FANSA KO ƘIYAYYA

#21

by @109051246447263646587

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*




_Page21 _

      Wani salihin murmushi Binazir tayi da faɗin  "gaskiya bai kyauta ba tunda gashi ya saki asarar kuɗin mota and na gode da jaje kam ƙwarai sosai naji daɗi"   

Kallonta Bishira takeyi da mamaki gashi dai ko a ido ma da yanayin jiki ta girmeta amma ji yadda takeyi mata bariki muraran lallai wannan itama 'yar ta kife ce ba wacce Za'a ciwa tuwo akan gado bace.  Yaƙe tayi da faɗin  "ba batun asara wajan aikin lada" sai kuma tayi shiru.

Binazir dai na daga zaune tana kallonta fuskarnan pal fara'a amma koban faɗa mukuba, ku kunsan irin wutar dake ruruwa a ƙasan zuciyarta

"Ance case in illicit drugs ne ko? ta tambaya dan ta rantse saita tarwatsa dukkan farin cikin gidan kamar yadda suka tarwatsa mata nata farin cikin daga lokacinda taji zancen auransu, kafin ta shigo da ƙarfin iko dana sa'ar da wani amintaccen malamai data samu ya bata laƙani .

  "Ai wai dama biki tabbatar ba? aina ɗauka kinsan komai?" Binazir ta gaya mata still fuskar nan da murmushi but zuwa wannan lokacin idan kayiwa fuskar duban tsanani zaka hangi murmushin iya bakine amma idanunnan cike suke da azaba dan harda wani kwantaccen ruwa a ciki 

Shiru Bishira tayi batace komaiba, tana daga tsaye a bakin ƙofa entrance na palon hakan ya taimaka mata jin alamun kamar ana taɓa gate, da sauri ta juya da faɗin "sai gani na biyu kuma" fitt tabar palon.

Da ido Binazir ta bita har saida ta ɓace wa ganinta sannan ta janye idanunta a wajan tareda sakin ajiyar zuciya, tsam ta tashi ta nufi bedroom inta, ba tunanin komai ta faɗa kan gado tareda sakin wani irin azababben kuka mai ciwo. Tunda aka kama Dady, ba wanda ya taɓa faɗar ainihin laifin Dadyn saidai ayi musu fatan alkairi a kuma jajanta musu, but yau sai gashi wannan matar da ta kira kanta da budurwar Majnun tazo tana kusan goranta mata da laifin mahaifinnata har tana iƙirarin yayannata ne yabata labari? and she believe cos ko sanda akayi hukuncin Dady 'yan media basuzo kotunba dat means talla yakeyi da ita a familynsa kenan? bayan he is the cause of everything, wani kukanne yazo mata mai ɗaci tanayi tana girgiza kanta a haka Naja ta shigo ɗakin, a matuƙar kiɗine take kiranta da tambayar abinda ya sameta amma ina bata ko sauraronta, hakan yasa Naja ta fita jiki a sanyaye kitchen taje ta ajiye kayan cefanen tagumi tayi tama rasa abin yi sai tunanin dalilin kukan Auntyn nata takeyi ta kama wancan ta saki wannan, ganin bamai ɓullewa bane yasa ta sakin ajiyar zuciya tareda fara aikin girki jiki a mace amma dukkan hankalinta ta maidashi cikin palon

Tana cikin girkinne taji alamun shigowar Yayan nata plon, da sauri ta fita wajansa kallonta yayi ganin ta shigo palon kamar wadda aka jefo itama shi take kallo ko sannu da zuwanda take masa ta kasa "lafiya wai?" ya tambayeta a ɗan harzuƙe ganin ta kafesa da ido ta kasa cewa komai.   

  "Aunty ce taketa kuka tun ɗazu" ta amsa masa a sanyaye, ƙuri yayi mata da ido yana kallonta sai kuma ya saki numfashi tareda nufar ɗakin, ajiyar zuciya ta sauke tareda komawa cikin kitchen.

Sanda ya shiga ɗakin a lokacin tana zaune kan gadon ta jingina bayanta jikin allon gadon ta daina kukan amma sai huci da ajiyar zuciya kawai take saukewa.

Jin alamun shigowa yasa ta ɗaga idanunta takai wajan, ƙurr ta kafesa da ido harya ƙarso cikin ɗakin ya tsaya a gaban gadon haɗida saka hannuwansa cikin aljihun wandonsa yana kallonta shima, janye idanunta tayi daga nasa dan share wani hawaye daya taru a idanun nata zuciyarta kuwa in banda suya ab abinda takeyi ga abubuwa marasa kyau da zuciyar tata ke raya mata da tayi masa.

  "Meya faru?" Ya tambayeta a sanyaye idanunsa har lokacin a kanta.    batayi niyar kulasa ba, amma jin tambayar da yayi mata sai taga kamar ta rainin wayau ce, hakan yasa ta ɗago da idanuta ta watsa su cikin nasa tareda maimaita tambayar da yayi matan  "meya faru?" ta faɗa murya a dashe sakamakon kukanda taci dan bana wasa bane.

"A tambayarki nake meya faru?" wani miskilin murmushi tayi me zuwa da ruwan hawaye da faɗin "ba abinda ya faru amma muddin kana turomin 'yanmatanka suna gorantamin damin habaici kan laifin mahaifina da sunan jaje, to watarana bazan iya riƙe zuciyata ba kuma hukuncinda zan ɗauka bamai kyau bane" ta faɗa a sanyaye tareda share hawayenda ya zubo mata.

Kallonta yake cikin mamakin abu biyu, na farko mamakin kalamanta yakeyi dan shi kwata kwata bai fahimci kan maganar ta ba amma kuma kalmar "ka daina turomin 'yanmatanka" ya bashi wani haske hakan na nufin wasune suka zo gidan kenan, mamaki na biyu tunda yake da ita bata taɓayi masa magana mai sanyi irin hakaba, lallai abinda akayi mata babbane tunda har girmansa zai danne girman ƙiyayyarda take masa.  Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya juya yabar ɗakin, da harara ta bishi ƙwafa tayi tareda runtse idanunta ita kaɗai tasan me takeji a cikin zuciyarta.

Kai tsaye ɗakin Naja ya nufa jin motsinta a kitchen ne yasa ya canza ya shiga kitchen in.

Kallonta yake yana ganin yadda take aiki a sanyaye kamar wata mara lafiya,  "ke Naja" ya kirata murya buɗe, a ɗan tsorace ta juyo dan bataji shigowarsa ba sai sautin amon muryarsa daya daki dodon kunnanta  "su waye suka zo gidannan?" Ya tambaya idanunsa a kanta. 

"Aunty Bishira ce kawai"  

"Me tace datazo? ya ƙara jefo mata tambayar idanunsa a kanta,  hannunta ta watsa da faɗin  "wallahi bansani ba dan sanda ta shigo gidan nikuma lokacin zani cefane lokacin da na dawo shima a bakin gate muka haɗu zata tafi sai sauri takeyi dana shigo banga Aunty a palo ba saina bita ɗaki shinefa na sameta tanata kuka" ta faɗa a sanyaye kamar itama zatayi kukan. 

Kallonta yayi na wasu sakanni sannan ya saki huci tareda barin kitchen in. 

Wani irin tafasa yaji zuciyarsa keyi masa, ba tareda ɓata lokaciba yabar gidan kai tsaye mai Napep ya tara  har gidan Baba Garba dan ji yake idan har bai sami Bishira ba ayau to da matsala dan abin zaita damunsa ne a zuciya. 

 Sanda yaje gidan bai shigaba, a waje ya aika yaro yayi masa sallama da Bishira.

Koda yaron ya shiga ya faɗa mata ana sallama da ita, ba wani batun jan aji ta fito, bayansa ta iya gani dan ya juya baya daga yanayin tsayuwarsa kawai ta fahimci bana wasa bane, Cikin yanga ta isa wajansa tareda yi masa sallama murya maƙe.

Wani ɓacin raine yaji ya kama zuciyarsa, wai yanzu wannan abar Umma takeso ya aura, yarinyar da ba kamun kai yanzu dagajin anyi sallama da ita tun batasan wane ba, harta kwaso jiki ta fito tana lanƙwashe murya kamar mai ciwon maƙogaro, fuska ya ƙara haɗewa tareda jiyowa yana fuskantar ta.

wata irin bugawa zuciyarta yayi mata tareda zaro idanunta waje 

"Meya haɗa ki da Binazir?" Ya jefo mata tambayar da tazo mata a bazata dukda tasan ba alkairi ne ya kawosa gareta ba.

"Wace Binazir kuma?" ta tambaya cikin mamaki dukda tasan inda zancan nasa ya nufa amma da gaske batasan ainihin sunan taba tadai ji kaɗan daga cikin labarin yadda akayi auren nasu ne wajan wata ƙawarta dake siwes a Headquartern su dukda labarin shima wani ba daidai bane andai gyara labari yadda zaiyi daɗin baɗawa.

   "Ohh da kika tashi binciken mahaifinta biki binciko da sunanta ba? Ko kuma shi munafikinda ya baki labarin mahaifin nata bai haɗa miki harda sunanta ba?" Ya faɗa cikin matuƙar ɓacin rai kamar zai rufeta da duka.

Ji tayi ranta ya fara ɓaci amma saita dake da faɗin "idan ma matarka kake nufi ni Allah sanya alkairin biki naje yimata sai naga kuma bai dace ace na taso ba tareda nayi mata jajeba"

"Meya kawo sunana a ciki da zakice nine na faɗa miki wai na turokii?" Ya tambaya a harzuƙe  yamutsa fuska tayi kawai dan wani ɓaci raine ya ziyarceta amma saita danne tareda kauda kanta gefe tana dannar zuciyarta kada ta watso masa magana mai zafi, dan har yanzu tanada buri a kanshi bata haƙuraba.

Yadda tayin ba ƙaramin hasala shi yayi ba, hakan yasa ya fara watsa mata kalamai "daga yau bake ba gidana na haramta miki shiga tunda ba alkairi ne yake kaiki ba, sannan kuma na rabaki da iyalina bake ba ita idan kun haɗu ko zumuncin banaso kowa yayi rayuwarsa"ya faɗa tareda juyawa zaibar wajan, har yayi taku ɗaya sai kuma ya dakata dan gani yake abinda zai faɗa mata yayi matuƙar yin kaɗan so yake itama taji zuciyarta ba daɗi kamar yadda ta sa nasu zuciyar ta baƙanta.

"Da fatan wanda ya baki labarin ya shaida miki nine na nemi alfarmar a bani aurenta ko?  Ki kuma sani ba mai Kasuwanci illicit drugs ba, ko shike haɗasu wannan bai daman ba ni abu guda na sani soyayyar 'yarsa dake cikin zuciyata wadda daban sameta ba, da yanzu kuna zaman makokina" yana gama faɗa ya wuce ta gefenta cikin takun isa.

Janye idanunta tayi daga kansa tareda dafe ƙirjinta ta durƙushe a wajan sakamakon wani irin bugawa da ƙirjin nata yayi sai kuma kuka ya biyo baya, tunda take ba wanda ya taɓayimata irin cin fuskarda yayi mata, tasan yasan tana nuna masa zazzafar soyayya a aikace amma ya ture wannan yazo har gidansu yana shaida mata dabai samu watanta ba da tuni suna zaman makokinsa? wai harda faɗa mata ya yanke alaƙarda ke tsakaninsa da matarsa? Lallai dole ta tashi tsaye kan wannan lamarin domin sai tayi da gaske kafin ta mallaki cikar burinta.     Share hawayenta tayi sannan ta miƙa ta nufi gida jiki a saɓule.

  Koda ya koma gida bai shigaba kai tsaye, masallaci ya nufa sakamakon kiran magrib da aka farayi kuma bai tashiba har saida aka kira salla isha'i. bayan an idar ne ya nufi gida, Naja ya samu ita kaɗai zaune a palo zaune tana karatun Qur'ani, tsayawa yayi harta kai ƙarshen Aya! Itace tayi saurin yi masa sannu da zuwa , saida ya samu waje ya zauna sannan ya amsa mata da tambayar taci abinci? Kai ta ɗaga masa alamar taci, iska ya fesar da faɗin "itafa?" Ko bai faɗa ba tasan wadda yake nufi cikin yanayin jimami tace "ko palon ma bata sake fitowa ba amma naje na sameta tanayin sallah"    shiru yayi na ɗan wani lokaci saiya numfasa da faɗin "ki shirya mana abinci ki kawo nan palon" da sauri ta miƙe da faɗin "to" shima miƙewar yayi ya nufi ɗakinsa, toilet ya shiga yayi wanka sannan ya shirya cikin kayan bacci ya nufo palon bai samu Naja a wajanba, zama yayi yaci abincinsa, saida ya gama sannan ya ɗibi wani a plate ya nufi ɗakinta dashi.

A zaune ya sameta jingine da fuskan gadon ta miƙar da ƙafafunta ga pilo rungume a ƙirjinta ta ƙurawa waje ɗaya ido

Kai tsaye gadon ya nufa tareda zama bakin gadon wanda zaman nasane yasa ta juyo a ɗan razane , idanunta ne suka sauka cikin nasa wanda hakan yasa ta ɓata ranta, miƙa mata plate in hannunsa yayi, kallo ɗaya tayiwa plate in ta maida kallonta garesa tareda tattare naman goshinta sai huci take saki jira kawai take ya taɓota dan tariga ta tanadi abin faɗe yau kome zare idanunsa da hargaginsa bazata bari suyi tasiri a kanta ba.

Ajiyar zuciya ya saki yana ƙara cusa idanunsa cikin nata  "banzo dan nayi miki wani kalami dan ina jin tsoron rashin kunyarki ba iya gaskiyata zan faɗa miki" ya jawo kalaman da taketa haɗawa tun a cikin Napep dan bata haƙuri dan anyi mata ba daidai ba anyi mata laifinda dolene kowane duk haƙurinsa zuciyarsa taji ba daɗi ballantana ita da take a sama 'yar dama take jira da zata tsige shi ta tsikareshi.

Iska ya janyo daga huhunsa ya fitar ta bakinsa sannan ya cigaba  "Ni tunda nake da yarinyar nan ban taɓa yi mata maganar da ta wuce ta gaisuwa ba shima saita gaisheni nake amsa mata , Ni bansan ainahin abinda tace mikiba amma zan iya rantse miki ba abokiyar yina bace ba kuma abokiyar hirata bace kuma wallahi duk abinda ta faɗa miki a kaina ƙarya ne niba abinda na faɗa mata ta samu information ne a wani wajan tazo dan ta haɗa mana fitina a gida" shiru yayi ganin wani kallo da take watsa masa "kiyi haƙuri nasan ta ɓata miki zuciya amma ina tabbatar miki hakan bazata sake faruwa ba dan na ɗau mataki akan hakan amma Wallahi rabona da ita tun sanda naje gidansu kan maganar auranmu, Ni wait tsaya ma!" Ya faɗa yana kallonta "me kika ɗaukeni? to mu aikinmu ba haka yakeba aikin sirrine wani aikin ma ko mahaifiyarka ba komai akeson ka dinga faɗa mata ba, koda mutum yayi winning case da wuya kiji y buɗe baki yana bada labari da kansa tunda na fara case innan ban taɓa zancen da kowaba a Headquartern mu sai manyana da suka ɗorani akan aikin daga sanda aka tura su Dady Court Kuma dagani har su ba wanda ya ƙara tada maganar dan we already move to our next mission, how comes za'ace na tsaya ina bawa civilian labari kuma waima mace ai it does not make any sense, apart from manyana Ummace kawai na Bama labari lokacin zan nemi auranki and itama ba komai na faɗa mataba kuma tun daga ranar bamu ƙara zancan ba" ya faɗa yana sauke numfashi.






*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*