Free page 8
🦋🐾 *BADRIYA* 🐾🦋
A lady with concealed gender (MX)
~Storie and written by~
*~Unknown Author💅🏻📖~*
*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya😍🤲🏻*
*~PAID BOOK 300~*
~Little note!!!~
*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za'a kiyaye nagode🙏🏻*
*FREE PAGE* 8
*بسم الله الرحمن الرحيم*
9:30 daidai ta kara gyara ƙwanciyar ta tana ƙara nitsawa cikin lalausan gadon mai bala'in dadi jinta take kamar a duniyar laushi ko tace audiga a hankali aka zame lallausan bargon yamutsa muska tayi jin sanyin ac ya ratsata kamar kulya ta nannade gu ɗaya tana kara komawa baccin ta bunta,iskar da ta ratsa tafin ƙafarta ita ta sanyata bude idanunta masu cike da bacci tana budesu kamar bata so da aljannar duniyar dakin ta fara cin karo kara ware manya kuma kyawawan fararan idanunta take a dakin karamin bakin ta sake lailai masu kuɗi sun huta wannan kalan daki haka du azuci dake wannan lissafin ta karaf idonta suka sauka kan baby setting dake tsaye tana kallan ta kara wara lolo eyes dinta tayi tana kallan matar
morning ma'am your shower is ready cewar baby settings tana rissinawa
Wai danma ba hausa kikai ba cewa badriya tana kara kallan kayan dake jikin matar azuciyar ta ce dagani ba tambaya arniya ce a baiyane tace toh ni kuma na shiga uku miya haɗani da ƙedara
Ganin irin kallan da matar ke mata yasa ta kama baki tana zare ido tace nashiga uku kiyi hakuri wlhi ba dake naked ba
Matar da bata jin hausa gaba daya bata gane mi yarinyar take cewa ba dan haka ko ajikin ta saima karaso wa da tayi kusa da badriya wacce tasha jinin jikinta dan ta ɗauka dakuwa zatai amma ga mamakin ta sai taga taja hanunta har zuwa toilet a gaban babban bahon wankan suka staya inda aka fara daru da badriya ita ba mai ganin mata jiki ita bazata shiga rafin nanba dan bata iya ruwa ba ita baza ai wanchan ba ita bazatai wan can ba sai ƙananun kokekoken banza take
in matar ta tanka toh taji hausa dan ita ta bayar sangar ta ce kawai ke damun badriya irin ta yayan masu kudu,lokacin da nany ɗin tazo wanke mata kai ihun da ta dinga yi saida ɗaya daga cikin hadiman dake falo ya shigo jin ko lafiya bisa umarnin abubakar
da kuka da ihu haka nany ɗin ta wanke badriya tas kamar sabon bargo ita kanta sai taji tana jin wata fresh air na shigarta ta ko ina bayan ta yimata daurin ƙirji da sabon towel din dake bayin sai kuma ta daure mata gashin da wani towel din da ban, ita da kanta tai mata brush kan ta ce tai alola ita dai badriya ko mostawa batai ba dan bata san me matar tace da hausa ba inda gane hakan yasa ita da kanta tai mata alolar duniya sabuwa shine shine kawai abunda badriya ke cewa azuciya wai har ita akema alola gata
Bayan sun fito matar ta sata tai sallah bayan ta bata hijab ta dora kan towel din da ya saukar mata har kafa zumudi ma ya hanata yin sallah da kyau
Koda suka karasa gaban madubi badriya taga kanta washe fararan hakuranta tai tana faɗin la irin na baturiyar sabulun wanka sai kara kallan nadin kanta take a mudubi gani take kamar ba ita ba iya yau kawai tana ganin kamar an sauyata
matar ita tai mata komai hatta da saka kaya kan ta gyara mata dogon bakin gashinta wanda gyaran da ya samu yanzu ya kara fito dashi sai daukan ido yake ko da aka gama shirya ta chikin doguwar riga yar kanti pink mai farin net da kuma toms dinta shima pink da fararan kwalliya ajikin sa kasa dena murmushi da kallan kanta tai wlhi itace fa ta dawo sak irin ta tv din maman bilki kan ta lalace ina ma su biba na nan suga yadda ta dawo kamar baturiya
wata farar alkebba aka kawo aka dora mata kan kayan ta mai masifar kyau ga ƙanshi tana tayi
in kaga badriya bazaka gane ta ba tayi kyau kamar irin little princess ɗinan ta masu kuɗi
tare da nany din suka fito palo in da breakfast na alfarma ke jere du kuma dan ita,tana fitowa hadiman suka fara dukawa gaisheta cike da girmamawa ita kallan su ma take kawai da mamaki sai ta bayar ko nany suke gaisar wa dan haka ko ajikim ta ta wuce su
nany ce taja mata kujera ta ɗare sannan ta bude mata duka abincin wanda duna cin yara ne tace ta zaba bata fahimce taba dan da turamci tai maganar dan haka zuru kawai tai tana kallan kayan abincin ganin ba zata zaba ba yasa nany fara zuba mata egg da chips sai kakkauran tea sanan ta haɗa mata da sandwich sai farfesun hanta dake ta kanshi da tiriri
Kai wlhi har saida badriya ta fara tinanin kodai tabar duniya tazo aljanna ne musamman yadda taga alamun duka kayan table din nata ne ita kadai saida taci tai nak abun ta ba kama hannun yaro san nan suka koma ɗaki ta kara yin brush bisa umarnin nany kan su nufo babban falo inda su mai martaba suke
Har suka zo kofar shiga falan hannunta na cikin na baby setting ɗin tata dogarai biyu kuma a bayan su
Suma dogaran dake kofa sai da suka gaisheta cike da girmama wa sanan suka bata hannya ita ɗaya ta wuce ciki ta rasa mai yasa suke gaishe ta bayan sungirmeta koma tace wasunsu sun haifeta
a bangaran dogaran kuwa abunda yasa suke gaishe shine wannan alƙebbar dake jikin ta domun a masarautar du wanda ko wadda ka gani da alƙeba komai ƙanƙan tarsa toh ba abun watsar wa bane iya manyan masarautar ne ke sa alƙebba wato ahlin sarki kamar su sarki,ginbiya da sauran iyalan sarki na jini dan hala ganin ta da alkebba ya isa ya sanar musu cewa sudin bayin tane dan haka bata girma ya wajafta basai wani yace musu ba
da alhaj abubakar ta fara haɗuwa ta washe baki tana faɗin sabon baba dama anan kake kaima ta fada tana nufarsa ta zauna kusa dashi tana koƙarin leka fuskar sa ganin sai wani sunkuyar da kai yake baba bakaga kayan da matar nan ta samun ba kagan su ta fada tama taɓa kayan jikin tam bata damu da kin dago kansa ba da yay ta kuma cewa kuma naci abunci masu daɗi har da kwai aciki da......
gyaran muryar dataji ne yasa ta juyawa tana kallan me martaba wanda shi yay gyaran muryar yana kishin giɗe yau ba rawani a kansa farar dattijuwar fuskar sa zuwa wiyan sa yau du abuɗe suke fuskar sa mai matuƙar ɗaukan hankali itama a bayya ne take sai wani sassanyan kanshi dake tashi ajikinsa
kara wara ido tai a kekkyawar fuskar tasa wadda zata iya rantsuwar cewa bata taɓa ganin kekkyawan tsoho ko dattijo mai irin kensa ba sihirtatcen kyau ne dashi mai jan hankali duda tsufan da fuskar ta nuna a kallo ɗaya zaka hango tsantsar kau haiba kwarjini dakuma izza tattare da fuskar tasa masha allah gaskiya kakan nan nada kyau kuga madarar kyau ya ilahi badriya ta faɗa a baiyane duda ita lissafinta azuciya ta fada sai kara kuresa take da kalo har wani karkata kai take hagu da dama cike da yarinta da kuma alajabin kyau irin wannan ta lalace a kallan sa bata ma sani ba
Duda dariya ba halaiyar mai martaba bace amma ya samu kan sa da yin ta mai sauti wadda hatta abubakar saida ya dan dago yana kallan sugaban nasu cike da mamaki bawai baya dariya bane ah ah kullun fuskar mai martaba cike take da annuri wanda ko baka kirashi da murmushi ba baza ka kirasa da fushi ko bata rai ba amma dariya irin wannan daga mai martaba ba karamin abun mamaki bane
abubakar bai mutu da mamaki ba saida yaji muryar mai martaba na fadin habu ko zaka bamu waje jin sunan da mai martaba ya kirasa dashi yasan cewa shugaban sa na cikin nishadi matuka yau ɗin dan haka shima yaji salama na rastashi kan yace
Allah ya ja da ranka ya shugaba na fatan farin ciki a har abada ga adalin sarkin mu daga nan ya fice daga falon
Bayan fitar abubakar mai martaba ya dawo da kallan sa kan badriya da har lokacin shi take kallo
Murmushi yay kan ya mika hannu yana fadin zo ginbiya riya
Saida ta kalli hagu da dama taga ba wata sai ita dan haka ta washe hakori ta rarrafa ta karasa kusa da shi ta zauna a kasa kusa da kafafun sa
Bayan mai martaba ya shafa kanta yace allah yay miki albarka ƴa ta tashi ki dawo kan kujera ya fada yana nuna mata kujerar dake kusa da tashi
Nan badriya ta dawo bayan dawo warta mai martaba ya dinga yi mata tambayoyi a hikimance game da yan gidan su inda badriya baki abun magana aka samu gu nan ta fara sambado masa baya nai dallah dallah har da labarin kawayan ta da makaran tarta labarai kala kala na dariya suyi tare na kuka tayi ita daya sosai ta sake da mai martaba tana ta masa surutu zuwa lokacin shi ya gaji da magana yay mata suru sai dai ya amsa mata da daga kai ko murmushi in kashigo kaga yadda suke hira harda tafawa zaka ce anemo maka mai martaba ba wannan ba dama abunda yake nema kenan daga wajan ta yana so ya gina kekkyawar alaka stakanin su yanaso ta saki jiki dashi ta kuma saba dashi ta daukesa kamar kakan ta na jini toh yayi sa'a indai akwai magana toh badriya itace number one har kusan daya na rana suna tare zuwa lokacin bacci ya kwashe badriys a nan kan kujera mai martaba kuma ya shiga chiki dan hutawa....💅🏻
Salaam muta nan kwarai fatan kuna lafiya ya gida ya iyalai fatan kowa da komai lafiya allah yasa
Ina gamin comment din Ku da addu'oi ina godiya Sosai da sosai allah ya bar zumunci ina jin dadin yadda kuke comment 🤩🩷☺️☺️
2 pages to go fatan kun shirya 💃🏼💃🏼
_Karku manta kuyi sharing a group's group's dinku na WhatsApp nagode da kasancewar ku tare dani taku har kullun_
*The unknown author💅📖*