NAZNEEN.....

Page 12

by @maidambu41

*NAAZNEEN❤‍🔥<Twelve >*

EXQUISITELY BEAUTIFUL 


#Mai_Dambu


'Top-Notch

Season 3

بسم الله الرحمن الرحيم

Murmushi irin na manya Malam yayi, yana kallon Alhaji Adamu, sannan ya kalli Chioma da take kara k'ank'ame Yarta. Kallonshi tayi hawaye na zuba mata, ta zube akan gwiwarta, ko nauyin yar bata ji ba. "Me yasa ka tafi? Me yasa baka kuma waiwaya ta ba? Na cancanci haka daga gare ka? Ni fa marainiya ce? Ban san Uwata ba, mahaifin da nake jingine da shi ban san dadin shi ba, wancan kawai nasan dadinshi. Me yasa ka raba ni da shi? Ko tausayina baka ji ba, kasa ina tsaka da karatu aka kore ni, kasa kowa ya guje ni. Kasa duniya ta juya min baya, kasa duk inda na shiga, kowa farmaki yake kawo min. Kasan zaka tafi ka bar ni me yasa ka aure ni? Ban san ciwon kaina ba, just 16yrs yarinya karama da ni kayi abandoned dina ka tafi abinka."

    Bai damu da idanun kowa da yake kanshi ba, haka ya nufi inda take durkushe. "Wallahi ban gudu ba, ƙaddara ce ta same mu?" Tasss ta wanke shi da mari. Babu wanda yayi yunkurin dakatar da haka, "bukatarka ta biya, na haifa maka Y'a har office din hukumar bautar ƙasa naje na tura maka sako, ka bibiye ni?"

"Jiddah!" 

"Don't!" Ta daka mishi tsawa, "na zata Allahnku yana jin rokon kune, ashe yaudara ce kawai. Na zata idan nayi sallah nayi.azumi kace zai amsa min bukatata. Karya kake? Kasan yadda na sha wahala? Na Barka na bar addininka, dama Amanda na kawo, amma i decided na juya da ita, ba zan iya barinta a hannunka ka lalata min rayuwarta ba."

   Kamar karamin Yaro, kuka yake da dukkan zuciyarshi. Wannan itace ranar da yake gudun zuwanta, "Jiddah!" "Idan ka kuma kirana da useless name din nan, sai na kashe ka."

   "Tahir! Ka bata hakuri, ka gaya min me tace." Inji Malam,

 A hankali ya shiga bawa Malam labarin abin da ta ce. "Kace mata, Allah yana jin rokon bawansa koda bazata yi imani da shi ba, tayi hakuri a matsayin mahaifin shi na bata hakuri." Ya cire rawaninsa, ya fara kokarin sauka akan kujeran, tayi maza ta rike gwiwarshi. Tana girgiza kai, ta cewa Tahir da yake gaya mata abin da Malam ya faɗa. "A'a idan ka durkusa min, zan mutu ina danasanin kimarka da na tab'a." A hankali ta sauke Amanda da take nishi sama sama. Ya zubawa fuskarta idanu da babu mayafi. "Kunga ikon Allah ko? Yarinyar nan jinin, Babawuro ne kuga kamar da take kwance bisa fuskarta."

   Sannan ya kalli Alhaji Adamu wanda yake kuka kamar me. "Ko ban ce maka Allah zai saka mata ba, kai kanka kasan tabbas sakayyar Allah sai ta bika. Na sha tambayarka me yasa kake cewa mu yafe maka, sai kace babu kome da ace tun wannan lokacin ka gaya mana abin da yake faruwa da mun magance maka shi, sai da kome ya lalace." Kan shi a kasa hawaye na zuba miishi kamar karamin Yaro, sai girgiza kai yake yana hawaye.

   "Malam ban gane ba, kun saka min Yaro a gaba kai da arniya sai cin mutuncin shi kuke me ya faru?" Inji Innayo, wacce take cika tana batsewa bata so haka ya faru a gaban Umma ba, taya zata facing kishiyoyinta da zancen da bata fahimta ba.

    Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya fara basu labariin, bai kai ga karshe ba Innayo tayi tsalle ta dira zani a hannu, ta ce mishi. "Wallahi idan na yarda Allah ya tsine min albarka. Wannan ai munafunci ne, taya Adamu zai auri mace a bayan idanun mu. Har ya haihu da ita bamu sani ba. Karya ce ba yar Adamu ba ce ta kwaso shegiya ce don ta bata mishi suna." Ta fada tana haki.

"Indoh kin san dai nan babu me Miki karya, sannan ga Babawuro nan, tambaye shi da kunnenki."

    Ya nuna mata Alhaji Adamu, wanda ya kara diriricewa, ba zaka ce yana da mata da Yara ba. Domin ya rikice kamar Yaro karami. "Adamu wai yarinyar nan Yarka ce?" Kamar saukar aradu, haka yaji tambayar, a hankali ya d'ago kai, ilahirin jikinshi kerma yake kamar kasa ta bude ya nutse tsabar kunya, baki daya wurin kannen shi ne.

      Babu wanda yasan lokacin da ta iso wurinshi tana huci. "Gaya min Yarka ce?" D'ago kai yayi a karo na biyu, kafin ya san me take shiri ta kifa mishi mari, ta ce mishi. "Yarka ce?" Hawaye ne yake zuba miishi ya gyad'a mata kai. Bata san lokacin da ta rufe shi da duka ba. "Ni zaka kunya ta, da girmanka ka ajiye karuwa a waje har da yar dakar kuka. Wallahi ba zaka ja min abin kunya ba. Wallahi tun wuri ka san yadda zaka yi da su, ka kore su domin ba zaka ajiye min abin kunya ba."

 Yadda take magana da ihu, zai tabbatar al'amarin ya girgiza kwakwalarta da zuciyarta. Cikin wani irin heavy breathing ta fashe da wani irin kuka. Ta zauna a wurin tana kuka. "Ka cuce ni Adamu, duk Yarana a rasa wanda zai janyo min abin kunya sai kai da girman ka, tow wallahi na rantse da Allah da rayuwata da mutuwata take hannunshi, ba zan tab'a kaunar yarinyar nan ba, domin da ita gara na ga mala'ikan mutuwa. Ka je yadda ka sani kuka."

     "Keeeee! Aisha ina zaki kai rabon wannan yarinyar? Baiwar Allah da babu ruwanta, kada ki sake ki mishi baki, ƙaddara ce babu wanda ya tsammaci daga haka, kowa yasan yadda ƙaddara da rabo yake."

   Ita kan Chioma tsoron Innayo yasa ta kara rungume yarta. Mikewa Innayo tayi tana binsu da mugun kallo kafin ta ce mata. "Ban karbi yarki a matsayin jini na ba, don haka ta tattara ta su bar gidan nan kafin na bude idanuna."

     Duk da bata san me Innayo take fada ba, amma jikinta ya bata magana take gaya mata, don haka ta mike zata bar taron. Amanda ta farka, tana kallon Uwar murmushi tayi ta ce mata. "Nne ai na gaya miki ba zan bi ki ba." Rikota tayi, amma ta zame a jikinta ta koma gefen Alhaji Adamu, ta kwantar da kanta a jikinshi, "Papa ka gaya mata cewa, duk sakon da ta tura ya same ka, na ka ne bai same taba. Ka daina kuka. Zaka samu abin da kake ta son samu yau shugaban kasa zai saka maka hannu." Kuka yake amma haka ya rungume ta.

"Malam Aishatu Nazneen Y'ata ce." Ya faɗa yana kuka, ya cigaba da cewa. " Duk sakonta yana isowa ta hannun hukumar bautar ƙasa, kuma nima nawa nasan ya isa can Anambra, ban san ya aka yi haka ya faru ba."

   "Matar Babanta da Babanta suke rike duk abinda kake turo mata." Hannu ta kai xata d'ago yarta, "Nne kije ba zan bi ki ba."

 Ta faɗa tana kara shigewa jikin Babanta, baki daya gidan tausayin Alhaji Adamu da Chioma suka koma ji, domin itama kuka take ya bata yarta ta fasa bashi yar, ta fasa auren kowa zata zauna domin yarta. Ita kuwa Yarinya ta ce bata zuwa ko ina taga ubanta. Abin tausayi haka Obinna ya rikota tana kwacewa ta ce mishi. "ka kyale Ni ba zan bika ba, yarinya ta tana hannunsa."

 "Chioma kizo muje, ba zasu baki yarki ba sannan ki yi godiya tunda gashi ya amshe ta ."

"A'a bar ni na amshi Y'ata "

"Idan kina son Yarki, sai dai idan zaki zauna da ni." Wani uban tsalle tayi ta koma bayan Obinna, jikinta yana rawa. "God forbid na dawo rayuwarka a karo na biyu, bayan ina gani Mahaifiyarka, bata amshi Amanda ba." Ƙasa magana yayi, yana riko yarshi, domin kuwa ba zai iya bata hakuri ba, baki daya yan uwanshi sororo suka yi domin babu wanda ya fahimci yadda za a kawo karshen rikicin nan.

     Wasa wasa har aka yi sallah magariba da isha, ana magana daya, Chioma bata fasa rokon ya bata yarta ba amma ina yaki, tunda tace ba zata yi Muslunci ba, kuma ba zata zauna da shi ba, haka yasa aka barwa Malam al'amarin yafi kowa sanin abin da ya dace. Amma a daren aka kai Innayo asibiti, saboda yanda ta yanki jiki ta fadi, a can suka kwana.


           Washegari aka tashi da magana, Malam ya kira Chioma da Obinna, ya tambaye shi alaƙarsu, nan yake gaya mishi ai suna son juna, kuma kafin zuwa Alhaji Adamu suke soyayya, zuwan shi ya lalata soyayyarsu. Ya tambayi Chioma tana son Obinna kuwa? Ta gyada mishi kai, yaso ta bawa Adamu damar ya aureta a karo na biyu, amma haka ya roke ta da ta bar mishi Aishatu Nazneen. Ƙasa magana tayi tana kuka, don Allah ya gani tana tsoron kada su kashe mata yarta. "Ki yi hakuri ba zan tab'a barin wani abu ya sami Nazneen ba!" Inji Alhaji Adamu, wani harara ta watsa mishi, tana jiran Abinda Malam zai ce, wani abin mamaki rokonta Malam yayi tare da neman alfarmar ta bashi yar zai riketa.

   cikin sanyi murya tana share hawaye ta ce mishi. "Idan kai zaka rike ta, na amince amma ina tsoron a bashi ita." Tahir ya faɗawa Malam, Alhaji Adamu yana kallonta, yayi laifi amma hukuncin yayi mishi tsauri.. "Chioma nayi laifi amma, hukuncin yayi min tsauri,ki bari a bani yarinya ta zan bata farinciki."

   Murmushin takaici tayi tana faɗin. "Lokacin da ya dace ka riketa me yasa baka zo ba? Sai yanzu da na kawo ta zaka ishe ni da munafurcin kana son yarka, ba zan baka ita ba, ni dai kada a bashi Y'ata."

   Sunkuyar da kai yayi, ya rasa me zai ce mata har ga Allah akwai shiga hakki. Amma haka ya hakura domin yau da yaje asibiti Innayo koran kare tayi mishi, don dole ya dawo, sauran kannenshi kuwa dauke kai suka yi suna jin haushinsa.


   Dakyar Chioma ta amince ya dauke ta, amma don Allah idan za a cutar da ita. Ya dawo da ita wurin Malam don tasan shine kawai zai rike mata Yarinya, shima kuma abinda yasa ya amince da ya tafi da ita don yadda Innayo ta d'aga hankalinta akan yarinyar ne. A ranar suka bar Bauchi, bayan malam ya mata shatara na arziki, domin yace ba zai biya ta abin da tayi mishi na rikon yar ba, yasan ta sha wahala. Da wannan suka bar gidan, shima kuma a ranar yaso ya wuce amma yasan dole ya jira a sallami Innayo yaji me zata yanke akanshi da yarshi, wacce take kwance ciwon ya dawo sabo. Duk wahalar da ake sha, wurin danneta shi daya yaƙe riketa. Idan tana irin wannan abin wani lokaci hawaye yake da murmushi, har malam yake yawan tambayar shi meyasa yake murmushi akan ciwonta. 

"Malam ciwon gadarshi tai, haka nayi fama da mahaifiyarta."

  "Amma kuma ka tafi ka barta da wannan laluran?" Malam ya tambaye shi.

"Malam tsoron yadda zaku amsheta. Amma wallahi na rantse da Allah, ina sonta."

  "Allah ya sa haka ne mafi alkhairi!" Hawaye ne ya zubo mishi. Haka yanayin ya kasance har ranar Monday, aka sallami Innayo, tana shiga cikin gidan, ta hango NAZNEEN da take bakin famfo anyi sa'a yau an tashi jikin da sauki, tana shigowa ta hango yarinyar tana wasa da ruwan, dake ta tsani yarinyar shiga kitchen tayi ta dauko itacen marke ta nufi yarinyar ta shiga labta mata, amma Yarinyar ko gizau. D'ago kai tayi tana kallon Innayo, murmushi tayi tana faɗin. "Ai bani kike duka ba, ga wanda kike duka nan." Ta nuna mata gabanta wanda yake tare dukan, kallonshi tayi tana kyalkyale mishi dariya, "Guardians da zafi?" 

Fisge itacen aka yi, tare da watsar da Innayo da itacen. Ta kyalkyale da wani mugun dariya. Ihun Innayo yasa kowa ya fito, Sakamakon d'aga itaccen da aka yi za a buga mata bata ga kowa ba. "Kyaleta!" NAZNEEN ta faɗa tana tsalle da murna tana tafa hannunta. Cikin farincikin da sauri Alhaji Adamu ya rungume yar shi, yana kallon Innayo da Goma ta d'agota tana mata sannu. "Su goma uwar munafunci, murna kike a ranki." Inji Nazneen,

    ★★

Lagos......