Page 3
by @gureenjoh
KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*PAGE 3*
*FREE BOOK*
Tunaninta ya yanke ne a sadda taji ta dafe kyauren gidan tana sauke ajiyar zuciya da godiya ga Allah da be bari ta kai ƙasa ba, da kallo ta bi budurwar da ko waiwaye bata yi ba har ta shige sashen Yusuf, girgiza kai tayi duk cikin ƴan matanshi da yake kawowa gidan babu marar mutunci kaman firdous, in har ta zo ta dinga wahala kenan.
A ganin firdaus hakan ne ze rage mata kishin Hidayat tunda Yusuf ya ki sakinta, bata da masaniyar da tana da inda zata da bazata taɓa zama da wannan kadararren auren ba.
Tsaki tayi ita tun kawo ƴan matanshi na damunta har ya zo ya dena damunta kwata kwata, ɗaki ta shige ta kishingiɗa jefi jefi su kan yi magana da Usman Aisha ta tafi islamiyya, anan ne ma ta yanke shawarar ta fara sana'ar gawayi.
"Mama in na girma bazaki sake yin wahala ba, zan gina miki babban gida da mota in zuba miki masu aiki irin na gidan Alhj mudan"
Murmushi ta saki tana kallon Usman ɗin da tsakaninsu da Aisha kwata kwata shekara ɗaya da rabi kenan don yanzu yana cikin shekara na 6 da ƴan watanni, tace
"in shaa Allahu babana, Allah ya bamu yawan rai"
Cike da jin daaɗin ganin murmushinta yace "Ameen".
Ta miƙe tana saka hijab tace
"bari in shiga nan maƙota in nemi yaron da zan aika ya saro min gawayi a chan hanyar hadeija yafi kyau"
Yace
"Mama gawayi zaki fara sayarwa?"
Tace
"eh Usman, ka ga unguwan nan babu masu sayar da shi sossai kuma ana amfani dashi, dayawa se sun je layi na gaba suke samowa kaga zamu yi ciniki in shaa Allah"
Gyaɗa kai yayi yace
"Allah yasa kar su maman zubair su hana ki, kaman yadda suka zo nan suka hana ki sayar da kayan miya"
Murmushi kawai tayi tare da girgiza kai, yaran yanzu se a hankali komai sun sani, tana tafiya tana Tunanin yadda mutanen unguwan suka haɗe mata kai sbd ɗan cinikin da take yi a kayan miyan da take sayarwa karfi da yaji suka sa ta dena sana'ar su suka cigaba se a lokacin ta san eh lallai duk kankantar samunka wani baƙin ciki yake da kai, baƙin cikinta da sana'ar take samun na biyawa yaran nan ɗan kuɗin PTA da na islamiyya se kuma ɗan abunda zasu saka bakin salati Dukda shima ba na arziki bane, suturu kam ba'a magana.
Har ta isa gidan tana Tunanin duniya, da sallama ta shiga daga tsaye suka gaisa da matar gidan da ta kira da Asabe, kan ta ɗaura da
"Dan Allah ko a cikin yaran akwai wadda ke kusa aike ne nake ɗan so in yi"
Habiba dake kofan ɗakinta tayi Charab tace
"se kuma ki rasa yaran aike se na gidan nan?"
Bata kalleta ba idanunta na kan Asabe da Seda ta jira karshen maganan habiba kan tace
"kin ga kuwa wlh duk basa nan kiyi hakuri in sun dawo ko zuwa gobe se in turomiki ɗaya daga cikinsu"
Lantana dake zaune kofar ta tana tankaɗe tace
"munafunci da iyayin banza, in an ga dama a karɓa kawai a je yanzu ba se an jira yara ba karshen soyayya da tausayi kenan"
Habiba da Zulai da itama ta ɗaga labule tana jin Abunda suke faɗa suka kwashe da dariya.
Fita Hidayat kawai tayi ba tare da tace musu komai ba, bata san me ta tare musu ba ita rayuwar da take ciki ma kaɗai ya ishe ta, yadda suke mata ko tsakaninsu da suka Haɗa miji basa yi se da ita.
Asabe ta kallesu tace
"wlh bakwa kyautawa abunda kuke yi, baiwar Allahn nan tana fama da lalura ga wahalar rayuwa Dukda haka bata fasa baku girmanku na maƙota kuma ƴan uwa a musulunci ba, amma kun kafa mata karan zuƙa..."
Katse ta Zulai tayi wacce ita ce uwargidan su tace
"mu ji duka kan mu san kina yi Asabe"
Habiba tace
"Ah to!"
Daga haka bata sake magana ba ta cigaba da abunda take yi, waye be san irin rayuwar da hidayat ke yi a gidanta ba! Waye be san irin kaddararen miji da Allah ya Haɗata dashi ba! Ko basu tausaya mata don komai ba sa tausaya mata sbd cikin dake jikinta da kuma kankantan shekarunta cikin Kab matan da suke layin.
Hidayat kam na fita bata tsaya sake shawara ba ta taka zuwa bakin titi ta tsare machine suka yi ciniki ta hau se hadeija road, anan ta saro gawayinta se sauri take sbd magrib da ya karato gashi yaranta na gida su kaɗai, rokan me machine ɗin tayi ya kawo ta har kofan Gida Albarkar abun cikinta ya amince, anan ya dire mata buhun gawayin hannunta rike da leda wadda cikinshi ledoji yellow masu zanen baƙi ne ciki na kulla gawayin.
Almajirai ta nema suka shigar mata ciki ta basu hamsin, da gudu Aisha ta zo ta karɓi ledan tana mata sannu da zuwa.
Usman da ya samu karfin jiki ya kawo mata ruwa, murmushi tayi ta karɓa tana godiya duk halin da take ciki idan har zata zauna ko da na seconds da yaran nan nata se taji zuciyarta yayi haske, kaunar da suke mata ya samo asali ne daga tsananin tausayinta da suke ji, duk kankantar shekarunsu sun san duk abubuwan dake wakana a rayuwarsu, ita kuma burinta shine rayuwar su ta inganta, bata son ganin sun yi kukan wani abu bata taɓa Barinsu da damuwa ko da kuwa ita cikin ranta dankare yake da damuwar.
Hakin dake yawan damunta tai tayi Dukda ruwan da ta sha sede be dena ba, da kyar ta samu ya lafa ta kalli Aisha tace
"shatu! Ki shiga Gidajen maƙotan mun nan ki faffaɗa musu muna saida gawayi kin ji? Kar fa kiyi nisa iyakacin layin nan kinga magrib ya gabato"
Kai Aisha ta gyaɗa kan ta fice da gudu.
Seda aka fara kiraye kirayen sallah kan ta dawo tana bata labarin waenda suka yaɓa mata magana da waenda suka amshe ta suka ce se sun zo saya da waenda ko kallon arziki ba'a mata ba da waenda masu gadi suka koro ta daga kofar gidan.
Tana ta murmushi kawai tana matse kafafunta da suka kumbura, Seda suka saki kan ta mike tayi alwala suka gabatar da sallarsu a tare, anan suka zauna suka yi azkar don duk rintsi bata barin su su kwanta ba tare da sun yi azkar ba haka bayan sallar asuba, karatu suka ɗan yi na Qur'ani kan ta basu abincin da ta rage musu, yaran na da tsananin wayau hakan yasa basu ce mata komai ba sede fa duk wadda yayi loma ɗaya ze sa mata ɗaya idanunta cike da hawaye take karɓa har suka gama suka sha ruwa suka zo suka kwanta sbd basa fita ko ina daga magrib yayi, in sun yi isha kuma haka zasu kwanta suna hira tsakaninsu har bacci ya sace su hakan yasa yaran nata ke da tsananin kulafucinta wani irin shaƙuwa da kusanci ke tsakanin su.
***
Alhamdulillah Hidayat ta fara sana'ar gawayi kuma daidai gwargwado tana samun ciniki sbd kafin sati buhun ya ƙare ta samu napep ta je ta sayo buhu biyu ta cigaba da sana'ar ta sbd ita tun daga washegarin ranar da ta fara sana'ar gawayi bata sake saka Yusuf a ido ba tun kuma 1k da ya wurga mata.
Usman ya warke garas yanzu ya koma makarantarshi boko da Islamiyya, ita kanta ba yaran ba hankalinsu a kwance yake na rashin saka Yusuf ɗin a idanu sbd a sake suke komai ba tsoro da kaffa kaffa.
Da ɗan cinikin ta ta fara tara wasu abubuwan da suke dole wurin haihuwa sbd tana da tabbacin ko yau ko gobe zata iya tashi da naƙuda don har ta ma wuce Edd ɗinta.
Yau haka kawai ta tashi da son ganin Abba, hakan yasa ta ajiye duk wani fargabarta da tsoron ta ta shirya cikin kodaddun kayan ta da hijab ɗinta da yayi fari fat sbd koɗewa ta fita ta hau achaɓa, cikin sanyin murya ta faɗa mishi unguwar da ze kaita cikin mintuna kasa da talatin suka isa ta sallameshi gabanta na faɗuwa ta shiga gate ɗin gidan.
Allah ya taimake ta bata gamu da kowa a wakeken tsakar gidan ba har ta isa sashen Abba, da sallama ta shiga uwar ɗakin se suka Haɗa idanu da dattijon a take ta saki murmushi shima fuskanshi a take ta washe baya iya magana amma a cikin idanunshi ta karancin murnar ganinta da yayi, babu abunda ya raba shi da Yusuf se tsufa da ze nuna mishi.
Da sauri ta karasa gabanshi ta duƙa tace
"sannu Abbana!"
Kallon cikinta yake yi, hakan yasa ta miƙe tana fahimtar so yake ya hanata duƙawar sbd cikinta tana murmushi tace
"ya jiki Abba? Allah ubangiji ya baka lafiya yasa kaffara ne wannan ciwon"
Idanu ya lumshe, yana me kallonta tace
"Abba su Aisha na gaisheka duk suna lafiya sun je islamiyya ne yasa ban taho dasu ba"
Sake lumshe ido yayi ya buɗe tace
"Abba ka sha maganin ranar ka kuwa? Abba ya kake zaune kai kaɗai?"
Bata jira Cewarshi ba ta gyara ƙimar ɗinta ta taimaka mishi ya zauna da taimakon Allah ta mayar dashi kan kujerar shi na turawa wato wheel chair sbd ganin rashin tsabtar ɗakin da take, ta turo shi varender inda yake shan iska, komawa tayi ciki ta fara da wanke bayi, ta gyara bedroom ɗin zuwa parlorn Kal Kal ta saka room fresheners dake ɗakin ta ɗan kara Ac sbd zafin da garin ya ɗauka yanayi ne da damina ke dab da sauka hakan yasa a kullum zafin ke kara yawaita.
Bayan ta gama ta miƙe da kyar sbd bayanta da ya kage ta koma ta turo shi suka dawo, kunun da ta samu a flask ta tsiyaya ta bashi da spoon dukda rabi ke shiga rabi na zuba haka ta bashi ta goge inda ya ɓaci a jikinshi, nan ta zauna kasan kafan shi ta miƙe kafa tana ta bashi labarai tana murmushi.
Hidayat is a strong girl/woman he has ever seen a rayuwarshi, lumshe ido yake yana me mata Adu'a a zuciyarshi Allah ya gani ya bata Yusuf ne da tunanin ze riƙeta amana ya kula da maraicinta be san ganganci yayi ba seda lokaci ya kure, ba yadda ze yi ne yake ganinta cikin wannan kangi na rayuwa, a kullum ya kan roki Allah lafiya ne sbd ya samu ya kwatar mata hakkinta.
Yarinya ce da ta tashi cikin wahala ta Rayu cikin wahala tayi aure cikin wahala, she deserves a better life, natsuwa, hankali, ilimi da kyau Duka tana dashi why life choose to be so rude to her? She's so jovial faram faram ce da matukar wuya ka fahimci damuwarta.
Duba yanzu kaman ba shi ya haifi iyalin da suke gasa mata aya a tafin hannu ba, duk ranar da ta zo wurinshi ya kan tsinci kanshi cikin farin ciki sbd yadda zata zage ta bashi kulawa tayi making time ɗin lively da hirarrakinta ta tsabtace mishi muhalli wadda matar da yake aure kuma uwar Yayanshi bata mishi ba, duk cikin yaranshi babu me tsayawa yi mishi wannan hidima se me aiki, be taɓa sanin wani lokacin kuɗi kan zama masifa da bala'i ba seda wannan kaddarar ta same shi, da shi ɗin talaka ne, da lokacin neman kuɗinshi be shiga lokacin iyalinshi ba da ya dasa shakuwa da tausayi a zuƙatarsu, ya kan ga laifukanshi a kaso mafi yawa cikin abubuwan da suka faru da rayuwarshi kuma yana ɗaukan darasi in ya mutu falillahil hamd idan kuma yana da rabon lafiya ze yi iya kokarinshi wurin ganin ya gyara.
"ABBA..!"
Hidayat ta kirashi tana waving hannunta fuskanta cike da shagwaɓa wadda ya fidda asalin ainihin kananun shekarunta tace
"ko Hirar bata maka daaɗi ne naga idanunka sun sauya kala?"
Idanun ya zuba mata se ya lumshe su alamun a'a, tace
"in cigaba?"
Ya sake lumshe mata idanu, idanunta ne suka sauka kan agogo ta wara ido yaran suna gab da dawowa bazata so su dawo su tarar bata nan ba, mikewa tayi tace
"Abba zan tafi zaka kwanta?"
Ya lumshe mata idanu sau biyu alamun a'a sbd ya gaji da kwanciyar, hannunshi yake ta motsawa wadda yatsu biyu ke iya ɗaguwa hakan yasa ta fahimci magana yake son mata, kallon inda yake kallo da kokarin pointing tayi taga bedside drawer ɗinshi ne ta kalleshi tace
"A'a Abba ina da kuɗin machine"
Haɗe fuska yayi yaki kallonta hakan yasa ta fahimci fushi yayi, se ta taka zuwa wurin ta buɗe tare da sa hannunta akan kuɗin zata zare 1k kenan aka turo kofan, karab idanunsu suka haɗe wadda ya haddasa mata mummunar faɗuwar gaba da sauri ta miƙe sbd Kab duniya babu wacce take kallonta taji hanjin cikinta ya kaɗa irin umma, ta gana mata azabar da ko sunan umma taji an kira se gabanta ya faɗi.
"La'ila ha'illallahu Muhammadur rasu lillahi salla lahu alaihi wa sallama... Sata? Hidaya abunda kika koma Kenan? Ɓarauniya..!"
#like
#share
#comment
🖤Gureenjo🖤