FANSA KO ƘIYAYYA

#23

by @109051246447263646587

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*




_Page23 _

    Saida ya gaji dan kansa sannan ya rabu da ita tareda mirginawa kan gadon ya kwanta rigingine idanunsa lumshe yana sakin numfashi.

Wani irin kukan takaici da baƙin ciki ne yazo mata bayan ta samu kanta, kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita in banda tsine masa ba abinda takeyi a cikin zuciyarta.

Yana kwance yana sauraron kukan nata dake sukar zuciyarsa, idanunsa ya buɗe tareda juyowa yana fuskantarta yana kallon yadda take rusa kuka kamar wadda aka aikowa da saƙon mutuwa.

A jikinta taji idanu a kanta, hakan yasa ta ɗan tsagaita da kukan haɗida buɗe idanunta da sukayi luhuluhu dan girma da jaa,  ɗiff kukan nata ya ɗauke sakamakon idanunta da suka sauka cikin nasa,naman goshinta ta tattare ganin hakan yasa ya tashi dan sauka daga gadon dan bazai iya jurar maganganunta ba, zasu zamo kaman famine kan wutarda ke ruruwa a zuciyarsa 

 "Allah ya isa na mugu, fasiƙi mai yiwa 'ya'yan mutane fyaɗe" ta faɗa tareda shafa leɓanta da suka tasa.

Cakkk ya tsaya tareda juyowa yana ɗora birkitattun idanunsa a kanta. Ko kaɗan a wannan gaɓar bai bata tsoroba dukda yadda idanunsa suka birkice kamar ba shiba, dan jikinsa har wani rawa taga yakeyi.

"Na faɗa in, kayi duk abinda zakayi, nagaji da wannan zaluncin na haƙura na aureka ina zaune dakai hakan bai isaba sai kayi ƙoƙarin keta min haddi? Nafaɗa fasiƙi mai yiwa 'ya'yan mutane fyaɗe ko zaka kasheni ne?" ta tambaya a fusace da fitar hayyaci cikin zare idanu dan abinda yayi matan wani abune da ba mahaluƙinda ya taɓa yimata ko kuma ya kwatanta hakan kuma ita a tsarin rayuwarta ba wannan saboda wani babban dalili nata.

Batayi auneba ba kuma tayi zato ba sai ji tayi ya kama wuyan rigarta da hannuwansa biyu ya jasu har ƙasa, saiga jikinta a bayyane, cikin matuƙar kiɗima idanunta waje ta fara girgiza masa kai amma ina ta riga takai shi maƙura da wulaƙantattun kalamanta da suka zama kamar barkono akan ciwo, tabbas tayi babban kuskure kuskurenda da tasan ma'anar yin hakan a gaba da bata jefesa da wa'yannan kalaman ba masu rikita ƙwaƙwalwa da tuno da wani shafaffan lamari da yake ƙoƙarin mantawa da shi saboda kuma itan ya keson mantawa ya kuma barwa Allah komai.****

Bai ƙyaleta ba saida ya aikata abinda ta alaƙantashi dashi dan abune da yayi matuƙar taso masa da wani gyambo a zuciyarsa, shi baima san meya aikata ba, saida ya samu kansa kallo ɗaya yayi mata ya kauda kansa ɗan ko kaɗan baiji tausayinta a lokacin ba, asalima wata tsanarta ce ta dirar masa a zuciya lokaci guda tareda tariyo kalamanata cikin ƙwaƙwalwar kansa, miƙewa yayi cikin rangaji yabar ɗakin, kai tsaye nasa ɗakin ya nuna fa tareda faɗawa kan gado.    Wani irin siririn hawaye ne ke fita ta cikin idanunsa, ba abinda zuciyarsa keyi sai ƙuna da tafasa, sai ayau yaga laifin zuciyarsa data ingizata harya nemi auranta dukda yasan tarin ƙalubale dake lulluɓe shi da ita,  duk da batada masaniyar komai amma kuma ai shiɗin mahaifinta ne ita kuma jininsa ce, ya sani son zuciyane yakaisa neman auranta dukda hakan ba haramunne a musulunce ba amma abin ba tsari, bai yiwa Umma da Naja adalciba, ya munafurcesu saboda son ransa ya kuma san haƙƙinsune yasa har yanzu Ubangiji ya kasa daidaita al'amura shi da ita, amma fa dukda wannan halin da zuciyarsa ke ciki, baya tunanin na second ɗaya zai iya rabuwa da ita NEVER! ba wannan a ransa zai kuma cigaba da ɓoye wannan sirrin har ƙarshen rayuwarsa, amma a yanzu kam bayason yaje inda take harsai zuciyarsa ta daidaita.

Ajiyar zuciya ya sauke haɗida miƙewa jiki a sanyaye ya nufi toilet, Saida ya sakarwa kansa ruwan sanyi sannan yayi wankan tsarki haɗida sabon wanka ya fito, so yake ya shirya a gurguje dan ya makara a aiki, amma sam jikinsa ba wannan kuzarin dan abu yake kamar wata mace yau abubuwa ne suka tarar masa a zuciyarsa wanda yakejin zai jima kafin zuciyarsa ta wuce, ayau ji yake zai iya kai awa biyar bai huceba saɓanin da dayakeyin minti biyar.

A farfajiyar gidan ya samu Naja tanata tilawar hadda, lumshe idanunsa yayi tareda buɗesu lokaci guda ya tsaya yana kallonta, yafitota yayi da hannu da suka haɗa idanu.

  "Ki koma palo ki zauna ko zata kiraki, amma indai bata kiraki ba karki sake ki shiga ɗakin sannan ki ɗanyi haƙuri da karatun a fili kar a kiraki biki jiba" yana gama faɗa ya nufi gate.

Galala Naja take kallonsa harya sa key ya buɗe gate in ya fita.  Tabbas yau gidan nasu ba lafiya dan daga yanayin yayan nata tasan something is missing, ba haka yakeba kuma ɗazu bayan ta gama break ta shiga ɗakinta tanajin kamar sautin tashin muryar Auntyn tata cikin kuka amma batada wannan ikon na shigar mata ɗaki a wannan lokacin saboda ƴaƴanta na gidan Umman ta haneta dayin hakan, jin kamar sautin yaƙi denawa ne yasa ta fito waje dan yin tilawa dukda rabin hankalinta na akan Auntyn tata Dan haka kawai takeji jikinta ba daɗi jikinta na faɗa mata akwai wani abun sai gashi kuma  yanzu yana gaya mata wani magana wai karta shiga ɗakin harsai ankirata kuma itada mai ɗakin bata taɓa yimata shamaki ba. Ajiyar zuciya ta sauke jiki a saɓule ta nufi palon tayiwa kanta matsugunni a kujerarda tafi kusa da saitin ɗakin Auntyn tata.    a ƙalla tayi awa guda zaune bataji motsin komaiba dukda haka bata ƙosa ba, saima gyara zamanta da tayi a haka har bacci ya kwasheta tana daga zaune.

   BINAZIR

iya azaba ta gansa dan rashin imani da tausayi sosai Samir ya nuna mata tun tana iya ambaton Allah a zuciyarta har ta kasa saidai kawai girgiza kai da tauna leɓe a haka wani wahalallan bacci yayi awon gaba da ita. Cikin baccinne tayi mafarki yana ƙoƙarin kusantarta, hakan yasa ta farka a matuƙar razane tana zare idanunta, ganin ba kowa a ɗakin yasa ta saki ajiyar zuciya yunƙurin miƙewa tayi amma ina wani azababben ciwo da taji a ƙasanta yasa ta runtse idanunta haɗida komawa kwanciyarda take idanunta na ɓulɓulo wasu sababbin hawaye na azaba da takaice ga wani irin tsoronsa haɗida tsanarsa daya shiga zuciyarta. saida ta samu wajan ya daina zugi sannan ta lallaɓa ta miƙe a hankula ta jingina da jikin allon gadon.  Cikin dasashshiyar murya ta fara ƙwalawa Naja Kira amma ina sautin muruyar baya fita, wani hawayene na takaici ya zubo mata, ganin kukan bazaiyi mata maganiba yasa a daddafe ta lallaɓa tana dafa bango cikin azaba ta nufi cikin toilet, ruwa mai zafi ta haɗawa kanta ta zuba antibiotics a ciki sannan ta shiga ciki, idanunta ta runtse haɗida sakin wani ƙara sakamakon wani azaba da taji a ƙasanta amma hakan ta jure ta shiga ciki, saida taji ruwan ya huce sannan ta fito daga ciki kuma ba laifi taji daɗin jikinta, wani ruwan ta ƙara haɗawa saida tayi sau kusan biyar sannan tayi wankan tsarki haɗida wankan sabulu ta fito, ba laifi taji jikin nata da sauƙi amma ba duka ba, tun daga kan bedsheet inda ke kan gadon ta tattaro duka harda kayansa daya bari da nata ta naɗosu ta wurga cikin toilet, pilo kawai ta zare daga ciki a haka ta kwanta kan gadon ba ko shimfiɗa sai tsurar katifa, ko kaya bata saba sai towel in jikinta a haka ta kwanta akan gadon sakamakon wani jiri dake ɗibarta.

Naja ce ta farka a firgice dan ji tayi kamar Auntyn ta kira sunanta, agogon ɗakin ta kalla, ganin shabiyu na rana yasa ta miƙewa kai tsaye ɗakin nata ta nufa cikin sauri. 

a kwance ta sameta tana nishin zazzaɓi, da azama ta ƙarasa bakin gadon tana kiran sunanta a hankali.

Jin Muryar Naja yasa ta buɗe idanunta da suka canza kala cikin azabar ciwo tace "Naja'atu haɗamin tea zansha".   da sauri ta amsa ta fita cikin minti kaɗan ta kawo mata tea sai tururi yakeyi, ita ta taimaka mata ta miƙe zaune sannan ta bata tean, ba kuma laifi tasha sosai dan tasha fiyeda rabin kofin sannan ta miƙa ma Naja ta gyara kwanciyarta tana rufe idanunta bacci ya kwasheta.

Ajiyar zuciya Naja ta sauke tareda buɗe wardrobe in kayanta inda taga tarin zannuwan gado, wani duvet ta ɗakko ta rufe mata jikinta dashi sannan ta ɗauki cup in ta nufi kitchen.

 Yana zaune shiru a cikin motar operation insu bayan sallar Azahar ya haɗa kai da gwiwa, abin farin cikine ya samesa a yau in a cikin office insu but Sam ji yake jikinsa ba wani daɗi dan har bakinsa ji yake yayi loosing appetite , sai yanzu yake cikin complete sense insa na abinda ya aikata a yau he just do it out of his mind and he blame nobody but her, Sam batasan maganganunda zata dinga faɗa masa a matsayinsa na mijinta ba, shi kuma yanada matuƙar sanyin hali but when it comes to dignity he even lost his mind not only temper amma yanzu yana regretting abinda yayi matan so yake kawai yaje gida a yanzu but yana tsoron abinda zaije ya gani.

Ajiyar zuciya ya sauke jin an bubbuga glass in motan, buɗe motan yayi ya fito ya nufi cikin Headquartern ba tareda ya kalli wanda ya ƙwanƙwasa motan ba.

 Iya jigata ta jigata ga zafin jiki gana zuciya ko hannunta bata iya ɗagwa sosai, sallah ma daƙyar ta iyayinta a zaune tareda taimakon Naja, a haka har akayi la'asar ba abinda yake iya shiga cikin sai ruwan tea, da la'asar data sha tean sai kuma amai, haka magungunanda Naja ta siyo mata tana sha sai amai, duk tabi ta jigata, dan akan sallayar ma ta kwanta a ƙasa, Naja kam ji take ciwon kamar a jikinta yake dan wani lokacin idan ta kalli Auntyn nata har wani ƙwallan tausayi take sharewa burinta kawai Ƴaƴanta ya dawo, gashi ta nemi wayan Binazir in ta rasa.

Suna a haka tana jiƙa towel a ruwa tana shafawa Auntyn tata taji alamun shigowar Yayan nata, duk da matsuwar da tayi na yayan nata ya dawo saita kasa miƙewa taje garesa saboda ta fahimci Auntyn tata najin daɗin yadda take matan.

Da sallama ya shigo palon, jiki a sanyaye jin shiru ba a amsa ba, ya nufi ɗakinsa dan watsa ruwa amma sai yaji ya kasa samun sukuni, ba tareda wani nazari ba ya nufo ɗakinta, tsayawa yayi yana kallon kan gadonda ba wani shimfiɗa a kansa balle mutum, idanunsa ya fara wurgawa cikin ɗakin daidai sanda Naja ta miƙe dan sako wani ruwan gaishesa tayi tareda yi masa sannu da zuwa     

"Me ya faru?" ya tambayeta tareda kai idanunsa inda yaga ta tashi

"tun da safe Aunty take kwance ba abinda takeyi sai amai kuma ta kasacin abinci" ta faɗa kamar ta saki kuka   kallonta yayi na wani lokacin, sai kuma ya tako ya karɓi abinda ke hannunta idanunsa a kan Binazir dake kwance tana bacci.

Ganin hakan yasa Naja fita daga ɗakin gaba ɗaya.

A hankula ya tako inda take kwance, hannunsa yakai ya taɓa jikinta da sauri ya zare hannun haɗida ɗan buɗe idanun nasa sosai a kanta sakamakon zafinda yaji jikin nata ya ɗauka kallon fuskarta yakeyi cikin tausayi da danasani, hijabin jikinta ya cire a hankula dan ta samu iska ya shigeta. Toilet inta ya nufa dan shanya towel in hannunsa, anan ne yaci karo da kayan kan gadon, ba tareda ɓata lokaciba ya tattare hannun rigarsa don wanke kayan, sanda yazo kan rigarta kam tsayawa yayi tareda ɗaga rigar sama yana kallon yadda ya wulaƙanta ta, numfashi ya furzar haɗida ci gaba da wanke kayan, yana zuwa kan zanin gadonne yaga wayarta da saura kaɗan takai ƙasa, ɗaukar ta yayi ya dawo ɗakin tareda ajiye ta kan mirror ya koma toilet Dan cigaba da aikinsa, bedsheet in ya ɗauka da niyar wankewa, anan yaci karo da mummunar ta'asar da yayi mata, idanunsa ya runtse na wani lokaci sannan ya girgiza kansa tareda cigaba da aikinsa, saida ya wanke komai tsaf ya shanya ya gyara toilet kana ya fito, wardrobe inta ya buɗe yana dubawa, anan yaci karo da tarin bedsheets inda ke jibge waje guda 

Wani zanin gado mai laushi ya ɗakko tareda shimfiɗawa akan gadon, ba tareda jinkirin komaiba ya cicciɓeta ya ɗora akan gadon har zuwa lokacin kuma jikinta zafi ɗau, bayan ya kwantar da ita ne ya zauna a gefenta tareda kallonta, daga cutar yini ɗaya har ta rame tayi wani haske kamar ba jini a jikinta.

Sallamar Naja ce da tayi daga bakin ƙofar ta katse sa, Ajiyar zuciya ya sauke tareda bata umarnin shigowa ciki.

Ruwan tea ne mai zafi mara madara sai zallar kayan ƙamshi dake tashi a ciki ta kawo da faɗin "Yaya ko zata sha wannan tunda shi ba madara" ta faɗa sanda take ajiye trayn kofin shayin a gabansa bata jira amsar saba tayi saurin ficewa a ɗakin.

Saman kansa ya shafa tareda maida kallonsa gareta, kamar almara daidai lokacin itama ta buɗe idanunta da basu sauka a ko'ina ba sai cikin nasa idanun, a wani irin zabure ta ja baya tareda tashi zaune tana kare jikinta da hannuwanta idanunta a kansa sai faman zare idanu takeyi kamar wata mara gaskiya.

Duk abinda take kallonta kawai yake ba tareda ya janye idanunsa daga kanta ba,  Ajiyar zuciya ya sauke tareda ɗakko shayin da Naja ta kawo mata yana miƙa mata, ai da sauri tasa hannu bibbiyu ta karɓi kofin dan wani irin tsoronsa ne ya shigeta.

Sha kawai takeyi ba jinkiri, ganin zata iya illaya kanta ne ga shayin da zafi yasa ya miƙa mata hannu dan karɓar kofin, ba wani bata lokaci ta ɗora masa cup in a tafin hannunsa tana sakin ajiyar zuciya.















*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*