Page 10
by @maidambu41
بسم الله الرحمن الرحيم
Dan murmushi tayi tana kallon, roundabout din kofar fada. Ganin bata kuma magana ba, yasa shima yayi shiru har suka nufi titin unguwar, "Chioma gobe zamu koma ko?" Ya tambaye ta, saboda yana gudun kada su haɗu da Adamu Malami tace ta fasa bin shi. "Obinna ka yarda dani." Ta faɗa daidai lokacin da Amanda ta cewa drive din. "Ga gidan nan, me almajirai." parking yayi yana faɗin. "Taya kika san nan ne gidan?" Shiru tayi tana kokarin bude kofar motar, Uwar ta riko hannunta.
"Ama ina zaki ne kike iri wannan saurin?" Nuna mata kofar gidan Malam tayi tana faɗin. "Grandfather na ne!"
"Ama bana tunanin zan barki a wurin Musulmai, domin zasu mai da."
"It is Fate!"
"But fate is cruel for me and you! Ki rufa min asiri kada ki yarda da kowa. "
"Nne! Ba zan iya binki ba, domin nan ne dole na, wurinki ba dole ba ne na zauna."
"Keep quiet! Ina magana kina magana!" A hankali ta zame mayafin da ya rufe mata fuska suka haɗa idanu da Uwar.
"Ya isa haka!" Inji Obinna, fitowa suka yi a tare, daidai malam yana tsakiyar almajirai ana karatu, wurin karfe hudu da wani abu na yamma. Kamar an ce mishi ya d'ago kai, ya hango yarinyar da Uwarta. Exactly mafarkin shi, Hadiye yawu yayi. Tare da mikewa yana kallon yadda Yarinyar take tafiya a iska, domin ba ta taka ƙasa.
Kallon inuwayoyin da suke bin ta yayi, yaga daya cikinsu ya ja ya tsaya, bakar inuwar. Sai daya inuwar ne ya tsaya a tare da ita, fita yayi daga cikin almajiran ya nufe su.
"Sannunku da zuwa!"
"Baba Malam!" Ta kira sunanshi, murmushi yayi yana shafa kanta.
"Na'am"
Ya kalli Chioma da jikinta yayi sanyi, "Barka da zuwa Y'ata!" Sannan ya juya ya kalli Obinna, ya kira shi. Ba musu ya dauki kayansu, yana isa wurin almajirai suka amshi kayan, suka shiga da shi cikin gidan. A zauren gidan ya sauke su, sannan ya shiga cikin gidan da Amanda, yana faɗin. "Hajiya Sa'a! Zo ki taimaka min idan akwai sauran abincin, a bawa baki." Fitowa Innayo tayi tana kallonshi.
"Wasu irin baki ne haka, da kake wani rawan jiki a kansu. "
"Allah ne ya turo min su da baiwar Allah, gata nan."
Fitowa Umma tayi, tana faɗin.
"Kasan akwai wanda na saka aka yiwa Attahiru gashi nan, a basu sai Jamilah ta kuma min wani."
Ita kan Amanda kallonsu tayi, tana murmushi da farinciki.
Amsar abincin yayi zai juya ta ce mishi.
"Baba malam, bani na dauka."
"A'a ba zaki iya ba."
"Zan iya mana!" Ta saka hannu ta amsa, yana biye da ita har zauren, ta ajiye ya fita ya kira almajirai Biyu ya basu dari biyar guda bakwai ya ce su tafi Bauchi club su sayo mishi namar kaza, sai kayan sanyi a shagon Mudan.
"Tow Malam!"
Sosai suka zauna suna kallon abincin, Amanda kuwa budewa tayi tana ci hankali kwance, tana faɗin. "Ku ba zai ji dadi ba idan baku ci ba"
"Amaryata ke daya kike cin abincin?"
Ya tambaye ta, "Eh Baba Malam." Shigowar almajirin da ya aika ya kawo ruwan sanyin, ya ajiye sannan ya fita.
"Baba Malam!" Ta kira sunanshi a hankali. Kallonta yayi yaga tana kokarin bude coca cola, ya ce mata. "Amarya ba zaki iya budewa ba." Sai gani yayi ta buɗe murfin, ba tare da ta saka bakinta ba.
A hankali ta sha sosai, sannan ta ajiye kwalbar cikin harshen Igbo ta cewa Uwar.
"Nne! Kici abincin, uncle ba zai ci ba."
"Amarya bari na baku wuri."
Waje ya nufa ya sallame Almajirai, sannan ya bi ta daya kofar, ya shiga cikin gidan. Yana shiga ya samu su Innayo, Goma da Umma. Sai Jamilah da suke jiran karin bayani.
"Malam bakin daga ina suke?"
"Ban sani ba." Ya faɗa, yana me zama a bakin rijiya.
"Ke dauko mishi kujeranshi."
"Ita yarinyar da kuka shigo tare suke?"
Kallon Innayo yayi sannan ya ce mata.
"Yadda Attahiru da Amir suke kirana haka itama take kirana."
"Nima nayi mamakin, yadda ta kira kamar tana cikin gidan nan!"
"Jini na yake yawo a jikinta, baiwar Allah ce da babban al'amari."
Ya faɗa a hankali, can wurin biyar almajirin ya dawo, ya kawo namar, ya ce a saka a tire a kai musu zauren.
Haka kuwa Jamilah tayi, ta kai zauren.
"Gwaggo Jami, ki cewa Baba Malam ya zo." Yadda tayi maganar babu wasa a cikinsa yasa Jamila ta amsa da cewa
"Tow!"
Bayan ta shiga ta gayawa Malam sakon shi, sannan ta kalli su Innayo ta ce musu.
"Arna ne fa, ba musulmai ba."
"Can musu!" Inji Innayo, sannan ta juya dakinta.
Malam yana fita, Attahiru yana shigowa zauren, gaida su yayi yana rike da wayar Motorola. Gaisawa yayi yana faɗin.
"Baki kayi ne?"
"Eh Attahiru!"
Ya gaishe su cikin harshen Ingilishi ya saka kai zai wuce, Amanda ta ce mishi.
"Da ka dawo ka zauna, ayi maganar da kai domin su basu jin hausa. Malam baya jin turanci. " Wani irin abu yaji ya dira a kanshi ya dawo yana kallon yadda take cin nama.
"Eh kuma haka ne, zauna ayi da kai."
Zama yayi yana faɗin "tow!"
Shiru zauren ya dauka, kafin Obinna ya fara magana da harshen turanci, ya ce musu. "Wannan sunanta Chioma ita ce ta haifi wannan Yarinyar, Amanda." Yayi shiru kafin ya ci-gaba da cewa. "Wato Adamu Malami Jajja, shi ya haifi wannan yarinyar nan." Wani irin shiru Attahiru yayi yana kallon yarinyar da take cin kasarta hankali kwance.
Ganin yadda Attahiru yake zufa, malam ya dafa shi yana faɗin. "me ya faru?" "Wai sun ce yarinyar nan yar Baba Adamu ce." Murmushi Malam yayi, ya ce masa. "Ka tambaye su, da aure aka haife ta?" Sai lokacin Amanda ta ta d'ago kai tana kallon Malam. Yadda Tahir yayi tambayar yasa Chioma gyada kai tana faɗin. "Da aure aka haife ta. Shi sir Adam ya san kome." Tahir ya gayawa Malam, murmushi yayi sannan ya ce mata. "Ba zata hakura ta zauna da shi, ko akwai wasu rabon. Ni ta dauke ni a matsayin uba, ba zan taba barin wani abu ya same ta ba." In Sha Allah
Yadda Tahir ya faɗa, sai da Obinna ya kaɗu, sannan ya kalli Chioma kamar zai kuka ya ce mata. "Kin ga abin da nake gudu ba." "Baba Malam." Ta kira sunanshi a hankali. Kafin ta ce mishi, "ka barta tana da nata Rayuwar." Shiru suka yi da Tahir kafin ya kuma magana, ta ce mishi. "Ya zaka yi da Innayo?" Sai da yayi shiru kafin ya bude baki zai magana ta ce mishi. "Mu ba mazauna ba ne, tafiya zamu yi ita yarinyar itace taku, Uwarta ku barta tana da rayuwarta. Kasan ƙaddarar da tasa muka kawo su nan? Hmmm Alhaji Sani Malami Jajja, zamu tafi amma lokaci zuwa lokaci zamu na kewayowa. Amma kafin nan ina son ka sani ita yar din jikar kace, ba iya mu ɗaya muke tare da ita ba, sai dai zuwan ta nan yasa muka bayyana daga gare ta. Mahaifiyarta zata tafi, dole ka saka idanu akan rayuwarta. Mun barka cikin amincin Allah."
Daga haka, kwanta a wurin tana nishi.
Nufar kanta Chioma tayi tare da riko hannunta. Yanzu take magana amma kuma yanzu jikinta ya kuma rikicewar kamar kwanakin baya a can Enugu. "Tahir ka kai wannan mutumin gidan baki, ita zamu shiga da Ita!" Haka kuwa aka yi, Malam da Chioma suka shiga cikin gida da Amanda, bai yarda ya kaisu wani wurin ba, dakin Hajiya umma ya kai su, har lokacin Ama birgima take tana kuka. Uwar ma kuka take domin ta gaji da ciwon Ama. Amma ba zata iya barin a wannan yanayin ba. Ta zata ta warke ne, sai dai me suna zuwa ciwo yana dawowa.
Kiran sallah magariba, yarinya ta fara suma, tana ihu da gurnani. Tsaki Innayo tayi ta ce. "Saboda saka kai wahala ya dauko mana, arna zai musu magani."
"Baki ga yarinyar taki yarda a ga fuskarta ba."
Inji Hajiya Goma da munafunci yake cin ranta. "Can ta matse musu." Suka wuce dakinsu. Dakyar Umma tayi sallah, tana addu'a Ama ta fara ihu. Sai da ta shafa sannan ta kalli Chioma da bata jin Hausa itama kuma bata jin turanci. Shigowar Malam da wasu manyan dalibansa, suka shiga falon, anan aka shiga mata addu'a tare da fara karatu malam yana can gefe yana rubutu, ana bata tana sha da karfin tsiya.
Ba karamin wahala suka sha ba, har zuwa lokacin da ta fara barci. Babu wanda ya huta domin tana fara barci zata fasa ihu ta fara shure-shure. Har wurin karfe daya na dare kafin suka samu ta yi barci, a lokacin kowa ya watse, sai dai me? Lokacin da suka nufi hanyar gidan kwanansu, anan suka hadu da wani abin al'ajabi. Domin kuwa wani katon bunsuru ne da gemunshi yake jan kasa, Idanunshi jajjur, ya kasa su da mugun gudu. Har suka shiga cikin gidansu dakyar. Tahir kuwa yana shiga dakinshi, a gajiye yayi addu'a ya kwanta. Babu abin da ya faru da shi sai mafarkin da yayi. Wai ya fito cikin dare. Ya ga wata yarinya a gindin rijiya, farin gashin kanta ya lullube ta baki daya. Tana diban ruwa daga rijiyar tana watsa shi a ƙasa ya nufi wurinta zai mata magana. Ta fasa wani irin ihu me bala'in ƙara, da ya tilasta mishi tashi a firgice. Yana kallon kofar dakinshi da yake wangale. Abin ya bashi mamaki dole ya mike tare da rufe kofar.
Malam ma an kai mishi ziyara, sai dai basu kwashe da dadi ba, domin yana Sallar dare, aka zo mishi, basu yi nasara ba. Sai dai cikin daren akayi ta watsi da kayan aikin gidan, sai dai kaji an buga kofi da kasa, tare ihu me ƙarfi.
Sai asuba aka daina motsi da kayan gidan.
★★
Gimbi
Tunda Saif ya kirata, ya gaya mata zai wuce Azare kafin ya iso Bauchi, domin ta Kano zasu sauka, haushi ya cika ta. Bata kuma ɗaukar kiran shi, ya turo mata sako ya kai bila'adadin.
Kamar tayi hauka, ita ɗayarta sai wani irin huci take tana jijjiga kafarta. Ita Saif zaima wulakanci?........