5
by @asmybaliyu
Zaune yake cikin katafaren room ɗin da ya sauka na baki, ya dafe kansa da hannayensa duka biyu zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi da ƙarfi. Bai taɓa tunanin zai so Rahama Abubakar Galadanci farat ɗaya haka ba, sannan kuma ba shi da wani sha'awar auren zumunci ko kaɗan tun ta sowarsa. Abu ɗaya yasani, yasan tun tana ƙanƙanuwarta ya tsani halinta wato sangarta, kuma babban abunda yasa baya shiri da ita kenan. Ko ada can baya idan taje gidansu hutu Abuja inhar ya dawo school hutu baya doguwar magana da ita, ba kuma ya sakar mata fuska, duk akan karta rainasa, dan yasan yarinyyar nada tsaurin ido sosai bai taɓa tunanin zuciyarsa zata hango masa soyayyar Rahama Galadanci nan kusa bare har yakai ga san aurenta.
A can baya ƙanwarsa wato Deejah Galadanci na yawan yi masa hirar Rahama kasancewar kusan shekarun su ɗaya da Rahama Abubakar Galadanci, haka kuma kusan tare a suka taso da ita. Sosai suke kaunar junan su. Yaja numfashi a wahale yana tunanin yanzu ta wace hanya zai nunawa Rahama Abubakar Galadanci kulawa har ta fara sonsa? Dan tun ɗazu da ya baro ɗakin ta tunanin da kwakwalwarsa keyi kenan. Idan ya tuna kuma Rahama tace bata sonsa bata kaunarsa ba kuma zata aureshi ba, sai yaji gabansa ya faɗi. Hirar da suka yi a parlor ɗazu ta shiga dawo masa, lokaci ɗaya Ra'is ya faɗo masa arai.
Ƙarfe biyar ya shigo gidan lokacin mu'allem ɗinsu ya tafi wanda ke koyar dasu karatun addini a cikin gidan. Ummi kaɗai ya samu a parlorn ya ɗan russuna da respect ya gaisheta ta amsa cike da fara'a tana tambayarsa yana buƙatar wani abu ne? Ya ɗan shafa kai karo na farko da yaji wani irin nauyin Ummi ya saukar masa wanda bai taɓa jin hakan ba. Ya shiga tunanin kodan yanzu yana san gudan jininta ne? Tabbas dan tana mahaifiyar Rahama Galadanci ne yake jin wani irin nauyinta a ransa. ''Ummi Ra'is fa.?" Tace dashi, "Suna can tareda Hajja, kasan idan Hajja na gidan nan toh duk suna part dinta, duk da yanzu suka shigo gidan ko nan basu zo ba suna can." Bece komai ba ya fice. Part ɗin Hajja ya nufa wanda itama tana da part a cikin gidan saboda idan tazo nan take sauka. Ƙaton parlor ne sai kuma ɗakuna guda biyu da kuma ƙaramin Kitchen acikin parlorn duk da bawai girkin takeyi ba, sai dai wata rana idan bata son na masu aikin takan sarrafa abincin da takeso irin nasu na gargajiya. Suna zaune cikin parlorn Ra'is kadai ne keyiwa Hajja hira, Rahama tana ɗaya daga cikin bedroom ɗin Hajja da wayar Hajjan a hannunta tana ta ƙoƙarin gwada ƙiran Imran Matawalle amman still number baya zuwa. Farooq ya zauna yana faɗin. "Ra'is Hajja kake tayawa hira da fara'a haka?" Ra'is ya juya idanuwa yana faɗin. "Ehhh Yah Farooq." Ya kalli Hajjan yana faɗin. "Zamu fita da Ra'is zamu zaga gari me zan siwo maki Hajjaju?" Hajja tayi murmushi tana faɗin. "Kayan marmari zaka zo min dasu da kuma tsire mai zafi." Wani irin murmushi yake yiwa Hajja murmushin da ya tsayawa Hajja arai ta kuma rasa kona menene.
Mamakin Farooq take. Meya canzashi farat ɗaya haka? da sauri Ra'is ya miƙe tsaye yana faɗin. "Yaya Farook na kira Yayah Rahama mu fita tare?" Da sauri Farooq ya girgiza masa kai yana faɗin. "No need! kyaleta Kawai Ra'is." Da haka suka yiwa Hajjah sallama ta bisu da addu'ar Allah ya saukesu lafiya. Tun a mota Farooq Galadanci cikin hikima yake jan Ra'is da zancen Rahama. Shi kuma amsa kawai Ra'is ke basa yana front seat zaune yana game da wayar Farooq ɗin. A wani babban mall yai parking yace suka shiga Farooq yace ya dauki duk abunda yakeso. Washe baki Ra'is yayi ya shiga kwasar kayan daɗi tun daga kan sweet, chocolate, biscuits masu tsadar gaske da sauran abubuwan kwalama. Sai da ya gama ɗaukar nashi Faroonk yace ya ɗaukarwa Rahama itama. Ai kuwa babu musu Ra'is ya shiga zabarwa Rahama favourite ɗinta da ya sani. Sai kusan magrib suka koma gida cike da tsaraba duk ta dalilin Yaya Farook. Suna dawowa parking motar kurum yai ya fito tare da rufe motar. Alwallah yai acikin compound ɗin gidan. Shima Ra'is akan dinning area yabar ledojin yaje yai alwala shima. Tare suka nufi masallaci shida Farook Galadanci wanda yake a cikin layin.
Suna dawowa kai tsaye Ra'is Kitchen ya nufa wajen Ummi dake tsaye tana haɗa dinner itada mai aikinsu. Baiga Rahama a Kitchen ɗin ba, sai kawai ya nunawa Ummi kayan da Farooq ɗin ya siya masa shida Rahamar. Da fara'a Ummi ta karba tana ganin abubuwan tace. "Toh Allah yayi albarka, idan Abba ya shigo sai ka nuna masa shima ya gani." Ra'is ya ɗaga kai ya fice daga Kitchen ɗin, kai tsaye dakin Rahama ya nufa, samunta yayi akan sallaya tana bitar haddarta, dan yau sauran ƙiris tasha duka a wajen mu'aleem, sabida rashin iya hardar da ya karɓa. Shi yasa tana idar da magrib bata ɗaga kan sallayar ba take yin bita. Da kallo ta riƙa bin Ra'is wanda ya zauna kan soofa yana washe mata baki, a hankali ya shiga buɗa mata ledojin da ya Farooq ya siya masu chocolate. lokaci ɗaya Rahma ta haɗe rai ta ɗauke kai tana faɗin. "Tashi ka fita ni bana so." Da mamaki Ra'is ke faɗin. "Yaya Rahama meyasa?" Ta zare masa ido tana faɗin. "Ka tashi ka fita da kayan nan Ra'is kafin ranka ya ɓaci." Ta faɗa tana daka masa tsawa tamkar shi yayi mata laifin. Ra'is ya kwashi ledojin shaye da toka yake faɗin. "Kinyiwa kanki ai." Ya faɗa yana nufar ƙofa. Wani kallo ta riƙa yi masa mai cike da haushi, caraf kuma suka haɗa ido da Farook Galadanci, tayi saurin ɗauke kanta, zuciyarta na zafi tayi bala'in haɗe rai lokaci ɗaya.
Farooq ya kalli Ra'is dake shirin fita yana cewa. "Ajiye mata ta ta ledar Ra'is." Babu musu kuwa Ra'is ya dawo ya aje mata ya juya yabar ɗakin. Tsaye yayi tare da jingina bayansa jikin ƙofar, hannayensa a zube cikin aljihun wandonsa. Wani irin ni'imataccen ƙamshin turarensa ne ya cika mata hanci wanda yasa dakyar take iya catching breath ɗinta. Wannan karon zama yayi da ɗuwawunsa akan marbles ya lankwashe ƙafafunsa yana kallon cikin idanun Rahama Abubakar Galadanci, wacce zaɓar ɓacin rai yasa ta yi masa kallan cikin ido. Zuciyarsa na bugawa da wani irin azababbiyar soyayyarta, sai faman cije lips yakeyi.
Runtse ido tayi hawaye suka fara rolling akan face ɗinta, matsawa tayi can ƙarshe tana jin kusancin su yana hanata yin numfashi dai dai saboda bayyanar Farooq Galadanci a wajen, yaja numfashi tare da shafar lashes ɗin dake kwance a face nasa.
"Duk saboda nine ake wannan zubar hawayen Rahama?'' Yayi maganar da rashin amo acikin muryarsa. Ƙin buɗe ido tayi haka kuma bata basa amsa ba, sai duk yaji babu daɗi ganinta cikin wannan yanayin. Ya tausasa murya yana faɗin. "Bance dole sai kin soni ba Rahama, ni kaina nasan kinyi min ƙanƙanta a soyayya yanzu, kinga karatu kike so kiyi yanzu, haka kema baki shirya yin aure yanzu ba right?'' Da sauri ta buɗe ido tana kallonsa da wani irin yanayi dan ya taɓo mata inda yake mata kyaikyayi. Cikin rawar murya take faɗin. "Abba yana so yayi min aure, kuma ni bana son yin aure karatu nake so nayi." Farooq ya ɗan saki murmushi yana shafa sumar kansa da take cikin wani murɗaɗen style ganin plan ɗinsa zai fara aiki akanta. Ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin. "Toh share hawayenki ni zanyi magana da Abba a bari har sai kin gama jami'a keda yin aure, amman da sharaɗi. Da sauri ta kallesa cikin rawar murya take faɗin. "Sharaɗin me Yaya Farooq?" Farooq Galadanci ya ɗan saki murmushi cikin zuciyarsa, kallonta yai yace. "Zakiyi ƙawance dani, ma'ana na zama best friend ɗinki." Rahama ta girgiza kai da sauri tana faɗin. "No Yaya Farooq, Imran Matawalle shine best friend ɗina, canza wani abun banda wannan. "Kallonta yake da dukkan idanunsa yana karantar yanayinta yace. "Kenan shi ba saurayinki bane? Ko kin manta kince shine a zuciyarki?" Rahma ta girgiza kai tana faɗin. "Ya Farooq yace dani shi ba saurayina bane shi best friend ɗinane, yace ban san ma'anar soyayyah ba, haka yake ɗaukata bayan kuma ni nasan ina sonshi." Ta faɗa tana wani haɗe rai. "Oh my God, kenan Rahama Imran Matawalle bai taɓa cewa yana sonki ba right?" Wannan karon zuciyar Farooke Galadanci bugawa takeyi saboda fargaba, addu'a kawai yakeyi Allah yasa tace bai faɗi yana sonta ba. Rahama ta turo baki tana ta ware masa manyyan idanunta tana faɗin . "Eh bai faɗa min ba, yace min sai zuwa nan gaba, wai yanzu kwakwalwata bata isa ɗaukar waɗannan abubuwan masu girma ba, kuma ni nasan soyayya tunda ina kallan yadda akeyi acikin indian series, amman suma duk ya hanani kalla wallahi, ban san meke damun Imran Matawalle ba wani lokacin." Nannauyar ajiyar zuciya Farooq ya sauke yana cewa.
"Ke kuma kika daina kallon saboda shi?" Rahama ta ɗage kafaɗa tana faɗin. "Toh Yaya Farooq yana iya? Kai bakasan rigimar Imran Matawalle bane " Girgiza kai yai ya haɗe rai yana faɗin. "Toh naji idan har bazamu zama friend's dake ba ni kuma bazan yiwa Abba maganar yai hakuri kici gaba da karatun ba, kinga sai ya aura maki duk wanda yaga dama, ni dama na haƙura dake tunda kin faɗa min da bakin ki cewa bakya so na, so duk wanda Abba yaga dama sai ya baiwa aurenki Rahama." Hankali a tashe take faɗin. "Dan Allah ka rufamin asiri Yaya Farooq, naji na amince zamu zama friend's ɗin ni da kai." Ta faɗa tana miƙa masa hannun damarta da wani irin murmushi acikin kyakkyawar fuskarta wanda ya kusan zautar da zuciyar Farooq Galadanci.
Yabi farar fatar hannunta da take miƙa masa da kallo, a hankali ya miƙa masa nata sukai holding. Farooq yaji wani sassanyan shock, besan lokacin da ya sake matse hannun nata ba. Rahama ta shiga zarewa yai saurin kallonta idanunsa na wani canza launi yace. "Promise me." Kawar da fuska tayi, so take kawai ya cika mata hannunta saboda wani zafi da taji ranta yana yi dan sun haɗa hannun. Tana ƙaƙalo murmushi tace. "I promise you Yaya Farooq bazan baka kunya ba." Kasa sakar mata hannun yai saboda wani irin feeling da yaji yana ratsa ilaihirin jikinsa. Muryarta ce ta katse mai shauƙin da ya fara lulawa ciki, yaji tana cewa. "Yaya Farooq my hand." Kunya ta kamashi ya saketa yana janyo ledar da sukai mata shopping mai dauke da sunan mall din ajikinta yana faɗin. "Kiyi amfani dasu for our new friendship." Ta shiga gyaɗa masa kai alamun zatayi ta kara da cewa. "Thank you so much Yaya Farooq." Dogon hanci yaja ya miƙe tsaye idanunsa akanta yace. "Ki fito dinner anjima." Rahama tace, "Toh." Farooq ya fice tabi bayansa da harara tana ture ledar daga gabanta. Kwanciya tai akan sallayar tana rintsa ido a fili take cewa "Naji kirjina yana zafi, nasan rashin ganinka ne Imran, shin dagaske Matawalle ya rabamu? Ina ya kaika Imran? Gashi nan za'ai min auren dole ina zansa zuciyata?" Hawaye suka shiga zirarowa daga cikin idanunta, a hankali taji ansa hannu ana share mata fuskarta, a zabure tai saurin buɗewa dan sanin waye.....