FANSA KO ƘIYAYYA

#22

by @109051246447263646587

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*



_Page 22_

   Kauda kanta tayi gefe tereda cire filonda ta rungume a hannunta ta gyara kwanciyar ta haɗi da juya masa baya. 

Ajiyar zuciya ya sauke ya kira sunanta a hankali 

"Binazir" shiru tayi masa ba tareda ta ko motsa daga kwanciyar da takeba "ki daure dan Allah ki tashi kici abinci badan niba kiyi kodan lafiyarki" yana gama faɗa ya juya jiki a sanyaye yabar ɗakin.

Saida ta tabbatar yabar ɗakin sannan ta sauke ajiyar zuciya tareda tashi zaune, haka kawai taji ta yadda da maganarsa ta aminta da bashine ya faɗamata kuma ya turo taba dan da shine tasan bazaiji shakkar gayamata ba amma daga yadda yake magana cikin sanyin murya da kwantar dakai ta fahimci zallar gaskiyar sa, amma koma wane ta ɗau alwashi bazata bari cin mutuncinda wannan baiwar Allahr tayimata ya tashi a banza ba, koyane saita rama wannan alƙawarine.

Miƙewa tayi a sanyaye ta nufi toilet dan yin wanka, bayan ta gama ne ta ɗauki abincinda ta gani dan yunwar takeji amma takaici da ɓacin ransa ne yasata kasa komai but tunda ya wanke kansa, ta gama da babinsa saura na waccan babbar bazawarar zatayo kanta ne.

************************************

Washegari Kamar koda yaushe bayan an idarda sallar asuba Naja ta shiga ɗakin Binazir da sallama, a zaune ta sameta da waya a hannu dan lokacin gama wayarta da Mummy kenan, da fara'a ta amsa mata, hakan yasa Naja ta ƙarasa wajanta cikin ƙwarin gwiwa ta zauna akan side drawer, sosai suka gaisa sai kuma ɗakin yayi shiru.

 "Naja'atu dan Allah tambayarki zanyi" Binazir ta katse shirun, cikin bata dukkan hankalinta Naja ta amsa mata tareda gyara zamanta.

"Jiya kina fita mukayi baƙuwa ko kin ganta a hanya?" Da sauri Naja ta ɗaga kanta sama alamar a 

"Bishira ce 'yar gidan ƙanin babanmu ce wai nan son Yaya takeyi Kamar ta mutu shikuma baima san tanayiba wallahi dan banda ma Umma batada riƙo aida tuni mudasu mun yanke layi , to tace mana muyi haƙuri shidai yaya yana kulasu ba laifi amma nidai na haramtawa kaina gidannan ko za'a kasheni saidai wani ikon Allah".  

A iya bayanin Naja ta fahimci abubuwa ba laifi ta kuma gasgata zuciyarta, Numfashi ta sauke da tambayar  "kunada wani biki ko taro a danginku wanda itama zata iya zuwa?" Shiru Naja tayi tana nazari, kai ta girgiza da faɗin "gaskiya babu dadai gidan Ummane tana yawan zuwa kafin asa ranar auranku amma tunda akasa shiru bata ƙara zuwaba harma bikin batazoba sai mamanta da tazo take harare harare Kuma ba wanda yabi ta kanta ko nan gidanma nafi tunanin wajan 'yanuwanmu da sukazo biki ta tambaya amma da wuya idan taje gidan Umma" Naja ta faɗa cikin tabbatarwa idanunta akan fuskar Binazir.

"Shikenan jeki ki huta kafin gari ya gama haske a ɗora break" 

Jimm tayi sai kuma tace  "Aunty wai meya saki kuka jiya? badai itace ta faɗa miki wata maganarba?" 

Murmushi kawai Binazir tayi haɗida girgiza kanta, ganin hakan yasa Naja miƙewa tana tafiya tana magana "idan ma wata maganar ta faɗa miki karki damu Allah Aunty ta faɗane Dan kawai ta ƙuntatamiki kishine kawai kishinma na rashin sanin ciwon kai dan ita kaɗai ke haukanta dan indai yayane da ita da babu wallahi duk ɗa..."  Maganar ta maƙale sanda ta haɗa ido da yayannata dake jingine jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji.

Ido ta zaro waje sai kuma tayi ƙasa da kanta sanda zata giftashi, da sauri ta fice a ɗakin, Ajiyar zuciya ya sauke tareda ƙarasa shigowa cikin ɗakin, a gabanta ya tsaya idanunsa a kanta haɗida zura hannuwansa cikin aljihun jallabiyar jikinsa 

Ɗan ɓata fuska tayi tareda kauda kanta gefe dan ita ta tsani wannan shegen kallon nasa

"Kar dai kice min har kin fara kishina"  taji saukar maganar tasa kamar an watsa mata ruwan dalma a jiki, a birkice ta juyo tana watsa masa wani kallo, ganin sassauci a fuskarsa ba alamun ɓacin rai yasa ta fara zuba masa rashin kunya  "Har abada, inyi kishinka ince nayi kishinwa? ka ajiye wannan ba wannan tsakanin ni dakai wallahi Never Kai ni koda ba wani abin tsakanin nidakai baka cikin jerin mazan da suke burgeni ballantana kaiɗin You are terro and Monster to me"   

Wani yalwataccan murmushi ya saki da faɗin "karki yaudari kanki 'yan mata, kinsani kuma kinsan na sani i am the most perfect man to you, tun baki ganni in my perfect structure ba Kika mace a kaina, so mene ya rage kuma?" Ya tambaya tareda ɗaga mata gira.

Wani malulun ɓacin raine ya tokare mata maƙoshi tama rasa mai zatace kawai saita haɗiyi yawu da faɗin "Allah ya sakamin" murmushi ya kumayi tareda juyawa har yakai bakin ƙofa ya dakata ba tareda ya juyoba yace "ki rubuta ki ajiye nikuma nace one day you must be jelous of me, bana ce ga lokacin ba , slowly but surely" Yana faɗa yabar ɗakin.

Ƙiris ya rage bata auna masa ashar inda taji zuciyarta ta haɗa ba, sai Allah ya taimakesa yabar ɗakin, ita yanzu wani nazari da tayi akansa ma shine kamar ya maidata mahaukaciya dan ta fahimci gabaki ɗaya tsokanarta yakeyi a duk sanda yaso, idan ya tabbatar ya kunnata kuma saiya ƙara gasa mata magana ya barta cikin haukanda ya sata.  wani yawu ta haɗiye mai ɗaci haɗida miƙewa dan taimakawa Naja a kitchen ko ta samu zuciyarta tayi sanyi kan abinda takeji.  

A haka suka cigaba da rayuwarsu abin sha'awa, Binazir ta sakarwa Naja fiyeda tsammani saboda kawaici da hankalin yarinyar, duk irin hirar da suke da zarar ƴaƴanta yazo wajan tsam zata miƙe tabar wajan, batayi musu sa'ido ko kaɗan kuma duk abinda zata faɗa saita taceshi take faɗa mata.

Shikam alaƙar 'yar ƙanwar tasa da matar tasa yakan bashi mamaki amma kuma wani lokacin saiyaji mamakin nasa bai wani tsananta ba saboda yasan wace ita yasan zuciyarta ta ainihi, shi abu ɗaya yake da buri sanin rayuwarta ta baya, koda da sunan makarantar da tayi na secondary abin ya gagara dan yana ganin daya san sunan school in sauran bayani ya ƙare amma hakan ya gagara sam.

Yaune ta cika sati biyu a gidan, yana idarda sallar asuba ya shigo gidan fuska a tamke ba fara'a, kai tsaye ɗakinta ya nufa tareda yin sallama ciki ciki.

A zaune take a gefen gadon tanason kiran Mummy su gaisa kamar yadda ta sabayi duk asuba, jin shigowarsa ne yasa ta ɗago suna haɗa ido ta kauda kai tareda miada idanunta kan fuskar wayar, haka kawai taji ƙirjinta ya buga sakamakon yadda taga fuskarsa "kina sane da yau zaki fara amfani da matsiyatan kaya ko?" Ya tambaya idonsa a kanta.

Ƙirjinta ne ya sake bugawa haka kawai amma cikin dakewa tace "saida ka faɗa na tuna! amma gaskiya bazan iya barin kayanda nazo dasu daga gidan ubana ba dan suma sababbine yadda kake ganin ka kashe kuɗi ka siya dukda ba saka akayiba haka suma nawa iyayen suka kashe kuɗi sukayi min" ta faɗa cikin jarumta.

Tunda ta fara magana yake kallonta harta dire watakam ita bakinta baya mutuwa kenan, duk yadda ya haɗe fuska duk dan tasan ba wasa ya kawosaba amma saida ta musa masa ƙwafa yayi da faɗin "shikenan kinji na rantse miki muddin kikasa wani kaya ba na akwatinki ba saina mummunan saɓa miki Idan kina ganin wasa nakeyi dan Allah ki gwada yanzu ina jiranki ya juya a fusace yabar ɗakin, haka kawai taji ya mugun bata tsoro ga wani hawayen takaici, wai ace bakason miji amma dole saiya zuba maka iko? wannan abin na matuƙar damunta cikin ɓacin rai mai haɗe da hawayen takaici ta miƙe a zafafe ta nufi ɗakinsa 

Ba ko sallama ta Banka masa ɗakin lokacin yana tsaye a ɗakin yana sakin numfashi bayason yana tursasata yana mata zafi amma ita ɗince zuma saida wuta, dan kalmar matsiyatan kaya data kira kayanda suka kusan cinye masa kuɗin account ba ƙaramin ƙona masa zuciya abin yayiba.

Jin an banko ɗakin ne ya ɗan juyo da sauri idanunsu ne suka sauka cikin na juna..

"Wannan ai rashin adalci ne, dan kana taƙamar kai wanine a hukuma saika dinga tauyemin haƙƙi? idan nacigaba dasa kayanka su kuma nawa kayan watsar dasu zanyi komai kakeso nayi musu hakane naka salon shugabancin da adalcin a cikin gida?" ta tambaya idanunta cikin nasa fal hawayen takaici.

Kallonta yake cikin nutsuwa tareda nazartar yanayinta, wani gauron numfashi ya sauke da faɗin "Ni bance ki watsar da kayanki ba, nadai rantse daga yau nawa kayan da kika zaga zaki fara sawa harsai sanda naga dama dan kaina zan umarceki ki cigaba da saka naki but for now nawa zaki fara sawa" ya faɗa cikin jaddadawa but in low tone.

Juyawa tayi kawai zata bar ɗakin tana hawaye zuciyarta fal takaicin yadda yake juyata son ransa

 "BINAZIR!"  ya kirata murya a sanyaye,     dakatawa tayi da tafiyar ba tareda ta juyoba sakamakon yadda kiran ya shiga jikinta wanda ya haifar mata da faɗuwar gaba

 "Ki daure sau ɗaya kibi umarninna ba tareda na tursasaki ba, ni ko a mafarki bana fatan nayi miki rashin adalci Binazir, har yau ina ganin tarin alkairanki gareni bazanso ko wanine ya cutar dake ba, kome nayi kece kika janyo hakan, ke kika faɗamin maganarda ta ɓatamin raina har tasa nayi rantsuwa akanki, amma ina baki haƙuri ki daure kiyi yadda nace I know what I am doing Binazir, I will never harm you"ya faɗa tareda sauke ajiyar zuciya, kawai sai yaji zuciyarsa sakayau kaman an cire masa wani abu mai nauyi.

Runtse idanunta tayi dan Bama ragowar hawayenda ya maƙale damar fitowa, saida ta tabbatar da fitarsa sannan ta buɗe idanun haɗida barin ɗakin jiki a sanyaye. 

Ɗakinta ta wuce tareda kwanciya akan gado, wani hawayene taji ya tawo mata hawayen sallamawa da takaici bataso ya karya mata zuciya da kyakyawan kalamai ba taso ace ya biye mata ya kafe akan ra'ayinsa ta ƙarfin tsiya ita kuma ta nuna masa bai isaba amma sai gashi yayi mata magana cikin tattausan lafazi har yana yaɗata da Allah.

Ganin kukan bazaiyi mataba yasa ta share hawayen tareda miƙewa ta shiga toilet danyin wanka.    Bayan ta fito ne, ta tsaya tana ƙarewa kwatunan kallo, wani huci ta furzar tareda sauke akwatunan tana buɗewa.

Wani abu daya bata mamaki shine akwati guda data gani cike da irin kayanda takesawa ready made na zaman gida, sosai taji daɗin hakan a ƙasan ranta, shiryawa tayi cikin wata abaya mara nauyi sannan ta koma kan gado ta kwanta dan bazata iya fita da kayan jikinta indai yananan ba, gwara idan ya fita ta fito, tana a haka bacci ya kwasheta.

Saida gari yayi haskene samnan Naja ta Shiga kitchen ta haɗa musu break fast, bayan ta kammala ne ta haɗa komai yadda ya kamata sannan ta koma ɗaki danyin wanka kamar yadda ta koya wajan antyn Tata 

Kusan a tare ta fito palon itada yayannata, da sauri ta koma kitchen dan haɗa masa kayan break.

Saida ya cika cikinsa sannan ya maido da hankalinsa ga Naja da faɗin "Ya kamata kije ki gaida Umma fa"   "nacewa Aunty zanje jiya amma saitacemin wai dan Allah nayi haƙuri kar naje tunda muna waya na jirata idan ta fara fita unguwa sai muje tare wai kar naje Umman taƙi barina na dawo"  Najar ta faɗa sanda take ƙoƙarin haɗawa kanta tea.

Shiru yayi baice komaiba sai zamansa daya gyara yayi balance haɗida lumshe idanunsa, numfashi ya sauke haɗida buɗe idanunsa, tsam ya miƙe ya nufi ɗakinta, a kwance ya sameta tana bacci, kayan jikinta yake kallo bazai manta da rigar nan ba dan a Headquartern su wata ma'aikaciya ta kawosu harya wuce dan ba magana yakeyi da matan ba, sai kuma ya dawo ya kira wani ɗan team insa kan ya ɗaukan masa rigar idan ba maishi dan kayan yayi masifan birgesa dukda ba wani adone sosai a jikiba.

 Matsawa yayi saitin ƙafarta ya zauna daga bakin gadon yana ƙare mata kallo, ajiyar zuciya ya sauke haɗida jan yatsan babbar ƙafarta.

Cikin bacci taji kaman ana ja mata ƙafa, hakan yasa ta miƙe a ɗan firgice idanunta ne suka sauka cikin nasa ɓata fuska tayi haɗida janye ƙafafunta  "Good morning" ya faɗa idanunsa a kanta, baki ta ɗan murguɗa tareda sauka ta nufi toilet, brush tayi tareda wanke fuskanta da 🧼.

Turus tayi ta tsaya a bakin toilet in tana kallonsa ganin har lokacin bai fitaba, tattare girar sama da ƙasa tayi sannan ta nufi kan gadon dan ɗaukar wayarta, tana zuwa bakin gadon yasa hannu ya fizgota sai gata ta tayi zaman dirshan akan ƙafafinsa, kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, cikin ɓacin rai ta fara ƙoƙarin ƙwatar kanta amma ya hana hakan dan ya zagayeta da hannuwansa ne tareda riƙe nata hannuwan.

Kansa ya ɗora saman wuyanta ya saukemata wani hucin da saida ta ballaƙe bayanta tareda sakin ajiyar zuciya.

 "Bazan gaji da tambayarki past inkiba but for now so nake kawai ki faɗamin sunan secondary School inda kikayi" ya faɗa a daidai saitin kunnenta.  

Wani irin bugawa ƙirjinta yayi jin abinda yace mata, meyakaisa tunanin zuwa Makarantar su, to ko ya samu wani bayani ne? a ina? tayiwa kanta tambayarda bamai bata amsa ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke dukda ƙirjinta na bugawa cikin ƙarfin hali da dakewar zuciya tace "malam ka cikani niba 'yar iska bace ka wani riƙeni" bai kulataba ya wani birkitota tareda kwantar da ita akan gadon shima yabi samanta.     wani irin bugawa ƙirjinta yakeyi dan fuskarsa da take dabda tata, ga idanunsa da suka sauya cikin nata, baki ta buɗe da niyar yi masa magana kawai sai taji nasa bakin cikin nata, shan bakin yake kamar ya samu wani alewa, zuciyarta kam in banda suya da bugawa ba abinda takeyi, ƙoƙari take ta ƙwaci kanta amma ta kasa kawai sai ta saki ruwanda ya tarar mata a idanu dan kuka takesonyi amma yaƙi bata dama.




*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*