Last free page
🦋🐾 *BADRIYA* 🐾🦋
A lady with concealed gender (MX)
~Storie and written by~
*~Unknown Author💅🏻📖~*
*Da sunan allah mai rahama mai jin kai ina wa allah godiya daya bani ikon kawo muku wanan littafin na BERDRIYA fatan zaku Bini sannu a hankali dan jin mai labarin yake tafe dashi ina fatan yadda allah yasa na fara lafiya allah ya bani ikon gamawa lafiya😍🤲🏻*
*~PAID BOOK 300~*
~Little note!!!~
*Ban yadda wani ko wata ya juyamun labari ta kowacce irin hanya ba littafin BADRIYA mallaki nane sanan ka kaggen labari ne bata yadda zaiyi kama da tarihin ki ko labarin ki domun ban yishi dan cin zarafin wani ko wata ba do mun bada shawarwari ko wani korafi kofa abude take fatan za'a kiyaye nagode🙏🏻*
*FREE PAGE* 10
_Last free page_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
haka abubakar da mai martaba suka wuni agun salla ce kaɗai ke tada su ba wanda yaci wani abu acikin su danma allah yayi tsohon da karfin zuciya da wanime da tini an bashi gado allah ja da ran mai martaba yau ba dogarai ba kuma hadimai bodyguard din ma abubakar ya aekasu waje saboda halin da mai martaba yake shiga bai kyautu su ganiba
6:45pm agogon dake maƙale a wani gu daga cikin asibitin yabuga wanda har masallatai an soma kokarin kiran sallah inda suma su mai maitaba ke ƙoƙarin tashi suje su sallah su dawo har sun juya suka ji karar buɗe kofar ɗaki dan haka suka juya baki ɗaya suna sa ran ɗakin da aka shiga da badriya ne sun lissafa dedai dan shek ne ya fito tare da doctors huɗu abubakar ya kalla ganin yafi mai martaba juriya yace ko zaka bini office sai nama bayanin komai
kan abubakar yace wani abu mai martaba da jikinsa ya kuma mutuwa ya rigasa da faɗin muje dai baki ɗaya
ba musu suka ɗun guma har zuwa office din shek auwal saida suka zauna kanya fara musu bayani
Ku kwantar da hankalin ku ko dan ku fahimce ni sabo....
Muna jinka faɗi kawai cewar mai martaba gani yake kamar ja musu rai kawai dr yake amma badriya ta mutu
Numfasawa yay kan ya yace mun samu nasarar yin aekin lafiya kuma mun gama lafiya amma bayan ga mawar kuma an tafi da ita cikin na urar gwaji dan tabbatar da nasarar iakin inda anan aka gano wata matsala ta daban,.shuru dr ya kara yi dai shi baiyi gaba ba bai kuma yi baya ba
Ran mai martaba ya fara baci sarautar na niyar dawowa dan haka cikin asalin muryar sa mai cike da dattako da izza yace dr auwal kana ɓata mana lokaci muna da abubuwan yi da yawa agaban mu ba wasane ya kawo mu nan ba
allah ya huci zuciyar adalin sarki tuba yake mai ZA'AMOON baki ɗaya ce war abubakar
Jin yanayin da mai martaba yay magana yasa shek shiga taitayin sa san nan ya tina da wanda yake magana dan haka yace alla ya huci zuciyar ka ya ma'abocin alkairi kan cikin serious voice yace matsalar da aka samu shine komai da komai na aekin da akai mata yayi kuma ana fatan nasara anan gama amma inda damuwar take shine yarinyar ta riga da tayi loosing memory dinta baki daya wanda ya nuna hatta da magana sai an koya mata da sauran abubuwa wanda hakan yasa bazata iya tina komai game da rayuwar ta ta baya ba
Wata nannauyar ajiyar zuciya mai martaba ya sauke yana jin relief at list dai yar mutane bata mutu a hannun saba Alhamdulillah kawai mai martaba yake ta furtawa azuciyar shi na godiya ga allah ata bangaran abubakar ma hakan dama masu iya magama kance komai lalacewar biyu tafi daya iya loosing memory ne bawai rasata sukai baki daya ba wanan ma nasara ce
probability na recovery din memory dinta wanan har yanzu hanya daya muka iya gano shine idan har tayi hadari ko kuma ta samu buguwar kai sosai inba ta wadan nan hanyoyin ba har abada bazata kara tina wa da komai nata na baya ba hatta da iyayan da suka haife ta wanan shine dan haka a yanzu sai iya abunda aka fada mata aka kuma dorata a kai zata bi komai nata zai kan ce kamar na yaran da ya fara gane iyayan sane wanda daga lokacin wasu iyayan suke dora yayan su a turbar da suke ganin ta dace dashi
Allah sarki badriya allah ka yafe mun ya kuma bani ikon neman yafiyar ki data iyayan ki allah kuma ya baku ikon yafe min kuma mai maryaba yay addu'ar a zuciyar sa cike da tausayin ta yana kuma hango abunda zai faru gaba
Yanzu zamu kaita dakin hutu zuwa nan da awa uku zaku iya ganinta zamu bada magungunan ta da kuma lokacin da zata na zuwa ganin likita akuma kiyaye dokokin da za'a sa mata sai kuma wadda zata koya mata komai daya danganci rayuwa na yau da kullun,sannan kuma kunsan asalin dalilin aikin dan haka inaga wanan itace damar mu ta karshe wajan anfani da hakan dan mu maida lissafinta inda muke so dan haka mai kula da itan nai mata bayanin yadda zata tafiyar da ita, dama kuma ita mai kula da itan bangaran tane hakan karku samu damuwa zata koya mata komai da komai wanda zai kasan ce ko kiranta kuma zaku dena da jinshin mace saidai na miji dan a yanzu ita kanta bata san mine wani jinsi ba bare ta ba kanta dan haka mu zamu bata jinsin,mu kuma karkata mata lissafinta zuwa kansa dan haka matukar an kiyaye dokoki da sharudan da zaa gindaya mata to har bayan shekara biyar ta cika baza a samu wata mastala ba insha allah
hakan yayi amma damuwar a nan dr shine masarauta nata nemana kusan wata daya da sati kenan rabona da chan bansan ya suke gudanar da masarautar ba duda dai sodanjije nanan ga kuma waziri wanda masarautar ke hanunsa amma da bukatar inkoma dan na samu wani rahoto daga mutane na sannan sodanjijo ma ta fara korafin rashin dawo wata so na sanar da koma warmu nan da sati biyu bayan gama wankan badriya kenan ya kake gani ga wannan abun ya taso
Ba wata damuwa duka abubuwan za'a iya mata su cikin kwana sha hudun har ma wankan addu'ar inda daga manne za'ie mata general chekup shikenan an gama komai in kun koma sai akula da shan maganin ta da kuma ganin likita da zata nayi du bayan wata biyar
Mai martaba na godiya allah saka da alkairi cewar abubakar tare da shek suka fita zuwa masallaci sai alokacin suka samu damar komawa masaukin su inda sukai wanka sukaci abinci kan su dawo asibitin du yadda abubakar yaso mai martaba ya huta yaki
Koda karfe goma ta cika har gadon da badriya ke kwance shek ya kaisu,.tana kwance sanye da kayan asibiti light blue da sukai matukar haska farar fatarta fuskar tayi fayau kamar wadda ta kwana tana jinya kananu kuma pink lips dinta a bushe yadda kirginta ke sama da kasa shi zai shaida maka bacci take cikin kwanciyar hankali
har gaban gadon mai martaba ya karasa ya zauna a kujerar kusa da gadan kan ya kai hannu ya riko siraran yatsun hannun ta cikin nasa ya damke gam cike da soyayya da tausayinta ya kafe fuskarta da ido zuwa bakin gashi ta mai daukan ido ga stayi sosai dan har ya wuce kafadun t sai gaban goshinta inda kananun gashi ke kwance luf luf kamar kan jariri sabuwar haihuwa a bayyane yace ki yafe mun ki gafar ceni jikata haka mai maryaba ya wanzu hannun sa cikin na badriya da har lokacin bata farka ba har lokacin tafiyar masu jinya yayi suka tafi bata farka ba shek ya fada musu su kwantar da hankalim su ba wani abu bane allurar da akai matace zuwa dare ko safiya zata farka
Sanmakon fari su mai martaba sukai wa asibitin tsinke shek har mamaki da ta'ajibin lamarin yake lokacin da suka shiga tana bacci amma mai kula da ita ta basu tabbacin ta tashi da dare hat wanka tayi san nan ta koma
da mai kula da badriya da abubakar sai ahek suka fita dan tsara abubuwan dakin ya saura daga mai martaba sai badriya dake bacci ya dawo kusa da ita kamar jiya haka ya riko hannunta cikim nasa yana mata addu'a alamun motsawar hannunta dake kicin nasa yaji da hanzari ya maida kallan sa zuwa fuskarta a hankali take kifta dogayan eyelashes dinta kan ta bude idon ta duka ta sauke kan mai martaba wand shima itadin yake kallo alhdala yay a bayyane kan ya tashi ya tai maka mata ta zauna ya ruko duha hanunta biyu yana fadin sannu bardy fatan ba inda ke miki ciwo ko shuru tai kawai tana kalan sa dan bata san mi yake yi ba bari na kira liki ta fa dafa yana daukan wayarsa dan kiran shek du inda yay ko mi yayi idon ta na kansa...
A gurkuje 😂
Yau kwanan berdy 11 da yi mata surgery sannan kwana na goma da fara mata wankan addu'a wanda ya rage musu saura kwana 3 su koma masarauta a iya dan wanan lokacin badriya ta tashi daga badriya da koma *adriyan* wanda rayuwar ta ta canza baki daya tin sunan da aka chanza mata sabuwar mai kula da'ita itake koya mata magana da sauran wasu abubuwan tana magana amma ba kamar daba da take da dan banzan surutu yan zunma ba baya bace gun surutun saboda rashin sanin ma'anar wasu maganganun da kalmomin yasa bata surutun da yawa sosai harshan ta ya karshe cikin larabci da turan ci dan su aka fiyi a kusa da ita sai hausa ita sama sama ne saboda da mai martaba kadai take yinta sai ko hadiman ta in ka ganta zaka ranste ka kuma rantsewa ba mace bace do mun ita kanta bata san ita din mace bace ana miji take daukan kanta kama daga kayan sawanta da sauran kayan amfanin ta duna maza ake siyo mata san nan kowa a namiji yake mata magana da nema suke mantawa amma yanzu yabi jikinsu su kansu mancewa suke da cewa ita din badriya ce ba adriyan ba,a yanzu a jikin ta inka dauke private part dinta ba wani abu nata daya kasan ce na mata sai gashin ta wanda shima suke kokarin yage mata shi ya dawo irin na larabawan garin, takan fita wasa da sauran yaran compound din maza wanda shek ya bada shawarar haka saboda kara sanin rayuwa da abubuwa daya danganci jinsin ta sukan kaita wajan wasa shima duna maza toh sunyi nasara dan a yanzu inaga badriya sai tayi fada dadu wanda zai kira ta mace dan ita ba mace bace taya ma zata fara lissfa kan ta acikin mata bata da wani abu da zai shaida mata hakan,an yanke mata gashin amma ba duka ba tana da gashi mai laushi da santsin gaske har ya wuce fadunta inda aka yanke kusan rabi da kwata aka barmata kadan sai akai mata starin gashin irin na yan Korean wanda in aka bazashi gaba d baya zai kai har yarufe idon ta kusan wannan shiya kara bayyanar da yanayin jikin ta na maza in kaganta sai dai kace masha allah kawai a wuce gun amma zaka zata irin yaran nan yan kasar Korean ko yaran larabawa ko turawan nanne dama gata fara tas bata da jiki yar siririce bawai sosai ba amma dai kana kallanta kasan siririya ce bata da stayi sosai shekarun ta tsayin ta.
sosai suka fara shirye shiryen komawa hongkong domun sun gama komai gobe zasu bi flyt din karfe 9:00 na safe
siririyar voice dinsa mai matukar zaki ce ta kara de falon da sallama sanye yake cikin t-shirts mara hannu irn ta yan ball din nan Wanda ta bayyanar da duka sangala lan hannun sa awaje Sai cropped jeans Wanda ya wuce guwarsa da kadan kafarsa sanye cikin takalmin soso haf cover wanda yay matukar haska karamar kekkyawar kafarsa baka ganin fuskarsa saboda p-cap din daya sa hannusa sanye da Rolex watch na kanfanin BK gaba yada karamin gayen ya cika ya cike ka kirasa handsome tin kan kaga fuskarsa ma dan iya starin shigarsa da yadda fatar sa ke daukan ido zaka san gidan abun ka taras wato kyau😂ni albasa jama'a badai berdy dinmu ce haka ba dan yanayin jikin kaf natane
Cire p-cap din yay inda lallausan gashin sa wanda yasa gyara ke zube ta bayansa ya kwanta a keyarsa sai wani dan silin gashin nasa wanda ya biyo ta gefen goshinsa har zuwa wajan bakin sa yaushe aka rage kan amma har ya kara stayi kusan ragewa ta uku kenan da a kai wa gashin yanayin yadda gashin nashi ya tafi ya kwanta da gefe da gefe shiya kara fito da kyan da allah yay wa fuskaf
*badriya* kenan ko nace *adriyan* murmushi ta sakarwa mai martaba da tin shigo warta yake sakar mata nasa murmushin shima
G-pa masa'ul khair (barka da yammaci G-pa)
Mai matarba ya amasa da bikair ya hafidy (barka dai jikana)
Gpa kana hutawa abunka sosai fa cewar badriya da hausa
kaima ia haka ko baka hutawa fadan naji akwai wanda yake saka aeki ne cikin hadimai ko a waje
Ah ah nifa ban ceba ya fada yana yar dariya ganin mai martaba na kokarin rikice daga yar magana
Atoh koda naji da yanzu aga bacin raina
Mukai murmushi baki daya kan mai martaba ya fafa magana da cewa
Dama dalilin dayasa na kiraka shine kan maganar tafiyar mu kaga har yanzu ba muga iyayan kaba kuma mun bada sanar wa harkawo yau basu same suba toh inaga zan barka wajan shek anan shi zai kula dakai da komai da koman ka har zuwa lokacin da allah zai baiyana iyayan inna samu lokaci zanna kawo ma ziyara
Nidai G-pa zan bika dan allah karku tafi ku barni anan kuma ma inaso naga masarautar ka dan labarin ta yana burgeni dan allah kaji kaji karka rabu dani kamar yadda iyayena suka guje ni kai ka dai gareni kaji dan allah adriyan ya kare zancen nasa cike da rigima yana ruko hannun mai martaba yay raurau da ido yana shirin fashewa da kuka
Irin abubuwan da yake tina musu da cewa shi mace ne ke nan in ana maganar shagwaba , rigima da san jiki ko toh ka samu adriyan ka huta
Sai da mai martaba ya shafa kanshi kan yace kasan kowacce masarauta da tsarin ta so tamu inba hadimai ko bayi ba ba'a maraba da kowa sai ko yan uwa na jini dan haka bazan iya tafiya dakai can ba dan baza a barka ka shiga ba ba amma in kana so akwai hanya daya wadda itace zata baka damar shiga masarau tar har ma kana ganina ko ni ina san ganin ka inzo hanyar in ganka kuma zaka ga masarauta har ka gaji hanyar itace zan tafi dakai inda zanka zauna gidan baba habu har sai an fara daukan bayi kaima zaka shiga chikinsu daga nan in ka shigo masarau tar ni zan sa a kaika bangaran *dudo* nasan zai kula dakai san nan du sanda kake san ganina zaka zo nima in inaso zan zoo kaga shike nan ko
Farin ciki ya lullube adriyan jin za'a shiga dashi masarautar har baisan ya rungume mai martaba ba yana koro godiya
Shafa kansa mai martaba yay yana fadin dagani to mage kan kamun bacci a jiki nasan ka sarai, ai zaka zauna gun *dudo* din ko yana da tausayi da kirki nasan zai kula dakai
G-pa waye *dudo* ne kusan kullun sai kamun maganar sa sannan kuma kana yawan kiran shi a waya ko ya kira ka in nace ka bani na gaishe sa sai kaki
Dudo jikana ne kamar kai kuma shine zai kasance a kujerata in allah yasa mun koma lafiya shine yarima
Wow G-pa i can't wait to see him na farin ciki sosai zan bika
Murmshi mai martaba yay yana shafa kan adriyan yace kaita farin ciki har abada adriya shine burina
am ma a zama day DUDo dole sai ka zama mai juriya hakuri da dauriya sauran bayanan kuwa zaka jisu lokacin da aka daukeka aeki a bangaran sa so wannan hanyar ta zama sirrinmu mu biyu
Okay badriya ta fada cike da jin dadin za'a tafi da ita dan yatsanta ta dago tana kallan mai martaba da murmushi a fuskar ta tace pink promise,shima ya mika nasa suka kulla kan su wa juna murmushi
Bari naje naiwa su samir sallama cewar adriyan
Ajiyar zuciya mai martaba ya sauke bayan fitar adriyan ganin plan din su yayi aeki
ayadda sukai masa bayani shine sunce stintar ta sukai sannan kuma annemi iyayan sa anrasa suka kuma tusa mata kaunar masarautar arai sannan suka zo masa da maganar tafiya abarta suna fatan ta amince ta yadda da kanta zata bisu kuma zata yiwa yarima aeki ba tare da ta kawo komai a ranta ba wanan kenan
11:15 private jet din nasu yay landing a babban filin girji na untertoonal 3* hongkong...💅🏼
toh jama'a a nan na kawo karshan free pages
*shin ya rayuwar badriya zata kasance a masarautar ZA'AMOON*
*Shin wanene ma yarima sarkin gobe*
*Ta wata hanya adriyan zai samu shiga masarautar san nan in ya shiga shin mai martaba zai cika masa alkawarin sa na kaisa bangaran yarima ko ya abun yake*
*Shin ya zaman adriyan da yarima zai kasance*
*Sannan shin su abubakar zasu samu nasara a aikin su wanda shi yasa ma su kaiwa badriya abunda sukai mata*
*Mu dawo bangaran malan shin mi zaiyi da kudin da ya karba bayan ya sayar da badriya*
*Ina dangin mahaifiyar badriya suke*
_Da dai sauran tambayo yin ku_
*~Notice NOTICE~*
*Yar uwa duka wadan nan amsohin na cikun paid pages na badriya ki garzayo ayi dake karki bari a yi bake dari ukun 300 ki ta biya miki buka domun karin bayani ku tin tibi wan nan number *** ban da kira WhatsApp only*
_Akwai gara basar ragi ga mutun biyar na farkon yin payment wanda yanzu haka ina da mutun 3 da suka rage sai ku hanzarta_
*Sai kuma mutanan mu guda 15 wato wadan da suka lashe gara basar shiga paid group kyauta da group ya kammala zaku jiku a ciki muna da list din kowa*
Bissalam fatan zasu hutun karshan mako lafiya allah ya sada mu da alkairan wanan raya ta juma'a💫🌟
Nagode🫂🩷💃🏼
_Karku manta kuyi sharing a group's group's dinku na WhatsApp nagode da kasancewar ku tare dani taku har kullun_
*The unknown author💅📖