FANSA KO ƘIYAYYA

#36

by @109051246447263646587

*FANSA KO ƘIYAYYA?* 💔


*©️AuntiMamee*


_Page 36_

      

Tattare naman goshinsa yayi yana kallonta cikin mamaki, janye idanunta tayi tareda sa hannunta ɗaya ta share hawayenta, matsowa tayi zata ratsa ta gefensa ta wuce, amma sai yaƙi bata damar hakan ta hanyar shan gabanta ya ɗauke nasa idanun daga kanta ya mayar kan hannunta dake rungume da babynsa a kafaɗarta. Wani irin bugawa ƙirjinsa yayi wanda ya haifar masa da kasala tareda wani feeling na daban cikin jini da ƙashinsa, hannu yasa da niyar karɓar babyn amma saita kufce tayi baya cikin bugawar zuciya tace  "zan wuce" 

Ajiyar zuciya ya sauke tareda miƙa hannunsa kamar zai karɓi babyn sai kuma ya shammaceta ya zare key in motarta da yake saƙale cikin ɗanyatsanta guda ya nufi cikin gidan.

Da ido ta bishi, zuciyarta nayi mata wani irin suya na tabbatuwar zancen aurensa da Umman ta ƙara jadda mata, sai kuma wani rauni da ɓarin zuciyarta yayi mata, haka kawai taji duk ɗokin kasancewa dashi a yau ya kau dan abinda Umman tayi mata tunda take a duniya ba wanda ya taɓa tozartata irin hakan. Share wani sabon hawaye daya zubomata daga idanuwanta tayi tareda nufar waje, wani mai napep tagani tareda ta tsaida sa ta kwatanta masa inda zai kaita.

  Da sallama ya shiga murya ba yabo ba fallasa.

  "a'a, kai kuma daga ina? badai ka haɗu da waccan matarba a hanya?".   Ta tambayesa idanunta a kansa

 "Meya faru ne tsakaninku wai Umma?" Ya tambaya yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa ga Umman dan ita ɗin abar girmamawace.

  "o'o'o'o, meko ya faru? wai nan zuwa tayi faɗamin sunyi arba'in, niko nace data sanima bata wahalar da kanta tazoba dan ana gama bikinku da Bishira za ayi musu maganar kwasar kaya" Umman ta faɗa kai tsaye tsakaninta da Allah.

Wani yawu mai ɗaci ya haɗiye tareda kallon Umman    "meyasa kika damu na auri Bishira?" Ya tambayi Umman a sanyaye

"Saboda tana ƙaunarka Babban mutum nikuma duk mai ƙaunarka ina sonshi wanda bai damu dakaiba kuma a wajena kashi ya fisa daraja" ta faɗa cikin tabbatarwa .

Wani murmushin takaici ya saki "Umma" ya kira sunanta a hankali.

 " Badan Bishira na sona kike ƙaunarta ba, kina sonta ne saboda raɗin kanki, umma dakin damu damai ƙaunata baza'a shigo da gudan jinina nan gidan ki kasa mutumtasu ba, Umma har da bakinki kike faɗin da basu zoba zaki nemesu wai maganar kwashe kaya, tunda nake dake umma na taɓa cemiki na rabu da matata?" Ya tambayi Umman muryarsa ta fara sauyawa daga sanyinda take zuwa na alamun ɓacin rai, dan yau Umman ta kaishi ƙarshe wajan bashi mamaki da sauyawar ɗabi'unta.

Galala Umman ke kallonsa cikin mamaki 

Kauda kansa yayi daga Umman yaci gaba.

 "Nayi miki kawaici da alkunya, nayi miki biyayya gwargwadon iyawata kan bin umarninki ba tareda ina sha'awar hakan da ƙwayar zarraba, amma Ni kin kasa bawa mahaifiyarda ke uwa ga gudan jinina uzuri ba tareda tayi miki laifin komaiba, duk abinda ke faruwa nafa sani umma a zamtakewarku da Binazir, bata taɓa cutar da keba, bata taɓa saɓa mikiba, danme ke zakiyi fushi da fushin wani ga yarinyarda haryau tana baki fiyeda girma da mutumtakar da nayi tsammani daga gareta"

  "Au Allah?" Umman ta tambaya da mamaki 

  "Ni duk wanda baya ƙaunar jinina nine baya ƙauna, yadda kike mutumta mai ƙaunata haka nima nake ƙaunar mai ƙaunar jinina, yadda kijejin zafi idan an wulaƙantani wallahi Umma nafiki jin zafin wanda ya wulaƙantamin gudan jinina"

  "Wai Babban mutum saboda yarinyar can ta gaya maka ƙarya da gaskiya shine zakazomin da wata sabuwar ɗabi'arda ban sanka da itaba? anya kuwa lafiya ta barka? Yau ni kake faɗawa magana hardasu gori?

  "Ba haka bane umma".  Ya katseta 

 "Bata isa kuma batakai matsayinda zata faɗi wata magana ta ɓatanci ko kuma mai Kamada ta zugani akanki ba, amma fa ita 'in matatace, yadda kikeda haƙƙi akaina haka itama takeda haƙƙi a kaina dolene yadda zan kare miki mutumci itama na ƙare mata nata mutuncin, kuma umma Ni ban goranta mikiba, amma idan kinji wani abu mai Kamada gori a zuciyarki to da sabuwar ɗabi'arki da nayi miki kawaici amma kin kasa fahimta nake,   kuma dan Allah umma ki riƙe girmanki a natsayinki na suruka kada ki manta Ni mijinta kika haifa ba itaba, yauda gobe, kamar yadda Ni da nake ɗanki yau na kasa jurewa ɗabu'unki, haka ita da take ba 'yarkiba wataran zata kasayi miki kawaici umma zata gayamiki magana mai ciwone kamar yadda kike gaya mata wanda ke kikaja hakan kuma ƙarshen ta Ni zakusa tsaka mai wuya ace uwar 'ya'yana bata shiri da mahaifiyata."

  Ajiyar zuciya ya sauke tareda kallon Umman cikin idanunta "ki gyara umma dan Allah keɗin babbace keya kamata daki jure babba akasani da juriya ba yaroba, anyi miki dukkan wani abu daza ayi miki Umma, ankiraki an faɗa miki haihuwar amma bikijeba, gashi har gida an kawo miki jaririn ki gani amma kin kasa gode hakan bawai ina nufin Binazir tafi kowacce mace ba, amma zan iya rantsuwa da ba ƙaramin martabaki takeba da har takai wannan matakin tsakaninki da ita". Yana gama faɗa mata ya juya ya fice sakamakon magrib daya ƙarato kuma yasan tana jiransa tunda ya karɓe mata key inta.

 "Innalillahiwainnailaihirrajiuna jama'a yau naga takaina , ɗana ya zama bawan mace" umma ta faɗa da dukkan muryarta cikin sallalami tareda zabga tagumi, dan tawani ɓarin na zuciyarta yayi sanyi amma kuma data tuna da Bishira sai taji tausayinta ya kamata, anya kuwa wannan matar zata bari ayi aurennan? wai harda shi bai saketaba? kai ina yajede ya gama fushinsa ya huce ya dawo dolene ayi magana a buɗe". , jiki a mace ta miƙe tana tunanin irin gogaggun maganganunda babban mutum ya shimfiɗa mata yau. 

Wurga idanunsa yayi sanda ya fito waje kozai ganta amma sai yaga watan batanan. Hakan yasa ya kaɗai kai ya nufi masallaci dan yasan zata aikata fiyeda haka.

Allah Allah kawai take sukai gida, koda ta isa mai gadi ta bawa Umarnin ya biya kuɗin ta shigo gidan a haukace, kai tsaye ɗakin Mummy ta nufa.

Ɗago kai Mummy tayi cikin mamaki jin an banko mata ɗaki, suna haɗa idanu da Binazir ta taɓe bakinta tareda maida kanta ga abinda take, ganin Mummyn bata kulataba yasa ta miƙe ta kwantar da Nafi sannan ta shiga toilet dan gabatar da alwala.

Harta fito Mummy nakan sallaya, hakan yasa itama ta tada sallar, bata wani jimaba ta idar lokacin har Mummy ta idar ta goya Nafi a bayanta. 

"Duk yadda nakeson Samir Mummy na haƙura da kasancewa dashi, yau naga ƙiyayyata a idanun mahaifiyarsa Mummy" Binazir ta faɗa cikin takaici da rauni.

"Humm" Mummy ta faɗa tareda gyara zaman goyon Nafi a bayanta.

"Da ace zan hanaki daughter cewa zakiyi na cuceki kona ha'inceki, shiyasa na ƙayaleki kije gidan kiga dalilinda yasa duk yadda nake ƙaunarki da Samir amma ban yi miki tayin komawa gidansa bayan nasan kin gano cewa har zuwa yanzu keɗin matarsa ce, saboda na fuskanci wasu abubuwa daga mahaifiyarsa wanda ba lallai ne saina faɗa miki ba kuma shima akwai abinda nakeson ya fahimta game dake, amma dagaske daughter mahaifiyar Samir bata sonki a yanzu" Mummyn ta faɗa cikin tabbatarwa.

  "Na Sani Mummy, ƙanwarsa Naja ta gayamin komai, har shima ta faɗanin halinda yake ciki, da nayi zaton abin mai sauƙine zan iya yaƙin Ni kaɗai amma Mummy na fahimta yanzu bazan iyaba, ina buƙatarki a wannan lamari."

Murmushi Mummy tayi da faɗin "yanzu kikayi magana mai ma'ana daughter, tunda kinsani a ciki ina mai tabbatar miki da zaki mallaki Samir, amma kuma shizai nemeki dakansa a matsayinki na isashshiyar mace yar gatan Dady da Mummy"

  "Mummy" ta faɗa cikin Muryar shagwaɓa idanunta na fitarda ƙwallar tuna mata da sunan Dady da Mummy tayi.

  "Mummy wai dama haka akejin kishin miji a zuciya? kaji wani abu ya tsaya maka a ƙirji yaƙi tafiya ga wani ɓacin rai da fargaba duka Lokaci guda?" Ta tambayi Mummyn da dukkan gaskiyarta.

Murmushi kawai Mummy tayi ba tareda tayi magana ba, kamar bazatace komaiba, sai kuma zuwa can tace  "shi kishi ba lallai saina miji bama Binazir, a komaima mutum yanayin kishi saidai na wani yafi na wani, wani mai sanyayawa ne wani kuma mai zafafawane kamar dai naki kishin, yanada zafi, dan wani lokacin ba tareda kinsan kinyiba, dani kaina kina kishi sanda mahaifinki yake da rai, kinga kuwa dole naki salon kishin akan miji kijishi da ciwo matuƙa, amma idan kinbi komai a sannu zaizo miki da sauƙi, kada kisake wata mace ta firgita ki, ki riƙe kanki kawai kisa a zuciyarki ke kaɗaice a zuciyar mijinki ba wata bayanke, hakan zaisa kiji sauƙin wani abin idan kishin ya taso miki"

  "Mummy ni yanzu na haƙura, bazan sake kiransa a wayaba kuma bazan sake bi ta wata hanyarda zatasa na ganshiba koda ace sonsa ne zai zama ajalina Mummy bazan Kai kaina inda ba'a sona ba, taje ta aura masa matan duniya ma ƙarewar Bishira" ta faɗa cikin jin zafi.

Sallaman da akayine ya katse maganarda Mummy keson yi.

Asabe ce ta shigo bayan an bata izinin shiga.   "Baƙo kukayi yana palo" ta faɗa cikin girmamawa.

"Ganinan zuwa" Mummy ta faɗa tareda miƙewa ta nufi ƙofar fita Nafi goye a bayanta.

  Turus Mummy tayi dan ganin wanda ke falon, numfashi ta fitar tareda nufarsa da sallam,.

Saurin zamowa yayi daga kan kujerarda yake kai tareda zama a ƙasan carpet.

"Barka da dare Mummy, mun sameku lafiya"

"Alhamdulillahi, ya Ummanka?" Mummy ta amsa masa tareda tambaya.

Tsakiyar kansa ya shafa da faɗin "Alhamdulillahi tana lafiya"

Sai kuma palon ya ɗauki shiru.

"Ɗazu na haɗu dasu a gidan Umma shine na amshi key in motanta sai kuma tayi tawowarta ba tareda ta tsaya ta karɓa ba shine na kawo mata"  ya faɗa cikin jin Nauyin Mummyn tareda ajiye keyn motan Binazir a kan saman kujerar da ke kusa dashi.

"Allah sarki sannu da ƙoƙari"  Mummy ta faɗa cikin jin kunya.     Sai kuma palon ya ƙarayin shiru kamar ba mutane a ciki kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarsa kuma kowa yanada abin faɗa, amma jin nauyi ya hana kowanensu magantuwa.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda miƙewa da faɗin "saida safe Mummy"

  "SAMIR" Mummy tayi ƙarfin halin kiransa dan ta gaza danne abinda ke cinta cikin zuciyarta.

Gabansa ne ya faɗi daga jin sautin Muryar Mummyn yasan magana zatayi dashi mai muhimmanci. Ji yayi dukkan gaɓoɓinsa sun saki, a sanyaye ya koma ya zauna a ƙasa tareda fuskantar Mummyn amma bai bari sun haɗa idanu ba.

  "Magana zamuyi dakai amma kada ka ɗaukeni matsayin mahaifiyar Binazir, ka ɗaukeni a matsayin Uwar allumma mai gyara ga kowanne ɓarna da idanunta ya gane mata" ta faɗa tareda sauke numfashi.

Rusunar da kansa yayi ƙasa ba tareda ya kalleta ba alamun yana sauraronta 

   "Inaso ka faɗamin tsakaninki da Allah, shin kana zargin Binazir?"

Ɗan ɗago kansa yayi ya kalli gefenda take sai kuma ya maida kansa ƙasa.

Fahimtar yanayinsa dake nuna bai fahimci mai take nufi bane yasa ta sakin numfashi dayi masa gwarigwari

" Ina nufin Kanada shakku akan 'yarda Binazir ta haifa ba jininka bace?"

Da sauri ya ɗago kansa sama yana kallon Mummy Sakamakon maganarta da ya jita a bazata wanda ya haifar masa da wani irin bugawar ƙirji da ƙarfi dan maganganune biyu da suka shigesa, na farko jin ƙaruwar da ya samu ta 'ya mace, sai kuma zancen zargi, tabbas yasan yana kishinta sosai itada Salim, amma ko kaɗan bai taɓa hasashen zarginta kan cin amanar aureba, to akan mene zai zargetan, shidai yasan Salim ne kaɗai daya kasa ciresa a ransa ganin da yayi musu ranar sadakar bakwan mahaifinta, sai kuma maganar da ta ta gaya masa kan Salim zata aura nab gaba wanda hakan yasa kishin Salim Mai tsanani a zuciyarsa amma bai taɓa zarginta da hakanba yasan rashin sanin muhimmancin aurene yasata faɗar hakan bawai dan tana da wata alaƙa da Salim in ba. Saman kansa ya shafa sai kuma ya furzar da iska ta bakinsa tareda yin ƙasa da kansa ya girgiza kan nasa kaɗan "ko kaɗan Mummy ban taɓa zargin Binazir ba, kuma banji daɗin yadda kikayi zaton haka daga gareniba" ya faɗa cikin mutumtaka.

"Alhamdulillahi" Mummy ta faɗa a cikin zuciyarta tareda sakin ajiyar zuciya.

 "Idan har baka zargin Binazir, me yasa ka kasa sauke haƙƙinka a matsayinka na Uba ga abinda ta haifa?" Mummy ta tambaya tareda kallonsa sosai. Yana shirin magana ta tareshi da faɗin "ba wai ina nufin ka hidimta da dukiyar kaba, ina nufin kulawa da martaba gudan jininka, Samir yau Binazir kwananta arba'in da huɗu da haihuwa amma baka taɓa takowa kazo inda muke ba, koda bakasan inda ta tafiba, amma ya dace kazo gareni ka tambayi halinda take ciki tunda kasan da tsohon ciki a jikinta ta dawo gida amma shiru bakai ba wani naka" Mummy ta faɗada muryartata mai cikeda kwarjini.

"Ni bazan tambayeka dalilin hakan ba, dan ba kada hujja ko kaɗan akan hakan da zaisa kayi mata wannan hukuncin,   saidai inaso ka amsa kuskuranka da kaida kanka kasan kayi lafi baka kuma kyauta ba, ba kuma kayiwa yarinyarka adalciba, ban kuma taɓa zaton haka daga gareka ba Salim, háka Ummanka bazan ɓoye makaba tayi abinda ya bani mamaki, ana haihuwa na kirata a waya na shaida mata amma daga irin yadda ta amsamin na fahimci bata farin ciki da ƙaruwar da aka samu, ban kuma tabbatar da hakanba, saida na irga kwanakin haihuwar har kwana bakwai amma ace ta kasa zuwa kuma bata bi kirana ba da nayi mata a waya wanda hakan Ya matuƙar baƙanta min rai da bani mamaki, sai ga naka lamarin mai ɗaurewa mutum kai ace a matsayinka na Uba ka kasa zuwa inda gudan jininka take balle har ka ɗauketa kayi mata addu'a? Me yayi zafi Samir?"   Mummy ta tambaya cikin sanyaya muryarta tareda miƙewa tsaye ta kunce goyon Nafi dake bayanta.

Har lokacin kansa na a ƙasa tabbas abinda Mummy ta faɗa gaskiya ne baida wani hujja dazai kare kansa kan laifinda aikata, idan baya shiri da Binazir mezai shafi halittarda bata gama sanin kanta ba?

 "Karɓi kaga " Mummy ta faɗa sanda take miƙa masa Nafisa dake hannuta. 

Ɗago kansa yayi dan ganin abinda Mummyn take miƙa masa.

Jiki a mace ya miƙa hannuwansa biyu ya karɓi yarinyar jikinsa har wani rawa yakeyi.

 "Ka duba salim kaga Ni'imarda ALLAH yayi maka amma ka kasa zuwa ka gani ka gode masa," Mummy ta faɗa raunane tareda komawa kan kujera ta zauna tana kallonsa.

Rungume yarinyar yayi a ƙirjinsa tareda runtse idanunsa sakamakon wani irin harbawa da ƙirjinsa yayi lokaci guda haɗida tsinkewar jinin jikinsa.

Wani irin soyayya, ƙauna da tausayin yarinyarda ke rungume a jikinsa ne ya shigesa, sai yanzu ya fahimci girman laifinda yayiwa 'yar tasa, gaskiyar Mummy dole tayi zaton ko yana zagin Binazir kan samuwar yarinyar, idan ba hakaba shi yama rasa maiya shiga kansa da har ya kasa zuwa ya ture batun Binazir a gefe? Yayi laifi kuma dolene ya gyara laifinsa.

 Ajiyar zuciya ya sauke tareda buɗe idanunsa ya ɗorasu aka yarinyar yana bin dukkan wata halittar jikinta da kallo.      "Tabbas nayi laifinda na cancanci kowanne irin hukunci , na biyewa ɓacin zuciyata na kasa sauke haƙƙina na mahaifi akan 'yata, dan Allah Mummy kuyi haƙuri, ku kuma bani dama dan Allah na gyara laifina" ya faɗa cikin matuƙar raunin murya .

Ajiyar zuciya Mummy ta sauke tareda miƙewa dan bada Umarnin a kawo masa abinci  "ka ambaceta da sunanta da mahaifiyarta tayi mata huɗuba da kanta kayi mata addu'a dashi, Allah ya raya mana NAFISA yasa haƙurinta yafi na takwararta NAFI" Mummy ta faɗa tareda barin wajan.

   


*Contact me 👇

**** 

*Comment*

*Vote*

*Share*

*Follow me on *Wattpad@*AuntiMamee*