata ba , amma babu Dalilin da ze sanya kace babu kai babu Aure arayuwarka wannan kuskurene , in sha Allah Ridwan sai kayi Aure harda ya'ya .". ya karashe zancen da guntun murmushi a fuskarsa.
Ridwan ba tare da ya bashi amsa ba , ya koma kan kujerar office dinsa mai lilo , yana zaune yana juya kujerar ." cikin yin kasa da muryansa in ba ka kasa kunne ba , bazaka taba jin me yake fade ba , file a hannunsa dauke da biro ya ce , " ai Mansur ya'yanka nawa ne in ka haifa sai ka bani su amma banda ya'ya Mata." ya kai karshen zancen yana mai yan rubu-rubucensa kamar bashi ya yi magana ba.
Murmushi mai sanyi , Mansur ya yi tare da tsurawa Ridwan idanu yana kallon kyakyawan fuskarsa mai dauke da yalwataccen saje da aka taje su suna sheki da walwali , kallonsa yake yanda baka iya banbance shi in har ya shiga cikin labaraba domin fari ne tass , kyakyawan matashi ajin farko , jajayen labbansa yake kallo yana , kara kallon sumar kansa masu tsantsin da sheki , nan ma murmushi ya yi yana magana a zuci , tare da daukan alwashin canza masa duk kudirinsa , maye masa gurbin kuka da dariya , murmushi yake sakarwa shi kadai , wanda hakan ya jawo hankalin Ridwan tare dan dago kansa yana fadin " Mansur wai me ka ke wa dariya ne? , gulma dai babu kyau ". ya yi magana yana mai harhada takardun dake gabansa.
Mansur cikin sanyin murya ya ce " ni bazan baka ya'yan da zan haifa ba saide ka haifi naka da kanka , har fadi kake kada na baka ya'ya Mata , yanda kasan na hannun yarjejeniya ni dakai , duk abinda kake fade in sha Allah saina canza shi ". Yakai karshen zancen da guntun hawaye a fuskarsa . Ridwan kwabe baki ya yi tare da cigaba da abinda ke gabansa.
Kano
Asibitin Murtala.
Salim kwance agadon asibiti sam be san wanda yake kansa ba , domin tunda aka kawo shi , baya iya magana, saide ya yi ta zuba idanu yana kallonka babu kiftawa , Mahaifiyarsa sanye cikin atamfar roba , me dauke da dinki buba , cikin mutuwar jiki da rashin kuzari take masa fifita da abun fifita , shikuwa Salim da idanu yake bin ta da kallo . Mahaifinsa da kannensa dake c'en gefe daya suna kallon halin da Salim yake cikin , cikin rawar murya mamansa ta ce ," kana jin docto ya ce sai anfitar dashi waje za'a masa aiki domin ya samu matsala a cikin cikinsa , wannan abun duk kune kuka ja da tun farko kun saurare shi da hakan bata faru ba , to in har shine ya fitar dasu tunda dai ba'a gansu ba , basai a hakura ba , yanzu ina yaran da kasa su masa duka suke ? Kaga kafarsu a asibitin nan , ya kamata in ranmu ya bace kada hankalinmu ya gushe , duk dangi mu babu mai arziki ina zamu samu kudaden da za'ayiwa Salim aiki , kuma shine kadai ke fadi tashi wajen nemo mana abinda zamu ci , yau gashi a kwance be iya tabuka komai , kai kuma ba wani kokari gareka ba ". tayi furucin cikin fada tana mai hararan Mahaifinsa da kannensa.
Abban Salim gaza magana ya yi banda " Uhmmm." Babu abinda yake maimaitawa.
Tunaninsa ta ina zasu samu kudade masu yawa har miliyan biyar !! Kara shiga matsananci damuwa ya yi a karo na biyu tareda zabga uban tagumi.
ABUJA CITY
Ghetto
Bayan kwana biyu misalin karfe goma na safe Papy kwance akan katifarsa , yana mai sauraron rediyo yaji Muryan Amatullah tana fadin " Papy zanje ko zan samu bara domin yanzu kayan abinci gare mu babu na siyen biredi da kayan miya." tayi magana tana mai dauko hijab dinta dake makale kan kofar dakin , karkada mata kai ya yi alamun sai ta dawo , kana yakara maida hankalinsa akan Rediyo da yake saurare.
Ahanzarce ta fice tana tafiya tana fadin Allah yasa ta samo sadaka , cikin tsananin tsoro da Fargaba taga Karfin Iko zaune akan wata katuwar dutse da dukan Alamu waya yake yi mai muhimmanci. Ba jinsa take sosai ba , amma kunneta ya jiyo mata inda yake fadin " Haba Mandula ka hanzarta kuje Kafachan dake jahar Kaduna , ku bincika gidan Alhaji Ado mai kaji , in sha Allah za'a nuna muku . Dan Allah ku tabbatar kunyi garkuwa dashi , kuma in kun cika aiki ku sanar dani zan gyara muku muhallin da zamu ajiyeshi ". yakarashe zancen cikin babban muryansa .
Zazzare idanu Amatullah ta soma tare da sa hannayenta ta toshe bakinta , da baya_ baya tafara tafiya tana kokarin sanya gudu , ganin kamar ze waigo ne yasa ta gyara tsayuwarta hade da kakalo murmushin dole ta fara taku ahankali kamar wacce ruwa ya cita kokarin wuce shi take , taji Muryansa me ban tsoro yana fadin" ke!!! .". nan da nan hantar cikinta ya kada batasan sanda ta saki fitsari awando ba.
Tasowa daga zaune da yake yayi karaso kusa da ita kafafunta yake kallo yanda ruwan fitsari ke bin ta , cikin Mamaki ya ce " daga ina kike !? Kuma me kike nema anan ko anan Gidanku yake ? ." cikin hanzari ta girgiza masa kai tare da masa alamun A'a ba anan suke ba .
" Me kike nema anan wurin?." Ya yi magana cikin tsareta da idanu yana hura hanci .
Bata bashi amsa ba illah kawai kara yin kasa da kanta ta yi banda harbawa babu abinda Zuciyarta take yi.
" Nasan bara zakiye , kuma nasan har dakin ku , zuwana nan saboda ke ne , waya na tsaya yi da tuntuni kin ganni kofar dakinku ". Nan da nan hantar cikinta ya kada jikinta ya hau rawa kamar mazari , cikin rawar murya ta ce " dan Allah karka zo Gidanmu Papy bayaso kowa yazo inda muke banason na rasa shi ɗan Allah kar kazo". Takai ayar zancen cikin kukanta mai tsuma zuciya .
Papy dake cikin dakin sa jin kamar muryan Amatullah da wani yasa ya juyo ta bayan Gidan yana kallonsu ba tare da sun gansa ba , yana sanya idanu akan Karfin Iko nan da nan hantar cikinsa ya kada , jikinsa ya hau rawa kamar mazari , hango wani kango yayi daga c'en gefensa cikin sanda sanda ya tafi c'en ya boye tare da tattare kansa waje daya.
Karfin Iko kama hannun Amatullah ya yi suka karaso har Gidan nasu. Kana yashiga dakin nasu , daga ita har shi kallon juna suke. Cikin mamaki take fadi a zuciyarta kardai Papy ya gudune kamar yanda yanda yasha furta mata , muryan Karfin Iko ne ya dawo da ita cikin hayyacinta , jin yana fadin " daman Papyn naki yafita ne ? ". Girgiza kai tayi tare da fadin " eh ya ce min ze je unguwa sai bayan la'asar ze dawo ". ta idasa zancen cikin tashin hankali da ba'a sanya masa rana .
Karfin Iko sosai ya shiga nazartan yanayinta ganin duk a tsorace take dashi ya sa shi fadin " ni fa ba mugu bane babu abunda zan miki sai Alkhairi , zan baki dubu ashirin kije ku siya duk abun da kuke bukata ".ya karashe zancen yana mai zaro bandir din kudin daga aljihun wandonsa .
Da murmushin yake a fuskarta ta karba tana masa godiya , shikuwa ganin wayarsa tafara ring ne , ya fito cikin sauri takalman ƙafarsa manya manyan irin na masu shiga ruwa take bi da kallo , kana takai dubanta akan gashin kansa mai dauke da kitso irin na *Bob maley* sanyayan ajiyar zuciya ta sauke ganin ya fice yana waya , sannan wani karin tashin hankali ya kara zuwar mata ganin babu Papy awajen harta daura hannunta akai zata kurma ihuu ne , ta ji an dafata da baya , afirgice cikin tsoro ta waiga, ganin Papy na mata dariya ya sa sauke nauyayyen ajiyar zuciya tare da fadawa jikinsa aguje , wani marayan kuka ta saki stil cikin narke murya ta ce , " Dan Allah Papy karka gujeni". yanda tayi magana saida ta karya masa zuciya , hannayensa ya sanya domin share mata hawayenta , cikin tsananin mamaki da fargaba suka ji takun tafiya alamun anzo gab dasu , atare itada papy suka kai dubansu akan ...........
Makauniyar Shari'a taku ce .
Domin son magana dani ***
Share and comment pls