SHEIKH IMAM 🌹

9

by @autarmama

🌹 SHEIKH IMAM🌹



By


YAR LELEN ROYAL STAR..




Normal group #300

Special group #500



1499884120

Umma Salma Sani

Access bank



***


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}


***

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alk’alaminmu ‘yancinmu*


Second 2 the last free page.



Page.....9



Lafiya Lau suka karaso cikin k'asar ta Dubai Mai cike da tsaro na musamman, a hankali matafiya suka shiga saukowa daga cikin jirgin, suma haka suka fara saukowa dukkansu sanye da bak'ar Abaya sun yi rolling kansu da mayafan abayar da suka musu kyau na gaske, barin ma Aizza, kayan sun mata kyau sosai kamar Balarabiya.



Ko da suka sauko idanunta na kan jakar da take bayan tasu, haka suka tafi gurin da ake screening mutum kafin bari ya shige, tsakaninsu duk sai da suka bada tazara ta a kalla mutane biyar², don haka Aizza ce a gaba, sai bayanta mutum biyar ne kafin Beerbah, tsakanin Beerbah da Layleerh kuma mutum biyar ne.



Ana zuwa kan Aizza aka sa mata wata na'ura, a jikinta, kuka na'urar ta shiga yi, kallonta mutumin ya yi itama ta kallesa, a'lama yay mata da ta bude handbag din da take rataye a kafadarta, zare handbag din tayi daga kafadarta ta cire tare da mika masa, Bincike aka fara ciki, sai dai babu komai na abun laifi a ciki don daga kudi sai phones nata kawai a ciki, mace aka sa ta bincika ta ba a samu komai a jikinta ba, hkr suka bata ganin ba'a samu komai a jikinta ba, Jakarta suka bats da Kara bats hkr kafin ta wuce, haka duk aka musu, amma ba'a samu komai a jikinsu ba, securities din sai mamakin wannan abu suke, su kuwa suka fuske tare da ci gaba da harkokinsu, gurin da za'a tantance jakunkunansu suka k'arasa.



Kamar wancan haka aka chaje jakunkunansu Amma ba'a samu komai a ciki ba, sai da suka dauki jakunkunansu suka fara tafiya, kafin suka ji, an ce "waye bai wannan jakar ?", Duk juyawa suka yi banda Aizza da ta ci gaba da tafiyarta, daga gefen da mutane suke, aka daga wani kyakyawan hannu sama, da sauri mutanen da suke gabansa suka matsa masa.



A hankali cikin natsuwa da Kamala ya fara tafiya zuwa gurin da ake tantance jakunkunan, cikin sanyi da Kuma harshen larabci yace "akwai wata matsala ne ?", Da sauri securities din suka juyo garesa, saboda muryar da suka ji, kallonsa suka yi suka kalli jakar.



Cikin larabci suma suka ce masa "zamu iya bude jakar?", Jinjina musu kai ya yi, a'lamar ba matsala.



Da sauri suka zuge jakar, fiffitar da kayan da suke ciki suka fara yi, ba wasu kaya bane sosai, laptop nasa ne sai wasu sai wasu abubuwan Amfani, daga chan kasa aka fara fitar da wasu yan madaidaitan robobi, bude robobin aka shiga yi, da sauri ya ja baya, yana k'ara kallon jakar, "innalillahi wa'inna ilaihi Raju'un!", Ya furta daga chan k'asan zuciyarsa ba tare da kowa ya ji ba.



Daya daga cikinsu ne ya matsa kusa da shi tare da cewa "Yallabai zamu tafi da kai Office, domin muna buk'atar bincike a kan ka", jinjina kansa ya yi, tare da bin bayansu, haka suka sa sa a tsakiya wasu na bayansa wasu na gabansa, lafiyayyiyar mota Mai kyan gaske aka shigar da shi, tare da wucewa da shi Chan headquarter din su.




Suna barin gurin ta saki sanyayyiyar ajiyar zuciya da murmushi a tare, duk kallonta suka yi, ganin irin kallon da suke mata ne yasa ta kawar da kanta gefe, tana gintse fuskarta .




Wata lafiyayyiyar mota ce Mai kyan gaske ta tsaya a gabansu, daga ciki aka bude musu, shiga suka yi, Mai motar kuma ya jaa ta da wani irin speed.



Basu tsaya ko Ina ba sai wata tsararriyar unguwa Mai kyau da tsari , anguwar da ko a k'asar Dubai din ma masu kudin k'asar ne suke zauna a cikinta



Gaban wani tamfatsetsen gidan mai kyau da girman na gaske, suka tsaya, bude musu get aka yi kafin motarsu ta sulala cikin gidan.



Gida ne Mai girma da fadi, wanda yake dauke da abubuwan more rayuwa, sun dan yi tafiya a cikin gidan kafin su karaso wani tankamemen kofar parlour, ana driver ya yi parking, firfitowa suka yi, Aizza na gaba Layleerh da Beerbah na bayanta suna tafiya a hankali kafafu a bubbude.



Suna shiga cikin gidan, suka tarar da wasu mutane da fararen kaya da a'lama Dr ne da nurses, sannu da zuwa suka musu, cikin yarfe hannu Beerbah tace "Dr we need your help, " ta fada cikin radadin azabar da take ji.



Gyada kansa ya yi yana kallonsu, wata kofa suka nufa, Aizza kuma ta zauna anan gurin da Dr din ya tashi.



Minti kadan da shigarsu dakin ta fara Jin ihu da kururuwarsu, a hankali ta tashi daga inda take ta nufi inda suka shiga, guri ne kamar Asibiti don da akwai komai na bukata, kama daga kan kayan aiki da komai dai da aka San ana samu a Asibiti, kwance lame² ta gansu, sun gwagwafe cinyoyi sun budewa Dr din kafafunsu, Abu yake kokarin ciro musu a cikin gabansu, Amma yak'i ciruwa dai faman ihu da kuka sosai.



Kallansu ta yi da kyau, fuskarta da jikinta bai nuna tsorata ko wani Abu a zahiri ba, sai dai a bad'ini tsorace take da yarda ta ga suna yi, sun wani gwagwafe kamar masu labour, jingina tayi da jikin Bango tana kallonsu.




An jima sosai ana kokarin fitar da abun da suka sa a gabansu Amma Abu ya faskara, tun suna ihu da karfindu har ya fara karewa, daga su har Dr din da nurses din cikin fargaba da tashin hankali suke, ga wata uwar zufa da take karyo.musu.



Cikin fads Dr din ya fara cewa "da hankalinku da tunaninku, zaku yarda ku aikata. Wannan aikin?, Shi likitan da ya muku bai fada muku ilolinsa ba ?, to ku sani babbar illa garesa, don ko Wanda kuke zuwa a fasa cikinku a sa muku, matukar illa ne da shi balle wannan da zaku Bude prevent part naku a sa muku, ku yanzu baka tsoron ma abun ya fashe muku a jiki, ko Kuma a nemesa sama ko k'asa ba'a gansa ba ?", Ya karasa fada da sigar tambaya.



Su dai ba baka sai kunne don bala'in da suke ciki ma kad'ai ya ishesu, jin su suke su ba k'asa ba su kuma ba sama ba, mika hannu Dr din ya yi, wata nurse ce ta mika masa Scissors, Mai kaifi irin Wanda ake Amfani da shi gurin k'ara mace ya yin haihu, gaban Layleerh ya koma, cikin rashin tausayi ya kama fatar da take jikin Prevent part nata ya tsarga, ihu Mai karfin gaske ta saki, tare da kankame farin bedsheets din da aka luluba akan gadon da yake tamkar na Asibiti.



Wani karfe ya dauka tare da zura mata shi cikin prevent part din nata, kara yankawa ya yi, sai da ya yanka mata gaba daya fata bakwan da take gurin, kafin ya sa mata hannunsa Mai dauke da safar hannu.



Tun tana kuka da kururuwar neman taimako har ta dai na sai dan nishin da take kamar akuyar da ta gagara haihuwa.



Da yatsu biyu ya kama abun tare da fara zarowa, ta sha bak'ar wahala kafin ya fito da abun, da mamaki yake bin robar da ya ciro da idanu, roba ce madaidaiciya mai murhi an rufeta rikif, girgiza kansa ya yi, Yana jinjina wannan lamarin, ashe akwai wanda zai iya salwantar da lafiyarsa saboda neman kudi, Neman kudin ma ba na Allah ba kudin Haram, bak'ak'e kudi da basu da albarka .



Ba tare da tausayawa ba ya fara dinketa kamar kwarya, sai da ya dinketa Ras, kafin ya koma kan Beerbah kamar yarda yawa LAYLEERH haka ita ma ya mata.



Juyawa ya yi gurin da Aizza take, gaba days ta sha jinin jikinta, ga kasa motsawa daga inda take , ta kafe Abokan cin mushenta da idanu, tana kallon irin bak'ar wahala da suka sha a gurin neman kudinsu, "you see ?,zan baki shawara ko watan wata rana, kar ki sake kice zaki yi abun nan don yana da side effects,"ita dai bata ce masa komai ba bata ma kallesa ba, balle yasa ran ta ji abun da ya fad'a.



Zuwa tayi zuwa chan ciki, sama ta haye, tare da fadawa wani room, kamar dai room din ta na gida wannan ma sak abun da yake chan shine anan, a gajiye take Hakan yasa bata zauna ba sai ta shiga band'akin, a hankali ta zare kayan jikinta, gefen cikinta daga dama inda yake manne da plaster ta tsurawa idanu tana kallo.



A hankali ta shafa gurin tana sauke ajiyar zuciya, wani Abu kamar leda tasa ta daure gurin, tare da sakarwa da kanta ruwa, numfashi ta shiga saukewa a hankali tana Kara baza gashin kanta , sai da ta ji ruwan ya daki tsakiyar kanta sosai kafin ta kashe shower din ta fito daga cikin bathroom din.



A hankali ta fito tana daure da towel tafiya take kamar Yana Jin tsoron taka k'asa, haka ta ci gaba da tafiyar har ta k'arasa gefen gado ta dan zauna, barci ne sosai a idanunta don jiya dadewa ta yi ba tayi barci ba, Hakan yasa ta kwanta tana dafe da gefen cikinta Mai dauke da plaster .



Lulube jikinta tayi da duvet tana lumshe idanunta...kafin wani lokaci gaba daya gidajen radio har na Nigeria sun samu labarin wai an kama babban Malamin Addini ya yi safarar cocaine daga Nigeria zuwa Dubai, take kasashe suka dauka, tun kafin su karasa chan headquarters din har an fara kiyaye² daga k'asashen duniya, akan San Jin ba'asi da gundarin bayani.



Kowa yasan yarda Dubai ke da tsauri, Basu kula ki wacce kasa ba, suka ce sai sun yi bincike sun gane asalin abun da yake faruwa.



Sun yi tafiya mai tsayi gaske kafin su karaso wata babbar headquarter , Mai abubuwan ban mamaki, jiragen da suke tashi da sauka a cikin headquarter'n kad'ai ma abun tsoro da Al'ajabi ne.



Wani babban gurin ajiye motoci suka ajiye motarsu, budewa Imam kofar motar aka yi tare da basa hanyar wucewa, cike da confidence, ta fito daga cikin motar, kamar ko yaushe fuskarsa bata dauke da murmushi sannan Kuma ba daure take tamau ba, don a halin yanzu fuskarsa ma tafi bayyanar da annurinsa.



Ciki aka wuce da shi, ko da suka shiga ciki, kasantuwar case din ya had'a da gurbata k'asa da son kawo musu bara gurbi, sai kawai aka wuce da shi gurin tuhuma kai tsaye.



Tuhumarsa aka shiga yi, da Jin abun da ake tuhumarsa da shi sai ya kasa magana, sai kawai ya sauke idanunsa kasa, bai nuna wata a'lama ta razani ko tsoro ba, haka zalika bai gusa da fargaba da mamakin abun da ake tuhumarsa da shi ba, har zuwa dare shi dai bai yi magana ba, tunda bai San Mai zai ce da su ba, jaka dai gata jakarsa ce aka ga kayan a ciki, bai Isa ya karyata ba tunda yasan Jaka tasa ce, haka kuma ba zai ce shine wanda ya aikata ba, saboda haka ne yasa ya kasa magana sai dai kawai ya sauke kansa kasa yana wasa da zoben hannunsa.........




Normal group #300

Special group #500



1499884120

Umma Salma Sani

Access bank



***



YOUR YAR GABAN GOSHI 😂



YAR LELEN ROYAL STAR......