KOWA YA GA ZABUWA…

Chapter 2

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

  (DA ZANEN TA YA GANTA)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.       

     (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

And Now 

*Kowa Ya ga zabuwa..*


           *PAGE 2*


*FREE BOOK*


"Maman Usman yaron nan ai ba chemist ya kamata ki kawo shi ba asibiti ya kamata ki kaishi yana jin jiki sossai.."

Share hawayen ta tayi sbd mammatsa cikin Usman da malam Musa ke yi yana ƙara cikin azaba se taji ina ma zata iya cire mishi ciwon ya dawo jikinta Allah sarki uwa kenan.


Cikin damuwa tace 

"babu halin ne Dr da akwai da na kaishi, in na tafi asibiti da dubu guda babu me saurara ta, ka taimaka ka bashi ko na rage zafi ne kan in je in nema Dan Allah"

 cike da tausayinsu Dr Musa ya Haɗa musu magani kuma be karɓi kuɗin ba yace 

"ku je ku gwada Allah ya bashi lafiya"


Ta mika mishi kuɗin 

"gashi se ka cire"


"A'a maman Usman ke de Allah ya bashi lafiya"

Godiya sossai tayi mishi kan ta kamashi Aisha ta taya ta suka dawo gida, ruwa ta samu ta bashi ya sha ya kwanta bacci ya samu ya ɗauke shi.


Zugum ta zauna tana Tunanin yadda zata bi da dubu gudan nan har ya kai musu karshen wata, kaman yadda Hamma Yusuf ya faɗa ko da mutuwa take idan har watan nan be kare ba ba basu kuɗin nan ze yi ba, dafata da Aisha tayi yasa ta buɗe idanunta da suka yi laushi da gajiya, yunwa, damuwa da ciwo ta zube su kan yarinyar.


"Mama Tunanin me kike?"


Aisha na da wayo ko ta ƙi faɗa mata haka zata yi ta naci tayi ta naci se ta sani.


"Ina Tunanin yadda kuɗin nan ze kaimu wata ne Aisha"

Ta faɗa mata ne kawai ba don wai da tunanin samun mafita daga yarinyar ba, ita ma rashin abun cewa ya sa tayi shiru kawai ta zubawa wuri guda ido..


Kaman saukar aradu haka taji a sadda kunnuwanta suka jiyo mata sallamar wasu mata da suka shigo su hudu, akallah ba akasara ba babu wacce zata haura 28 cikinsu, se matashiya da zatayi sa'a da Hidayat kaman yadda naji Hamma Yusuf ya faɗa sunan.


A maimakon farin cikin da kowa yake yi idan yayi baƙi saɓanin Hidayat tashin hankali ne ya bayyana karara a fuskanta tana shirin magana ɗaya daga cikinsu tace 

"Shafaffiya da mai yau ko arzikin sannu da zuwan ba zamu samu ba kenan ana baƙin ciki da lafiyarmu"


Baƙar tace 

"Eh to Salamatu ba dole tayi baƙin ciki da lafiyanmu ba tunda da shine muka tako muka zo har gidanta"


Matashiyar tace 

"A'a Aunty kausi gidan ɗan uwan mu dae... Ni wlh in banda ya Yusuf banga abun ɗauka a wanna ƙashi da ran ba se fari kaman aljana"


Na karshen tace 

"ke kuwa Surayya baki da labarin ita ce ta shiga ta fita sbd ta sha a nono tayi yadda tayi ta sa shi Yusuf ɗin ya fara son ta har Abba ya Haɗa auren, to da aka zo ba'a samu yadda ake so ba kuma an kasa bari an manne kaman dangin maita"


Na farko wacce aka kira Salamatu tace 

"To wa ya sani Abu a duhu.."


Budurwar Surayya tace 

"a kuma cikin baƙar Leda"


Suka kwashe da dariya...


Aunty kausi tace 

"wai kuma dan bala'i Da aka tashi auren aka Haɗa da nawa Abba har da yiwa wannan munafukar annamimiya kayan da suka fi nawa har yau in na tuna kaman in mutu"


Dariya duk suka yi Salamatu tace 

"ki bar ɓata ranki yanzu duk suna ina?"


"Gidan Boka"

Cewar Fahariyya itace ta karshen.. Suka kwashe da dariya tare da tafawa..


Wucewa sukayi har Surayya na bangajeta Seda suka shiga ɗakinta kaman yadda suka saba suka yi filla filla da ɗan tarkacen ta suka gama kan suka nufi parlorn Yayan su suna masu ci gaba da ci mata mutunci daki daki.


Idan dutse ya tanka to fa Hidayat ta tanka, se kara jan Aisha da ta lafe jikinta tayi tana me mayar da idanunta ta lumshe, ta riga ta saba da duk wasu maganganunsu da muguntarsu tunda a ciki ta tashi, a ciki tayi wayau a kuma ciki aka raine ta har tayi aure, dukkansu babu wacce bata saba da bautar ta da kuma duka da zagin ta ba, tun tana damuwa har abun ya zo ya bi jikinta..


Tana nan zaune Yusuf ya fito shi da Surayya suka fice bata buɗe idanunta ba kaman yadda basu kalli inda take ba, bata san mintunan da ta ɗauka haka ba kawai ji tayi saukar ledoji a jikinta da kuma karfi, a razane ta furta 

"A'zubillahi minasshaiɗanir rajeem"


"sede in kece sheɗaniyar ko kuma uwarki"

Cewar Surayya.


Yusuf yace 

"oya maza tashi sun zo suna jin yunwa, sannan ba su kaɗai ba ina da baƙi biyu anjima tashi ki ɗaura musu sanwa yanzun nan"


Aisha take shirin kwantar wa ta mike don ta san rashin mikewa da wurin ma ka iya zama laifi sede bata kai ga zame ta ba ya daka mata tsawar da ta kaɗa har abunda ke cikinta Aisha dake bacci ta farka a firgice.

"kin tashi ko se na taushe ki???? Ana magana kina wa mutane abu lagwai lagwai kaman lagwani"


Kallon babanta take har Mamanta ta mike ta tattare ledojin da har wasu abubuwa sun watse a ciki ta nufi inda take hura wuta.


"Ga min ƴar banzar yarinya ke don uwarki kin dena kallona da waennan Mayun idanun naki ko se na tsole miki su kin makance?"


Hawaye ne suka zubo mata cikin rawar murya tace 

"Abba mama fa bata da la..."


Marin da ya ɗauke ta dashi yasa ta hantsila maganan bakinta ya yanke, duka ya rufe ta dashi tana ta ihu babu wadda ya iya fitowa a cikin goggoninta ya amsheta, Hidayat dake duke bakin murhu da yaro matashi ya shigo da itace busasshu ya zube da Alamu aikan Yusuf ne ko ɗago kai bata yi ba.



Seda ya gaji ya kyale ƴar yarinyar yayi wucewarshi inda ƴan uwanshi dake shewa suna kallo a parlorn shi, da gudu Aisha ta mike ta zo ta faɗa jikin uwarta tana me sakin sabon kuka wadda Seda ya sa Hidayat hawaye..


"Mama me yasa Abban mu baya son mu kaman sauran Abban kawaye na? Ko shi ba shine Ab..."


Hannu Hidayat ta sa ta toshe mata baki.

"Kar na kara jin hakan daga bakinki mamana, shima yana son ku kiyi ta mishi Adu'a in shaa Allah watarana se labari"


Da taimakon Aisha take aikin Dukda ba wani abun Arziki ta iya ba har ta Haɗa jollof rice me kaza a ciki.


Fagen girki Hidayat ba baya ba sbd ta horu dashi tun bata iya ba ake sakata tayi in be ciyu ba ace se ta cinye in bata iya cinyewa ba wani sa'in a mata ɗure da amai da komai wani sa'in kuma ta daku iya dakuwa...


Lumshe idanunta tayi tana tambayar kanta amsan da ta ba Aisha 'ko se yaushe wataranan ze zo?' da wannan tunanin ta gama girkin ta tsabtace wuraren tas, Haɗawa tayi ta kai kofan parlorn tare da knocking basu amsa ba suna ta shewarsu gajiya da tayi da tsayuwa yasa ta tura da sallama a bakinta ta ajiye musu daga bakin kofa zata wuce Aunty kausi tace


"Eh ga mayunwata in yunwa ta kusa halakamu se mu rarrafa mu ɗiba ko?"


Yusuf dake wani faffaɗi cikin jin shi ya isa da gidan shi yace 

"ke ɗauko ki kawo nan, ki shiga kitchen ɗina ki haɗo musu duk abun bukata ki kuma zo kiyi serving ɗinsu, Allah ya Taimakeki kwarzane baki yi min jikin warmers ba.. Hmm"


Seda ta sake duba warmers ɗin na hannunta da kyau gudun matsala kan ta karasa gangansu ta ajiye tana ɗagowa surrayya na toshe hanci wai wari, bata ce komai ba ta je kitchen ta haɗo plates da spoons da cups ta zo, bazata iya dukawa a duƙe ta sa musu ba hakan yasa ta tafi kan gwiwowinta hannunta dafe da mararta da yayi mugun kullewa, a haka ta sassaka kan ta lallaɓa ta miƙe ta ajiyewa kowa a gabanshi..


Babu godi bare na gode haka ta fito, ɗan wadda ta rage a ƙasan tukunya ta zubawa Usman da Aisha, a chan ɗaki ta kular dasu sbd idan har uban su ze gansu suna ci babu abunda ze hana shi kikkifa mata mari da kiranta da suna ɓarauniya, ita ta dinga lallaɓa Usman da kyar ta samu ya ci kaɗan ya sha magani, sauran ta rufe ma yaran akan se anjima ita kuwa ta fito ta kankare tukunyar ta ci ta sha ruwa.


Tana rayuwa ne kawai ba don tana jin daaɗin shi ba, in har zata zauna ita kaɗai damuwa da Tunanin rayuwarta kan jefa ta wani yanayi me matuƙar wahala, sallama da ta ji ana dokawa ne yasa ta ɗago kai da sauri tana ɗan murmushi tace


"Ummi sannu da zuwa, yau ke ce a gidan namu?"


Wacce ta kira da ummi na jefanta da kallo me cike da tausayi tace

"ni ce hidayat"


"maraba Lale, karaso ciki" 

Ɗakinta suka shiga don bata son masifar su Aunty kausi ya bi kan ƙawarta Dukda ba haƙuri ne da ita ba sede su kwasa in dae ummi ce.


Da sauri ta karasa kan Usman da ta gani kwance tana taɓa shi tace 

"hidayat Usman ɗin ba lafiya ne?"


Kai ta gyaɗa mata tana cewa

"da sauki ma ai, ɗazu muka samo magani daga chemist"


Cike da wani yanayi ummi tace

"hidayat har se yaushe? Uhm! Har se yaushe zaki hutashe kanki da wannan azababban rayuwar?"


Manyan idanunta da suka rame se haske ta zuba mata kan tace 

"ummi in na Rabu da hamma Yusuf ina zanje? Gidan su fa zan koma, a da da nake buduruwa ma basu riƙeni da zuciya ɗaya ba se yanzu ga yara? Kin dae san halin umma tun muna makaranta ba ma ita kaɗai ba ina kike so na kai jidalin su Surayya?"


Girgiza kai Ummi tayi cike da dumbin tausayin hidayat kwarai da tana da taimakon da zata mata wurin neman dangin ta ko na uwa ko na uba da ta yi, wannan wahalar har ina? 


"Ina namesake ɗita?"


Hidayat na murmushi tace 

"yanzu ta tafi islamiyya, ya su Maami?"


"Suna nan lafiya"


Mikewa Hidayat tayi da kyar ummi na mata sannu taje ta ɗibowa ummin ɗan sauran shinkafar da ta rage ma yaran na dare da ruwa a cup, ta zo zata ajiye ummi tayi saurin mikewa ta karɓa tace 

"da na san tashin nan nawa ne da ban bari kin miƙe ba"


Murmushi kawai hidayat tayi ta zauna, ummin bata ci abincin ba ta barshi a rufen shi, ba kuma wai don kyama ko reni ba, ta san a tsabta babu na biyun hidayat tun suna school daga primary har suka kai ss1 hidayat ce ke samun prize duk speech and price giving day Inde best in neatness ne, duk da kuwa irin kangin rayuwar da take ciki.


Hira suka ci gaba da yi suna dariya, sossai ummi ke deɓewa hidayat kewa take kuma bata shawarwari, ummin ƙawarta ce sun yi school tare har zuwa ss1 kan kaddararta ya yanke karatun sbd babban bangon ta da ya faɗi ciwo wadda har kawo yanzu be tashi ba.


Duk yadda tayi da ummi taci abinci ƙi tayi akan ta ci kenan ta fito Dukda ba daga ma gida take ba, kawai bata son ci ne sbd ta tabbatar iya abinda hidayat ɗin ke dashi kenan ta bata, Allah yayi hidayat me son kyauta da karamci ita ko last kobo ɗinta ne ko da zata takuru ne zata ba ka, ta sha bata transport da kuɗin break ɗinta idan ta yar da nata, ummi gidansu basu kai inda Hidayat ta tashi hali ba hakan yasa ba'a zuwa ɗaukan su daga gida da mota sede a basu transport saɓanin su hidayat.


Sun sha hira ko tafiyar su fahariyya basu ji ba, se dab magrib ummi ta mata sallama zata tafi a nan ta ajiye mata 2k Dukda yadda hidayat ta nuna ba se ta shiga ɗawainiya ba, harara ummi ta zabga mata wadda ya sa ta dariya tace 


"to godiya nake, Dan Allah ki gaida min maami da su Noor"


Har ummi ta fice daga gidan bata sake waiwayawa ba, rayuwar hidayat na sakata kuka da tana da halin bata abunda yafi haka zata bata, ita yanzu take university wani lokacin se taji da ma hidayat ce ta samu wannan dama yadda kowa ya Santa da son karatu ga kwazo sede dubi inda rayuwarta ya ƙare.


 hidayat na shirin Juyawa kenan daga rakiyar da ta yiwa ummi ta ga shigowar ta, kan ta kauce ta bangajeta a razane tayi baya tana me zare idanu saboda tabbatarwa da tayi babu abunda ze hanata faɗuwa...


#like

#share 

#comment



           🖤Gureenjo🖤