6
by @autarmama
🌹 SHEIKH IMAM🌹
By
YAR LELEN ROYAL STAR
Littafin kud'i ne.
NORMAL GROUP #300 post ba kullum ba sannan bb update a weekend.
SPECIAL GROUP #500 kullum post biyu ,safe da dare, sau daya a weekend..
Domin Jin yarda za'a biya, kuyi mgn da wannan number.
***.
Daga masu daukar shirin har masu saurare da kallo, kaf babu wanda ya so aka datse shirin, saboda yarda suke kara samun ilimi , sai dai suma sun san ya zaunu, kuma ya yi hakuri sosai duba da yarda tun ba'a fi 30 minutes da farawa ba ya fara yatsina fuska da amsa magana a gajarce, duk da hakan da yake bai sa sun ji shirin ya gunduresu ba, basu kuma ji dadin tashi ba, don da yawa sun yi niyyar fitowa su yi tambayoyi, basu samu dama ba, haka suka k'ulle tulin tambayoyinsu da nufin in Allah ya kai mu karshen watan gaba zasu baje masa su.
Cikin gajiya ya lumshe Manyan idanunsa tare da jingina a jikin kujerar da yake zaune, cikin wahala da jin k'ishi , ya sauke sanyayyan numfashi, da sauri Asrat ya mika masa ruwa mai dan rangwamen sanyi, cike da Jin dadi ya karb'i ruwan dan a halin yanzu bb abun da ya fi buk'ata sama da ruwan, balle Murfin ruwan yay, cikin natsuwa ya fara Shan ruwan idanunsa a lumshe, sai da yay rabin gorarKafin ya cireta a bakinsa, cikin tausayawa Asrat ya mika masa handkerchief, goge bakinsa yay, cikin natsuwa kuma ya Mike da kan kujerar da yake, Jim ya dan yi ya tsaya, tare da dan girgije kafarsa a'lamar ta masa sanyi saboda dadewar da ya yi a zaune ba tare da ko motsi mai karfi ba.
Hannu mutanen suka ringa basa suna gaisawa, cike da Jin dadin yarda ya gabatar da komai kamar yarda suka saba, har gurin mota suka rakasa, manager ne da kansa ya bude masa ya shiga, d'aga masa hannu suka shiga yi, shi kuwa kansa ya mayar jikin set din motar ya lumshe Manyan idanunsa yana jin yarda suka masa nauyi kamar wanda zasu masa ciwo.
Lokacin da suka karaso Anguwarsu Lokacin Sallah ya gabato, hakan yasa yay wa Drive a'lama da ya tsaya a Masallacin kofar gidan, shafa ciki Asrat ya yi, kafin ya kallesa , cikin murya mai sanyi yace "Ayya SHIEKH ni kam yunwa nake ji", bai kulasa ba ya fice, dole ya bi bayansa, Yana tafiya a hankali iska sai kad'asa take, saboda rashin nauyinsa, Asrat dogo ne sosai, don ya kusa kere Sheikh Imam ma a tsawo, bashi da k'iba sosai Amma Manyan kayan da yake sawa suna kara sa masa kwarjini da wata haiba ta musamman, yana mugun yana yi da Sheikh sai dai akwai banbanci sosai a tsakaninsu, Asrat na da duhun fata while Sheikh na da hasken fata sosai, Asrat bashi da wani k'iba, SHEIKH Kuma kakkaura ne, yana da faffadan kirji sosai, Asrat bashi da SA gemu don bashi da ra'ayin tarasa sosan nan sai dai yana da nasa dai² misali irin na gayu, sab'anin Sheikh mai cikar gemu sosai gashi bak'i sid'ik, Asrat na da raha da tsokana,akwai sa da saurin sabo, dandanan zai saki jikinsa da Kai, baya son zuwa aiki, kullum Yana mak'ale da Mamarsa, Sheikh kuwa bashi da wasa musamman akan aikinsa, yana da Dan zafi, sannan yana da sanyi, bashi da surutu , sannan baya ma tsokana shi idan ya ga mutum irin Yana dariya yana wangale baki sai yay ta kallonsa da mamakinsa, kasantuwar shi likitan kwakwalwa ne wani lokacin in ya ga mutane suna wasu abubuwan Yana musu uzuri sosai, don gani yake kamar sun dan tab'u ne, bashi da sakewa da mutane, zaku iya zaman shekara da shi Amma sai ka ringa ganin kamar Yana d'ari² da kai, amma sam ba haka bane yana yin halittarsa.
Sau da dama wasu na ganin kamar baya son mutane ne, idan ya ji haka ransa na dan b'aci, sai ya ga Mai ma ake nufi da shi ne wai ?, Allah ma da kansa ya karrama mutane balle kuma shi karan kad'a miya, kawai dai ba'a fahimtarsa ne bawai baya son mutane bane kawai dai bashi da magana ne shi yasa ake ganinsa a haka....kwada kiran Sallah aka yi, kafin a dauki tsawon lokaci mai tsawo ana Sallah don a kalla an fi tsawon 30 minutes ana gabatar da Sallah.
Jin muryarsa na raira karatun Al-qur'ani ne ya tabbatar wa da Ummie dawowarsa, don dama tunaninsu take tayi musamman Autanta don tasan basu ci komai ba, gashi kuma bashi da rik'on yunwa yanzu sai ka ga ya koma wani abun tausayi yana wani lallabew baya iya cin Abin cin waje balle tayi tunanin ko ya kasa jurewa ya ci tunda ta ga har an Kai war haka basu dawo ba, shi yasa duk ta tausaya masa.
Ko da aka idar da Sallah Sheikh gyara zamansa ya yi, a cikin masallacin, shi kuwa Asrat ana idaraa ko Addu'a bai tsaya yi ba ya cika wandonsa da iska, don shi mutum ne da baya iya jure yunwa.
Da sauri ya shiga cikin parlourn, cikin Dan daga murya yake kira "Ummie!, Ummie!! Ummie!!!", Da sauri ta daga kanta ta kallesa, cikin kunshe dariyarta tace "lafiya Auta?", Ta fada tana kallonsa duk da ta ga yarda ya fita hayyacinsa Kuma tasan ko akan Mai ya fita hayyacinsa.
"Wayyo Ummie zan mutu ki ban Abin ci", ya fada yana zama a k'asan carpet, da sauri ta hada masa Abin ci, tana ajiyewa , hannunsa ya sauka akan cup din tea da ta had'o da shi, cikin wata iriyar yunwa Mai kakkatsa yan hanji, ya k'afa cup din a bakinsa ba tare da ya damu da zafin da tea din yake da shi ba, tun da ya d'aga cup din tea Mai saukesa ba sai da ya shanyesa tas, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da fara cin Abin cinsa, Yana bawa Ummie labarin, don shi cin Abin cinsa kenan, da ya fara sai ya fara bawa mutum labari.
Kamshin turaren Viktor&Rolf Flowerbomb Haute couture ne ya sanaar da su zuwansa, daga Kai Ummie ta yi tana kallonsa , ganin yarda fuskarsa ta koma sai duk taji ya bata tausayi.
"Karaso ciki mana Sheikh", cikin kasalar da ta saukar masa ya karasa shigowa cikin parlourn, yana dan lumshe idanunsa, yana budewa bakinsa Kuma ko na second bai gushe da Ambaton sunan Allah huwayi gagara misali ba.
Nuna masa gefenta kan kujera ta yi tare da Dan bubbugawa a'lamar ya zauna, cikin natsuwa ya sulale kasan gurin ya zauna, yana saukar da kansa k'asa, hannunta ya ji a cikin sumar kansa ta nutsa tana shafawa a hankali, duk da bai dago ya kalleta ba yasan addu'a take masa, lumshe idanunsa yay Yana Jin wani sanyi na saukar masa jikin jikinsa, a hankali yake sauke sanyayyiyar ajiyar zuciya.
Sun jima a gurin , shi bai yi magana ba itama bata ce da shi komai ba, hannunta na cikin sumar kansa tana shafawa a hankali...tsaye take akan kafafunta, tana duban mutumin da yake gabanta cikin Hali na rashin girmamawa, "ba magana nake miki ba ?", Ya fada cikin tsawa, idanunta da suka chanja launi ta dago ta watsa masa, cikin fada itama tace "I am over eighteen years old, the law allows me to do anything, let me do what I want pls", ta fada cikin tsawa, "ni mahaifinki kikewa fadawa haka ?".ya fads yana tsareta da idanunsa, cikin karaji tace "and so f**k what. Ka shiga rayuwata da yawa, duk da kasan bana son hakan, bana Neman komai a gurinka in kudi ne Ina da nawa, komai da ka sani Ina da shi, in ban fi ka arziki ba to zamu iya karawa, Ina son shakar iskar yanci, so leave me alone, please?" , Ta fada idanunta na chanja launi daga fari zuwa jazir, a'lamar ranta a b'ace yake, waje tayi , Yana mata magana amma bata ko bi ta kansa ba ta fice, motarta ta shiga tare da fisgarta a 360 .
Cikin takaici ya dafe kansa tare da fadawa kan kujera da baya², wani zazzafan numfashi yake saukewa, cikin Kuna da tafasar zuciya, yatsunsa ya sa akan bakinsa, Yana cizawa, da fitar da huci Mai zafin gaske.
Dandana idanunsa suka kad'a suka yi jazir, cikin takaici yake sauke numfashi da k'wata Akai², "Yan magana kan ce idan baka tankwasa icce tun Yana danye ba, to fa tabbas in ya bushe ba zai tankwasu ba, ka baro gini tun rani, ba wai in jifa ta wuce kanka ta fada kan kowa ba, don wata rana da yiyuwar jifar zata iya maimai ta dawo ta same ka..", "kimin shiru Aisha",ya fads cikin zallar madarar b'acin ran da take kwance lame² a ransa, cikin fads ya fara "dama na san tun asali ba son yarinyar nan kike ba , kin tsaneta bakya son ta, ne man laifinta kad'an kike, ki haye, kin sata a gaba, waya sani ma ko kece kike sanyata duk abun da take ?, to ki fita a idona na rufe tun kafin na rufe da ke, don ba zaki ji dadi ba, aikin. Mtswww banza kawai", ya fada yana nufar sama.
Ita kuwa jinjina kamta tayi kafin tace, "Allah ya kiyaye ranar da zata jawo ma bala'i, ko kuma ranar da zata sa kayi kuka da idanunka, ranar da zaka ji da haihuwarta gwara 6arinta, ranar da nadama bata da wani Amfani a gare ku duka".Bayan Sallar issha , a Jere suka shigo parlourn fuskarsu na fitar da annurin musulumci, sanye suke da Jallabiya kala daya, hatta da takalmansu kala daya ne, fuskar Asrat yalwace da murmushi ya yin da fuskar Gogan take a tamke sosai .
Da sallama suka shiga cikin parlourn, Amaya da take zaune tana home work ta Amsa musu, Asrat ne yace "Ummie fa ?", " Tana Bedroom", jinjina kai yay, tare da zama a gefenta.
Cikin natsuwa ya tura kofan, wani ni'imtaccen sanyi da kamshi ne suka daki hancinsa, lumshe idanunsa yay na Kara Bude hancinsa, don shi a duk duniya babu abun da yake so sama da kamshi Yana son kamshi sosai, shi yasa baya rabo da turaruka masu dadin gaske.
"Assalamualaikum", ya furta daga chan kofa ba tare da ya shigo ba, daga chan cikin muryarta mai kama da ta shi tace "shigo mana", a hankali ya tura kofar tare da shiga ciki, duk takun da zai yi sai ya lumshe idanunsa, saboda sanyin ACn da ta kama ko ina na cikin parlourn ga Kuma kamshin turaren mai dadin gaske.
A tsakiyar parlour ya tsaya yana kalle² kamar wannan ne farkon shigarsa cikinsa, kawataccen parlour ne mai kyan gaske , da aka yalwatasa da kayan da, irinsu tuntu da sauran kayayyaki irin na
masarautun da.
Zaune ya hangeta kan carpet ta nade kafafunta tana duban wani Azkar, sanye take da wata bak'ar Abaya Mai kyau da tsada, ta yane kanta da Dan kwalin abayar, siririn farin glass ne a idanunta irin na likitoci da jigaggun yan Boko, shigarta ta b'oye shekarunta, don a yarda tayi din nan zaka iya rantsewa ba ita ce mahaifiyar Sheikh ba, saboda yarda take ji da ado da gayu, ga son kamshi kamar dai yarda Dan nata yake.
Gefen damarta ya zauna, tare da nade k'afafunsa, ita kuma sai ta ajiye karatun da take yi, cikin nuna tsantsar kulawa da kauna tace "sannun Hammad na", ta fada tana sakar masa murmushi, karon farko da shi ma ya saki yalwataccen murmushi, Wanda yay sanadiyar lomawar dimple nasa, murmushin ba karamin kyau yay masa ba, cikin nishadin gani sa cikin farin ciki, ta shafa kansa, cikin tsananin kauna tace "Allah ya yi maka Albarka Muhammad Imam", cikin girmamawa da tsananin so da tattali yace "Ameeeen Ummie'na", ya fada cikin taka tsantsan da harshensa.
Hira suka fara irin ta D'a da uwa, duk dai ba wata maganar kirki yake ba, Amma tana matukar Jin dadin firar da suke, don tana matukar kaunar ta ga ta zauna da shi suna fira, Amma shi bai Saba ba, ko don ba kusa da su ya tashi ba, bai yi irin shakuwsr nan da su ba, baya iya fira tare da ita, duk kuwa yarda ta so su yi, amsarsa daga uhmm sai uhmm² , hakan yasa bata takura masa, duk lokacin da ya so firar da kansa yake zuwa gurinta.
Ana cikin haka Asrat ya shigo, guri ya samu chan nesa da su ya zauna , tare da zuba musu idanu yana kallon firar manya Mai cike da tsari da dattaku ,kalmomi suke fada masu mahimmanci , ga firar cikin natsuwa ake yinta, a'lamar ma'abota firar ba masu son hayaniya bane.
Sai guraren 10pm.ya bar gurin Ummie ya wuce samansa, cikin natsuwa ya tura kofar parlonsa, bai damu sam da ya kunna fitilar da take kashe ba sai kawai ya wuce ciki, Kai tsaye Kuma bathroom ya shiga, wanka da al'wala ta dauro , daga chan yay shirinsa cikin farar Jallabiya sabuwar gal sai kamshi sabuntaka take.
Gurin mirror nasa ya nufa, kwalbar turarensa na Viktor &Rolf Flowerbomb Haute couture ya dauka, tare da fara fesawa jikinsa, sai da ya ji kamshi ya masa dai² misalin yarda yake so kafin ya ajiye .
Gefen Bed nasa ya koma, Apple laptop nasa da take kan bedside drower ya jawo, cikin natsuwa ya fara operating nata.
Kamar dai daren jiya , yau ma haka ya raya daren yana mai bautar Allah da d'ayantasa, sai guraren 3:30 ya fito a daga bedroom nasa, dining room ya nufa, a kasalance ya bude Show glass din da aka jera mata cups da spoon, cup da spoon ya dauka, tare da matsawa gurin da wash hands baby yake, dauraye cup da spoon din yay,kafin ya koma gurin fridge nasa, a hankali ya bude, wani babban jug da yake cike da kyakyawar ingantacciyar tatsatsiyar sannan kuma dafaffiyar madarar shanu ya dauko, zubawa yay a cikin cup din, bayan ya zuba ya mayar da ita inda take, ingantacciyar zumarsa pure ya zuba akan madarar shanu da take cikin cup din.
Hada madarar shanu da zumar yay ya motsasu, sai da ya gama ya koma parlour kan kujera ya zauna, tare da k'afa cup din a bakinsa, cikin natsuwa yake sha, Yana lumshe idanunsa, saboda yarda dadin hadin ke ratsa gaba daya jijiyoyin cikin bakinsa, ba karya hadin , hadi ne Mai dadi da sanya natsuwa, sai da ya shanye tas kafin ya dauraye cup da spoon din ya mayar a ma'ajiyinsu, cikin bedroom nasa ya koma, tare da shiga bathroom , wanke bakinsa yay da ingantaccin toothpaste, ya sake wanka, ya fito cikin Jallabiya kalar brown Mai kyau da daukar ido.....
***
YOUR YAR GABAN GOSHI 😂
ƳAR LELEN ROYAL STAR......