Chapter 11
*Makauniyar Shari'a*
_Sai a Lahira_
*NA*
_*IKILIMA ADAM*_
_( kyauta daga Allah)_
*Littafin nan , na kuɗi ne da zaran free page ya kare zaki daina ganin sa.hanzarta kibiya naki kada ayi babu ke.*
*Dari biyar kacal*
*3115484026 Ikilima Adam firts bank*
*Tura shaidar biya akan wannan lambar* *( ***) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.*
*Siyen Nagari maida kudi Gida*
_*Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma.*_📚📚
SHAFI NA SHA DAYA
Cikin rawar murya da tashin hankalin da ya bayyana karara afuskarsa ya ce " dan girman Allah be bar muku number wayarsa ba ? ". Ya karashe zancen murya a raunace , sabon babin tashin hankali ne ya bayyana karara a fuskarsa , yanzu kenan inhar be kara waiwayo tashar ba shike nan wahala ta same shi , ji yake kamar ya kurma ihu dan tsantsar bacin ciki , tunaninsa katsewa yayi jin Drever na fadin .
" Gaskiya bamu amshi lambarsa ba amma shi kam ya amshi namu ,yace zeyi ta tuntubar mu ko za'a dace ". Drever na kai karshen zancen ya barsa agurin tare da shiga motarsa domin zuwa shan mai.
Faruk ya danji sanyi aransa domin hakan ya tabbatar masa ze iya kira a kowani lokaci , tashin hankalinsa befi tunanin abinda ze ringa ci kafin yaga Megidansa ba , yana hangar me shayi a ketaran titi dabara ta fado masa akan yasa ya yanke shawarar yaje ko Allah zesa adace ya dauke sa aiki koda aikatau ne.
_______________
Sun sha tafiya mai dan nisa a headquarters na yan Sanda kafin suka samu zama kan kujeru na afarman saukan baki , Commissioner dake zaune a kujerar da ke kallon nasu , fuskarsa babu yabo ba fallasa yake kallon kowannensu musamman Ridwan da ya dukar da kai tun shigowarsa dakin , sosai yake ji tsananin tashin hankali wacce ba'a sanya mata rana , sanye yake cikin farar shadda wacce yasha aiki farin zare gun kwararan tela , farar hularsa nake bi da kallo yanda ya zauna masa daram akansa ba karamin kyau gilashin dake sanya a idanunsa suka kara masa ba . Dakin zagaye suke da ma'aikatan yan sanda kowannensu goye da hannayensa ta gaba . Commissioner Bashir Muhammad ne ya yi gyaran murya hakan yasa kowa dago kai suna fuskantarsa , fesar da numfashi ya yi idanunsa na kan Ridwan da shidin ma shi yake kallo .
" Haba Ridwan Mai Nasara taya zaka ajiye aiki yau kusan shekara daya kenan , anyi anyi dakai kaki komawa akan aikinka , ai zamanka amatsayin shugaban KEDCO na Nigeria ba shine yake nunan cewar bazaka iya hada ayyukanka ba , tun da ka tafi ba'a samu mai kokarin ka ba har ila yau , Ridwan ka tuna fa abaya ba ka dau aiki dan ka ajiye ba ina da yakinin ba tsoro ne yasa ka ajiye aiki ba , akwai kwakwaran dalilai, haba Ridwan talakawa suna bukatarka wa'yanda aka tauye musu hakkinsu suna bukatarka , Ridwan naso ace kaine a kan kujerata , amma kuma zamanka a wannan kujerar baze baka damar yin aikin da ka saba ba , haba !! haba !! haba !! kayi tunani mana , dan zatin Ubangiji ka dawo aikinka ya Ridwan ya karashe zancen murya kasa kasa alamun takaici.
Ridwan jikinsa har tsuma yake kamar mazari , kasa jure zaman da yake ciki akan kujerar ne yasa ya mike ahanzarce tare da bin gefe sauran jama'a ze raba su ya fice cikin hanzarinsa , har yakai hannunsa kan handle din kofar ze bude yaji kakkausar muryan Commissioner Bashir yana fadin " Ridwan yanzu kana nufin ban isa dakai ba ?". Ya karshe zancen yana kallon keyarsa cike da takaicin taurin kan nasa.
Cak yatsaya be cire hannunsa akan handle kofar ba , be waigo ba , banda tsananin buguwar zuciya ba abinda yake tsananta a tattare dashi , kamar baze waigo ba yanda yake tsaye kikam , Commissioner da sauran ma'aikata da idanu suke kallonsa kowannensu . Ba zato ba tsammani suka ga ya waigo , jajayen idanunsa da suka kada jajir suke bi da kallo , daga inda yake tsayen ya kara gyara tsayuwarsa , cikin rawar murya me nuni da zallan bakin ciki ya ce " Afuwan mai girma Commissioner Bashir , ban bijire ba kuma na yaba da nagartan aikina da kuka yaba , kuma ina mai muku fatan samun wanda yafini ko da anan kusa nasan za'a samu fiye dani karku damu , na ajiye aiki bazan.....". Sauran kalaman dake shirin furtawa ne suka samu damar makalewa jin wani dattijon dan Sanda ya rike hannunsa , idanunsa sun kada jajir kamar gauta yana girgiza masa kai alamun kada ya karasa furucinsa yasan in har rantsuwa ta shigo ciki tabbas Ridwan yabar abunnan har abada babu waiwaye.
" Dan Allah Dana kayi hakuri, ko dan tsufana, karka cire hannu acikin aikinka , karka ce zaka raba hanya damu yakai yaron kirki ". Ya karshe zancen yana ƙoƙarin durkushewa kasa dan magiya .
Ganin haka ahanzarce Ridwan ya durkushe wajen tarosa hakan yasa idanunsu tsarkewa cikin na juna shida dattijon , be san sanda ya kaiwa Dattijon wawan runguma ba , domin dattijon yana daga cikin wanda yake jin dadin aiki dashi a headquarters.
" Baba zan dawo aiki nan da wata daya in sha Allah". Ya karashe tare da dagowa dukansu daga durkushen , kallonsa ya maida akan hall din yan dakin yanda aka zuba musu idanu ana kallonsu , Commissioner murmushi kwance akan fuskarsa yake fadin " Alhmdulillah ". A Kasar Zuciyarsa. A fili kuma kasa magana ya yi dan farin ciki .
Ridwan be tsaya jira abinda zasu fadi ba ya hanzarta barin office din jiki babu kwari.
Dattijon kuwa dawowa tsakiyar dakin yayi yana kayataccen murmushi ,bakinsa na rawa ya ce " Yallabai in sha Allah tunda Dsp Ridwan Mai nasara ya dawo aikinsa zancen ya kare kawai lokaci zamu jira , ahaka da suka ci gaba da tattauna tsare tsarensu.
Shi kuwa Ridwan a farfajiyar ma'aikatan yana gaisawa da yan sanda dake kai kawo , murmushi kwance kan fuskarsa yake gaisawa da wani abokin aikinsa da yazo wajensa suna tattauna yaushe rabo , juyawar da zeyi idanunsa ya sauka akan yan mata yan tallah masu dauke da robobin abinci , irinsu shinkafa da wake da miya da salad , nan da nan ransa ya ɓaci , suna hada idanu da Ridwan nan da nan hantar cikinsu ya kada sunsan ya hanasu kawo tallan abinci da kananun shekarunsu , kokarin yi musu magana yake yaji muryan Mansur yana fadin " kaga shiga Mota muje zan duba Mama batada lafiya sosai fa ". Ya karashe zancen cikin tsanani damuwa .
Ridwan hankalinsa ya dauke akan yan mata masu tallah , be tsaya bata lokaci ba ya shige motar inda suka ba motar wuta a 360 domin gani suke sam basa sauri ayanda akace Mama tana jin jiki.
Kasar Benin Cotonou
Alhaji Isah Sharifai zaune a farfajiyar Gidansa shi da Hajiya Basma wacce take sanye cikin kananun kaya riga da wando ba karamin kama jikinta yayi ba , shikuwa daga shi sai gajeren wandonsa da rigar shan iska mara hannu , babyn wasan yara ne a hannunsu yana jefa mata tana maida mashi , fuskokinsu dauke da murmushi mai sautin , cikin shagwaba fuska ta duniyanci ta ce " Alhaji ni de ko sai ka goyani". Yanda tayi furucin sosai ya basa dariya har kuncinsa ya lotsa.
Cikin yar tsokana yake fadin " kema kin bi wakar nan da ake yayi ko ? ai ba matsala bane dan masoyi ya goya abar kaunarsa kuma.....". Kasa karasa ragowar kalamansa ya yi ganin Yasmin ta fito kamar wata yar mabarata , ahanzarce dan sauri sauri take tafiya , sam bata gane inda take sanya kafafunta , tana karasowa kusan Alhaji da Matarsa ,kallo daya ta musu ta dauke kanta , ganin su ma ita din suke kallo da mamaki fuskokinsu sannan babu fara'a a fuskokinsu . Da idanu Alhaji ke bin ta da kallo ganin kodaddiyar doguwar rigar dake jikin ta , kara rufe baki ya yi ganin ta isa gun Baba Mai Gadi , muryanta na rawa ta ce " Baba Dan zatin Ubangiji ka taimaka ka bamu aron dubu daya , wallahi yau kwana hudu bamu samu labarin yaya Umar ba , kuma Wallahi Mamy olsa dinta ya tashi kwana biyu bamu ci ba , dan zatin Ubangiji kamar yanda Allah ya taimakeka ka taimaka mana wlh inna samu zan maida maka kudin ka , ko kuma in antina tazo za'a baka , wlh kakata ma yanzu haka tana cen kwance , karka ce min babu komi a hannunka dan Allah !! ". ta karshen zancen cikin kuka mai gunji.
Bala mai Gadi cikin rudewa ya ce " Subuhannallah muje daga ciki ina da dubu biyar zan baku har sai kun samu ". Yakai karshen zancen yana mai shiga dakinsa domin dauko kudin , da kuma robar faro faron kununsa a hannunsa.
Yana fitowa mika mata kudin ya yi kana tayi gaba cikin hanzarinta shima ya take mata baya.
Duk abinda ke faruwa akan idanun Alhaji Isah shida Basma , siririn tsaki yaja , tare da kai dubansa akan Basma cikin nuna kulawa ya ce " daman dan A'isha baya garin nan ?". Yayi mata tambaya cikin rawar murya.
Basma na dan nan ta bata fuska kamar wacce akayi wa albishir da ranar mutuwarta cikin jin haushinsa ta ce " wai kai Alhaji kai har yanzu baka san sharrin Yasmin ba , duk pretendin take , domin a tausaya mata take kuma wallahi karya take , ni dazun ma naga Umar din , amma kaji yar rainon matsiyaciyata tana fadin baya garin , wai kai Alhaji ina ruwanka da lamarinsu ne , kasan dai yaranta ne ka daina sanya mata idanu da yayanta , banda abunka ma , kabarsu acikin Gidan ka kar yau mutuwa ta riskeka suce suna da Gadon ka , gaskiya ka dau mataki ". Ta idasa zancen cikin ruwan bala'i. Alhaji sosai maganganunta sukayi tasiri a ilahirin jikinsa, kamar ankada shi da ganga zumbur ya mike , ya kama hanyar da ze sadashi da sashinsu Yasmin cikin zafin nama , ita kuwa Basma ganin ya fice sai da ta ranka guda kana tabi sahunsa tana tafiya tana karairaya har ta iso inda yake. Bankada kofar da karfi ya yi ya shigo dakin .
A kidime Yasmin da Baba mai Gadi suke kallon yanda yake huci kamar zakanya .
Mamy dake shan faroron kunun da me Gadi ya kawo mata da shanyayyun idanunta take kallonsa dan zata iya rantsewa rabonta data sanya shi a idanunta anfi shekaru uku .
Shi kuwa kallon su yake yana hura hanci kana ya kalli gefensa ganin Basma tana kusa dashi , ita ma kallon banza take binsu dashi tana kwabe baki .
Cikin zazzafan kalamai ya ce " Aishatu na baki daga nan zuwa gobe ku tattara ina ku , ku bar min gidana , sannan ina fatan in zaku tafi ku hada da Mamata ku tafi da ita dan kun shayar da ita guban halinku , wanda ni Isah bazan iya zama da ita ba , sannan...". Ba tare da ya karasa ba , Yasmin ta dakatar dashi ta hanyar fadin .
" wallahi tallahi , na rantsewa wanda numfashina yake hannunsa idan.........
Makauniyar Shari'a taku ce
Comment and sharhi pls