6
by @asmybaliyu
Hajja ta gani durƙushe a gabanta tana share mata hawayen fuskarta, cikin sauri Rahama ta shige jikinta wani irin kukan bakin ciki yana sake fitowa tun daga cikin zuciyarta, tace da Hajja wacce ke shafar bayanta alamar lallashi. "Meyasa Yaya Farooq zai min haka Hajja? Nasan lokacin da ya tsaneni wallahi, har idan nai magana ya daka min tsawa ya koreni daga wajan, shine yanzu zai nuna yana sona? Why Hajja? Meyasa ya amince lokacin da aka ce za'a bashi ni?" Hajja taja numfashi ta sauke a hankali, hannun Rahama ta jayo cikin sanyin murya take ce mata. "Duk abinda yai miki a baya ya wuce ki dinga yin afuwa a rayuwarki Rahama. Sannan wannan haɗin da za'ai muku kowa yana so a cikin dangi, zumunci kuma zai sake ƙulluwa tsakanin iyayenku, zan kuma fi kowa jin daɗi da hakan." Rahama ta janye jikinta daga na Hajja, cikin kuka take faɗin. "Bana san Yaya Farooq Hajja." Cike da mamaki take tambayarta.
"Ai har yanzu baki san meye so ba Rahama, ki kwantar da hankalinki, kuna yin aure gaba kika ƙara mallakar hankalinki zakisan cewa anyi miki gata." Ran Rahama Galadanci ya sake ɓaci da kalaman Hajja, ta shiga dafe kirji jin yana mata wani irin bugu, cikin murya mai ban tausayi take faɗin.
"Kema ashe bakya san farin cikina? Hajja dake za'a yi min aure yanzu? Wayyo Allah na ina zan saka rayuwata?" Hajja ta sake janyota jikinta tana faɗin. "Kemeyasa bazaki so namu farin cikin ba Rahama? Kinganni nan? Lokacin da akai min aure shekaruna tara, na dawo daga islamiya aka ce na tube kaya ai min wanka, Allah yaji ƙan rai mahaifiyata ta shirya ni tsab aka miƙa ni ɗakin miji da bansan waye ba. Amma fa yaga shirme tunda lokacin bansan me ake nufi da auran ba. Haka mijina yai ta kula dani, bamu taɓa rabuwa ba har Allah ya ɗauki rayuwarsa, Allah yaji ƙan Galadanci."
Rahama ta ɗago ta kalli Hajja da jajayen idanunta wanda still basu dena zubar da hawaye ba. "Yanzu irin auranki za'ai min Hajja? What about Imran Matawalle da nakejin damuwa akanshi Hajja? Wannan abun da nakeji akansa duk ba love bane? Tell me Hajja ya ake gane so? A ina akejin love idan har aka farayi." Cikin takaici Hajja take kallanta tace da ita. "Wai Rahama har guda nawa kike yanzu? Dududu shekararki nawa da har kike san jefa kanki cikin fitinar soyayya? Anya ba wani abu akai miki ba Rahama?" Share hawayen tayi tace. "Allah yasa Yaya Farooq ya riƙe alƙawarinsa, Hajja cewa yai ya hakura dani zaijema ya gayawa Abban mu."
Yadda Hajja taga yanayin Farooq Galadanci a ɗazu, yanayin ya nuna mata Farooq ɗin yana cikin budurwar soyayya, ta gane cewa ya shiga fagen yakin samun Rahama Abubakar Galadanci, bata tunanin zai haƙura ya barwa wani ita dan ta fara hango tsantsar soyayyar Rahma a gurinsa tun randa sukazo gidan nan. Tasan lokacin da suna Abuja koda akai masa zancen Rahama cewa yai bazai auri ƴar yarinya ba, infact shi yana da ƴan mata masu aji kuma balagaggu ba kwaila ba.
Da kyar ma ta samu yabiyota zuwa Kano, sai gashi suna cewa zance ya canza, Farooq har ya fara rasa nutsuwar shi akan Rahama.
Hajja ta kalli Rahama "Kici gaba da addu'a Rahama kinemi zaɓin Allah akan karatun ko auran, da kuma alkairin dake tare da hadin ku da Farooq." Rahma ta turo baki. "Babu wani alkairi nida Yaya Farooq Hajja, Imran ma alkairi ne a wajena." Ture ta Hajja tai daga jikinta tana faɗin.
"Ke kinfisan mashayi kenan? Haba Rahama kowace uwa ana so ta samarwa yaranta uba nagari, kinsan da cewa Imran ɗin nan mugun mashayi ne kowa yasani a unguwar nan, shine ke kike shirin shiga rayuwarsa? Wai Rahama baki san cewa Matawalle baya kaunar mahaifinki ba ne? Da yanzu Abubakar ne a matsayin Matawalle amma yai masa fin ƙarfi, duk baki gani ba Rahama kike kokarin debo mana ɗan iskan ɗansa matsayin suruki kome? Shi yana sanki ko kuma kece kike wahalar da kanki?"
Shiru Rahama tayi tana zirarar da hawaye, itama batasan meyasa Imran yaki furta mata kalmar so ba, ta rasa dalilin da yasa idan tai masa maganar yana santa? Sai yace ba lokacin maganar bane ta bari sai nan gaba, toh yaushe yake nufi.? Ganin tayi shiru ne yasa Hajja miƙewa tace da ita. "Ki fito kici abinci tun kafin kisa ciwon damuwa ya kamaki, shi yana can be hana kanshi ci dasha ba sai ke zaki matsawa rayuwarki." Hajja bata jira Rahama tayi magana ba ta fice daga cikin ɗakin tana ta mita ita kaɗai.
Tsabar yunwar da takeji ne yasa ta miƙewa, parlorn ta sakko inda ta tarar duk sun hau kujerun dining Hajja ce kaɗai a can tsakiyar parlor an kai mata nata can dan ta tsani zuwa dining cin abinci, a cewarta banda irinta masu jiran mutuwa yau ko gobe. Kai tsaye Rahama ta nufi wajan Hajja dan taga Farooq a gurin su Ra'is ita kuma bata ma san ganinsa bare ta zauna kusa dashi. Tana zama kusa da Hajja taji Farooq ɗin na mata magana. "Rahama dawo nan." Cikin ɓacin rai da take neman haɗiyewa tace.
"Yaya Farooq zamuci da Hajja anan." Farooq ganin zata yi embracing ɗin shi yasa yace da ita. "So kin manta alƙawarin mu?" Ranta a mugun ɓace ta miƙe ta nufi wajansu, taja kujerar kusa da Ra'is tana haɗe rai. "Let me save you my new friend, me kike son ci? Tuwo ko white rice?" Rahma tai saurin ɗaukar wani plate ɗin tana faɗin.
"Zan zuba da kaina Yaya Farooq." Kafin yai magana tuni ta fara zuba abinda takeso, ganin haka yasa shima ci gaba da cin nashi yana kuma zuba mata ido, duk wani reaction nata yana kansa har ta gamaci ta tashi tabar wajan. Koda Abba ya dawo hira suka sha da Farooq, maimakon yai masa maganar da sukayi da Rahama sai yaki saboda dama can ba wai zaice da Abban ya hakura da ita bane.
Farooq Galadanci ya yi hakan ne dan Rahama ta saki jikinta dashi har su saba ta haka yake tunanin zai cusa mata soyayyarsa.
*****
Shirye ta fito cikin uniform ɗinta ta shiga room ɗin Ra'is tana cewa. "Kai kullum sai kasa munyi latti ne? Kasa uniform kawai sai ka tsaya kana yiwa mutane nawa, dalla can ka fito ko sai Abba yazo ya, fara min faɗa yace nice babba?" Ra'is ya ƙarasa sanya rigarsa yana ɓalle botin yace. "Yaya Rahama wahala nasha a toilet, kinga yadda nai wani irin k..." Rahama ta juya tana cewa. "Banza ni basai ka gaya min kayan amai ba, kazo muyi breakfast kafin Abba ya sakko." Saida ya gama sanya safarsa da takalmi kafin ya sakko daga stairs ya biyota zuwa dining. Suna cikin yi Abba ya fito bayansa Ummi ce riƙe da jakarshi, tun kafin ya gama sakkowa yake faɗin. "Oya a tashi mu tafi."
Duk suka miƙe kowa ya ɗauki school bag nasa ya goya. "Allah ya bada sa'a." Ummi tai addu'a tana komawa ciki. Sai da Alhaji Abubakar ya fara zuwa wajan Hajja ya gaida ita sannan ya fito ya shiga mota. Ra'is ne a front seat Isa driver na wajan tuki, Rahama da Abba suna baya. Kokarin fita daga gate ɗin sukeyi, Farooq yai saurin zuwa gurin mota. "Abba bari na rakaku, idan naga school ɗin anjima sai naje na ɗakko su." Abubakar Galadanci yaji daɗi yake. "Thank you my beloved son, ɗakko motar sai ka biyomu." Juyawa Farooq yai, mota ya ɗauka Rahama zuciyarta tamkar konewa zatai, indai haka Yaya Farooq zai mata batajin zasu kai alaƙarsu tai musu nisa dan tun yanzu taji ba zata iya ba.
Abba na sauke su Rahma tai saurin shiga wa class ɗinsu cike da damuwa. Abba ya wuce wajan aiki, shi kuma Farooq ya koma gida suka sha hira shida Hajja. Ana tashin su break ya ƙarasa cikin makarantar, neman ta ya ware idanu yanayi, ganin ko mai kama da ita be gani ba yasa ya kuma kiran wayar ya tambayeshi, gaya masa ajin nasu yai hakan yasa Al-Amin ƙarasawa, ta window ya hangota zaune tayi shiru, yasa wata yarinya dake tsaye wajan door ta kirawota. Hango Al-Amin yasa Rahama tashi da sauri ta fito, bakinta yana rawa tace.
"Imran yana ina?" Wayar hannunsa ya miƙa mata dai dai lokacin Imran ya sake kira Rahama ta kalli wayar, my favorite friend tagani a rubuce, da sauri ta ɗaga hawaye na zirarowa daga idanunta tace. "Why Imran? Why?" Imran ya rintsa idonsa, kukanta da yakeji cikin kunnuwansa ya shiga sara masa kai yana faɗin.
"Sorry R Galadanci, kina zaton zanyi miki haka da gangan ne? Yanzu haka muna Russia, Daddy ya lura banayin abinda ya kawo mu ƙasar nan ya kwace passport ɗina da duk wani abu da yasan zan iya dawowa Nigeria, nasan randa kika koma gida Abba ko Ummi wani ya dokeki saboda kinzo gurina ba?" Hawaye basu dena zubowa a fuskar Rahama Abubakar Galadanci ba, jin muryarsa kaɗai yasa taji tana jin rigima tsantsa, duk kuwa da farin cikin da zuciyarta ke ciki, bayan hannu tasa tana gogewa murya so cool take faɗin. "Imran baka sona?" Tambayar ta zo mai a wani irin yanayi dan beyi expecting ɗinta ba a wannan lokacin, dan haka ya rasa abinda zai ce da ita. "I know kana ɗaukata like your blood sister, amma ni kuma..." Rahama Galadanci ta kasa ƙarasawa sai kuka da ya kwace mata. Cikin tashin hankali Imran Matawalle ya riƙe handle ɗin motar da yake tsaye ajikinta, ji yake tamkar ya fasa wayar ya ganshi a gaban Rahama. Besan mezai ce mata ba saboda shi kanshi har yanzu ya kasa tantance wane irin matsayi Rahama take dashi a ransa? Wace irin alaka yake jin zuciyarshi nayiwa yarinyar, kawai yasan dai tana da matuƙar muhimmanci a cikin rayuwarsa.
"Kaga Abba aure zai min da cousing brother ɗina." Cewar Rahma cikin wata irin murya, kirjinsa yaji ya wani irin harbawa cikin wani irin tsoro da fargaba ya dafe wajan da zuciyarsa take yadda yaji tana wani bugawa ba yadda ya dace ba. Muryarsa na rawa yace. "This can't be happen Rahama, wane mai ƙararren ƙwanan ne yake shirin kasancewa da abin hannuna? R baki sanar dashi cewa ke ɗin abin hannuna bace?" Imran Matawalle yai maganar tamkar zai fito ta cikin wayar saboda masifa. Da kakkausar murya yake faɗin. "Ki sanarwa da duk mai shirin yin wannan gangancin cewar ba'a taɓawa Imran Matawalle abinda ke hannunsa da abinda yake da muhimmanci acikin rayuwarsa. Imran Matawalle baya sharing abin hannunsa ga kowa." Farin ciki ya kama Rahama Galadanci, sai dai zuciyarta ta kasa nutsuwa tana san ta gano mai kalaman Imran Matawalle suke nufi na cewar ita ɗin abin hannunsa ce? Santa yake yi kokuma dai wani abu yake nufi? A ruɗe tace "Do you love me Imran?" Rahama ta kuma jefa masa tambayar, zuciyarta cike da tsoran abinda zataji daga bakinsa......
#Asmy B Aliyu
#Hajja ce