#32
FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔
*©️AuntiMamee*
_Page 32_
Wani irin murɗawa cikinta yayi wanda yasa tayi saurin dafeshi da hannunta guda, idanunta ne sukayi jaaa sakamakon kukanda keson zuwo mata amma ta hana faruwar hakan, dan ba yanzu takeso tayi shinba, so take saita karance dukkan wata ƙwayar takadda sannan ta bawa zuciyarta damar zartar mata da dukkan wani hukunci da ya kamata. so take ta daure amma hakan ya gagara sakamakon wani irin riƙewa bayanta da ƙugunta sukayi, amma haka ta daure tana girgiza kai haɗida cizon leɓenta cikin azabar ciwo tunanin rubutun Samir ne keson faɗo mata Cikin zuciyarta, amma tayi saurin kauda hakan dan ba yanzu takeson wannan hukuncin ba.
tana a haka har taji ciwon ya lafa sannan ta sauke wani ajiyar zuciya haɗida ɗakko takadduna ke ɗauke da rubutun Dady tana kallonsu gabanta in banda bugawa ba abinda yakeyi, ambaton ALLAH tayi tareda runtse idanunta ta buɗesu sannan ta fara karanta na Dady.
"Jamila! Wannan rubutun wake kaɗai nayi shi, tabbas nasan na cutar da zuciyarku keda Binazir banyi muku adalci ba na janyo muku abin kunya amma ina mai neman yafiyarku bisa hakan ina neman alfarmar ku tayani da addu'a wannan al'amarin ba ƙagagge bane rubutaccene tun kafin haɗuwata dake Allah ya rigada ya hukunta hakan.
Na umarceki daki fara karanta ɗaya takaddar ne dan kifi fahimtar nawa rubutun.
a wani tafiya da nayi na haɗu da wani iftila'i, wani abokin kasuwancin yake shaidamin irin kasuwanci da yakeyi mai kawo mahaukatan kuɗi, da fari naƙi amincewa har nake masa nasiha da nuna ɓacin raina kan yadda zaimin maganar da bata kamaceni ba, amma cikin hukuncin na Ubangiji da bawa bai isa ya tsallake ƙaddara saba, kuma koda yaushe yana kwaɗaita min hakan inda yake tabbatarmin ina safararsu da zarar munje Nigeria ko awa ba zasuyi a hannunaba za'a siyesu haka na yarda sheɗan ya cigaba da ƙawatamin irin ribarda ake samu take, kasancewar mun riga da mun saba da ma'aikatan immigration sai Allah ya hanesu da duba kayana yadda Yakamata dan Allah ya rigada ya ƙaddara faruwar hakan gareni. bayan mun dawo gida ne a ranar ya shirya mana zama da masu siya.
A wata unguwa mai ƙarantun gine-gine dan bansan unguwarba nadai je gidansa ne daga nan muka tafi. A lokacin ƙaddara ta biyu ta riskeni, muna cikin kasuwancin danni bansan ya akeba na barwa abokin kasuwancin nawa yayi mana ciniki, suna cikin buga harƙallane aka kirasa a waya hakan yasa ya miƙe ya ɗan matsa nesa damu dan amsa kiran kwatsam sai mukaga wata budurwar yarinya ta biyo ta inda muke tana dubedube kawai sai mukaga ta shigo ɗan gininda muke ciki, da sauri muka miƙe a firgice muna kallonta dukda itama a firgicen take kallon namu.
Masko mai siyan kayan namu da daidai lokacin ya shaƙi hodar bamu ankare ba, sai ganinsa nayi ya nufi wajan yarinyar da tsoro ya hanata motsawa, kai tsaye kanta ya nufa cikin'yan sakkani harya kaita ƙasa tareda yaga mata kaya yana ƙoƙarin ƙeta mata haddi, ganin hakan da nayine yasa nayi kansa da sauri ina ƙoƙarin ɗagata daga jikinsa wanda har kusan kokawa muka farayi dashi ya watsar dani ƙasa ya nufi kanta, nima a fusace na miƙe nayi kansa ina ƙoƙarin ɗagasa daga kanta a lokacin yarinyar da ko ihu ta kasayi sai girgiza kai da takeyi idanunta a waje ta riqemin hannu na da dukkan ƙarfinta daidai nan abokin nawa ya dawo daga wayar cikin mamaki yake kallonmu, kwatsam sai mukaji ƙarar waya a jikin yarinyar hakan yasa mukayi yunƙurin barin wajan tareda kwasar kayanmu, amma ta riƙemin hannu waigawa nayi ina kallon yadda takemin kallon neman taimako numfashinta nayin sama amma saboda tsoron kar wani abin ya biyo baya yasa na fizge hannuna data riƙe nayi waje da sauri dan sauran harsun fita kuma a motar abokina mukazo.
Inaji ina gani nabar yarinyar da Binazir zata girmeta cikin mawuyacin hali, nasan kuma wannan kuskuren da na alkata shike bibiyata ta wannan lokacinne kuma ta samu wani yanki na wrist chain ina, amma da gaske Jamila ban aikata abinda yake zargi akaina ba, ba kuma zan taɓa musawa ba, tunda mai bada shaidar bata raye Allah ya amshi abinsa zan barshi a hakan tunda nasan Allah bada hakan yake kallonaba, fatana kiyimin addu'a ki dinga nemamin yafiyan kuskuranda na aikata wajan Ubangiji, Ga Binazir ki riƙeta amana ki kuma cigaba da ɗorata kan tarbiyar da kika bata Jamila.
Ina baki haƙuri kan laifinda na aikata kiyi haƙuri.
" Ma ramaita izramait....... " Shine abinda ta iya faɗa daidai sanda wani azababben ciwo ya murƙusota ba tareda ta shirya ba ta saki wani ƙara wanda ya jawo hankalin Aunty Lubabatu tayo ɗakin da sauri, kanta ta nufa tana kiran sunanta amma ina ciwo yaci ƙarfin ta, da sauri ta lalubi inda ta ajiye mukullin motan Binazir ta fita dan ɗakko motar a maƙota, cikin minti uku ya dawo tareda rungumo Binazir, suna shirin fita ne Walida ta shigo da sauri ta jefar da jakarta tayi kansu.
A back seat ta kwantar da ita Walida ta shiga wajanta, sannan ta koma ɗaki dan ɗakko takaddun awonta ta dawo.
Wani Private hospital ta kaita cikin gaggawa aka karɓeta tareda yimata VE ashe harta kai fully, minti biyar batayi cikakke ba ta santalo kyakykyawar 'yar budurwa.
Zo kuga murna wajan Walida da mamanta, da shike haihuwar bata wani jigata ba, basu jimaba aka basu sallama suka dawo gida
Koda suka koma gida Aunty Lubabatu kam Bata zauna ba, duk wani abu daya kamata ayiwa mai jego shi tayi, kama daga wanka da gyara baby, haka ta aika Walida maƙota ta shaida musu 'yarta data zo da ita daga Kano ta sauka.
Sai dare Aunty Lubabatu ta kira Mummy tareda yi mata kyakyawan albishir tana faɗa mata idan tanada nomban Samir ko wani nasa ta kira ta sanar musu haƙƙinsu ne su sani. MUMMY Dan murna ji tayi kamar ta biyo hanya a lokacin amma bazata iya hakanba, dan tasan 'yarta na inda ya dace ba algus.
Nomban Umma da Binazir ta taɓa tura mata tun suna tareda Samir ta lalubo ta kira.
Bugu guda Umma dake zaune tareda Bishira zaman jiran Samir ya zo sakamakon kiranda tayi masa wayarta tayi ƙara.
Da sallama ta amsa, cikin dattako Mummy ta gaidata tareda shaida mata abinda ke faruwa.
Shiru tayi na wani sakanni sai kuma ta numfasa da faɗin "Barka Allah ya raya abinda aka haifa" qit saita kashe wayan ba tareda ta tambayi jinsin abinda aka haifan ba.
Da kallon mamaki Mummy tabi wayar nata baki buɗe "ikon Allah" ta faɗa a fili, sai kuma ta kaɗa kai ta fara kiran 'yan uwanta tana shaida musu amma yanayin yadda sukayi da umma ya bata mamaki, ganin abin zai zame mata damuwa yasa ta tattara ta watsar tareda cigaba da murnar samuwar jikar tata.
"Lafiya Umma na ganki haka?" Bishira ta tambayi Umma cikin nuna tsantsan kulawa.
"Uhum" Umman ta faɗa "wai matar Babban mutum ce ta sauka wai ɗazu shine nace Allah ya raya to inba hakaba maizance, ai sunsan dole duk mijinda matarsa ta tafi da tsohon ciki zai shiga damuwa amma suka goyi bayan 'yarsu shiru kinji abin takaici ashe sunada nambar wayata basu taɓa nemana ba sai yanzu" Umman ta faɗa cikin takaici.
Wani irin bugawa ƙirjin Bishira yayi amma da yake tana ganin ta riga ta kama Umma a hannu, sai ta watsar da fargabarda keson shigarta da tambayar Umman "yanzu zuwa za'ayi gidan nasu?" "Lalalala!". Umman ta faɗa tareda karkaɗa yatsanta manuniya, "uwar Tata fa haka tacemin tana Katsina acan ta sauka, to mai zanje nayi musu? ai suna sane suka kai 'yar tasu can sunsan zai damu ai suka ɓoyeta sai yanzu zasu wani aiko ta sauka? To Allah raya" Umman ta faɗa cikin takaici.
Naja ce data gama tatar gasara ta shigo cikin ɗakin, saida ta watsawa Bishira harara dukda ba ganinta takeba sannan ta tambayi Umman "Allah yasa dai magauta basu taɓa mana lafiyarki ba dai Umma a dai tsaya wajan cusa kan da ba kwarjini"
Wani irin murmushi Bishira ta saki tareda zaro wayarta tana danne danne a ciki.
"Magauta kuma a ina?" Umman ta tambaya cikin rashin gane zaurancen Najar.
"Umma gani nayi tunda aka fara nane miki abu kaɗan kiyita faɗa, Ni Bama wannan ba, meya faru naji kamar kina masifa?" Najar ta tambaya tareda ƙara kallon ɓangaren Bishira ta watsa mata harara.
"Wai matar Babban mutum ce ta haihu ɗazu shine uwar ta kirani a waya take faɗa min"
Shine zancen da ya kusa tarwatsa zuciyar sa daidai lokacinda ya shigo ɗakin, kalamanda suka sashi dage saitin zuciyarsa ba tareda ya shirya hakan ba.
"Umma wai Aunty Binazir ce ta haihu amma kike ta sababi?" Naja ta faɗa cikin farinciki da mamakin Sabon halin umman.
"To idan banyi sababi ba mezanyi? Sai yanzu sukasan damu? ai ba Katsina ba ko anan kanonne ko taake bazanyi ba ato" Umman ta faɗa idanunta kan Naja.
Kasa jure tsayuwar yayi hakan yasa ya shigo ɗakin da sallama murya a matuƙar sanyaye daidai sanda Naja take ƙoƙarin shiga uwar ɗaka cikin Muryar takaici tana faɗin "gaskiya Umma anjiƙa an wanke anbaki kinsha kuma an barbaɗa miki kin taka"
Da sauri Bishira da takasa danne haƙurinta ta ɗago kai danyiwa Naja nata gugar zanar taji daddaɗar muryarsa, hakan yasa ta maida idanunta garesa sanda yake shigowa ɗakin tareda gyara zamanta.
Itama Naja da sauri ta dakata da shiga ɗakin ta dawo garesa cikin murna tareda zama kusa dashi.
"Sannu Babban mutum anya kuwa ƙalau kake?" Umman ta tambayesa cikin kulawa ganin yanayinsa.
"Lafiya" ya amsa mata a taƙaice
"Ina fa lafiya anan Babban mutum! Yarinya kamar mayya tun sanda ta tafi kamar wadda ta tafi da kurwarka gaba ɗaya ka canza.…..." Dan Allah umma abar maganar nan haka" ya faɗa muryarsa da sirkin ɓacin rai.
"Yaya mai aka samu?" Naja ta tambaya cikin zumuɗi
Ajiyar zuciya ya saki tareda kama hannun Naja cikin nasa hannun dan dagaske yana tausayawa ƙanwar tasa, "zan faɗa miki" ya faɗa cikin sanyi.
"Meya sani dazai faɗa miki?" Umman ta faɗa cikin takaici.
Shiru ɗakin yayi ba wanda ya ƙara magana.
"Ina wuni yaya" Bishira ta faɗa cikin kissa da iyayi. Shiru yayi asalima nunawa yayi kamar baisan da wanzuwarta a wajanba
"Ana gaidaka, dama kiranda nake makane tanata zuwa kuna samun saɓani shiyasa nace gaskiya dai Yakamata yau ku haɗu ko kwa fara fahimtar juna" Umman ta faɗa cikin Muryar rarrashi idanunta akan Samir.
Gashin girarasa ya sosa tareda kallon Umman da tambayar "ki faɗawa Naja abinda kuke buƙata saita turamin ta waya ina jira zuwa safe" yana gama faɗa ya miƙe yabar gidan.
Ƙasa dakatar dashi umma tayi sai baki data buɗe tana kallonsa cikin mamaki.
Naja kam da tun fara zancen ta ƙurawa yatsun ƙafarta idanu tana jiran amsarda yayan nata zai bada tareda fargabar kada shima an mallakesa, jin amsarsa da fitarsa yasa ta sakin fiton da batasan ta iyashiba tareda miƙewa ta shige ɗaki tana waƙar "a banza, a banzazza"
Ƙwafa Umma tayi cikin takaici tareda sakin numfashi, zuciyarta fal tausayin yadda Samir yayiwa Bishira.
"Zan tafi umma saida safe" Bishira ta faɗa sanda ta miƙe, kafin Umma ta ankare harta kai bakin ƙofa.
A ƙofar gidan ta tsaya tareda sakin wani irin huci, tabbas indai ta samu auran Samir saita wulaƙanta Naja fiyeda tunanin mai zato, shi kuwa taci alwashin saiya zama abin kwatance a dangi dan duk wani wulaƙanci da jan ajinda yake mata saita rama. Saida ta daidaita nutsuwarta ne ta fara tafiya a hankali dan cuwonda taji kanta nayi mata.
Umma kuwa shiru tayi tana tunanin abin duniya da mafita.**************
Da dare bayan kowa na gidan Aunty Lubabatu ya kwanta ciki harda baƙuwar halittarda sukayi wadda ke numfashi gwanin ban sha'awa, sai a lokacinne mahaifiyarta take ƙare mata kallo, yarinya kyakykyawa da ita wadda ta haɗo dukkan kamannin iyayenta.
Kallonta Binazir keyi cikin ƙauna da soyayya, waida wannan kyautar Allahr zata salwantar? Sai kuma ta dakata da kallon nata ta shiga wata duniyar daban, duniyarda ke cikeda tarin tausayi da nadama a zuciyarta.
Ita batasan me zata kira wannan lamarin ba, amma tabbas tasan tayi kuskure da yawa wanda bata isa ta gyara ba, dan lokaci ya ƙure mata. Irin yadda ta nuna masa tsana, yadda take masa rashin kunya da kuma yadda take gaya masa maganganun da ko shi sa'an tane bai dace matsayinsa na mijin aurenta ta jefesa da maganar ba, wani irin ragargaza zuciyarta takeyi mata sakamakon nadamar da kecin zuciyarta, ayau ji take ta tsani kanta da kanta, kuma tanajin kunyar kanta, mutuminda yakeyi mata irin wannan ƙaunar, mutuminda ya yadda ya ha'inci ahalinsa saboda soyayyarta, mutuminda ya sadaukar da babban ƙudurin rayuwarsa saboda ƙimarta garesa, wanda ya ƙasƙantar da kansa ga mahaifinta dan neman yardar auranta duk da tarin mummunan laifinda yake ganin nata mahaifin ya aikata garesa, amma ya bashi ƙimarsa da daraja na Uba yake haɗashi da Allah cikin ƙasƙantar dakai kan ya bashi auran 'yarsa wai ace wannan mutumin mai tarin darajoji da ɓoyayyar baiwa da ni'ima ta wulaƙanta, tareda kiransa da mafi munin sunaye. Sai yanzu ta fahimci dalilin fusatar sa ciki hauka bayan ta kirasa da "FASIƘI MAI YIWA 'YA'YAN MUTANE FYAƊE". Runtse idanunta tayi sakamakon wani irin ɗaci da zafi ya daki ƙirjinta dan ji tayi kamar a yanzu tayi furucin kuma ji takeyi kamar ita aka jefa da wa'yannan kalaman. Wasu hawayene masu zafi suka zubo daga cikin idanunta, hawayenda ita a kanta batasan kona mene ba, Amma zuciyarta na faɗa mata wannan hawayen dalilin zubarsu naga Uban kyakykyawar Halittarda ke kwance a gabanta.
*Contact me 👇
****
*Comment*
*Vote*
*Share*
*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*