FANSA KO ƘIYAYYA

#26

by @109051246447263646587

FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*




_Page26 _

   Wani Private hospital daya gani a bakin hanya ya umarci mai Napep daya shigarda su.

Suna shiga aka shiga da ita lab, jininta aka ɗauka sannan akayi admiting inta tareda ɗaura mata drip.  Umma ce zaune a kusa da ita shi kuma yana lab jiran result.

Wani irin bugawa ƙirjinsa yayi sanda ya karanta result inda aka miƙomasa yanzu, a ƙalla ya karanta sau kusan goma amma duk dai abu guda yake gani, kai tsaye consultant room ya nufa ya bubbuga, izinin shiga akayi masa, bayan ya shiga sun gaisa ne yake sanarwa da likitan buƙatarsa na yanason ayiwa matarsa scanning na ciki, ba ɓata lokaci likitan ya miƙe saboda profit insane, har ɗakinda aka kwantar da Binazir yabi Samir suka tafi tare a lokacin da suka shiga drip in ya kusa ƙarewa dan an sakesa sosai sakamakon temperature in jikinta, suna tsaye ruwan ya ƙare hakan yasa likitan cikin sauri ya zare kanulan ya Umarci da ya kamota ya biyosa.

Kallon Umma yayi da faɗin "scanning za ayi mata yanzu zamu dawo"

Cikin tausayawa Umma ta kaɗa kanta da faɗin " shikenan Allah ya bata lafiya"

Rungumota yayi jikinsa gaba ɗayanta, ita dai batada ƙarfin jikin hanasa dan haka batayi yunƙurin ƙwatar kantaba a haka suka ƙarasa har scanning romm.

Gado ya nuna masa inda zai kwantar da ita, bayan ya kwantar da itanne ya zauna gefenta tareda riƙo hannunta cikin nasa ya damƙe haɗida sakin ajiyar zuciya.

 Da kanshi likitan ya shafa mata cream tareda fara scanning,

Ɗago kansa yayi yana kallon Samir daya ritsawa scanner screen idanu Kamar maison gano wani abu 

 "Lucky you aboki a living fetus of 15 days in her womb"

Yamutsa fuska Samir yayi da faɗin " yimin Yaren mutane ba naku na likitoci ba"

Dariya likitan yasa da faɗin "ka jira na baka a rubuce"

Shidai baice komaiba yana zaune har aka gama tareda printing wata takadda likitan yayi folding inta cikin envelop sannan ya miƙa masa, bai duba ba ya zura a aljihu tareda kamota ya maidata ɗakin da akayi admitting nata.

  Umma ce ta taso da sauri ta gyara mata wajan kwanciya ya kwantar da ita, cikin sauri yabar ɗakin dan sosai yakeson karanta abinda ke jikin takaddan.

Wani irin bugawa ƙirjinsa yayi ganin abinda scanning in ya ƙunsa,   yaji-yaji a cikin idanunsa hakan ya sashi runtse su wasu sanyayyun hawaye suka zubo masa, buɗe idanun yayi tareda sakin ajiyar zuciya.

Alƙibla ya fuskanta tareda ɗaga hannunsa sama yana miƙa godiya ga Ubangijin talikai daya azurtata da wannan babbar baiwar da ni'imar a lokacin da baiyi zatoba tabbas wannan wata rahama ce da arziƙi da ubangiji yayi masa ya amsa yana kuma farin ciki tareda godiya ga Ubangijin sa.

Juyawa yayi ya nufi ɗakin da sallama ya shiga lokacin har an saka mata ruwa na biyu jingina yayi da jikin bango yana kallon fuskarta da take rufe tana bacci, wani murmushi ya saki tunowa da irin artabunda za a sha idan har tasan tsaftataccen ajiyarda ya shimfiɗa a ƙasan mahaifarta. Lumshe idanunsa yayi ya buɗesu tareda kai kallonsa ga Umma dake gyangyaɗi.

"Umma" ya kira sunanta a hankali 

a ɗan firgice ta buɗe idanunta tareda amsawa

  "biki tambayeni sakamakon gwaji da scanning inda akayi mata ba" ya faɗa sosa gashin girarsa.

Murmushin su na manya tayi da faɗin "mezan tambayeka Babban mutum bayan nasan abinda sakamakon zai bada na ta samu albarka a mahaifarta" 

Waro idanu yayi yana kallon Umma "au dama kin sani?" Ya tambaya cikin mamaki

Murmushi ta sakeyi da faɗin  "tun jiya sanda tayi amai kan ta shaƙi warin kifi na gane Babban mutum shiyasa nacema lalura ce haka wasu suke fama idan Allah ya haɗasu da laulayi dan komai nasu sanjawa yakeyi, cimakarsu, yanayin abinda suke so wata ta baka tausayi wata kuma ta baka dariya, kamar dai ita wannan" ta nuna Binazir dake kwance tana bacci "naga abin nata yana buƙatar kulawa Babban mutum dan gaskiya tanajin jiki Abin tausayi dan Allah a dinga dannar zuciya komai kaga tayi kayi mata uzuri ba laifinta bane yanayine kuma da zarar Allah ya raba shikenan wani abinma idan ance tayi musawa zatayi"

Shiru yayi yana sauraron Umma tareda ajiye dukkan wani harafi na maganganunta cikin bangon allon zuciyarsa da ƙwaƙwalwar sa yana adana su, ta gefe guda kuma tsantsan tausayin Binazir ne ke malala a cikin zuciyarsa ga wani al'ámari mai girma da yayi kane kane a ruhinsa gameda ita, ajiyar zuciya ya sauke da faɗin "Umma inaji daga nan gida zamu wuce, inyaso Idan kin koma kya turo mana Naja"

"Anya Babban mutum kadai bari ta ƙara warwarewa kaga kana fita aiki"  "Umma dan Allah ki yarda kawai baga Naja nan ba zan tsara komai" ya faɗa da marairaicewa dan gaskiya bai shirya hakanba koda na second ɗaya jiya ma abinda yasa ya ƙyaleta haushin ta da yajine amma a yanzu kam sam bazai yi wannan gangancin ba.

  "Ai shikenan tunda ka kafe" Umman ta faɗa cikin sallamawa tareda miƙewa ta fita a ɗakin don shan iska.

Kujerar da Umma ta tashi ya janyota zuwa gaban gadon sosai tareda zama akai, kallonta yakeyi ba ko ƙifta ido tareda jinjina ƙudira ta ubangiji wai ƙwansa ne kwance a mahaifar ta, wani mulkin da isa saidai Ubangiji badai mutum ba, tabbas ya yadda komai bawa ya aikata ko kuma ya samu bawa to akwai wani aya da Ubangiji ya ɓoye gameda hakan.

Matsawa yayi daidai fuskarta tareda sumbatar goshinta wanda yayi daidai da buɗe idanunta, ganin mutum a kanta yasa ta buɗe baki zatayi magana kamar yasan mai take shirin yi ya maida bakinsa cikin nata bakin.

Ƙoƙarin ƙwace kanta takeyi amma ta kasa cikin hukuncin ubangiji Allah ya taimaketa ta gartsa masa cizo a leɓensa, amma hakan baisa ya ƙyaletaba saida yaji alamun ruwa a kuncinta sannan ya saketa tareda komawa kujerar da ya tashi yana sauke numfashi ido a lumshe

  "Allah ya sakamin" shine kawai abinda ta iya faɗa tareda share hawayen fuskarta daya zubo kuncinta.

Iska ya zuqa ta bakinsa ya furzar tareda buɗe idanunsa ya saukesu kan drip inda ke maƙale, da ɗan sauri ya miƙa ya cire mata kanulan ganin ruwan ya ƙare bai zaunaba ya fice daga ɗakin.  

Kanta ta juyo gefenda ya fita tareda miƙewa zaune zuciyarta a cunkushe itafa da gaske harga Allah ta tsaneshi mugun haushina takeji dan yabi yayiwa rayuwarta kane kane so yake ya birkita mata duniyarta ya hargitsata amma ta Allah ba tashiba, yana cin albarkacin mai albarka ne, banda haka da tuni shi da kansa ya daɗe da sallamarta daga gidan.

Umma ce ta shigo ɗakin da sallama hakan yasa tayi saurin share guntuwar ƙwallan daya zubo mata tareda ɗago kanta tana amsawa Umma sallamar cikin yaƙe

 "Jiki yayi kyau kenan tunda na ganki zaune" Umman ta faɗa cikin jin daɗin ganinta da tayi a zaune

murmushi kawai tayi tareda sunkuyar da kanta.

 Ɗakin ya shigo da sallama shida likita 

 "Da dai ka bari ta ƙara kwana koda ɗaya ne" likitan ya faɗa sanda suke ƙarasowa bakin gadon.

Bai kulasa ba sai kallon Umma da yayi da faɗin " za'a sallamemu ne fa Umma" 

 "Za dai ka sallameku" likitan ya faɗa yana wa Samir wani kallo

Gashin girarsa ya sosa kawai ba tareda ya ko kalli inda yakeba.

Ƙasa tayi da kanta tanajin Umma na haɗa magungunanta da aka siya mata, banda Umma na wajan da duk abinsa saita faɗa masa magana 

Koda suka iso bakin titi ji tayi Umma na faɗin  "nifa zancen gaskiya bazan biku ba, kuyi tafiyarku innaje zan turo muku Naja amma a kiyaye dai Babban mutum nasan likita ya baka shawarwari" shafa sumar kansa kawai yayi tareda tsaida wani Napep daya zo dab dasu.

da ƙyar Umma ta amince ta fara hawa dan da kafewa tayi saidai su fara tafiya saboda Jikin Binazir amma shima ya kafe da ƙyar ta amince ta fara yin gaba tareda bashi ledan magungunan Binazir tana ƙara jaddada masa ya kula da ita, murmushi kawai yakeyi tareda shafa sumar kansa, wai ya lura da ita to in Banda abin Umma da take jaddada ya lura da ita ai shi gani yake ma kamar an shiga aikinsa ne faɗamasa hakan .

Ita dai tana tsugunne batace komaiba amma zuciyarta dab take da fashewa dan ita a zatonta za ayi mata kara ace ta koma gidansu har ta warke kamar yadda taga wasu 'yan uwan Mummyn ta keyi idan ba suda lafiya saisu tawo gidansu jinya ko kuma su tafi gidan su Mummyn har sai sun warke suke komawa gidan auransu.

Tana tsugunne zuciyarta na wani wajan taji ya kamo hannunta fizge hannun takesonyi amma ta kasa hakanne yasa ta miƙe a fusace, Napep inda ta gani kusa da sune yasa ta sakin ajiyar zuciya tareda binsa ciki.

 Janyota yayi zuwa jikinsa tareda saƙalo hannunsa ta ƙugunta   "kinsan Allah kikayimin gardama tsaf zan baki mamaki a nan wajan?" ya raɗa mata cikin kunnenta, hakan yasa tayi lub a jikinsa tana shaƙar ƙamshin turaren jikinsa dayayi masifar yi mata daɗi wanda har lumshe idanunta takeyi a haka bacci ya ɗebeta.

Tsayuwar mai Napep yayi daidai da tashinta bacci amma jin ƙamshinnan yasa ta kasa ɗago kanta.

Ganin har Napep ya tsaya bata farkaba yasa yayi zaton bata farka ba, hakan yasa yakai bakinsa kunnenta tareda hura mata iska a ciki, ba shiri ta miƙe daga jikinsa tareda fita daga Napep in ta nufi gate.

Murmushi ya saki sannan ya fito traeda sallamar mai Napep shima ya nufi gate dan buɗe gidan.

 Yana buɗewa tayi saurin shigewa ciki dan so take kawai ta gasa jikinta.

************************************

Ganin har gari ya fara haske Binazir bata kira Mummy a wayaba yasa Mummy kiranata, tana fara ringing Naja dake kusa da jakar Binazir in ta zaro wayar tareda ɗaga kiran da sauri ganin mai kiran.

Gaisheta Naja tayi tareda shaida mata halinda Binazir take ciki 

"Ko kece Naja?" Mummy ta tambaya

Murmushi naja tayi a kunyace kamar tana ganin Mummy da faɗin "a nice"

  "Masha Allah" Mummy ta furta da faɗin "idan su Umman naki sun dawo kiyimin flashing"

"Insha Allah" Naja ta amsa a ladabce katse kiran Mummy tayi tareda runtse idanunta sannan ta buɗe su lokaci guda.

 Sanda Umma ta isa gida da sallama da sauri Naja ta fito tana tarbar ta ganin Umman ita kaɗai yasa tayi turus tareda leƙen bayan Umman.

 "Ba wanda zaki gani ni kaɗaice dai Naja yayanki ya kafe kan gida zasu wuce kema kiyi maza ki shirya ki tafi dan nasan tana buƙatarki a yanzu haka" umma ta faɗa sanda takewa kanta masauki kan tabarmar da ke shimfiɗe a tsakar gidan.

Shiru Naja tayi sai kuma tayi ɗaki da sauri tareda ɗakko wayar Binazir ta fito tsakar gida da faɗin 

"Yauwa Umma Zakuyi magana da naman Aunty tace na haɗaka" ta faɗa tareda danna layin Mummy, ana Kira ta ɗaya hakan yasa tayi saurin karawa Umma wayar a kunne.

Cikin mutumtaka suka gaisa sai kuma kowa yayi shiru

 "Ashe ba tada lafiya? Allah ya mayar kaffara sannan ina godiya da hidima Allah ya saka da alkairi" Mummy ta faɗi abinda keta cin ranta 

Murmushi Umma tayi tareda gyara zamanta cikin raha tace "haka zakice Allah ya inganta maganar godiya kuma ai anzama ɗaya"       

Nazarin kalamn Umma Mummy tayi, cikin 'yan sakanni ta gano ma'anar kalaman Umman hakan yasa ta zaro idanunta waje kamar tana gaban Umman da faɗin  "wai Binazir ince da ciki?" Mummy tayi suɓul da bakan faɗa wanda hakan yasa tayi saurin rufe bakinta da tafin hannunta

 "Insha Allah kuwa ƙwarai sosai sai a dinga sasu cikin addu'a itada abinda ke cikin nata" Umma ta faɗa cikin tabbatarwa.

Godiya sosai Mummy tayiwa Umma tareda kashe wayar tana jinjina lamarin Allah  "lallai ba ayiwa Ubangiji shishshigi" Mummy ta faɗa a fili dan abin yayi masifar ɗaure Mata kanta wai Binazir da ciki, ajiyar zuciya ta sauke tareda neman 'yar Uwarta Farida dan tayi mata rakiya zuwa gidan gudan jinin nata dan duba halinda take ciki.

  "Wai meya faru?" Naja ta tambayi Umma da ta gama magana da Mummy cikin nishaɗi.

"Kin kusa ki zama Uwa ko Aunty" Umman ta faɗa mata haɗida miƙa mata wayar.

Kamar an hasko mata majigin ma'anar kalaman Umma, cikin tsantsar murna da farin ciki ta juya dan haɗo wasu daga cikin kayanta.

 Ana kiran azahar Naja na bubbuga gidan.

Samir dake zaune a palone ya miƙe ya nufi gate ya buɗe mata ta shigo ciki.

Kai tsaye ɗakinda take ta nufa tareda ajiye kayanta sannan. ta ɗau ledar kayan Binazir ta nufi ɗalibta.

Lokacin fitowarta daga toilet kenan sakamakon wani zafi daya gigitata ba shiri ta shige dan watsa ruwa tareda ɗauro alwala.

Cikin kulawa ta kalli Naja da faɗin "Allah sarki Umma harta turokin kenan " 'yar dariya tayi haɗida ajiye mata ledar da umma ta bata  a gabanta

Da murna ta karɓi ledar tareda buɗewa tana ganin kayan ciki 

Wani yawu ta haɗiye da faɗin. "Allah ya tsundunaki a aljanna Naja ya Kuma nunamin ranar bikinki".

Murmushi Naja tayi tareda juyawa tabar ɗakin.

a ƙagauce Binazir ta gabatar da sallar ta anan kan sallayar ta baje tana fitoda kayanda ke ciki, baiwar Allah ji tayi yawunta ya tsinke, kamar wata zalamammiya haka ta ɗauki wata goruba tareda kaiwa bakinta ta fara ci dai dai lokacin ya shigo ɗakin, idanunsa a kanta.

dakatawa tayi da cin gorubar tareda janyeta daga bakinta, tana shirin ajiyewa ne yayi saurin ƙarasowa tareda riƙe hannunta da faɗin "kici abinki idan kina buƙatar wani zan siyo miki buhuma" ya faɗa cikin nuna kulawa 

"Uhummm" kawai tace tareda kauda kanta gefe

 " duk abinda kikeso ki sanar danizan siyo miki idan kuma akwai abinda ba kyaso a gidannan ki sanar dani" ya ƙara faɗa cikin kulawa, hakan yasa ta waigo tana kallonsa dan son tabbatarwa

 "Da gaske nake ki sanar dani"

Idanunta dake kansa ta janye tareda sunkuyar da kanta ƙasa 

"Ni banason ka da gidannan duka" ta faɗa a hankali kamar mai raɗa. 








*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*