Page 14
by @maidambu41
*NAAZNEEN*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
'Top-Notch
Season 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Ita kanta Amarya daga haka ta fahimci irin mijin da ta aura, mijin da matarshi take juya lamarinsa. Tsoron da take ji kenan, tun farko sai da ta nunawa Mahaifiyarta ita tana tsoron kada ayi auren ta zama koma baya, uwar da ke mace ce da ta san akwai samuwar Allah, yasa tayi ta rarrashinta tana nuna mata girman biyayya domin itama biyayya take yi, bata da zabi da ya wuce tayiwa mahaifiyarta biyayya.
Khalwat tayi hakuri ta rungume auren tunda har mahaifinta shima ya gaya mata, tayi biyayya domin shi na zai janye daga abin da ya saka ranshi ba, sannan da kunya Hajja Marih ta nime ya bada auren yarshi ga jikanta mafi soyuwa a ranta, shi yasa ya bita da addu'a.
A can kuwa Gimbi sai yadda tayi da shi, gashi wani irin tsoronta yake ji, da baya iya mata magana sai abin da ta ce. Haka yasa take juya shi son ranta.
Watansu daya da rabi da barin kasar, ya zuba mata idanu cikin tararradin abin da zai fito bakinta ya ce mata. "Ina son komawa bakin aikina, kin ga wata guda aka bani kada na yi wani abu su dakatar dani." Juya idanu tayi tana faɗin.
"Baka yi kama da makaryaci ba, balle nace maka karya kake, amma taya zasu kore ka? Bayan sun san yadda suke amfani da kai. Saif gaya min gaskiya ko kana son zuwa cin sabon wuri ne?"
Kamar munafiki haka ya sunkuyar da kanshi, jikinshi yana rawa. Domin yafi tsoronta da kome a duniya. "A'a wallahi ba haka ba ne."
"Haka ne mana!"
"A'a ki yarda da ni!" Yayi maganar kamar zai fashe da kuka. "Tow shi kenan." Daga haka ta bar zancen ta cigaba da abinda take, domin tasan matukar ta cigaba da magana zata zage shi ne, don haka ta share shi, har zuwa lokacin yana zaune a wurin kamar almajirinta. "Ai gara ka tashi ka tafi ka fara mana shiri ba, kada ka ce na hanaka zuwa wurin amaryarka."
Bai ce mata kome ba, ya tashi yana barin dakin ta buga tsaki. Tana kananun magana. Domin ta tsani yayi batun komawa gida.
★★★
Malami Jajja.
Tun ranar da Alhaji Adamu ya ɗauke yarshi suka bar gidan, ya kashe rabin tashin hankalin da yake faruwa tsakanin Innayo da Umma da Lami, domin kuwa zuwa yanzu ta masifar shiga hankalinta da zafin kishin da take yi, ba domin kome ba, sai abin kunyar da danta mafi soyuwa a ranta ya kwaso shi yasa take taka tsantsan da duk abin zai iya faruwa gudun kada a mata gori.
Bayan sallah la'asar malam yana kofar gida, wurin masu karatu. Tsakar gidan babu kowa dai ita ɗaya tana wanke geron da aka surfa mata. Wayarta da take can daki tayi kara, mikewa tayi ta nufi dakin. Ɗaukar wayar tayi, ta kanga a kunnenta. "Innallilahi wa inna ilaihi raji'u, Haulatu lafiya kike kuka?" Ta kira sunan matar jikinta a mace.
"Inna tunda Babawuro ya kawo yarshi, yake min abin da yaso itama yarinyar sai yadda tayi a cikin gidan ba a kwabarta ba a hanata kome, Innayo a gaji ya zauna da Yarshi zan bar mishi gidan ni da Yarana."
"A'a koda wasa, sai dai ita ta bar gidan ba dai ki bar gidan ba."
"Tow ya zan yi? Gara na bar mishi gidan yayi yadda yake so. Tunda ita ce mutum."
"In sha Allah baki bar gidan ba, ita ce zata bar gidan. Zan kira shi in sha Allah."
Da haka ta ajiye wayar, tana jin kamar ta isa abuja tayi ta zabga musu rashin mutunci.
Don haka ta shiga duba wurin kira, ta hango number, kiran layinshi tayi tana jin kamar ta shiga ta wayar ta mare shi. Domin Haulatu yar Yayanta ne, auren zumunta ne.
"Assalamu alaikum, ina wuni Innayo?"
"Bana bukatar gaisuwarka, idan har nice na haifeka da cikina da jikina, da jinina na umarceka da ka dawo da shegiyar yarinyar nan, idan kuma kana da uwar da ta fini sai ka zabi ni ko yarka."
"Ayya Innayo an biya kuɗin makarantar tafa."
"Nace kan dawo da ita, tazo tayi sale manga ko unguwar Borno!" "Shi kenan!" Ya fada yana me jiran ta kashe wayar. Ajiyar zuciya ta sauke ganin ta gama da karamin case idan yarinyar ta zo sai ta tabbatar da ta hana yarinyar sukuni, sai ta azabtar da ita kamar me.
----
A can Abuja kuwa, yana falonshi da Nazneen. Tana wasa da laptop ɗinshi, yake wayar."Innayo ta ce na ka mai dani ba?" Kallonta yayi, kwana arba'in da zuwanshi da ita, tun a can ake kiranshi ana mishi congrats na samu matsayi a hukumar lafiya ta kasa, kuma tun daga lokacin da ta ganshi ta gaya mishi zai samu karin mukami.
"Papa kada ka damu, in sha Allah sai ka sha mamaki. Allah zai bude maka kofofin samu sama da yadda kake yanzu."
Zama yayi a gabanta sannan ya ce mata.
"Baki biya min karatun da muka yi ba?"
Murmushi tayi tana faɗin.
"Papa zan maka bayani dalla dalla!
FARILLAN ALWALA GUDA BAKWAI NE.
FARILLAN ALWALA GUDA 7 NEH:
1. Niyya
2. Wanke Fuska
3. Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu
4. Shafar kai
5. Wanke kafafuwa
6. Cuccudawa
7. Gaggautawa
SUNNONIN ALWALA
• Wanke hannaye zuwa wuyan hannu
• Kurkure baki
• Shaka ruwa
• Fyacewa
• Juyo da shafar kai
• Shafar kunnuwa
• Sabunta ruwa agaresu
• Jeranta tsakanin farillah
MUSTAHABBAN ALWALA
• Yin bismillah
• Goga asuwaki
• Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye
• Farawa daga goshi
• Jeranta sunnoni
• Qaranta ruwa a nisa gabobi
• Gabatar da dama kafin hau.
AKAN FASALIN ALWALA
• Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwar abun.
• Idan kuma ya bar sunna, to saiya aikata ta ita kadai bazai sake sallah ba.
• Wanda kuma ya mance lam'a sai ya wanke ta ita kadai da niyya, in kuma har yayi sallah by an faruwar hakan toh sai ya sake ta
• Wanda ya tuna da kurkurar baki ko shaqa ruwa bayan ya rigaya ya fara wanke fuska, to bazai dawo gare su ba har sai ya gama alwalarsa, sannan sai yayi su
• Tsettsefe 'yan yatsu hannuwa yana wajaba, an so a tsettsefe 'yan yatsun qafafuwa, tsefe gemu mara dubu yana wajaba acikin alwala, tsefe gemu yana wajaba acikin wanka koh da mai duhu neh.
AKAN FASALIN ALWALA (2)
• Babu yana halatta ga wanda bashi da alwala yayi sallah, koh dawafi, koh ya taba al qur'ani koda acikin gafakarsa neh, bada hannunsa ba saidai idan *juzu'i* neh ga mai neman ilimi acikinsa.
• Yaro a wajen taba al qur'ani kamar babba yake, amma laifin yana wuyan wanda ya bashi al qur'anin ya taba.
• Wanda yayi sallah da gangan ba tare da alwala ba toh shi kafiri neh. Allah yakiya she mu."
Duk wannan karatun tana yi, hankalinta yana wurin wasa. "Nazneen!" Kallonshi tayi tare da barin wasan. "Zan mai dake gida, amma zan dauka miki wanda zai na zuwa yana miki karatu, naso Tahir ne amma nasan Innayo ba zata yarda ba."
"Babu kome Papa." Idanunshi ne ya cika da kwallar tausayinta. "Me yasa Jiddah taki zama da ni?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Papa saboda ba zata samu soyayyarka ba." Ta faɗa tana gyara zamanta sannan ta ce mishi. "Papa Innayo bata sona, kuma kana tsammanin zata zo Nne ne? Ba zata sota ba ita ɗaya ba Yaran Innayo yan uwanka idan aka cire Baba Rufa'i sauran suna tare da Innayo, don haka ka daina tunanin Nne zata samu damar zama da kai."
Tun da ya kawota gidan Allah ya shiga bud'a mishi ba iya da karin girma ba, har da budi ta hanyar kasuwancin da suke na haɗin gwiwa.
Wani abu daya da bai sani ba, shi ne tunda ya kawo Nazneen gidan, Matar shi Haulatu hankalinta yayi mugun tashi, na farko zaren ba kalar yadin ba ne, Allah shi yayi halittar Yaranta da Nazneen, amma idan kace kyau da kwarjini Nazneen ta fi su.
Tana da yara huɗu, Baba karami, sunan shi Muhammad Adamu Malami, suna kiran shi Baba karami yana da kusan shekarar goma sha takwas, Sai Munayyah wacce tafi Nazneen da shakara biyu, sai Yusrah wacce take da shekaru takwas, sai Adnan wanda shi ne kaɗai yayi welcoming din Nazneen tun kafin su iso Abuja aka gaya mata ai Nazneen ba yar Babawuro ba ce, sharri ne don ya auri Chioma shi ne ta kunso shegiya a waje ta kawo mishi. Da wannan itama ya gurbata Yaranta musamman Baba karami da Munayyah wacce take ganin kaf jikokin Malam babu wanda yake so kamar su, sai gashi zuwan Nazneen ta goge wannan mafarkin.
Da farkon zuwanta, sun yi yunkurin mai da ita baiwa. Wato sakata aiki ita kuma dake tana son yan uwanta, kome suka ce mata tow take cewa, sai da tayi kusan sati biyu ta fahimci bafa don suna yan uwanta suke saka ta aiki ba, domin sun fara kiranta da wasu irin suna musamman idan suka yi baki, haka yasa ranar da ta cika sati Uku, Baba karami ya shigo cikin gidan, daga wurin wasan ball.
Tana zaune ta saka tv a gaba tana kallon,. Shaun and the sheep, yana zuwa ya ce mata. "ke Bingo jeki dibo min abinci." Bata amsa mishi ba, ta cigaba da kallonta sake magana yayi ya ga da gaske bata kula shi ba, kawai ya taso ya kashe tv. "Don ubanki, tashi ki dibo min abinci" dama ire-iren iskancin da sukewa Mai aikinsu kenan, kuma uwarsu bata tsawata musu. Bata kalle shi ba ta kai hannunta gefe kamar zata kauda abu a gabanta, haka ta matsar da shi can gefe ta kafe shi a wurin, sannan ta nuna tv da yatsarta ta cigaba da kallonta.
Jin motsin ana shigowa yasa ta dunkule hannunta, sake shi tayi ta cigaba da kallo, tsoro yasa shi zubewa akan gwiwarshi. Yana kallonta. Shigowar Munayyah da sport wear, ta ce mishi.
"Tun dazu ka shigo baka koma ba?" Bude baki yayi zai yi magana, Nazneen tayi wani kyasta hannunta, tuni ya Hadiye maganar ya mike suka bar falorn. Munayyah tana mishi magana amma ina bai san tana magana ba, har suka fita kofar gidan. Zai nufi titin. Da gudu Adnan ya shigo cikin gidan yana faɗin. "Mommy kizo ga Yaya Baba zai tafi kan titi." Sake kyasta hannunta tayi, can a bakin titin hankalinsa ya dawo jikinshi. Da sauri wani mutum ya ture shi.daga tsakiyar titin.
Ya fadi can gefe, Munayyah da take bakin get kasa motsi tayi wani irin bala'in tsoro ta kamata. Lokacin da Hajiya Haulatu ta fito daga cikin gidan ta same su a kofar gidan ana mishi fada. Sai rawa jikinshi yaƙe.
"Mun gode sosai." Inji Hajiya Haulatu, sannan ta tura Yaranta suka shiga cikin gidan, Nazneen tana zaune a falon. "Ke little demon, baki san me ya faru ba ne kika zauna a wurin?" Inji Munayyah tana me kashe tv."
"Na sani mana, zuwa yayi ya zane ni shine na koya mishi tarbiyyar da ya rasa."
"Ke don ubanki har Tarbiyyar ce dake, yar karuwa."
"Mommy ki daina zagin mahaifiyata, bata da laifi, idan akwai mai laifi Papa ne, meye tayi miki?" Ta faɗa da mugun karfin da ya haddasa daukewar wutar lantarkin falon.
"Idan da tana da ra'ayin zama da Papa, baki isa yin kome ba...