FreeArewaPen original
ALBI (zuciyata)
- 1views
- 57chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · TRILLER
Yau tun ƙarfe bakwai tayi shirin zuwa school kasancewar ranar monday ce, Ummi ta fito daga kitchen tana kallon Rahama dake tsaye tana kallon Ra'is dake breakfast a hankali. Da mamaki Ummi ke fadin. "Ke bazaki yi breakfast ɗin bane kin tsaya masa aka.?" Ta turo baki tana fadin. "Munyi latti Ummi idan naje school zanyi." Ummi ta tabe baki tana faɗin. "Toh ki zauna ya gama mana." Ra'is ya kalli Ummin nasu da sauri yana faɗin "Duk tabi ta dameni Ummi, dakyar nake turasa." Ra'is ya faɗa cike da jin haushin Rahama cikin muryarsa ta yara dan shine ƙarami. Yana da kusan 10 year's ita kuma tanada 13 year's, shekara ukku ne a tsakanin su. Nan da nan suka fita gate ɗin gidan. Da sauri ta kalli Adamu driver ta marairace masa tana fadin "Dan Allah Yaya Adamu kabari na gansa minti goma yayi yawa." A fusace Ra'is ke faɗin. "Wallahi idan kika tafi tafiyar mu zamu yi, sai dai shi wanda zakije wajan nasa ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.