#31
FANSA ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
_Page31 _
Tafiyar awa biyu sukayi suka ƙaraso cikin birnin Katsina wanda basu sauka a ko'ina ba, sai a unguwar maƙera.
A bakin ƙofar gidan sukayi parking sannan suka nufi gidan da ƙofarsa ke a buɗe.
Da gudu yaran sukayo kan mamansu sunayi mata sannu da zuwa, wata ƙarar farinciki Walida ta saki tareda nufar Binazir wadda dawowarta daga school kenan tayi karo da mota irin ta Auntyn ta Binazir a ƙofar gida hakan yasa ta shigo cikin mamaki sai kuma tayi farin gani
Sudai sauran mazan kallon baƙunta sukayi mata dan basu saba da ita ba sosai.
Bayan sun natsa ne Walida tayi mata gaisuwa da sauran ƙannanta maza Aunty Lubabatu ta bawa Walida key tareda umartar ƙannanta dasu buɗe motan dake waje su kwaso musu kayansu.
Bayan sallan la'asar ne taje har gidan maƙotanta dakeda wadatar compound ta nemi arziƙin ajiye motanta, ba wani uzuri suka amsa mata domin ita in ta jama'a ce.
****************************
Zaman Binazir a gidan Aunty Lubabatu zamu iya cewa zaman 'yanci ne na 💯 cos duk abinda takeso shi ake dafawa kuma kullum cikin waya sukeyi da Mummy ta layin Aunty Lubabatu, dan tun randa tazo ta kashe wayarta bata kunnata ba.**
Allah ne yake jarabtar bawa a duk sanda yaso da kuma dukkan wani nau'in jarabta mai kyau ko akasin haka, wannan shine abinda SAMIR yake ayyanawa a ransa a kowanne lokaci idan damuwa taso yimasa illa da wannan tunanin yake samun sassauci yaji zuciyarsa ta dangana tareda barin komai ga Ubangiji amma har yau akwai hoton abu biyu daya kasa barin zuciyarsa. Na farko shine lokacinda idanunsa sukayi mummunan gani wani ƙato ya zaro handkachif ya bawa matarsa ta share hawayenta da sunan lallashi kuma abun takaicin ba musu tasa hannuwanta masu aji da daraja garesa ta karɓa ba tareda ta musa hakanba irin dama already jiran hakan takeyi. Sai abu na biyu dayafi wancan ƙuntata da ɓacin rai Cikin zuciyarsa shine wannan murmushin daya gani tayi masa wanda rabonsa da ganin sa tun lokacin yana Majnun insa a wajanta and wai "Allah ya shiryeka" that words hurt him alots cos a Koda yaushe tunaninsa kan meya faɗa mata da har tayi wannan killing smile in nata tareda nema masa shiriya. ya sani komai ALLAH ne ya hukunta masa hakan and yayi alƙawari insha Allah zai daure ya cije yaga yafi ƙarfin Zuciyarsa, zaiyi iya yinsa dan ganin ya cinya wannan jarabawar. Sai kuma wani abu da ya rasa yadda zaiyi shine takura masa da Umma take kan ina Binazir ta tafi?
"To ko gidansu zata haihune? ai Yakamata ace ta dawo ɗakinta kuma idan so suke ta haihu a can ai da sauran lokaci". "Kodai kun samu matsala da itane Babban mutum?". Wa'yannan sune zantukanda take yawan takura masa a duk sanda yakaimata ziyara kuma duk sanda tayi masa tambayoyin shiru yake dan baisan taƙamaiman amsarda zai bata ba, a haka harta gaji tasa masa ido, ita kuma Naja yana hankalce da ita a duk sanda Umma tayi wannan tambayar komai takeyi bari takeyi ta bada dukkan hankalinta danjin amsarda zai bada.
Shi da kansa shaida ne yasan sun shaƙu da juna kuma suna ƙaunar junasu hakan yasa yake tausayawa Naja dan batasan mene ainihin abinda ke faruwa tsakaninsa da Auntyn tata ba.*********************
BISHIRA
A yau tana cikin farin ciki sakamakon ziyarar da takaiwa sabon amintaccen malaminta. Da fari aikin bamai yiwuwa bane dan ya tabbatar mata da aikinda takeso ayiwa Samir bazai taɓa kamasa ba saboda aikin da turare akeyinsa ita kuma ta shaida masa bata haɗuwa dashi saidai abi takan mahaifiyarsa, cikin gaggawa ta amince da ayi da sunan Umman. Wani turare ya bata daya haɗeshi da ruwan rubutunda ya buga hatimi mai ɗaukeda sunan Umma tareda jaddada mata duk sanda zata je wajan Umma ta tabbata ta shafa shi kada ta kuskura kuma wani ya fara shaƙar ƙamshin saɓanin Umman. cikin farin ciki tareda murnar samun matakan nasara tabar wajansa wanda direct gidan Umman ta nufi.
Da sanɗa ta shigo gidan tareda laɓewa a soro tana leƙe, ganin ummance kaɗai a zaune Yasa tayi saurin ɗakko turaren ta shafa a jikinta tareda shiga babu sallama, saida tazo dabda Umma sannan tayi sallama.
Riƙe kanta Umma tayi sakamakon jin da tayi ya sara mata tareda ɗago kanta ta saukesa kan Bishira, cikin fara'a umma ta amsa sallamar tareda nuna mata wajan zama.
Cikin jin kunya ta amsa mata tareda zama tana sunne kai.
"Naja bata nanne? Ko haryanzu tana gidan Yayan ne?
"Uhum" umma ta faɗa tareda taɓe baki tana faɗin "ina fa tana nan bacci takeyi kawai ai tun randa sirikin babban mutum ya rasu Naja ta dawo gida kuma tun daga ranar haryau bamu sake jin labarin matar tasa ba, kuma bayaso ayi masa maganar" Umma ta faɗa ciki takaici.
"To kodai sun rabune?" Bishira ta tambayi Umman a sanyaye kamar gaske
"Haka nafi zargi 'yarnan wallahi, Ni wallahi tausayi ma yake bani tun mutuwar mahaifinta duk yabi ya canza sai ƙarewa yakeyi a tsaitsaye wanda ko mutuwar nasa mahaifin bai shiga yanayin da yake ciki a yanzu ba"
"To Umma ki bashi shawara ya ƙara aure mana, amma zamansa shi kaɗai cikin damuwa ba mace a kusa dashi ai matsala ne"Bishira ta faɗa cikin bugawar ƙirji tareda fargaba.
Shiru Umma tayi ba tareda ta ƙara cewa komaiba, can kuma ta nisa idanunta kan Bishira da faɗin " abinda kika faɗa gaskiyane sai dai nasan wane Babban mutum bazaiyi aurannan ba saidai na tilasta masa, kuma Ni yanzu banda wadda zan bashi wallahi" Umman ta faɗa cikin kallon yanayin Bishirar.
"Ni kodan kasancewarsa ɗan'uwana zan iya sadaukar da farin cikina Umma na aureshi idan Ni nayi miki, bazanso yaya ya kasance cikin damuwa ba Umma" Bishira ta faɗa cikin raunananniyar murya kamar zatasa kuka.
"aini indai kika yimin wannan alfarmar kin gama min komai wallahi wannan ai shine soyayyar gaskiya ta 'yan uwantaka, fatana Ubangiji ya tabbatar da wannan lamarin kuma yana zuwa zan sanar masa dan gaskiya bazan bari a wani ja lokaci ba kodan halinda yake ciki" Umma ta faɗa cikin zumuɗi da farin ciki tareda sawa Bishira albarka.
Wani irin sanyine ke ratsa Bishira wanda tasan wannan sanyin na tsantsan farincikine da kusantar cikar burinta. wai lallai dolene gobe ta koma wajan malaminnan dan yimasa kyauta ta musamman bayan kuɗin aikinda ya yanka mata.
Washegari da yamma bayan ya dawo aiki da yazo gidan Umma ta taresa da zancen Bishira, ba shi kaɗaiba, hatta Naja dake zaune riƙeda wayar Umma tana trying nomban Binazir Kamar yadda ta saba, saida ta miƙe tsaye a mamakance tareda faɗin "kan Uba!" sai kuma ta kaɗa kanta tareda shigewa ɗakin, hannunta riƙeda wayar Umman. A ƙagauce ta turawa Auntynta (Binazir) saƙo sannan ta ajiye wayar tana tunani da mamakin abinda ya shiga cikin kan Ummansu da har tayi tunanin yanke wannan ɗanyan hukuncin haka.
Shikam kamar saukar aradu yaji zancen, duk da yanayinda ya shiga bai nuna a fuska ba, sanda Naja tayi zagine ya ɗago kansa tareda kallon yarinyar harta shige ɗakin yana Binta da kallon tausayi tareda tausayawa kansa. Shida ita sunyi tarayya wajan ƙaunar abinda bai damu dasuba tunda harta zaɓi rabuwa dasu..
Ajiyar zuciya ya sauke tareda miƙewa yanayiwa Umma sallama ba tareda ya tofa ko 'a' a zancen auranda takeson rakito masa ba haka ya barta cikin bawa zancen nata rashin muhimmanci.
"Kadaiji na faɗa maka a to dan bazaka zauna kai kaɗai ba mace ba kana cikin damuwa nasa maka ido kawaiba Babban mutum, dolene a wannan karon ka amshi Bishira tunda ta furta da bakinta zata aureka dan kawai ta cireka daga cikin damuwa, kai inba ɗanuwa na jiniba wace zatayi maka wannan ƙoƙarin da sadaukarwar Dan kawai ka samu kwanciyar hankali?" Sune kalamanda Umma ta rakashi dasu harya bar gidan tana maimaitasu.
************************************
A yau ta samu sassaucin mutanen gidan da hayaniyar yaran sakamakon ƙanwar babansu datazo ta tafi dasu kasancewar bikinda suke dashi a danginsu, gidan shiru daga ita sai Aunty Lubabatu dake shirin leƙawa gidan bikin itama anjima idan Walida ta dawo daga school, hakanne yasa ta ta miƙe ta shiga ɗakinda suke kwana ita da Walida, ta jima tana jiran irin wannan ranar da zata samu kaɗaici dan yaran Aunty Lubabatu akwai saurin sabo dason mutane, da farko ne zasu nunama baƙunta amma idan ka kwana aikam saika kusa yin kuka saboda takura da surutu.
Akwatin data danna File in marriage contract inta ta buɗe ta ɗakko tareda zama kan katifa. Da bismilla ta buɗe tana kallon takaddun ciki, masu rubutu kala biyu dana Dady da kuma wani baƙon rubutun.
Ajiye na Dady tayi a gefe ta fara karanta ɗayan.
" Nayi baƙin cikin kasancewar abu guda ɗaya Alhaji Mani Cizo, kasancewar Binazir jikinka ce, hakan har kusan ciwon zuciya ya sakamin. Tun randa na ɗora idanuna akan 'yarka Binazir, naji wani al'amari mai girma ya shigeni gameda ita, amma saina ajiye lamarin dan gabatar da aikina kada na yaudari kaina duk da tunaninta na acikin zuciyata. Allah mai hikima kuma Alimussir ne shi, saiya janyo hankalinta gareni harta san da wanzuwata a wajan. Sanda ta fara nazarta ta a ƙofar gidanka abu biyu ne ya ziyarci zuciyata farin ciki da baƙin ciki, a ranar har ji nayi inama ba ta wannan hanyar Allah ya hukunta abincina yakeba da zan fuskanceta ne da dukkan zuciyata amma banda wannan ikon, hakan yasani cikin matuƙar damuwa, tun daga nan nasan Allah ya ɓoye wata buwayarsa akanmu.
A duk sanda tazo gareni nakanji na tsani kaina sainayi kamar ma zan ajiye aikina amma tuna girman alƙawarinda na ɗauka kafin nakai wannan matakin ke dakusar dani da kuma babban dalilinda yasa aka bani aikin naka dan binciko wani laifi mai girma da aka aikatamin wanda kaine silarsa Alhaji Mani.
Nayi iya yina ganin Binazir ta gujeni Amma ta kasa fahimtar hakan wanda ni kuma hakan ba ƙaramin raunana zuciyata da tunanin yakeba na abinda zai biyo baya.
A randa na gama tara dukkan wani hujjojina a kanka nayi kuka kukanda ban taɓa yin makamancinsa ba kuma a jikin gidanka nayi wannan kukan dan a ranar Binazir tazomin da albishir na zaka amince a kula da lafiyata, a haka cikin damuwa da ƙuncin zuciya na tuno muhimmanci abinda ke gabansa, na rarrashi zuciyata na gabatar da aikina a kanka, daga ranar kuma Allah ya ƙara linka girman al'amarinta dake zuciyata wanda ko isasshen bacci bana samun yi. Kwatsam randa naje bincike ɗakinka alokacin na haɗuda abinda nake fafutukar nema, Alhaji Mani Naga diamond wrist chain inka wanda aka rubuta 'MANI CI...' Karashen Kuma Yana wajena mai harafin ' ZO ' yana wajena wanda na tsincesa a tafin hannun ƙanwata NAFISA (NAFI) sanda akayi yunƙurin keta mata haddi."
"Kai ina! Ƙarya ne!"ta faɗa a kiɗime tareda girgiza kai haɗida ajiye file in a gefe ta dafe cikinta sakamakon wani irin juyawa da cikin jikinta yayi mata "
"KETA HADDI?". ta faɗa a fili cikin Muryar raɗa tareda runtse idanunta Zuciyarta na mata wani irin bugawa da ƙarfi. Ganin iface ifacenda takeyi baida wani ma'ana, indai harba jin ƙarshen wannan bahagon ƙagaggen rubutaccen labarin tayiba bazata ƙara samun wani sukuni a zuciyarta ba, hakan yasa ta buɗe idanunta tareda kallon File in Kamar mai nazarinsa, cikin juriyar ciwo ta ɗauki file in a tsorace .
"Naji ciwo na kuma yi dana sani sosai nayi kuka nayi jinyar zuciyata, ban isa na goge rubutacciyar ƙaddarar da ubangiji ya rubuta tun kafin wanzuwar magabatanmu ba, amma hakan bazai goge ɗacinda ke cikin zuciyata ba.
A koda yaushe burina na gano wanda yayi yunƙurin ketawa ƙanwata haddinta, wanda ta sanadin hakan aka turoni wajanka kan na gudanarda bincike a kanka wanda nasarar hakan aka alƙanwarta bani cikakken iko don gano makashin ƙanwata sai gashi a lokacinda ban zataba ban kuma yi tsammani ba, Allah ya bayyana min hakan.
Bakayiwa Binazir adalciba Alhaji, ka cuci rayuwarta, yarinyarda batasan komai da kowaba sai tsantsan ƙaunar mahaifinta, itace wannan mahaifin zai barwa mummunan tabo a rayuwa?
Ka cuci mutane da dama Alhaji, babban burina Allah ya bayyana min wannan ranar amma ina mai baƙin cikin kasancewar wannan ranar dan bazan iya ƙwatarwa NAFISA haƙƙinta ba saboda abu guda BINAZIR idan har na tuhumeka akan hakan banyiwa soyayyarta adalci ba, saboda ita kaɗai Alhaji, saboda ita zan munafurci ahalina dana haramta musu faɗar sunanta harsai na nemo wanda yayi sanadin shigar mu cikin ƙinci da damuwa amma ba yadda zanyi wata fuskar tafi ƙarfin mari na haƙura na kuma janye dukkan wani ƙudurina akan lamarin saboda BINAZIR Kuma kaf duniya ita kaɗaice ta isa ta kuma kai nayiwa wannan alfarmar saboda ita kaɗai Alhaji Mani na haƙura. saidai zan Barka ne kaida ubangijinka ka nemi yafiyarsa ka kuma yawaita istigifari dan Allah baya yafe haƙƙin wani amma yakan sassauta lamura su zama masu sauƙi ga bawa idan ya ƙasƙantar da kansa ya kuma kusanta kansa garesa.
A matsayina na siriki mai neman auren 'yarka ina neman daka amincewa buƙata ta ta auran Binazir, badan wata manufa ba, saidan a kowanne daƙiƙa n rayuwata tun bayan haɗuwarmu hakanne burina da fatana, ban tilastaka ba Alhaji kada kuma kayi dan wani alfarma dana taɓayimaka, idan har Kanada wani wanda ka zaɓawa BINAZIR zan rarrashi zuciyata zan haƙura koda hakan zai zama sanadiyar numfashina amma ina ruƙonka da Allah Alhaji ka bani auran 'yarka, ina sonta zan riƙeta amana, zan mutumta ta, zan kuma ƙare mata dukkan wani haƙƙi nata daya wajaba a kaina Insha Allah, BINAZIR ita kaɗaice burina da fatana a rayuwa, bazan ɓoye maka ba, rabuwata da Binazir daidai yake da rabuwa da wani ɓangaren jijiya da tsoka a cikin zuciyata.
Idan har ka yarjemin da zama siriki gareka, inaso kabar aurannan ya kasance a matsayin auran yarjejeniya ga Binazir dan hakane kaɗai zai bata damar fitarda wani ɓacin rai nawa da take ganin nayi mata ba daidai ba amma indai tasan da hakan zuciyarta zata kasance cikin azaba biyu, na abinda ka aikata gareni da kuma laifinda kake kansa a yanzu za kuma ta kasance cikin muzanta da tsanar kanta. inaso kuma wannan abin ya zama sirri tsakanin nida kai, bana buƙatar kowa yasan da hakan, ina fatan kuma zaka amsheni a matsayin sirikinka".
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*