Chapter 2
by @gureenjoh
⚡️*GAMON JINI*⚡️
*NA FATIMA MOH'D GURIN*
*GUREENJO*
*E.W.F*
*PAID BOOK*
*FREE PAGE TWO*
*TAURARI BIYU⭐️⭐️ DAGA TASKAR MARUBUTA BIYU✍️✍️*
*****
Garin yaya kaji rauni haka Lamido? Subhanallah khalid shigo mana ka duba min shi..."
Tuni ta kama Lamidon zuwa kan gado tana kwance d'aurin da yayiwa wurin da hannayenta gabad'aya ta shiga damuwa, hannunta ya rike yana d'an Murmushi yace
"Amah is not that serious fah...."
Buge hannunshi tayi tace
"Shut up"
Ta juya ta kalli kofa khalid na tsaye kanshi ne kawai ciki duka jikinshi na waje, tace
"Khalid Wai baza ka shigo ba?"
Yana ta Kallon yarinyar da ni kaina ban san wacece ba yace
"Amah baki ga da aljana Yayanmu ya dawo ba? Ko kema baki ganinta kaman shi? Ni kad'ai nake kallonta?"
Se lokacin hankalin Amah ya je kan yarinyar, bata kawo komai ba ta nufe ta tana cewa
"Subhanallah baiwar A...."
Ihun da ta tsala tana komawa bayan shi ta rike riganshi seda ya tsorata su duka, shi Amah take kallo yayinda shi kuwa idanunshi ke kan hannunta dake damtsen shi, seconds biyar ya d'auke idanun shi tare da kallon Amah, khalid kam tuni ya koma ko kan nashi ba'a gani.
A sanyaye Amah tace
"Lamido ina ka samo ta? Bata da lafiya ne?"
Cewa yayi cikin gajiya
"Amah taimakonta nayi I think bandits sunyi kidnapping d'inta se Allah ya turo ni ta hanyar na taimaketa but since then taki magana sannan motsi kad'an se ta rikeni I don't know why"
Cike da tsantsar tausayinta har hawaye na cika a idanunta tace
"Allah sarki baiwar Allah..."
juyawa tayi tana duba khalid sede ba shi ba alamun shi, dariya tayi tana girgiza kai tace
"Kaikam khalid matarka na kokari..."
Juyowa tayi tace
"Lamido bari In dubo khalid d'innan se ya zo ya duba Ku gabad'aya ko zata samu sauki samu Mu san inda ahalinta suke na san duk in da suke hankalinsu ba a kwance ba"
Mikewa yayi yace
"Amah bara na duboshi kema fah baki da lafiya"
Cewa tayi
"No gwara in je sbd ita bazata yarda ta zauna dani ba, kuma be dace kana tafiya da ita a haka ba ba d'an kwali ba takalmi tana bukatar hutu"
Bata jira cewarshi ba ta fice, kallon ta yayi kanta na kasa gashinta Har yanzu ya rufe mata fuska ruf, Allah ya sa ba masifa ya nemarwa kanshi ba, idan ze tuna tunda ya ceceta banda muryan kukanta be ji tayi magana ba, sannan wannan nanukewar na me? Shi da idan batayi magana ba yana son barinta wurin Amah ya koma aiki in ta samu lafiya daga baya ta koma gida.
Dan kallon d'akin yayi kan cabinet d'in gadon ya kalli robber lin da alamu wani abin aka warware dashi, d'aukowa yayi ya dawo ya zauna, a ranshi yana furta
'I'm just helping you, duk abinda zanyi miki I will do it out of pity...'
Hannunta ya kama ya zaunar bakin gadon ya saka hannayensa biyu ya had'e gashin nata zuwa baya ya d'aure mata tare da kurawa fuskanta ido.....
Abinda be ta'ba yi ba a rayuwarshi wai ya kurawa mace ido na fiye da minti d'aya se a kanta, ko ba komai baze mantata ba ta kafa tarihi a rayuwarshi, 'Tana da kyau' ya Ayyana hakan yana kallon daran darán idanunta da suke kasa.
"Baiwar Allah...!"
Shiru bata d'ago ba, yace
"Ya sunanki?"
Kawai se ta fashe da Kuka, Sossai take Kuka tare da rike hannun shi se ta fara nuna mishi waje, idanunta da suke zubar da hawaye yake kallo, zuwa lips d'inta da take motsawa a hankali alamun tana so tayi magana sede ta kasa ne be sani ba....
Rubbing goshin shi yayi yana kara kasa da murya sbd kanshi da ya fara sarawa yace
"Is Ohk.... is Ohk baki so a tambayi sunanki? Toh bazan sake ba i will just call you Amatullah... Ohk?"
Kanta ta mayar kasa hawaye na ci gaba da tsiyaya kaman an bud'e pampo a ranshi yace 'yaushe na zama parrot?'
Tsaki yaja sbd urge na ya rarrasheta ta dena kukan ne ya ke hawanshi.
'Someone please come to my rescue' ya kuma Ayyanawa kan ya gama aka turo kofar.
'Alhamdulillah' ya furta kan ya kalli kofan, Amah ce da khalid se murmushi take sakewa sbd dramar da suka sha da khalid shi be yarda ita mutum bace, da kyar ya amince ya biyota harara Abrar ya watsa mishi yana tsaki kaman ba ze yi magana ba kuma se yace
"Ina mace Wlh ban ga dalilin aurenka ba mata maza kawai..."
Tura baki yayi, ba hali yayi magana sbd ba alamun wasa a maganan yayan nasu da ma Abdulkadir ne Allah se Amah ta raba fad'a, kayan aikinshi ya d'auko ya fara yiwa yayan nasu dressing ciwon nashi Sossai kuwa bullet d'in ya goge shi don seda ya mai dinki, se kallon fuskan yayan nasu yake sede ko gezau alamun ya san ana ta'ba jikinshi ma be nuna ba ya Lumshe ido yana tunanin wani kaddara ne ya jefo da Amatullah rayuwarsu, tunani ba d'abi'arshi bane so yayi saurin yakice tunanin ya fara karatunshi a hankali.
Amah ta koma kan darduma ta zauna tare da dukar da kai don bata son ganin dagula ciwon da ake yi in ji ta da fad'e, yayin da Amatullah (sunan da Abrar ya rad'a mata) take bayanshi kanta na a kasa Har lokacin tana rike da riganshi sbd Khalid dake tsaye a wurin, bayan ya gama da shi ya dubeta kan ya ce
"Yayanmu ita kuma me za'a mata?"
Harara Abrar ya watsa mishi ba tare da yayi magana ba, Amah tace
"Yanzu a matsayinka na likita se an ce maka yarinyar nan na bukatar a dubata?"
Shafa kai yayi yana D'an kallon Abarar da be kara kallonshi ba, ganganta ya d'an matsa se ta koma baya ta kara rike Abrar, yace
"En mata ya su......"
"Amatullah..!"
Abrar ya furta ba tare da ya kalleshi ba, a tare suka kalleshi da Amah sede ba wadda ya tambaya ina ya sani sbd sanin halinshi.
"Amatullah me yake damunki? Me kike ji a jikinki yanzu haka? Feel free you are in a safe place no harm will come to you Ohk?"
Shigen muryansu d'aya da Abrar hakan ya sa ta d'an d'ago ta kalleshi na seconds ta maida kanta kasa.
Khalid yace
"Ina ga tana cikin shock ne ko wani abu ya faru da ita da ya sanya ta tsorata Sossai, tana bukatar kulawa na mussaman daga likitocin da suka shafi bangaren, dole kuma se an yi Admitting d'inta"
Abrar yace
"How sure are you zata samu kulawar da ta dace?"
Se da ya d'an kalli yayan nashi da yau yake magana sossai kaman ba shi ba yace
"In Allah ya yarda zamu yi iya kokarin mu, yanzu Bari na fara zuwa na duba Doctor d'in se a bud'e mata file ko Zata yarda ta bini?"
Kallonta Abrar yayi kanta kasa yace
"Amatullah.... ki bishi ku tafi baze cutar dake ba Ina da tabbacin yadda zan kareki haka shima kin ji?"
Kaman karamar yarinya haka ta make kafad'a tana sake rike riganshi tsawa ya daka mata sbd be da hakurin rarrashi sam be ma iya ba, tsoratar da tayi yasa tayi baya Zata fad'i numfashinta ya fara barazanar ficewa daga jikinta Khalid ne yayi hanzari tare ta, ta kuwa suma a hannunshi...
Amah da tayi saurin tahowa tana cewa
"Haba Lamido da hankalinka? Kana ganin yanayinta duk a firgice kake kuma kara tsoratata yarinya ce fah se da lallami, Khalid yi sauri ka Kira likitan Dan Allah"
Mikewa yayi daga bakin gadon ganin khalid na kokarin kwantar da ita, da sauri ya fice a d'akin zuwa kiran doctorn da ya dace ya dubata shi kuwa Abrar zaman shi yayi kan carpet d'in dake shimfid'e da sallayar Amah bakinshi na cigaba da motsi da alamu karatunshi yake yi hankalin shi kwance...
Amah dake rike da hannun Amatullah ta kalle shi ta sake, ko a jikinshi kaman be san me yayi ba, wannan hali na lamido na damunta sede ya ta iya? Haka ta Haifi kayanta sam be tsinci halin a titi ba...
Shigowar Khalid da wasu likitoti biyu da nurses biyu ne ya katse mata maganan zuci da take, da sauri ta matsa suka hau dubata, cikin ikon Allah suka samu ta dawo hayyacinta sede bata bud'e ido ba se Hawayen dake bin gefen idanun nata zuwa kunnenta, umarni d'aya doctorn yayi da su d'auketa zuwa wani d'aki a bud'e mata file, da sauri d'ayar ta fice ta turo gado ta dawo sede suna rike hannun Amatullah da niyyar d'agata tayi Wani irin karan azaba.....
Da sauri suka saki suna kallonta, se "Ashhh Ahhh wayyo Allah" take cewa, Doctor Ahmad yace
"Anya yarinyar nan ba sikila ba Doctor Khalid?"
Abrar Khalid ya fara kallo sede ganin be ma nuna ya san wainar da suke toyawa ba yace
"I have no idea sede in za'a yi mata blood..."
"Wayyo Inno zan mutu kirjina... ku danna min... wayyo bayana waiii Allah..." a take ta fara fita hayyacinta tana Wani irin kuka da duk seda suka ji jikinsu yayi sanyi, gashi taki su ta'ba ta daga sun Kai hannun da niyyar ta'bata se ta tsala ihu tana zafi, kar su ta'ba ta Zata mutu..
A lokacin ne ya iya d'ago lulu eyes d'inshi ya watsa musu, Yana jin haushin yadda duk suka tsaya jiki a sanyaye suna kallonta kaman basu san aikinsu ba, mikewa yayi ya nufi gadon tare da yin magana a natse cikin bud'add'iyar muryarshi me fita da wani amo me jan hankalin duk wadda yayi katari da sautinsa yace
"Amatullah... kin manta da wani abu guda d'aya babu me kawo miki sauki se Allah mad'aukakin sarki kiyi shiru ki dena wannan kiraye kirayen ki ambaci Allah a zuciyarki kuma ki Bari su d'aga ki su duba ki...."
Runtse idanunta tayi cikin wahala tana ji kaman Ana kakkarya kasusuwan jikinta ne ana had'awa Allah kad'ai ya san me take ji sam baza su gane ba...numfashi take ja da kyar tana furta
"Ya qahharu... ya rabb Arrahmanur raheem... hasbiyallahu wani'imal wakeel"
A haka suka samu suka maida ta d'ayar gadon suna turata suka fice da sauri, da kallo ya bi gadon har ya bar d'akin kan ya maida kanshi kasa tsananin tausayinta na ratsa shi, yanzu cikin wannan hali na rashin lafiya cikin wannan yanayi me azabtarwa waennan marasa tsoron Allahn suka rabata da gidansu da en uwanta suka kaita dokar daji don su cutar da ita.... wannan Wani irin rashin imani ne? Anya su ma da suka d'auki Alkawarin kare alummar kasarsu Allah baze tambayesu ba? Shin me mafita ne?....
"Lamido..."
Ajiyar zuciya ya sauke kan ya d'ago Yana kallonta da idanunshi da zuwa yanzu sun rine, zuciyarshi ta shiga tsananin damuwa da tausayin duk waenda suke hannun waennan mugaye na duk fad'in Nijeria kila wasu masu rauni ne irin Amatullah, kila masu ciki, kila tsofaffi kila kuma mata iyaye irin su Amah....
"Zata samu lafiya In Shaa Allah"
Ta furta tana kallonshi, kai kawai ya gyad'a kaman yadda ta san ba magana ze yi ba, ta kuma cewa
"Ko zaka tafi gida ka huta kan lokacin Sallah?"
Girgiza kai yayi, tare da komawa kan carpet ya zauna a kasalance yace
"Amah ki kwanta, kina bukatar hutu ni da khalid zamu kula da komai"
Bata musa mishi ba sbd yadda taji hankalin ta ya tashi da ciwon wannan yarinya se taji kaman kirjinta na nauyi, kwanciya tayi ya Mike ya kashe mata wutar tare da ficewa, a nan kujerun kofan d'akin ya zauna kanshi ya mayar kasa yana tilawarshi a natse dukda chan kasar zuciyarshi damuwa ne....
Tafiya da yaji ya sa ya d'ago idanun shi ya zubawa khalid da ya taho yana share hawaye da handkerchief d'in hannunshi zuciyarshi na tsintsinkewa be yi magana ba kaman yadda be motsa ba har Khalid ya iso se ya ja ya tsaya ya kasa magana...
Tsaye ya Mike yana aika mishi da wani irin kallo yace
"Me ya faru? Tana ina?"
Se kawai khalid ya fara zub da hawaye..
****