Mutum Mugu Ne

22

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     22


.......PI Rotimi, Sajid da wasu police ne suka je gidan Madam B. Suka buga gate d'in amma ba'a bud'e ba, sun jima suna bugawa kafin daga bisani aka bud'e, maigadin cikin magagin bacci yake tambayar ko su waye ne. Wani police ya daka masa tsawa nan ya tsure har da sake fitsari.

Kai tsaye suka shige gidan, basu sha wahalan gark'ame thugs guda biyu da suka samu a falo ba.

D'aya daga cikin d'akunan gidan suka samu Zaytunah da Azra d'aure.

Sajid wajen Azra ya fara zuwa yana kunceta hannunsa har 'bari yake yi. Yayinda Rotimi yake k'ok'arin kunce Zaytunah.

"Dad" Azra ta kira kafin ta fad'a jikin Sajid a sume. Jijjigata ya farayi yana kiran sunanta.

Rotimi na kunce bakin Zaytunah ta fashe da kuka tana cewa " my one, miyasa bakazo da wuri ba?" ko ta kan Zaytunah bai yi ba ya sunkuci 'yarsa ya fita da ita. a falo ya tsaya ya d'au goran ruwa da ya gani kan kujera, ya kwantar da Azra jikinsa ya yayyafa mata. Wani dogon numfashi ta yi sannan ta bud'e ido.

"My princess are you ok? Did they hurt you?"

"Dad I'm thirsty" ta faɗa a hankali

"Don't worry baby I'll get you water but first let's go home"

Zaytunah ta fito daga d'akin tana d'ingishi ganin Sajid d'auke da Azra ta langwa'be kai tace "my one ka bawa wannan ya d'auki Azra, sai ka d'aukeni wallahi k'afata ciwo bazan iya tafiy...."

Wani kallo ya watsa mata wanda yasa ta had'iye sauran maganan.

Fita yayi da Azra a kafad'arsa, ta biyoshi jiki ba k'wari tana d'ingishi.

Motar Rotimi ya shige gaba, ya kira Barr Idris ya sanar mai sun samu su Zaytunah.

Rotimi ya taimaka ya bud'e mata bayan mota ta shiga tana wani kumbure kumbure.

Shima Rotimin ya shigo zai ja motan tace "akwatina, akwai akwatina da jakana acikin gidan nan"

Sajid yace "let's go"

"My one, passport nawa dana Azra suna ciki fah"

Rotimi ya fita kafin ya k'arasa ma ya ga d'aya daga cikin police d'in ya fito da akwatin Zaytunah da handbag ɗinta ya k'ar'ba ya sa a mota suka tafi.

Kai tsaye wani private asibiti suka wuce mafi kusa, ko kallon Zaytunah Sajid bai yi ba balle ya damu da halin da take ciki.

Yana zaune aka duba Azra, gajiyane atare da ita da yunwa sai kuma wajen da aka d'aureta sun kumbura wajen yayi jaa abinka da farar fata. Zaytunah ma dai hakanne sai dai ita kasancewar tasha mari wajen da bakinta ya fashe ya kumbura sosai sai kuma buguwar da ƙafanta yayi.

Rotimi ne ya je ya siyo musu abinci kafin ya dawo Barr Idris ya iso asibitin shima.

Cikin akwatin kayansu Sajid ya fidda mata brush da wani kayan, dan har yanzu kayan da suka shigo da shi Lagos daga Abuja ne ajikinsu.

Ya d'auki Azra ya shiga band'akin dake cikin d'akin da aka basu ya mata wanka, da shike asibitin kud'ine sosai, har ruwan zafi akwai.

Yana fitowa ya saka mata kaya Allah sarki har tayi haske compared to yadda ya d'aukota agidan.

Wata nurse ce ta shigo tana sanar da Sajid cewa Zaytunah sai kuka take yi ta k'i bari a dubata wai sai ta ga Sajid.

Sajid ya maida hankalinsa ga Azra da yake bawa abinci a baki yace "kice mata ruwantane ta bari a dubata, ruwantane kuma ta zauna a haka"

Barr Idris da ya fahimci mi yake faruwa dan yasan ba da sanin Sajid Zaytunah ta zo Lagos ba yace " I know you are angry with your wife, but please go and see her, you should sort things out when you go home, but right now she needs you"

Bai yi masa musu ba, bayan ya gama ba wa Azra abinci da magani ta yi bacci sannan ya fita.

D'akin da aka kwantar da Zaytunah ya shiga, ya sameta zaune kan gado tana kuka, tana ganinsa ta taso taje ta fad'a jikinsa ta cigaba da kukanta.

"Haba my one duk irin halin dana shiga shine ka yi banza dani ko tausayamin ba za ka yi ba"

Wani takaici ya kama shi, da ace ba asibiti suke ba da Allah kad'ai yasan mi zai mata.

Ya janyeta daga jikinshi yace "je kiyi wanka"

Ta yi raurau da ido " my one mu shiga ka min wankan please"

Bai kulata ba ya samu kujera ya zauna ya fidda wayarsa yana dubawa. Ganin dai ba kulata zai yi ba sai ta shige band'akin dan dama ita kanta k'yank'yamin jikinta take ji tunda aka kama su basu yi wanka ba.

Kafin ta fito ya je ya d'auko mata kayanta da abinci a d'akin da aka kwantar da Azra.

Bud'e akwatin yayi yana neman kayan da zai fidda mata ya ga duk yawanci sexy dress ne a ciki, da k'yar ya lalubo wata Dubai Abaya kalar blue ya fito mata da shi ya ajiye akan gado.ya d'auko towel da brush ya mik'a mata.

Ta jima a band'akin kafin ta fito, d'aure da towel, ganin ya k'i kulata itama ta hau fishi da shi tak'i masa magana.

Sai da ta sa kaya sannan ta janyo take away d'in da ya kawo ta fara cin abinci yana ganin yadda take ci da sauri sauri alamar bak'ar yunwa ya cita. A zuciyarsa yace "ana zaman lafiya kin jawa kanki fitina"

Tana cikin cin abinci wani police ya shigo d'akin, suka gaisa da Sajid ya yiwa Zaytunah ya jiki ta amsa masa a kufule.

Ya mik'awa Sajid wayar Zaytunah yace "a wajen thugs da muka kama muka samu wannan, ganin hoton matarka ne a screen d'in shine muka dawo mata da shi, if you don't mind ina so na yiwa matarka wasu tambayoyi"

Sajid ya k'ar'bi wayan yace "go ahead"

"Madam za ki iya gaya mana abinda ya faru?"

Harara Zaytunah ta watsa mishi tace "can't you see I'm eating"

Ta juyo ta kalli Sajid dake duba wayanta tace "haba my one yanzu abinda kayi ya dace, ina cin abinci zaka wani ce wannan mummunan abin ya min tambayoyi"

Da mamaki ya kalleta, sannan yace "kin ga Zaytunah yadda nake binki sau da k'afa ki bini a haka idan ba haka ba, za ki yi mamakin abinda zan miki" daga haka ya ajiye mata wayarta, ya fita.

Shi dai d'an sanda bai san mi suke cewa ba dan ba Hausa yake ji ba.

D'akin da Azra take yaje har lokacin tana bacci, shigarsa ke da wuya Barr. Idris ya shigo d'akin.

"Dr Sajid you can't believe what I just heard"

Sajid ya bishi da ido yana sauraron abinda zai ce

" Yanzu na samu labarin Joseph Ndubuisi ya harbi nephew d'in matarsa, and Funmilayo ta kirani ɗazu tace Joseph shi ya kashe Late Alhaji Aliyu"

"Ya aka yi ta sani?" Sajid ya tambaya da mamaki

"Tace niece d'in Mrs Bridget ce ta gaya mata"

" I knew it, dama sai da na zargi hakan. So yanzu an kamashi?"

" Not yet, amma an bada warrant ayi arresting ɗinsa once sighted, and the bastard ya sace miliyoyin kud'in company kafin ya gudu"

"I hope a kama shi before Monday so that ayi komai a k'are"

"I hope so too" Barr Idris ya fad'i.

Wayarsa ce tayi k'ara da sauri ya d'auka ganin Alhajinsu ne ke kira.

Alhaji ya fara mai jajen abinda ya faru, mamaki k'arara a fiskarsa yake sauraron mahaifin nasa.

"Haba Sajid, yanzu har a sace Zaytunah da Azra ka kasa sanar damu"

Hak'uri ya bawa Alhajin kafin ya kwantar mai da hankali cewa ba abinda ya samesu kuma case d'in ma Insha Allah ran Monday gaskiya zata bayyana.

Tun suna waya da Alhaji kira ke shigo masa waya, yana gama wayar numban mommyn Zaytunah ya shigo.

Itama jaje ta fara masa, daga bisani Daddyn Zaytunah ya amsa wayar shima ya masa jaje. suma din ya shaida musu komai ya daidaita yanzu.

"Amma Sajid baka kyauta mana ba, yanzu shine har suyi kwana biyu ana garkuwa da su ka kasa sanar damu, ko addu'a bazamu taya ka da shi ba" inji mommyn Zaytunah

"Mommy kiyi hak'uri Dan Allah bana son d'aga muku hankali ne, tunda abinda suke nema d'in ba kud'i bane, evidence ne dake wajena suke buk'ata"

"Shikenan tunda suna lafiya, ina Azra?"

"Tana bacci"

Tun kafin ya musu sallama wayar Nadia k'anwarsa ya shigo yana d'auka tace "Saj abinda ya faru kenan bamu sani ba, ni har ina cewa zan shigo Abuja jiya ban samu dama ba ashe dana zo ba zan samu kowa ba"

Da shike Nadia itace autarsu kuma duk cikin 'ya'yan Ummi sun fi shak'uwa da ita yace " Wai auta waya gaya miki ne?"

"Ai dama na san ba za ka ta'ba gaya mana ba, toh yanzun naga Zaytunah tayi tweeting shine nace barin kiraka dan kasan ba shiri nake da itaba balle na kira wayanta. Amma fah Yaya ta ban tausayi wallahi, hoton da ta saka har wani bak'i ta yi ga shegen bakinta da take ji dashi d'in nan ya wani yi lakwas da shi"

Jikin Sajid ne ya fara rawa har sai da Barr Idris ya noticing ɗinsa.

Nadia ta ci gaba " Saj ina 'yata? fatan ba abinda ya sameta dan nafi damuwa da ita"


Da k'yar ya had'a bakinsa yace "she's sleeping" saboda he was totally agape

Yana gama wayan ya duba Twitter page d'in Zaytunah yaga tweet d'in da tayi ko minti talatin bai cika ba da ta yi.

K'ark'ashin hotonta da ta d'auka zaune akan gadon asibitin ta tweeting kamar haka:

* Iko sai Lillahi..... I never imagined in my entire life that I will be a victim of kidnapping. But it happens, I've been kidnapped for two days along with my dear daughter Azra.....*

*And My hero rescue us today, my one and only Husband Dr Sajid,.....love you*

Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oon shine abinda Sajid ya iya fad'i dan bak'in ciki har wuyansa.

Barr. Idris ya ce "take it easy my friend"

Sajid ya had'e kansa da gwiwa zuciyarsa na ayyana masa abubuwa dayawa, dole ne ya nunawa Zaytunah laifinta amma yanzu kam bashida dama dan har yanzu akwai abubuwa dayawa agabansa. Wayarsa ta ci gaba da k'ara mutane nata kiranshi suna son sanin mike faruwa amma ya kasa d'aga wayar. Ciwon kai, yunwa, gajiya duk yana jinsu amma ba sune damuwarsa ba, babban damuwarsa Zaytunah .

Ringing d'in wayar tasa da tayi yawa ya sa Azra tashi daga bacci.

Tana bud'e ido taga Dad d'inta ya sunkuyar da kanshi. "Dad where's Mommy?"

Muryan Azra daya doki kunnensa ya sashi d'ago da jajayen idanunsa ya kalleta, ya k'ak'aro murmushin dole yace " Mommy is fine my princess, go back to sleep"

Ta mak'e kafad'arta " I want to go home, I want to see Nuyen and Aamir"

Ya taso ya zauna gefen gadon ya rungumeta yace "you'll see them very soon, my Baby"

Barrister ya k'atseshi da cewa " na riga na kira Ishola yana waje, so if you need anything just call him. you and your family are welcome in my house"

Sajid yace " Thank you barrister I'll stay with Mr David's family today before I sort things out"

Musabaha suka yi sannan ya fita.

Azra ya d'auko a kafad'a ya nufi d'akin Likita da ita, neman a sallamesu yayi, Likitan yace ba matsala dama so yake su huta kafin a sallamesu amma tunda ya buk'aci sallama zasu iya tafiya.

Zuwa yayi ya biya bills d'insu sannan ya shiga d'akin Da Zaytunah take kwance.

Bai yi mamakin wayan da ya ji tana yi ba dan masu jaje take yiwa bayani tana cewa " wallahi kuwa, kawai fa mugayen mutanen nan suka d'auremu ko sallah basu bari nayi ba, sau biyu suke bamu abinci a rana, sau biyu suke kuncemu mu using toilet. Kai, Kai, abin nan ba dad'i"

"Idan kin gama wayar naki ki sameni a waje, an sallameki" Yana fad'in haka ya juya. Azra tuni ta sake komawa bacci a kafad'ar nasa saboda gajiya bai gama barin jikinta ba.

Ishola ya turo ya d'auka kayansu, har Ishola ya fito tana ciki sun kusan minti goma kafin ya hangota tana fitowa tana tafiya tana waya, har lokacin tafiyarta bai saitu ba. Saboda Azra na kwance cinyarshi yace Ishola yaje ya taho da ita tunda batasan motan ba, Yana ganin reaction d'inta lokacin da Ishola ya tareta yana mata magana sai wani tak'una fiska take yi.

Gidan baya ta bud'e ta shiga har lokacin bata bar waya ba, Sajid gidan gaba ya zauna. Bayan ta gama waya ta duk'ufa kan wayar tana chatting. Da shike akwai nisa daga asibitin zuwa unguwarsu Naziha.

Tana cikin chatting wayarta ta mutu ba chaji " oh gee, ya akayi haka 'yan iskan nan basu min charge ba"

Ta mik'o wayar wa Sajid tace "my one ka samin wayata a chaji dan Allah"

Yayi kamar bai ji abinda tace ba, ta sake maimaitawa ya mata shiru.

Tsaki tayi aranta tace "shikenan mutum yai ta fishi shi kad'ai"

Babu wanda ya kuma magana, har suka isa.

Zaytunah tana ganin sun parker motar a wani k'aramin flat tace " my one na d'auka hotel zamu je ai, Ina tunaninma Eko Hotel will be better"

A hankali ya fito daga motar dan baya son tada Azra daga bacci.

Ishola ya fito musu da kaya, ita ma Zaytunah ta fito ta tsaya gefen Sajid har jikinsu na gugan juna tace " Fisabilillahi My one tunda muka bar gidan nan, sai wani shareni kake yi, nine ma fa ya kamata na yi fushi da kai, ka bari munyi kwana biyu a hannun mugayen mutanen nan..."

"Ki kama kanki Zaytunah" abinda ya iya ce mata kenan kafin ya wuce ya shiga gidan.

A falo ya samesu, Mama, Gbenga da Ronke sai ya ji ba dad'i da bai ga Ziha ba.

Fiska sake Mama ta musu barka da zuwa tana yiwa Sajid jaje,

Zaytunah wani kallon k'ask'anci take binsu da shi musamman da taga Ronke sanye da sark'an cross a wuyanta.

Mama ce ta fara gaisheta ta amsa sama sama.

Mama tace wa Zaytunah ta zauna akawo mata ruwa. Ta tsaya k'ik'am tana kalle kallen kujerun falon.

Sajid yace wa mama " barin shiga ciki na kwantar da Azra"

"Yanzu ma Funmilayo ke gyara d'akin"

Ai kamar jira yake ta ambaci suna Funmilayo yai saurin wucewa guest room d'in da Azra a kafad'arsa.

Chanja bedsheet ya samu take yi ba ta ji bud'e k'ofar sa ba, ta juya masa baya tana gyara bedsheet d'in da ta saka.

Jikinta ya bata ana kallonta tayi saurin juyowa caraf suka had'a ido,

"Ehm..Uncle ..."

Yatsarsa d'aya yasa a bakinshi ya ce "shhhh"

A hankali ya tako wajen da take tsaye ya mik'a mata Azra ya mata nuni da ta kwantar da ita, tasa hannu zata kar'beta hannunsu ya had'u da sauri ta d'ago ta kalleshi shima d'in ita yake kallo abubuwa dayawa yake ayyanawa azuciyarsa.

Maimakon ya cire hannunsa sai ya taimaka mata suka kwantar da ita tare.

Tayi saurin janye hannunta ta matsa gefe. Kallonta yake yi ya kasa tantance abinda yake ji gameda ita.

Wai 'yar wannan yarinyar ne ta taimaka mishi ba sau d'aya ba ba sau biyu ba. Mi zai wa yarinyar nan ya saka mata bisa taimakon da ta masa.

Ganin irin kallon da yake mata yasa ta saurin tashi ta yi hanyar fita kici'bis suka yi da Zaytunah dake shirin shigowa d'akin.

Wani kallo Zaytunah ta watsa mata wanda yasa hantar cikinta kad'awa.

Zaytunah ta ja tsaki ta d'an tureta gefe tace "arnan banza arnan wofi kawai, k'azamai, gida sai wari kaman an ajiye mushe "

Naziha ta kalleta cike da takaici ta fita daga d'akin.

A zaton Zaytunah Naziha bata jin Hausa.

Tana isowa zata hawo gadon Sajid yace " kin gama zubar min da mutuncin nawa koda saura?"