Page 20 last free page's
by @maidambu41
*NAAZNEEN❤🔥*
EXQUISITELY BEAUTIFUL
#Mai_Dambu
Chapter 20
A hankali ta dauki magen, tana jin wani sabon farinciki yana kara lullubeta. "Na gode sosai." Ta dauki magen zata fita Jessica ta ce mata. "ki kula da ita kamar yar cikinki, domin ba kasafai ake samun irinsu ba. Ki kula da rayuwar luse."
"Zan kiyayye, kamar yadda zan kiyayye rayuwata na gode sosai yan uwa." Sannan ta fita daga gidan, bata tsaya ko ina ba, sai wani best eatery a kusa da unguwarsu, ta sayi abincin da Saif da Khawlat zasu ci, sannan ta wuce gida, ta fara gyara gidan domin yayi kura, rashin yarda irin na Gimbi taki amincewa ta dauki yar aiki. A hankali take aikin har ta gama, sannan ta ajiye kome ta wuce dakinta tayi wanka, ta dawo falo tana kallon luse da take ta lashe kanta. "Luse ina son na fita na nimo miki abincinki, amma ina tsammanin Saif suna hanya."
"Meow meow meow!!" Ta faɗa tana lashe jikinta, "na tafi kenan?" Gimbi ta tambayeta, sake mata kuka tayi da haka ta fahimci tana son abincin, don haka ta juya ta fita, tare da luse suka nufi motarta. Bude mata get din gidan akayi ta manna a guje. Can wani asibiti ta nufa, anan ta samu wata lebura da take shara a asibiti ta bata kudi, ita kuma ta je bola ta kwaso mata sabin mahaifar ta zuba mata a leda, sannan ta bar Asibitin,. Lokacin da ta koma gida su Saif basu iso ba, sai wajen karfe biyar na yamma, suka shigo gidan tana dakinta kamar me barci. Suka shigo gidan, sai wani dauke kai yake kamar ba tare da Khawlat suke ba. Haka ya wuce dakin Gimbi ita kuma ya barta a falon, tunda ya shiga ya sameta kwance, zama yayi a bakin gadon, yana jin wani irin kewarta.
"Princess!" Bude idanun tayi, domin taci uban kwalliya kamar me zuwa wurin biki. Tana ganin shi, ta wani rungume shi har da shashekar kukanta, ita tayi kewar shi. Haka tunda ta rungume shi, suka shiga wata duniya na daban, don dama an jima ba a hadu ba.
A can falorn kuwa, zama Khawlat tayi a daya daga cikin kujerun falorn, tana kallon yadda gidan ya hadu, dama haka yake da bala'in kudi, tana yi tana kallon kowani kusurwa na gidan, a can bayan kujeran kuwa Luse ce da ta gama cinye sauran mahaifar da ta zuba mata. Jinin da yake jikin mahaifar ya gama ratsata.
A hankali tayi ta sanɗa da bin bayan kujeran, Khawlat bata sani ba kawai shegiyar magen nan, ta dira a kafadarta tare da sakin wani fusattacen gurnani a daidai kunnen Khawlat. Ihun da tayi tare da wurgi da luse ya katse abin da Saif da Gimbi suke, suka fito daga dakin. Luse ta kara nufar Khawlat da gudu,. Ita kuwa ta arta da gudu wurin Saif da ya riga Gimbi fitowa. Jikinta yana rawa, turus yayi tsigar jikinshi yana tashi. "Subhanalillahi, waye ya kawo mana mage gidan nan?"
"Luse!" Gimbi ta kira sunanta, wuce su tayi ta nufi wurin Gimbi tana gurnani.
"Magenki ce?"
"Eh tunda ka tafi, bani da abokin hira shine ranar na fita na buge Uwarta ta mutu, shi ne ta bani tausayi na daukota, ai bata son mutane kuma ban gaya mata zaku zo da Auntynta ba ne, Luse kin gan shi nan, shi ne Dad ɗinki. Ni kuma Mom ɗinki, ita kuma wannan Auntynki ce zata na dafa abinci tana baki, gobe ma zasu wuce honeymoon, don haka kada ki kuma razanata kinji." Ta faɗa tana daukar lusen, "meow!" Lusen ta juya tana kallon Khawlat da take bayan Saif. "Sorry sister, Luse tana cewa kiyi hakuri." Gyada kai Khawlat tayi tana faɗin. "Ina tsoron mage ne, shi yasa ta ce, Ina wuni aunty Gimbiya!"
Zama tayi a daya daga cikin kujerun falorn, ta daura daya akan ɗaya tana faɗin. "Lafiya lau, ya amarci? Saif da fatan kana kula min da kanwata?"
Washe baki yayi yana kara jin son Gimbi na cika zuciyarshi, bai zaci zata sauko haka ba. "Muje na nuna miki dakinki domin nasan ko kin dawo ba zaki koma Bauchi ba, kawai ki cigaba da aikinki anan."
"Tow Aunty!" Gimbi tayi gaba dauke da Luse, Saif dauke da kayan Khawlat har cikin dakin da ta gyara ta tsaface shi. Da sallama a bakin Khawlat ta shiga dakin. Tana murmushi "Dakin yayi miki?" "Gaskiya yayi min, na gode sosai Aunty." Murmushi Gimbi tayi sannan ta juya ta fita, abincinsu ta sake dumamawa, sannan ta kara gyara ko ina, ta shirya ko ina, sannan ta raka Saif har dakinta yayi wanka ta ciro mishi kaya, yana kallonta.
"Ban zaci zaki amshi Khawlat hannu bibbiyu haka ba, na zata ko don baki son kishiya zaki ki bata fuska. Gaskiya na godewa Allah da ya bani ke, domin ba karamar sa'a nayi ba. Allah ya miki albarka."
"Amin Ya Allah!" Haka ta taimaka mishi ya shirya, sannan suka fito falo, ita ta wuce dakin Khawlat, da ta shirya cikin riga da skirt, tayi kyau murmushi Gimbi tayi ta ce Mata. "Kin yi kyau Amaryar Saif, zo muje kici abinci."
"Tow Aunty Ina zuwa, ban yi sallah la'asar ba ne." "Ok ba damuwa!" Ta fito tare da bin dakin da wani mugun kallo, sannan ta fito falo, ta zauna wurin Saif bai tambayata ba, gudun kada ta fassara shi yasa shi cigaba da cin abincinshi, "baka tambaye ni ina amarya ba?" "Oh, Baby gaya min ina take?" "Tana sallah, yanzu zata zo." "Ok ta kyauta nima dake na ganki, ban yi la'asar ba. Amma ina gamawa zan je nayi sallah domin dai kin san ci na gaba da sallah." A ranta tace. 'Ai ko zaka yi, ba zaka tab'a yin shi akan lokaci ba.' suna zaune a wurin Khawlat ta iso, ta ja kujerar zata zauna luse ta tawo da gudu ta haura kan kujerar..
"Baby Girl, sauka aunty ta ci abinci." "Meow" ta faɗa, tana me sauka daga kujeran, ta nufi wurin da take zama ta zauna. "Kai magen nan, tana jin magana ga hankali." Saif ya faɗa, yana kallon Luse da tayi kalar tausayi.
"Haka kowa yake faɗi. Idan nayi baki suka ga yadda nake mata magana tana yin duk abinda na ce, sai su ce dama sune da ita." Ita kan Khawlat bata ce kome ba, ta cigaba da cin abincin ta, wanda take cusa shi kamar dole, dakyar ta mike ta ce musu zata shiga daki yayi sallah magariba ta karato, sai lokacin Saif ya tuna sallah la'asar ta wuce mishi, sai da idanunshi yayi jajuur don bakin ciki.
Daga nan ya wuce yayi alola, ya gabatar da la'asar, sannan yayi Sallah magariba. Dakyar Gimbi ta barshi yayi Sallah isha, babu dogon addu'a suka fada duniyar maji dad'i.
Kusan wannan daren Khawlat bata rintsa ba, domin Luse ta hana ta barci. Domin ta rasa ta yadda magen nan take shigowa, bata samu barci ba sai karfe biyar na asuba, ta nime Luse ta rasa bayan ta idar da azkar ɗinta, ta koma ta kwanta.
.......
Wurin karfe sha daya na safe, Saif da Gimbi suka fito daga dakinsu. Lokacin Khawlat tana can, tana fama da wani irin mafarki ko nace idanu biyu, na wata mata me rabin jikin Luse, tana kokarin caka mata wuka, amma tana ta addu'a tare da dambe. Shigowar Saif dakin yaga tana ta kokuwa da kiran sunan Allah, ya isa wurinta da sauri yana me d'agota yana kiran sunanta. "Khawlat!" Ya kira sunanta da mugun ƙarfi, bude idanu tayi akan shi. Da wani irin sauri ta rufe fuskarta a kirjinshi, tana me fashewa da kuka. "Yaya Alhaji ka maida dani wurin Ummi don Allah!"
"Ya isa, hala baki yi addu'a ba, kika kwanta ko?" Ya faɗa yana bubuga bayanta. Shigowar Gimbi dakin tana faɗin. "lafiya kuka zauna baku fito ba?"
"Princess, Kanwarki na samu tana mafarki shine na tashe ta." "Ya Salam! Sannu kinji." Ta faɗa cikin matukar ban tausayi, "Kiyi wanka sai ki fito." Saif ya faɗa, yana kokarin barin jikinta. "Amma ai da ka taimaka mata, koda haɗa ruwan ne yadda take a firgice nan ai ba zata iya ba."
Wani karin mutuncin Gimbi ne ya kara tula a idanunshi, ya sakar mata murmushin farinciki ya ce mata. "Ina godiya da Ubangiji ya bani ke a gefena, Na gode." Fari tayi da idanunta, sannan ta ce mata. "Bari na hada mata kawai." Haka ta wuce ta haɗa mata ruwan bayan ta zuba abin da zata zuba, ta fito ta ce mata. "Sannu Khawlat shiga ki yi."
"Tow, na gode Aunty." Daga haka ta fita ita kuma ta shiga tayi wankar ta fito, ta gyara jikinta. A hankali ta shirya cikin doguwar riga, na material lace yayi mata kyau. Sannan ta gyara dakin, kafin ta fita wurinsu.
....... Tana fita falon ta samu sun gama, ta zauna ta fara ci, Saif da yake can tsakiyar falon ya ce mata. "Ki hanzarta saboda yau ne zamu tafi."
"Ok" ta ce mishi tana cin abincin, Gimbi tana jikinshi tana zuba zamaninta. Har Khawlat ta gama, suka fito tare da rakiyar Gimbi har airport, har jirginsu ya tashi tana nan, murmushin mugunta taii tana me juyawa zuwa gida da gudu domin idda sauran aikinta.
Ba karamin dadi ta ji ba, domin tun jiya Luse ta cire mata kurwan Khawlat. Tana zuwa ta nufi dakin da take aikinta, ta cire mayafin da ta rufe madubinta. Cikin raha ta kira Mamanta. Tare da tura mata wata yar kaza, ta ce mata. "Ga kurwar kishiyata."
"Lallai kin fini kokari, yanzu dai miko min ita, na duba ko tana da ciki "
"A'a bar min ita, nima zan iya ji da ita " kiri-kiri Gimbi ta hana Uwarta kurwan Khawlat, ta rufe labulen ta fita ta kira Jessica, ta gaya mata. "Zan turo miki da wani flowers pot guda biyu, daya zakina zuba mishi ruwa ne, daya kuma zaki na zuba mishi runshi ne, a gefensu zaki saka wani wani flowers, anan zaki daure kazar. Sai kina barin Luse tana aikinta a kanta."
"Da fatan ba zata mutu da wuri ba?"
"No ba zata mutu ba, ai ke zaki cinye abinki. Sai luse da zaku bata hanjin da kudun. An gama da tarihinta amma zaki cigaba da azabtar da ita."
"Na gode sosai!"
Wurin karfe tara na dare, aka buga mata kofar, tana budewa ta ga flowers pot din nan dai amma babu kowa, dauka tayi ta kai can backyard din gidan, ta ajiye ta yi yadda aka ce mata.
Sannan ta fito zuwa dakinta, ta dauki kurwar Khawlat da take yar karamar kaza, ta je ta daure. Duk da wani zuciya tana bata shawarar ta barta wata zuciyar kuma na bata shawarar ta kashe ta haka ne hukuncin duk macen da ta rab'i Saifullahi.
★★★
Saudiya.
Juma'a da safe
Za a iya Cewa, Allah yana tare da Nazneen ne, kawai amma Innayo bata ki ita da Hajiya Goma su salwantar da ita ba.
Sau uku suna barinta a masallaci, da farincikin su, suna bude dakin zasu isketa a saman gado tana barci. Haka ya sa Innayo hakura da abinda take, duk da ita kanta ba son ranta ba ne, amma tana kara jin tsanar yarinyar saboda bakin Hajiya Goma.
Yau da zasu tafi masallaci, Nazneen ta rigasu fita, domin ban da kyara da hantara babu abinda yake had'asu. "Innayo dama naga kamar hankalinki yana tashi, me zai hana, mu ce Nazneen ta miki sata kinga nan dokarsu da tsanani."
"Ban gane ba goma, kina nufin na mata sharrin sata? A'a duk kiyayyar da nake mata ba zan kashe ta ba, kuma ba zan mata sharri ba, abin da na sani na tsane ta. Ba don ba jinin Adamu ba ce a'a sai jinin da ta haɗa da arna, don haka bar zancen maganar sata."
Shiru goma tayi tana mamakin ashe, Innayo ta san me take yi, don haka ta ce mata. "Wai naga kina shiga damuwa ne, idan kika ganta, amma ya wuce ai."
***
A can masallaci kuwa, Yankar jiki wata mata tayi da take gefen Nazneen. Dake yau juma'a, Sheikh Abdulrahman sudais yana hudubar juma'a.
Juyawa Nazneen tayi ta nufeta, tana me tattabata, kafin ta isa wurin wata mata da take shige da fice na hukumar masallacin, tazo ta kira ma'aikatan lafiya suka tafi da matar. Komawa mazauninta tayi ta zauna, Hajja Marih da take kallon kome murmushi tayi sannan ta dawo wurin Nazneen da zama.
"Sannu yarinya me halin manya."
Murmushi tayi tana faɗin. "na gode hajiya, ina wuni?"
"Lafiya lau, ko zaki kawo min ruwa na sha?"
"Tow" ta fita can sai gata da ruwan zam-zam. Ta kawowa Hajja Marih.
"Ke dawa kuka zo?"
"Ni da kakata da kishiyarta, basu iso ba."
Haka suka zauna shiru, har aka yi sallar juma'a, kusan tare da hajja Marih suka fito, a waje ta samu ganinsu Innayo, ta cewa Hajja Marih, "ga kakata can "
Kusan tare suka isa wurin, Innayo ta zabgawa Nazneen harara. "ina kika shiga?"
"Ayya tana cikin masallaci ne."
"Hajiya kin san dan yau, baka shedan shi. Tun yaushe muna nan bamu ganta ba." Inji Hajiya Goma.
Kallon Hajiya Goma tayi kamar zata yi kuka ta ce mata. "Hajiya Goma ban gane ba, na zauna jiranku kin ce min, na saka ku a gaba kamar Mayu ai kun san hanya, na tawo kin ce baki yarda da ina masallaci ba, Hajiya Goma ki daina shiga harkata. Idan ba haka ba wallahi ko." Ai kuwa ta wuce su ko sallama da Hajja Marih bata yi ba, "Baiwar Allah, muna tare da ita, a cikin masallaci. Sannan kuna kyautata zato ga kowa domin Allah zai iya jarabtar ka da abin da kake zargin wani. Yarinyar nan tana da hankali. Domin kuwa."
Bata rufe baki ba, hukumar masallacin suka fito niman Nazneen, a ganta domin da taimakonta aka kai matar da ta fadi asibiti. Lokacin da larabawan suka zo Hajja Marih ta amsa musu, suka.yi ta larabci take gayawa musu ga kakaninta, sai kunya ta kama Innayo da Goma.
Aka yi ta musu godiya, da fada musu ai jikar ta Mutuniyar kirki ce,
Da rigima da fada, da tashin hankali aka gama umran, suka dawo Nigeria.
Tunda suka dawo sau biyu Innayo tana rashin lafiya, har lokacin azumi yayi, a lokacin Alhaji Abdullahi Malami ya zo hutu da iyalinsa. Akan idanunshi yaga yadda Innayo da Goma suka saka Nazneen a gaba, su mata a gaban jama'a, Duddiya su hana su barci. Don ma Malam ya kara kafe gidan. Alhaji Abdullahi da kanshi ya gayawa Umma zai tafi da Nazneen, ita kuma ta gayawa Malam, shima da ya gaji da halin Innayo ya ce su tafi da ita.
Haka aka yi azumi, kayan sallah Nazneen da Babanta ya saya mata. Innayo ta hanata, ita kuwa ta kwashe na Innayo ta saka a rufin dakin Innayo. Wannan abin yayiwa Innayo zafi, domin ana sallah jininta ya hau, Aunty Uwani da Aunty Hawwa'u, suka ce gaskiya Alhaji Adamu ya ɗauke yarshi zata kashe musu uwa. Wannan abun ya mishi ciwo ainun, ya gayawa Malam. "kada ka damu lokacin da zasu gane kuskurensu yana zuwa, yarinyar nan alkhairi ce. Amma ba kowa zai gane haka ba, Abdullahi ya ce zai tafi da ita gara ya nisantatta da nan "
"Alhamdulillahi! Kafin ayi babbar sallah zan nima mata visa na zaman can "
Duk da Alhaji Abdullahi iyalinshi suna, New g.r.a. ita Nazneen bata san dukkan yaranshi ba, Tahir ta sani.
Tahir yana da kanne, Anas, Amrah, Sadiq, sai Auta Naylah, karshen shekarar nan za ayi bikin Amrah, a can London din, wani dan Kano ne.
Duk sauran jikokin Malam, suna son alaka da su Tahir, amma kishin kakaninsu yasa suke taya kakaninsu kishii.
Naylah da take da mugun iyayi da gani-gani, ranar sallah. Da suka hadu da Nazneen sai da ta kasa boye mamakinta, domin har dakin Umma ta je ta ce mata. "Umma, yarinyar da ta shigo ita ce, yar Baban Abuja?"
"Eh ita ce Nazneen Aisha."
"Sai kace Baby doll. Tafi kowa kyau a gidan nan,. Ki ga dan kunnen da yake kunnenta diamond ne fa."
"Eh nice na saya mata, zuwana Umra kema na saya maki, ita nata pink ne ke kuma purple."
"Da gaske Umma!"
"Da gaske ki tambayi Mamarki na bata ta baki."
Kasa magana tayi, ta koma tana murmushi.
"Umma da ita zamu koma London?"
"Eh tare zaku koma, kiyi shiru da bakin ki."
Rufe baki tayi, daga nan ta fara cin masarta.
Washe garin sallah ana dawowa kallo, gidan aka taru, Washi garin hawa kuma akayi wunin sallah, baki daya yaran gidan sun haɗu, tunda Yaransu suka zo aka saka Nazneen a gaba, zagi hantara karshe dakin Malam ta nufa ta kwanta abinta. Sau biyu yana shigowa ya ganta tana barci, abincin gidan kuwa yadda aka zuba shi a cikin tukunyar ana izza wuta haka ya zauna babu al'amarin yasan ana izza wuta. Har wurin karfe biyu na rana ba a sauke abincin gidan ba.
Hajiya umma ta nufi dakin Malam, Nazneen tana ta barci, tab'ata tayi tana faɗin. "tashi Nana A'ishah, zoki duba mana girkin nan yaki yi, sannan ki gaya min me ya same ki."
"Zagina Mommy tayi,akan yan kunnena da Munayyah ta dauka zata saka na ce ta bani abina kada ta lalata min, shi ne suke ta dukana da zagina. Bayan malam ya hanani yin wani abu."
"Ina yan kunne suke?"
"Kin ga ta tsinka min sarka ta." Daukar abin wuyar Umma tai, ita kadai tasan yadda take ji, "kiyi hakuri kinji!" malam ya fada a bakin kofar dakinshi. "Wata rana zasu so, su isa matsayin da kike Allah ya daukaka ki, na hanaki mu'amala da aljanun ne don kada su zama rauninki. Jeki tura musu wutar."
"Tow."
Tashi tayi, ta fito ta samu kowa yayi cirko-cirko a tsakar gidan, ana ta mamakin yadda abincin yaki dafuwa, tana zuwa ta bude tukunyar ta saka.hannunta biyu ta wanke su tassa, sannan tukunyar ta hau tafasa. Ta wuce abinta tana jin kowa nacewa. "Tab ba zanci abincin nan ba."
"Duk wanda yaga ya ci abinci a wani wuri, tow gidanshi ne, amma tabbas babu me saka ni asara."
Haka kuwa aka kwashe duk suka ci abincin haka, ban da Nazneen da Umma ta bata dambu da cake.
Haka aka yi wunin sallah babu Wanda yaji dadinshi..
Bayan sallah da kwanaki visa din Nazneen din ya fito.
★
Mutanen Istanbul, ranar da suka shiga kasar ranar Khawlat ta fara rashin lafiya. Da farko Saif ya zata ai normal, sai da suka kwashe sati biyu, ciwo ya saka yar mutane a gaba. Don dole suka nufi asibiti.
Inda suka kwashe sati biyu a can, kafin suka dawo, kasancewar azumi ya gabato, haka Gimbi ta hana a maida ita gida, haka take jinya, Gimbi ke mata kome, har aka gama azumi. A lokacin jinyar yaci ƙarfinta.
Wata juma'a, sai ga Ummi da Maman Khawlat, domin hankalinta yaki kwanciya, suka zo, lokacin da suka iso gidan Gimbi bata nan, Saif suka samu Don sun zo da Nassif ne shi ya gayawa Saif gasu a hanya.
Lokacin da suka ga Khawlat, karfin zuciya ne irin na Uwa yasa bata zubda kwalla ba, amma ta karaya da Yarta, ai basu kwana a Lagos ba, sai bauchi. Domin Uwar na ganinta tace jinyar ba ta Asibiti ba ce, ga cikin da ya fito, das a ramamen jikanta.
★★
Sati biyu saura ayi Layya, Alhaji Abdullahi suka koma London, da Nazneen wacce abin yazowa Innayo bazata, sai da ta sami Malam da maganar ya mata wankin babban bargo. Sannan ta yi shiru.
★★★
A can Azare kuwa tunda aka dawo da Khawlat, ake maganin gargajiya da na Islamic, jinya ake amma jikin yana kara rikicewa, a ranar da gimbiya tazo Azare, kuka wiwi take, itama Khawlat kuka take, cike da kaunar Gimbi. Domin babu abinda zata ce mata, irin halaccin da Gimbi ta mata, satin Gimbi biyu, ta koma, bayan komawarta ne, Khawlat bakinta ya bude.
Take bawa mahaifiyarta labarin yadda Gimbi ta mata alkhairi da kula da ita, kusan zuciyar Uwa, take ta manta da wani abu a ranta, tayi ya yiwa Gimbi addu'a.
Bayan babban sallah da sati Uku, Gimbi tazo, a lokacin Jikin yayi sauki. Haka ta je gidansu Khawlat, suka sha hira, babu wanda Gimbi bata burge shi ba, Sai Nassif domin gani yake kamar fuska uku gare ta, satin ta daya, ta juyo zuwa lagos.
Bayan tafiyarta da kwana biyar, jini ya tsinkewa Khawlat, aka nufi FMC Azare, yadda aka shiga da ita dakin, emergency........
Alhamdulillahi anan na kawo karshen FREE page's. KaK'a k'ara ƙaƙa, Khawlat zata mutu ko zata rayu?....... Labarin zai cigaba da zuwa muku.... Arewabooks da Whatsp.
_NAAZNEEN, GENERAL NASIR ZAKI, BINTUN BATUL TOP-NOTCH TEAMS NA KUDI NE! Gaba DAYA UKUN 1300 NE_
BIYU=₦900
DAYA=₦500
CHAT ME IDAN KUNA BUKATA: ***