#19
FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
_Page 19_
Nishaɗinta kawai takeyi, to a inama sukayi maganar da Umman? Ya tambayi kansa ganin bamai basa amsa yasa ya kaɗa kansa tareda nufar hanyar fita, ganin fitarsa suka maida hankalinsu kan agogon bangon dake manne a palon, kowa miƙewa yayi da niyar yin Sallah, har cikin ɗakinta ta jasu don yin alwala, su Sabuwa a nan ma lalacewa akayi wajan bawa ido haƙƙinsa dan wadda take jira ta fito daga toilet har ta fito bata saniba tana kalle kalle a kaikaice saida ta zungureta sannan ta dawo hayyacinta tareda miƙewa ta shiga toilet inda Dukansu ba wanda bai zuba ƙauyanci ba suna idarda Sallah Kubra ta gabatar musu da lafiyauyen lunch inda ta haɗa ta kai musu palo sannan ta shiryawa Mijin 'yar uwar nata nasa daban ta ajiye a kitchen cabinet.
"Sis naki keda oga na kitchen nayi na Allah kuma" ta faɗawa Binazir dake shirin shiga toilet, da har zata shareta sai kuma ta juyo tareda mata murmushi da faɗin "Nagode sis sannu da hidima" sannan ta shige toilet in. "Nidai kiyi sauri ki fito na gasa jikina kona samu iska ta ratsani" bata jima a toilet inba ta fito shiryawa tayi cikin simple dress inta data saba sawa kubra data fito daga toilet ne ta wurga mata harara da faɗin "Sis bakya gudun baki, Please ki sake kayan jikinki kisa ɗaya daga cikin wanda Mummy ta ɗinka miki na biki" kallon Kubra tayi rai a ɗan ɓace, sai kuma ta fitarda numfashi tareda nufar inda sababbin kayanta suke wani cotton lace blue black mai adon yellow da pich ta ɗakko wanda akaiwa ɗinkin riga da siket, baya ta juyawa Kubra tareda canza kayan jikinta Tasbihi ga Ubangiji kawai Kubra keyi sanda taga kwantattar farar fatar 'yar uwarta cikin wannan haɗaɗɗan leshin ita kam murmushi tayi tareda fesa turare a jikinta ta fito palon.
Kunyace ta kusa kamata ganin yadda aketa zuzuta kyanta ba uwa Sabuwa a haka ya shigo palon ya samesu daidai sanda Sabuwa ke faɗin "irin wannan kwalliya haka ai saiki zautamin ɗan marayan ƙani" kalamanda sukayi masa maraba kenan wanda yaja hankalinsa ya kai idanunsa saitin inda take, idanunsa ya lumshe ya buɗesu lokaci guda a kanta tareda sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, ita dai murmushin kunya kawai takeyi, a jikinta taji ana kallonta hakan yasa ta ɗaga idanunta takai bakin ƙofa inda zuciyarta ke gaya mata a nan mamallakin idanunda ke kanta yake karaf idanunta suka sauka cikin nasa hakan yasa ta rage fara'ar fuskarta tareda watsa masa wata harara ta ɗauke idanunta.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda shafa sumar kansa sannan ya ƙarasa shigowa palon bakinsa ɗauke da sallama yadda kowa zaiji, kuma kowa yajin haka yasa suka amsa masa sallamar tareda ƙara gaisheshi haɗe da yimasa sannu da dawowa, a tsaitsaye ya amsa sannan ya nufi ɗakinsa.
tana tsaye harya juya sai zabga yaƙe takeyi sanda ake gaishesa "wai Walida da Naja bazasu fito suci abinci bane najisu shiru?" ta faɗa tareda sauke idanunta kan Aunt Farida da taketa faman zabga mata harara "ki fara zuwa ki sallami mijinki da yake wajibinki kafin ki tsaya tambayar wa'yanda tun miya nakan wuta suka ɗibi nasu" Kubra ta faɗa sanda take shigowa palon. Shiru tayi tana kallon Kubra rai ɓace "Wai bazaki wuceba?" Aunty farida ta faɗa cikin takaici "ku bita a sannu mana kumadai kunsan yanzu sai a hankula kuma gode Allah tanada kunya wallahi ba kamar 'yan matan zamaninnan masu yinwar abinba" Sabuwa dake fizgar naman kaza ta faɗa. Murmushin yaƙe su duka sukayi dan zancen ya sasu kunya banda Binazir da bata fahimci kan maganar ba, juyawa tayi tabar wajan sakamakon wani kallo da Aunty faridan ta watsa mata, kitchen ta nufa kai tsaye dan ɗakko tray inda Kubra tace ta shirya musu, danta baƙanta masa ko sallama batayi ba ta danna kanta cikin ɗakin nasa a lokacin yana zaune hannunsa riƙeda abokiyar tasa sai faman latsata yakeyi da sauri kamar mai aika saƙon gaggawa.
Ɗago kansa yayi jin alamun shigowar mutum, idanunsu ne suka haɗu cikin na juna, juya idanunta tayi da faɗin
"Ba injini ba sani akayi dole na kawo karma kayi zaton muguntarda kaimin ɗazu ta saka na fara jin tsoronka" ta faɗa sanda take dire tray in a ƙasa, bata kuma tsaya wani dogon nazari ba ta ɗauki plate guda ɗaya tareda ɗiban abinci Saida ta ɗibi yadda yayi mata sannan ta miƙe ta nufi gaban mirror na ɗakin tareda zama kan stool ta bashi baya ta fara bawa cikinta haƙƙinsa dan bata wasa da cikinta.
Da ido yake binta tun shigowarta har zamannata a gaban mirror, wani murmushi ya saki tareda miƙewa ya nufi inda trayn abincin yake, 🥄 ya ɗakko sannan ya nufo mirror.
Bata zata ba,ba kuma tayi tsammani ba, kawai sai gani tayi ya saka mata 🥄 cikin abinci, tsayawa tayi tana kallonsa cikin mamaki ko inda take bai kallaba ya fara ɗibar abincin yana kaiwa bakinsa daga tsaye, saida yayi empty plate sannan ya dawo dubansa gareta da faɗin "thanks secret hidder" da sauri ta miƙe ta ɗauki lemonda kekan tray ta tsiyaya tasha sakamakon ƙwarrewar da tayi, saida ta shanye sannan ta cire kofin a bakinta haɗida ɗora idanunta a kansa da faɗin "ai saika faɗa min kai kwancetaccen yunwane da saina zuba harda kai bawai daga sa abinci kazo ka cinyemin ba kaiko kunya bakaji" ta faɗa cikin takaici. Wani ƙayataccen murmushi ya saki tareda sosa gashin girarsa da ɗanyatsa tareda nitsar da idanunsa cikin nata idanun da yake masa kallon farauta, da faɗin "tsakanin nidake aga kwantaccen yunwa dan da bakinki kincemin abinci nane akace ki kawomin and kince ko kunya banaji ke bikiji kunyar zama a ɗakina kinacin abinciba?" ya tambaya da ɗaga mata gira ɗaya, wani ƙullutun haushine ya daki zuciyarta da faɗin "komai nayi na isa nayin kuma ba wanda ya isa ya hanani and isata har tasa na samu 'yar aiki a ɓagas ba tareda asarar dukiya ba dan haka ka shirya yau da sabuwar house girl zamu kwana" tana gama faɗa tayi saurin juyawa tabar ɗakin dan taga alamar maganganunta sun shigesa kar kwantacciyar haukansa ko tashancin sa ya motsa ya sauke mata a kanta.
Wani ajiyar zuciya ya sauke sanda tabar ɗakin ƙwafa yayi tareda ɗaukar wayarsa dan kiran Umma amma abin takaici layin yaƙi tafiya ƙwafa ya ƙarayi tareda hararar trayn abincin yanajin yunwa dan abincinda yaci ba wani mai yawa bane amma haushin wadda ta kawo abincin ya shafi abincin ƙwafa ya ƙarayi tareda zama bakin gadon yana sauke numfashi.
Saida ta daidaita kanta sannan ta ƙarasa cikin palon alokacin har sun gama ci sun gyara wajan su Aunty Sabuwa na shirin tafiya waje ta samu taba binsu da ido har aka kira Naja dan tafiya, sai alokacin ta miƙe ta nufi ɗakinta wasu manyan ledoji ta ɗakko da kuɗi sannan ta nufi kitchen, store ta shiga ta cicciko ledojinnan da uban Gara sai kace za akai wani garin, leda biyu ta miƙawa su Sabuwa biyu kuma ta bawa Naja haɗida kuɗin hannunta da faɗin "ledar ki bawa Umma sannan kiyi transport da kuɗin kada ki jima " da hannu biyu Naja ta karɓa haɗida godiya su Aunty farida ne suma suka fito cikin Shirin tafiya duk saitaji zuciyarta ba daɗi, tabbas ta yadda mutum rahamane "wai rowar angon naki kike manane da bazaki kirasa muyi sallama ba? Kubra ta tambaya cikin tsokana, kallon Aunty farida tayi, ilai kuwa idanunta a kanta, hakan yasa ta nufi hanyar ɗakinsa jiki a mace.
Ciki ciki tayi sallama da faɗin "ana kiranka zasu tafi" bata jira cewarsa ba ta juya palon ta koma ta shaida musu gashinan fitowa sannan ta koma kan kujera jiki a mace tana kallon yadda suke shirin tafiya.
Ƙeyarsa ya shafa da hannunsa tareda jujjuya gefe da gefe kansa sannan ya miƙe ya fita .
A palon ya samesu su duka, kusada su Walida dake faɗama Naja idan ta koma zata dinga kiranta da layin mamansu ta wayar Aunty Binazir, "hmmm" kawai ya faɗa a fili tareda samun hannun kujera ya zauna ya maida hankalinsa kan manyan, godiya yayi musu sosai na ziyarar da suka kawo musu sannan ya kalli walida tareda yafitota ƙarasawa tayi wajansa tareda rissinawa, kuɗi ya ɗakko a aljihunsa ya miƙamata da fari tasoyin musu amma ganin yadda ya haɗe fuska yasa ta waiga inda Binazir take, bakinta ta taɓe haɗida ɗauke idanunta a kansu, hakan yasa Walida karɓa da hannu biyu tana godiya ƙara haɗe fuska yayi hakan yasa ta miƙe tareda barin wajan ta nufi su Aunty Farida, suma godiya sukayi masa sannan suka fita tareda yi musu fatan alkairi ko kaɗan basu kalli inda Binazir take ba dan sunsan zamanta a kujerar jira kawai takeyi wani ya taɓota ta samu damar yiwa mutane taɓara. Numfashi ta sauke a hankali sanda suka bar gidan banda wannan saƙagon na tsaye da ba abinda zai hanata sakin kuka. bayan sun fita ne ya miƙe tareda miƙawa su Sabuwa da keyiwa Binazir sallama da godiya kuɗi da faɗin "maybe ma na rigaku isa dan gidan zani yanzu" ɗan ɗago kanta tayi ta kallesa, sai kuma ta maida kan nata gefe kamar wadda ta tuna wani abu tayi saurin dawo dakan nata wajansu Naja dake shirin fita daga palon dukkan wata murya da Allah yayi mata ta buɗe da faɗin "ki fayi sauri Naja'atu kar kikai yamma" "insha Allah Aunty da wuri zan dawo" Naja ta amsa mata sanda take barin palon.
Ajiyar zuciya ta sauke tareda lumshe idanunta. Tsayawa yayi yana kallonta mamakin ƙarfin halinta yakeyi, to dole yace ƙarfin hali mana tayaya a matsayinsa na maigida zata zartar da hukunci bada saninsa ba kuma wai akan ƙanwarsa? Ƙwafa yayi tareda nufar ƙofar fita shima. Har ya taɓa handle sai kuma ya dakata tareda juyowa yana kallonta, har lokacin idanunta a lumshe suke numfashi ya fitar da faɗin "zanje gidanmu ki kula da gidan" ya tsaya danjin ko zatace wani abin, gani yayi ta buɗe idanunta sannan ta miƙa tareda taɓe baki tabar wajan cikin takun isa da gayya. Ji yayi zuciyarsa ta sosu da yadda tayi masan, cikin zafin nama yayi taku huɗu ƙwaƙwƙwara tareda shan gabanta, ɗan ja da baya tayi kaɗan tareda yamutsa fuskarta amma zuciyarta sai bugawa takeyi dan sosai ta tsorata da yanayin nasa
"Allah this should be the first and last time dazan miki magana kiyimin shiru" "if not?" ta dake zuciyarta ta tambaya dan taga kamar ya gane alamun tana tsoronsa ne shiyasa ya fara zaƙewa da yawa.
"If not?" ya faɗi tambayar da tayi masa cikin mamaki "kinsan ko Ni wane da kikemin abinda kikaga dama har haka? "Likewise" ta faɗa a gadarance tareda kauda kai tana jijjige jijjige.
Runtse idanunsa yayi tareda saukesu cikin nata she did not deserve the other side of him in banda haka da tuni an fara neman masu ɗaurin karaya. Ajiyar zuciya ya sauke still idanunsa a kanta "zanje gida yanzu zan dawo and idan an buga gidannan karki buɗe cos nasan relatives inki sun gama zuwa a yau hakama nawa" ya faɗa cikin Muryar bada umarnin bai kuma jira cewarta ba ya bar palon a ƙasaice.
Wani ajiyar zuciya ta sauke haɗida zama kan hannun kujerarda ke kusa da ita tareda dafe ƙirjinta, bata taɓa tsammanin iya kalaman da zasu fito daga bakinsa bane, a tunaninta haukanne ya motsa haryya fara tunanin tsara yadda zatayi na yadda za'a raba auran ba tareda an samu matsala ba dan ta rantse duk sanda yayi gigin taɓa ta to daga ranar komai yazo ƙarshe dan daganan ta gama auran ta kuma shirya masa har psychiatric inda taso Dady ya taimaka ya kaisa sai ya jesa muddin yayi wannan gigin.
Kamar yadda ya faɗa kuwa ya riga su Naja isa gidan Umma da sallama ya isa cikin gidan Umma data fito tsakar gida ta ganshi, cikin ɗoki da murna take masa sannu da zuwa, tareda amsar gaisuwarda yakeyi mata, suna gama gaisawa ya miƙe da faɗin "Umma magana zamuyi fa na kira layinki bata shiga" bai jira cewarta ba ya nufi ɗakinsa na soro.
Mamaki ne ya kama Umma na muhimmanciyar maganar da zasuyi da har zai bar gidansa ya tawo a irin wannan rana.
A zaune ta sameshi yana dannedanne a waya , itama waje ta samu ta zauna da faɗin "ina jinka Babban mutum" "wai ke kika amince Naja ta zauna a wajanmu?" ya tambaya idanunsa akan na Umman. "Wai inji wa?" itama ta mayar masa da tambayar nata idanun a kansa, rusunar da ƙwayar idanunsa yayi da faɗin "Ni Umma dan Allah kiyi haƙuri idan kinsan da maganar ki faɗamin" "ƙwarai nasan da maganar kuma da amincewata dan ba abinda yarinyar nan zata roƙeni nayi mata naƙiyi saidai idan yafi ƙarfina, kuma na riga na amsa mata dan haka banga wanda ya isa yasa na fasaba dan bazan zubarda ƙimata wajan sirikar da ke mutuntani ba" ta faɗa idanunta fes akan na Samir, Numfashi ya furzar da faɗin "nifa bance wani abinba dama tambaya kawai nakeyi" ya faɗa cikin sallamawa dan ya fahimci Umma taɗau lamarin da girma .
"Ay nima bance wani abinba yoo Ni koda bata tambaya ba yadda ta shaidamin tana buƙatar mataimaki dan tanada lalura ai ko banda 'ya mace sai na nemomata ko wace ballantana inada 'yarda zata taimaka mata" Umman ta faɗa tareda miƙewa tabar ɗakin.
maimaita kalmar "Lalura" a zuciyarsa kawai yakeyi, watakam ta yaudari Umman da kiran rashin iya girki da aikin gida da suna Lalura, kansa kawai ya girgiza da faɗin "hmmm" a fili, koda yake gaskiya ta faɗa babbar lalura na damunta wadda yaso magance mata ita amma shine ta nemo Naja, ƙwafa yayi tareda miƙewa.
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*