Makauniyar sharia

Chapter 7

by @kyautadagaallah10

*Makauniyar Shari'a*

_Sai a Lahira_




SHAFI NA BAKWAI


Cikin tsananin mamaki suka ji takun tafiya alamun an zo gab dasu , atare ita da Papy suka kai dubansu akan Matar nan . Ajiyar zuciya mai karfi suka sauke dukansu ,

suka kai dubansu akanta , cikin zallan mamaki da nacin Matar , Amatullah take kallonta cikin idanu nan da nan ranta ya soma ɓaci , cikin muryan kamar wacce ke gab da shirin sakin kuka ta ce , " Baiwar Allah meyasa kike ta bibiyata ne ? In akwai abinda na miki ki sanar min dan Allah". takai karshen zancen tana kallon yanda Matar ta tsura mata idanu . Fesar da numfashi mai zafi , Matar ta yi ita ma fuskarta babu annuri ko walwala ta ce , " Amatullah kwantar da hankalinki , ban biyoki nan dan cutarwa ba amma shi Papy naki meyasa baya bude fuskarsa ? Ba wannan ba , bari in dauko miki wani hoto a wayata zaki gasgata abinda nake son nuna miki" . tana kokarin ciro hoto daga jakarta .

Papy kuwa kallon kallo sukeyi shi da matar , kana yakai dubansa akan hoton data fiddo acikin jakarta, tana kokarin nunawa Amatullah .

" Dakata ". Shine kalmar da Papy ya furta murya a khausashe.

" Ni zaki bawa na duba in ya cancanta ta gani sai in bata in kuma babu cancanta dan Allah ki koma da kayanki kuma ki kyalemu ". Yakai karshen zancen yana mai mika mata hannun alamun ta bashi.

Mika masa ta yi tana kallon kwayar idanunsa , so take ta gane ko ta taɓa ganinsa sauke idanunsa da ya yi be bata damar hakan ba .

Agigice yake kallon Hoton nan da nan ya fara zazzare idanu , yana kallon hoton yana kallon Amatullah , muryansa da harshensa na rawa ya ce , " Hajiya ya sunanki ? Inason ganinki na minti biyar ya yi magana tare dan janta gefe daya.


Amatullah da mamaki take kallon sun raba c'en gefe , fuskokinsu take kallo dukansu cike da tsananin damuwa , da mamakinta ganin Papy ta yi yana ma Matar magana yana mata nuni da hannayensa , alamu sun nuna kamar kwatance yake mata , kanacen baya yagama maganar , sai taga matar ita ma magana take tana rintse idanunta alamun maganganunsa masu tsauri ne".


Cikin damuwa ta ce , " Meyasa Papy ya hana in ga hoton nan , shin me yake faruwa ne ". Take tambayar kanta , ganin babu mai bata amsa sai shi , yasa ta nemi wuri ta zauna .

Mintina kusan arba'in suka dauka suna magana ,kafun su dawo inda Amatullah take , Matar kuwa kallon Amatullah tayi tare da fadin " Yar Gidan Papy zan tafi ki kula da kanki in sha Allah, zan kara waiwayo ku ".


Murmushin yake kwance akan fuskar Papa ya ce , babu matsala sai ta dawo din , kana ya dan mata rakiya , ganin ta fice ne ya dawo tare da shigewa dakin nasa. Yana ciki , jingina da bangon dakin ya yi yana mai tunanin maganganunsa da matar kana yakara gyara zamansa dakyau , yana kallon kasan dakinsu , katifar kwanciyarsu yake bi da idanu . Batareda ya ankare ba wani barci mai daɗin gaske ya yi awon gaba dashi , cikin barcinsa yafara mafarki .


Zaune yake akan babban kujera na Alfarma , wani babban daki na Alfarma yake zaune acikinsa. Daki ne wanda yaji kayan alatu na more rayuwa , fankan saman dakin kalar zinariya akayi goldin , kujerun dakin har ma da carpet din dakin , dîner table duk kalarsu daya , ga tarin takarduna a gaban sa yana sanye da hula irin na Alkalai akansa , dattijone shi ba Fari ba kuma ba'a sakashi sahun bakake ba , kyakyawa daidai gwargwado , cikin aikinsa yake yaji kamar ana tunkaro shi daga bayansa wanda yasa aguje ya waigo ga mamakin wata mata ya gani rike da wuta , wanda ya nuna da dukan alamu matarsa ce , zumbur ya tashi ya soma ja da baya baya , bakin sa na rawa ya fara kokarin magana ............ Bubbuga shi da karfi da Amatullah tayi ne ya sa shi farkawa arude , nan da nan ya jike shargab da gumi kana , cikin rawar jiki ya fara karanta innalillah wa'inna ilairajun .

Cikin rudu Amatullah ta ce , " Papy Lafiya kuwa kake ta muzurai acikin barci , wallahi duk na rikice Papy anya kayi aduar da kake koyamin in zamu shiga barci kuwa?.". Sai yanzu hankalinsa yadawo jikinsa , murya na rawa ya ce , " kawai mafarkin ban tsoro nayi dan haka alwala zanyi , kuma yau mu hada kayanmu zamu canza unguwa". Yayi magana babu wasa acikinta .

Amatullah kallonsa take yanda yadan rame na lokaci daya , tana son sanin me yake damunsa amma ganin be bata fuska ba yasa ta yin shiru tareda lulawa duniyar tunani.


Asokoro


Sai kusan karfe shida na yamma , Ridwan ya kama hanyar Gidan nasu , tafiya suke a mota suna hira shida Mansur , Tik tok Mansur ya kunna yana kallon Video Murja Ibrahim kunya yanda take tikan rawa , murmushi yake cike da zolaya ya ce , " Ridwan wannan yar Tik tok din in ka sameta ka huta wallahi , yarinya ga farin jini , kuma ma ance Abba Gida-Gida gwanar Kano ya ce , ta fito da miji ze mata Aure , dan Allah malam kafito ka aureta kawai awuce wajen ". ya karashen zancen yana dariya iya gaskiyarsa . Ridwan ta gefen idanu yake kallon video da murja ke rawan kana ya tabe baki hade da yin siririn tsaki , cikin takaici ya ce , " ai wannan ko a Aljanna Allah ya mallaka min ita nasan banyi abun kwarai ba , kaga ita ga fitsara a fili , sannan wannan kazamar yar kauyen nan da mukaso bigewa , da kuma haukanta ya motsa ta biyomu har cikin taro , ko akafa aka dauraminsu , cire kafafun zanyi na wurgar in huta da kuda , gwamma ta Tik tok din ko bakomai tana wanka , kai nace maka ka daina min hiran mata yau ma bansan dalilin dayasa na biye maka ba ". Ya idasa zancen cikin takaicin tuno da Amatullah.

Banda Dariya babu abinda Mansur ya keyi cikin , tsokanar muryan Ridwan ya ce , " ta kauyen nan bata shige maka zuciya ba kuwa naga meye na tuno ta daga ana hiran Murja , kodai kauyen zamu koma ". yakai karshen zancen yana mai kallon yanda Ridwan ya yi shiru kamar baya jinsa ..

Ridwan kam kasa magana ya yi yana jinjina kalaman sa , tare kara mai da hankalinsa ga tukinsa.


Tare suka karasa Gida shi da Mansur , suna fitowa daga cikin Motar su na Alfarma nan da nan Bodyguard da ma'aikata suka zagayesu , cike da bangirma suke masu barka da dawowa , fuska asake suka amsa musu , Ridwan cikin dabi'arsa da sam baka gane yanayinsa da kunci ko na walwala ne yakai dubansa akan su , ahankali kamar ana masa dole ya daga jajayen labbansa masu sheki da burgewa ya ce , " ina fatan babu wata matsala ko? sannan inason daga gobe Bodyguard dina su dawo aiki , akarshe kuma inason ku sani duk wanda ya kara Gulmata a gidan nan zan dau kwakwaran mataki akansa ." Yana kai karshen zancen ya kama hannun Mansur dake kallon yanda ya ke magana babu wasa ko daukan raini aciki , binsa yayi inda suka shige daga ciki .


Ma'aikata da Bodyguard sosai suka razana jin furucin da ya yi , to su wani irin gulmarsa suke yi , kuma ma waye ya f'ada masa hakan , Lallai acikinsu akwai munafukai cewar daya daga cikin ma'aikatan, gudun karsu kara sakin baki ya sa suka bar wajen tare da yin gum da bakin su.


Ridwan kallon Mamy ya ke yanda take zaune a falon da dukan alamu kamar tana cikin bacin rai , make kafada ya yi alamun ko ajikinsa. Kana suka karaso falon hannunsu cikin juna shi da Mansur , dukansu durkushewa suka yi suna mika gaisuwa ga Mamy , cikin fushi ta amsa musu gaisuwar tasu. Atare suka mike , Ridwan cikin kosawa yake shirin su bar falon shi da Aminiyansa , ya ji sautin muryan Mamy tana fadin " dan Allah Mansur zo ina son ganinka ".


Cak suka tsaya dukansu daga shi har Mansur din , sakin hannun Mansur din ya yi tare da yin gaba , shikuwa Mansur cike da fargaba ya dawo falon , yana isowa wajenta ya fara kokarin durkushewa gabanta ahanzarce ta hanashi tare da nuna masa wajen zama , kana ita ma ta dawo kusa da inda ya zauna din.


" Mansur kai fa Aminin Ridwan ne , meyasa bazaka fada masa ya ji tsoron Allah ba , ya fidda hakkin iyayensa musamman Mahaifiyarsa , ko ya manta girman Uwa ne awajen Allah , Manzon Sallallahu alaihi Wasallam saida yace abi Uwa sau uku sannan ya ambaci Uba sau daya , yanzu saboda Allah jibi arzikin Ridwan ace ko Makkah ban taba zuwa ba, ko Humra kuma bayan kullum saide inji yabiyawa mutane hamsin kujerar Hajji duk shekara, me na tsare mishi banda abincin da yake bamu babu abinda yake sinana mun , kullum saide inga abu a wani Gida amma banda Gidana , hatta wayar hannuna dakyar ya siyamin ka ganta nan airtel ". ta karashe zancen tana mai nuna masa wayar.


Shi ma wayar yake bi da kallo yanda aka manne ta da robe dan kada murfinta yacire .


" Yanzu ya dace ace Ni Mahaifiyar Ridwan Muhammad Mai nasara , ni ce awannan yanayin babu kyaun gani , fuskata duk kuraje , wallahi tallahi inajin bakin cikinsa , kuma yasan inna tsine masa ze bisa , kayi masa fada tun ban kai shi kara kotu ba .". takarashe zancen cikin muryan kuka da takaici.


Jikin Mansur ya yi mugun sanyi babu abunda ya gigita masa tunani jin furucin wai zata makashi a kotu , hannayensa ya daura akai alamun tunani , kana ya dawo ya dago kansa dake sarawa da tsananin ciwon kai na lokaci daya, idanunsa da suka kada jajir ne yake kallonta dasu , cikin rawar baki da disashewar murya ya ce , " Mamy da farko dai hakuri zan baki , kuma duk wanda ya yi hakuri yana tare da nasara , kinsan dai Ridwan ba jahili bane yana da ilimi daidai sanin da Allah yabashi kuma yana da tausayi da jin kai , amma bansan meyasa duk wannan halayen nasa ba , baya ji kwata kwata akanki , maganar kotu karki fara saboda Ridwan D'an da ki ka haifa da cikin ki ne , ni banda ya nuna min ya tsani Mata ba ina ganin kamata ya yi a masa aure kila a dalilin ganin yanada iyali ze bar wasu abubuwan ".

Cikin tsananin tashin hankali Mamy ke juya kalaman aure kuma a ranta , a fili kuma ta ce , " Please abar zancen auren nan banaso .

Cikin zallan mamaki Mansur ke kallonta , kana ya mike cikin rashin kuzari tare da fadin ze tafi gun abokinsa kuma ze iyakar kokarinsa ganin ya dawo dashi kan hanya da wannan kalaman ya samu damar barin falon ransa fal da tunanin me Mamy take nufi? batason Ridwan ya yi aure ne da wannan tunanin ya hau matakalan step.


Itakuwa rike da baki take juya kalamansa har Anisa tazo gabanta bata sani ba , sai magana take ma ta shiru ,Anisa murmushi ta yi tare da dafa Mamy , wanda yasa a firgice ta dawo hayyacinta , cikin subutar baki ta ce , " nace maka Ridwan bazeyi aure Please abar zancen nan.". da mamaki Anisa ke kallonta hade da taba ta , tana fadin " Mamy lafiya kike sambatu , kuma akan yaya Ridwan ".

Mamy dafe da kanta ta nuna mata bama tasan tayi furucin ba.

Ghetto


Tun adaren Papy ya haɗa musu kayansu , zasu bar unguwar, in ta kama Garin zasu bari .

Asuba tana yi suna idar da sallah suka kamo hanya fita daga unguwar riki riki da kayansu ahannunsu Papy ya rike wasu Amatullah ma haka , yana sanye cikin shigarsa ta buzaye kamar yanda ya saba ,sun kusa isa bakin titi , suka ga ansha gabansu antare gabansu da bayansu , babban cikinsu sanye yake cikin bakaken kayan sanyi masu kauri rigarsa mai haɗe da hula ne akansa ya juya musu baya , bayan rigarsa suke kallo , inda Papy yaga an rubuta..............



Makauniyar Shari'a taku ce.


Domin son magana dani ***


Share and comment pls