straight from the story...
by @autarmama
Cikin wani irin yana yi Mai kama da yana yin da ke nuna kan mutum ya kwance, ko baya cikin hayyacinsa, take buga kanta a jikin bed din Asibitin..bude kofar room din aka yi , kamshin turaren Viktor&Rolf Flowerbomb Haute couture Mai sanyi da kamshi Mai sa natsuwa, ya karade gaba daya gurin, ganin yarda take buga kanta a jikin gadon da yiyuwar zata iya illata kanta,cikin natsuwa ya karasa gareta, kafadarta ya rike tare da dagota, idanunta da suka chanja kala suka yi jaazir ga kwayar cikin idanun tayi wani irin Baki sannan ta kara girma sosai, , idanunsa ya nutsar cikin nata, zame hannayenta tai daga rikin da yay mata, wata iriyar rungumai ta kai masa, ta rik'esa sosai tana sauke wani nakastaccen numfashi na wahala da zalama, kafin ya janyeta a jikinsa yaji ta fara lasar masa gefen fuska da harshenta, rumtse idanu yay da karfi tare da cireta a jikinsa, duk da Hakan bata sanyi ba, da sauri ta Kara rukunkumesa tana kokarin ta ga ta biyawa kanta buk'ata kamar yarda kwakwalwa da zuciyarta suke tilastata mata yin Hakan wanda kuma duk aikin cocaine din da yake sarrafata.....