Ya Za A Yi ?

78

by @bintaumarabbale

MURFI

Wato rayuwa duniya tana cike da 'kalubale da tarin jarabawa iri-iri. Duk wani tsanani da 'kunci Yana zuwa ne daga Allah. S'auki da sassauci rangwami da farinciki Yana zuwa daga Ubangiji. 

Allah da kansa ya fad'a cewa; Duk Wanda ya dand'ani d'acin ba'kinciki idan ya yi ha'kuri da sannu zai d'and'ani za'kin farinciki.

Bahago ya zama garkuwa ga zuri'ar Malam Zangina kowa Yana amfanuwa da dukiyarsa.

'kasar sa tana amfanuwa da shi. Domin aiki yake tu'kuru domin Kawo cigaban a k'asa bakid'aya 

Wannan jajurcewar ita ce sanadiyar samun nasarorinsa a rayuwa. Ya fara gwagwarmaya irin ta Siyasa inda ya ri'ke mukamai daban-daban a cikin shekarun da suka gabata ya yi hidimtawa Al'umma da dukiyarsa babu wanda bai sauke farali ba a cikin iyaye da 'yan-uwa.

Masoya da ma'kiya babu wanda bai shiga rigar arzikinsa ba. K'arshe Alhaji Lawan sai da ya taka da k'afarsa ya je ya nemi afuwarsa. Lokacin Sakina tana gida auran ya mutu da Yara uku, kuma mijin ya gudu. 

Bahago ya d'auki jari na kudi mai kauri ya ba shi Amma babu ajandar aure a tare dashi tauraruwasa Jamila kad'ai ta ishe shi rayuwar duniya.



BAYAN SHAKARU GOMA


Yara duk sun girma Hasanaa da Husaina sun zama 'yan mata dan har sun fara 'kirgar dangi tunda lokacin shakararsu goma Sha biyu a duniya Kaninsu mai sunan Kawu Sammani wato Nasir Yana da shakara Tara Muna kiransa da Daddy sai kuma tagwaye maza da suka biyo bayansa Hassan sunan Kawu Danjuma Hussain kuma sunan Babana da wannan sunayen ubansu ya yi musu hud'uba, Amma muna Kiransu da Hassan da Hussani a cikin gida a makaranta kuma suna amfani da sunayensu na yanka.


Haihuwarsu ta zo mini da tsammatsi domin su din ma da na gagara C's a kayi mini. Daddy ne kawai na iya Haifa da kaina.

Sai nake Jin tsoron haihuwa saboda wahalar laulayi da gurin haihuwa. Shi kuma mai gayyar Yana ta k'ulafucin 'ya mace kuma wai ba'kar fata yake so na haifa Irina. Tunda duk Yaransa kama da shi sukeyi. Ya dinga kishi Yana fad'in ai su Hassana gasu nan sun d'auko girman jikina har da kalar fata ta. rigima ce kawai irin tasa Amma yaran da Ubansu suke kama sai dai abinda ba za a rasa ba.

Yau Lahadi Yana gida tun da ya dawo daga sallar asubahi ya uzzura mini wai lallai sai na yi 'kokari na samar da mai kama da ni.

Na rasa yanda zan yi na fahimtar da shi lamarin Ubangiji ne. Amma ya turje ya kwanta a gado wai ni zan zama shi.

Shi kuma ya zama ni, saboda ya ji likitoci suna fad'a cewa Duk Wanda ya fi 'kokari gurin auratayya idan an samu rabo to yaron da za a haifa zai yi kama da shi.

Dariya lamarin ya dinga ba ni. Da dai naga abin Yana nema ya zama rigima sai na fara gwadawa shi kuma ya yi gim! Na gaji sosai! Kawai na fashe da kuka na fad'i Saman gadon ina nishi nake fadin." Ba zan iya ba na gaji kawai ka yi addu'a Allah ya bamu masu albarka."

Be ce mini komai ba ya janyo ni ya rungume Yana ta sakin ajiyar zuciya.


Ko da na samu ciki sai na tsananta da addu'a Ubangiji Allah ya ba ni 'ya mace mai kama da ni kamar yanda yake so. Mun yi scanning sau hudu duk mace. To Amma bamu san wace kala ba ce fara ko ba'ka!

Muna ta addu'a har lokacin haihuwa ya yi. Cikin ikon Allah na haihu a gida abinda Bai ta'ba faruwa ba, nakud'a mara tsanani. 

 Shi da Baba Suwaiba Mai aikina suna ta hidimar gyara gurin.


Bahago kanwa ta kar tsami kwarnafi ya kwanta baby kamar na yi ka ki na tofar an ce wai ana gane farin mutum ta kunne to ita wannan babyn ko'ina na jikinta 'baki ne, hatta da kunnanta abinda yake da haske 'kwayar idonta da faratan yatsunta.


Aikuwa hidima ya yi irin wacce bai ta'ba yin irinta ba.

Ya yi mata Hud'uba da Hafsatu sunan Ummana. Ashe 'boye-'boyen da yake kenan bai fad'a mini ba sai ranar suna.

Na yi farinciki sosai kuma na tabbatar da cewa; 'kaunar da yake mini itace silar yi mini Kara ya sawa 'yarsa sunan Ummana.

Sai kawai muke kiranta da Fadila. Kuma kiri-kiri baya jin kunyar fifita ta akan sauran yaran. ko da wasa ban yi tsammanin zai daina yayin su Hassana ba, sai ga shi samun Fadila gwamnatin su Hassana ta rushe duk sun zama 'yan fadar Fadila. Ni ma idan ina son wani abu sai na shiga rigar arzikinta.


Rayuwa kenan.

Yau za'ki gobe mad'aci!

Ubangiji Allah ka sa mun cinye jarrabawarka



Na baku kyautar wannan chapter ku yi mini addu'a.

Zan fara sa muku Wani littafin nawa ina fatan zaku bibiye shi. Kamar yanda ku ka bi wannan. NA GODE SOSAI


*ALHAMDULLAHI*

Nan na kawo k'arshen wannan littafi Ina rokon Ubangiji Allah Ya yafe mini zunubi. Ya ba ni ikon rubuta daidai abinda zai amfani al'umma.

*BINTA UMAR ABBALE*