KOWA YA GA ZABUWA…

Page 4

by @gureenjoh

KOWA YA GA ZABUWA...

  (DA ZANEN TA YA GANTA)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.       

     (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

And Now 

*Kowa Ya ga zabuwa..*


           *PAGE 4*


*FREE BOOK*


Cikin rawar murya tace 

"A'a umma don Allah kiyi haƙuri wlh Abba ne ya matsa na ɗauki kuɗin machine shine zan zari dubu ɗaya.."


Wasu Zafafan maruka hagu da dama ta ɗauke ta dashi wadda Seda ta saka ta kaiwa kasa tana ji kaman amsa kuwwan maganan umma tana cewa 

"Munafuka! Algunguma sharri zaki yiwa Alhajin? Ina ya ga bakin magana da har ze matsa ki ɗauki kuɗi? Idan ba salon sata ba me yasa da kika shigo baki shiga cikin Gida ba kika sulale nan? Eyee wato da mudi me gadi bai ce min kina nan ba sede mu zo mu samu an wawushe Alhaji? No wonder kullum kwanan duniya ake samun kuɗi ya ɓata.."


Hawaye ne masu zafi suka zubo mata, ta sa hannu ta goge har lokacin bata ji daidai sbd umma ba bahaushiya bace irin kabilan kudun nan ce da suka ginu da tuwo da wahala hakan yasa hannunta na daga cikin hannun da in ta sauke maka se ka rasa natsuwa da ji na tsawon lokaci, cikin rawar murya tace 

"Wallahi ban taɓa ɗaukan abin wani ba umma kuma ke sheda ce, da ina sata da tun kan nayi aure da kin sani Allah ya gani b..."


Gwaɓe mata baki tayi wadda Seda ya fashe umma tayi.


"Rashin kunya kuma zaki min? Eh lallai dole.. Karki ga kaman kin haihu biyu ko kina da tsohon ciki wlh baki sauya a idanu na ba, be dame ni ba yanzu in lakaɗa miki na jaki in ga uban da ya tsaya miki a garin Kano, banza ƴar Zina...."


Faɗuwar mutum da suka ji yasa duk suka juya, Jijjiga Abba ya fara wadda har yana sulmiyowa daga cikin kujeran ba tare da sun kula ba seda ya faɗi.


Da gudu suka yi kanshi suna kiran sunanshi, umma na shikenan ta kashe min shi ta huta.


Kaman daga sama se ga Yusuf da kaninshi mus'ab da gudu suka ɗauki Abba suka fito zuwa mota.


Hidayat bata tsaya ba ta shiga motan tare da kafe shi da idanu tana zub da kwallar takaici da baƙin ciki, babu wadda ya kula sbd tashin hankali suka ja suka yi asibiti umma ta biyo su da motan ta, suna parking a harabar kumfa ya fara fita daga bakin Abba hankali tashe Hidayat ke share mishi da hijab ɗinta.


Buɗe idanu yayi ya kafe ta da shi, wani natsuwa da karfin gwiwa ta samu a take ta fara karanta Kalmar shahada abu da ikon Allah mutumin da ya shekara ɗai ɗai har shekaru bakwai da watanni a yanayi na jinya da rashin magana da tsananin ciwo ya buɗe baki kalmomin na fita a rarrabe ya fara cewa 


"Kiyi haƙuri da rayuwa, ki yafe min hidaya!"

Sune suka fito kaman an fusgo su daga bakinshi, kalaman da suka yi sanadiyar karasa ruɗata tsabar hawayen dake kwaranya har bata iya gani da kyau tana girgiza kai tace 

"baka min komai ba Abba..! Baka min komai ba..!!"


Murmushi yayi se ya fara karanta Kalmar shahada daga karshe numfashinshi ya tsaya Chakk.


Daidai lokacin da Yusuf ya fisgota waje ba tare da yayi la'akari da cikin jikinta ba, isowarsu kenan da gadon marasa lafiya don a ɗauki Abba sede likitan na lekawa yace 


"Innalillahi wainna ilahi rajiun! Sede haƙuri Allah ya riga ya amshi abun shi"


Ihu umma ta kwala, yayinda hidaya da ta riga da ta san da mutuwar sede bata yardar ma zuciyarta ba seda taji daga bakin likitan, chaak duniyar ta tsaya mata Sam bata san me suke yi ba.


Idanunta sun yi ja ga hawaye masu zafi suna gangarowa, ji tayi kirjinta ya mata nauyi ga wani zafi da yake aikin yi mata kaman ze kama da wuta ko ya riga ya kama, Ko sunanta zaka tambaya a lokacin tana da tabbacin bata san daga wata kalma ta fara ba tsabar tashin hankali, shikenan ita kuma alqiyamarta ta tsaya, bangon ta, jigon ta ya rushe ya zube! Shikenan fah bata da kowa da ya saura mata a duniya shikenan! 

Wani irin jiri ya ɗibe ta ta duƙe bisa gwiwowinta ta fashe da wani irin kuka da dukkan zuciyarta kaman wacce aka lodawa gabaɗaya damuwan duniya a kirji.


17 YEARS EARLIER 


Yarinya ce ƴar kimanin shekaru biyar tsaye jikin rariya Dukda Duhu da sanyi irin na asuba da ya mamaye garin ita tsaye take tunbur babu ko ɗan kamfai a jikinta, banda rawar sanyi babu abinda take yi hawaye kuma wani na bin wani a idanunta sbd jikinta dake raɗaɗin duka da taci da asubahin Allahn.


"Tsaye kika yi baki watsa ruwan nan kin zo kin fitar da kayan nan kin wanke ba?"


Da sauri ta ɗauki bocket ɗin ruwan ta kwarawa jikinta bayan ta ɗauke numfashi saboda azaban sanyin shi musamman umma ke ajiye shi ya kwana buɗe yadda ze yi sanyin da se ya kusa daskarar da gudun jininta.


Bayan ta gama ta taka a hankali zuwa cikin ɗakin ta ɗauki rigar ta da ya koɗe wadda kuncen Surayya ne ta saka, dukda ba wai ta girma bane ga rashin girman jiki da ya mayar da ita ƴar pirut ta ɗauko ledan pitsarin da zanin ta koma chan baya ta wanke ta shanya a saman soak away sbd tsawon ta da baya kaiwa igiya.


Har ta dawo ɗakin dukkansu yaran gidan na kwance suna bacci, tsabar kwarewar umma a mugunta Dukda akwai masu shara sede ita ɗin de ita zata yi a Cewar ta bata kai matsayin ƴan gida ba kuma dole ta dinga tunawa da ita ɗin Ɗiyar Riƙo ce, haka ta daddage tayi ta shara in be fita ba ta koma ta sake sbd a haka ta saba, se a lokacin yaran gidan suka tashi, manyan suna wanka da kansu yayinda yaran se de ayi musu har Surayya kuwa dake sa'ar ta, bayan sun gama aka shiryawa kowa breakfast ɗinshi wadda dankalin turawa ne da shayi me madara.


Raƙubewa tayi jikin dining ɗin tana jiran su gama ta bi plates wadda suka rage ta ci, hakan kuwa aka yi bayan sun koma parlor kowa na saka safa ta tashi ta bibbi plates ɗin ta cicci wadda suka rage ta tattare ta kai kitchen, ta dawo da sauri ta je ta saka uniform ɗinta sbd sun fara ficewa in kuwa ta ɓata musu lokaci ba karamin duka zata ci ba.


Bayan ta saka bata tsaya sa safa ba ta riƙoshi a hannu da jakanta ta fito da sauri, a gaban Abba ta same su da shima ya fito ze tafi wurin aiki, tun daga nesa ta sakar mishi murmushi shima yana murmushi har ta ƙaraso hannunshi ta riƙe tace 

"Abba ina kwana?"


Yace 

"lafiya ƙalau hidayat, an shirya kenan?"


Kai kawai ta gyaɗa sbd bata da yawan magana, hannu ya sa a aljihu ya ciro hundred hundred Naira ya ba kowaccen su, godiya suka yi kan suka yi mota a lokacin Yusuf na Level one a university.


Khausar da suke cewa Aunty kausi tana js2 se Mus'ab dake primary 6, se Salamatu dake pri 5, fahariyya tana Primary 4, se ita da Surayya dake primary 2, babu wacce ta mata kallon arziki a cikinsu sbd bata takale su ba inda ta saba duƙawa a ƙasan motar wurin ajiye kafafu ta duƙa don bata da darajar zama a seat har suka isa makarantar, kaman yadda ta saba seda ta kwashe jakkukkunansu ta kaiwa kowacce class ɗinta kan ta ɗauki nata dana surayya ta kai musu class, a seat ɗinta ta ajiye mata kan ta wuce nata ta zauna kusa da ummi.


Kaman ka'ida ana tashi ta bi ta tattare jakukkunan ta kai musu mota kan ta tsuguna a mazauninta suka kama hanyar gida, ko da suka isa gida ma a nan parlor suka dinga cillar da abubuwansu tana tattarewa tana kaiwa inda suke tara kayan na wanki, a ɗakin nasu chan lungu aka shimfiɗe mata taburma da zanin gadon da bata san shekarun shi ba alhali kowacce a cikinsu da gadonta na katako a wakeken ɗakin.


Anan ta cire uniform ta sauya na islamiyya ta fito, lokacin sun yi nisa da lunch inda ta saba zama ta zauna, minti minti wannan ze aike ta wanchan zata aike ta har suka gama, ta tashi ta bi plates ɗinsu ta ci abinci kan ta tattare ta kai kitchen, ganin babu wacce ke da niyyar zuwa Islamiyya cikinsu yasa ta fice.


Wuraren karfe biyar ta taso daidai kofan gate suka haɗu da Abba wadda driver ya dawo dashi daga office, bayan ya shiga be shige sashen shi ba se ya jirata har ta karaso ta gaida shi cike da kulawa ya amsa yace 


"hidayat ina ƴan uwanki? Me yasa baku taho tare ba duka kuke tafiya daban daban?"


Cike da yaranta tace 

"Abba ai basu je ba, ni kaɗai na je"


Ya jefa mata tambayar

"ko me yasa?" Da sauri.


Tace 

"nima ban sani ba Abba"


Hannunta ya kama suka wuce sashen umma, a parlor ya same su baje, masu kallo na yi masu danna waya na yi be yi wata wata ba ya zare cable ɗin TV Seda ya ba kowacce biyar biyar kan ya ja musu kunne akan ko da wasa ya sake samun su ran islamiyya basu je ba sun zauna suna shashanci yana kai nan ya fice.


Tunda aka fara dukar taji kaman fitsari na shirin kubce mata don ta san yau yankata ne umma ba zata yi ba, yadda take ƙaunar yaranta ko kuda bata so ya taɓa su, tunda Abba ya fice ta zube bisa guiwowinta cikin shesheka take cewa 


"Wallahi ba ni na faɗa mishi ba, umma wlh ban faɗa ba.."


Mikewa umma tayi ta nufota, yarfe hannu kawai take tana wayyo Allah, ko da umma ta iso ɗankwalinta ta cire ta cusa mata a baki tare da fusge hijab ɗin kanta ta ɗaure bakin yadda ihunta baze fita ba ta fara jibga kaman me faɗa da sa'ar ta.


Zata iya cewa ta suma a lokacin sbd azaba ga ba halin ihu bare roƙo, Seda umma taga tana shirin kashe rai kan ta sauka ta wuce ba tare da tace uffan ba ta karkaɗa kan yaranta zuwa ɗakinta, dab kofa ta waigo ga hidayat dake yashe ko motsin kirki bata yi ba tace 


"saura in ga gilmawarki da sunan neman abincin dare wlh wannan kaɗan na miki"

Tana kai nan suka shige.


Me aikinsu dake tsananin tausayin hidayat ɗin ce ta zo da gudu ta sunce mata bakin tare da ɗago ta ta bata ruwa tana share hawaye, wani irin rashin imani da tausayi ne wannan? Seda ta sha sossai kan ta taimaka mata zuwa makwancinta sauri sauri take komai don in umma ta ganta akwai matsala, bayan ta kwanta ta fice ta kwaso kayan fitsarin ta ta zo ta mata shimfiɗa ta taimaka mata ta kwanta.


Hidaya bata sake motsi ba sbd azaba da ciwo har Seda taji zuban ruwan sanyi a jikinta, a razane ta miƙe ganin yau bata yi fitsari ba yasa umma jan tsaki ta fice tayi niyyar yau tana kwaran ruwan sanyi tana shwaɗe ta ne se Allah ya taimake ta.


Da zazzaɓin tayi shara ta shirya makaranta inda suka saba haɗuwa da Abba ya basu kuɗin break suka haɗu yana kallonta yace 

"me ya sameki hidayat?"


Tace 

"Abba kaina ne yake ciwo"


Yace 

"sannu kin sha magani?"


Kai ta gyaɗa don gudun fitina, yace 

"Ina lunchbox ɗin ki?"


Tace 

"yana mota" alhali bata da shi don ba'a taɓa sa mata abinci a foodflask ba.


Sallamanta yayi tare da Adu'a, har suka tashi school hidayat na fama, daga karshe tayi ta kuka a islamiyya Seda wani malami ya kaita chemist aka bata magunguna.


Rayuwar hidayat a haka ya saba tafiya kuma a haka yake tafiya, inda take samun sauƙi ɗaya, Abba! Shi kuma ba me sa ido bane kan iyalinshi rayuwa ake na Turai, sede ko makaho ya shafa ya san hidayat na cikin Matsin rayuwa.


Saboda azaban umma ta dena fitsarin kwance, tana da shekaru bakwai ta fara girki a gidan da dolen dole, gishiri yayi yawa ta daku, Maggi be ji ba ta kirɓu, yayi ɗanye a kusa yankata haka bautar su Aunty khausi kullum tana cikinta.


Yau tunda aka tashi school bata jin daaɗi amma haka da ta dawo Seda tayi duk wani aiki da yake nata, an kara mata wanke wanke sbd umma tace bazata zauna tana ci da ita da tufatar da ita a banza ba, girkin dama Friday, Saturday and Sunday ne take yi.


Bayan ta gama wanke wanke ta tattare ɗakin da suka hautsina da gangan ta fito ta bibbi plates ɗinsu ta ɗan ci abinci kan ta shirya islamiyya ko kan a tashi zazabi ne sossai ya rufe ta, da suka dawo da kyar tayi magrib da isha bata fita neman abinci ba haka tayi bacci, washegari a school ta samu health prefect ta bata paracetamol, karfe 11:10 na yi malamin basic science nasu ya shigo.


Nan ya fara karɓan assignment, Surrayya ta miƙe ta zo gaban Hidayat tace 

"ke ina assignment ɗina?"


Da sauri hidayat ta ɗago gabanta na faɗuwa tace 

"banda lafiya ban yi ba"


Wani irin ashar ta lailayo ta zuba mata, kafin ta ɗaura ummi tayi saurin cewa 


"Auzubillah, ke Surayya me na zuwa mana desk kina wannan ashariyar ke hannunki me yake yi da ba ze yi assignment ɗin ba?"


Bata jira cewar Surayya ba ta juya ga hidayat tace 

"kema wlh ban ga dalilin da ze sa kullum in dinga yi mata assignment ba haka kawai, ba aji ɗaya muke ba kuma malami ɗaya duk ke koyar da mu ba?"


Hidayat zata yi magana sbd irin kallon da Surayya ke mata kenan malamin ya iso desk ɗinsu, ummi ta Haɗa da nata da na Hidayat ta bayar sbd ta karɓi littafin don ta kwafi note sbd bata zo makaranta ba shekaranjiya shiyasa tayi musu assignment ɗin duka.


Ai ko malami kam ya fidda waenda basu yi ba ya basu biyar biyar, tun ana dukan Hidayat ke kuka tana yarfe hannu zuciyarta kaman ya fito don bugawa yau umma zata kashe ta, ta bari an daki yarinyarta shikenan.


Surayya ta dinga kuka har aka tashi makaranta duk idanunta suka kumbura, a lokacin aka nemi Hidayat aka rasa babu inda basu zaga ba basu ganta ba, haka suka dawo gida drivern da kanshi yayi sallama ya faɗawa Abba an tashi hidayat bata makaranta...



#like

#share 

#comment



           🖤Gureenjo🖤