Sawun Giwa

4&5

by @realeshaa

*SAWUN GIWA*

 _Ya take na Raƙumi_



 _By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_



_Wannan shafin Sadaukar wane agareki Aunty Binta Umar Abbale🥰_



 *F-R-PG 4&5*

Ba kowa bace face tsintacciya ƴar gaba da Fatiha wacce aka tsinta akwararo cikin tsakiyar dare acikin jemem'men tsumma.

“Shin wacece tsintacciyar!?”.

Tambayar da ta yiwa kanta kenan duk da cewa bata da amsar tambayar.

Cikin wani irin yanayi na tsananin tashin hankali ta dafe kanta dake barazanar tarwatsewa gida biyu kana cikin rauni da bugawar zuciya tace.

“Dan Allah Aunty Lateefa kiyi min cikekken bayani yanda zan fahimta akan wa kike magana?,Shin wacece Iyayenta suka jefar da ita agefen Jujin! Saboda gudun abin kunya?”.

Ta dafe ƙahon zuciyarta dake wani irin harbawa da karfi har ƙirjinta na ɗaguwa muryanta na rawa ta cigaba da cewa.

“Ni dai nasan ina da Mahaifana wato Uwa da Uba sannan suna raye kuma Ina da ƙanne ko dai akan wata kuke magana!?”.

Sheƙeƙe Lateefa da Meenah ke kallonta cikin rainin hankali Lateefa tace.

“A'a Uwar data haifeki ce tsintsiyar kajimin Shegiyar yarinya mara mutunci kina nufin dama bakisan cewa ke Shegiya bace da aka tsinta akororo!?Ko kuma barikanci zaki nuna mana ƙaramar karuwa ƴar tasha!!?”.

Dogon tsaki Meenah taja kana ta watsa mata Harara tare da faɗin.

“Bar shegiya mai suffar karuwai kallo ɗaya zaki yiwa wannan munafukan Idanun nata da ko yaushe ke lumshe kisan cewa shahararriyar ƴar duniya ce ta bugawa Ajarida,Kana ƴar gaba da fatiha ce ba ƴar Sunnah ba”.

Cikin wani irin yanayi na tsananin ruɗu da ɗimuwa Neenah ta miƙe zuciyarta da ƙwaƙwalwarta na tariyo mata Kalmar Tsintacciya ƴar gaba da Fatiha lokaci ɗaya wani irin duhu ya lulluɓe mata idanu wani ƙara tayi kana tayi baya Suuuuuu. 


Akuma dai-dai lokacin aka buɗe ƙofar falon cikin wani irin sauri mai haɗe da sassarfa Imraan yayi wurgi da files ɗin dake riƙe ahannunsa ya nufi kanta da wani irin sauri ya riƙota jikinsa ta zube afaffaɗan ƙirjinsa hannunsa biyu ya sanya duka ya tallafota jikinsa...


Indu kuwa cikin sauri ta buɗe ƙofar toilet ta fito jin Ihun Neenah domin duk azaton ta tana cikin Bedroom ɗin tana fita ta nufi Falon Arazane ta zare manyan Idanunta tare da nufar kan Imraan da har zuwa lokacin ke rungume da Neenah aƙirjinsa ya kasa miƙewa sai bubbuga kumatunta da yake yana faɗin.

“Wake Up Neeraan!Open your eyes Neeraan please wake up³”.

Aruɗe Indu ta nufi frigde ta buɗe kana ta ɗauki roban Swan water ta nufi kan Neenah tana buɗewa.


Lateefa da Meenah kuwa mutuwar tsaye sukayi musamman Lateefa cikin wani irin yanayi na tsananin tashin hankali da mamaki take bin Imraan da kallo lokaci ɗaya jikinta ya shiga kyarma ta kasa koda ƙoƙƙwaran motsi Atake zufa ya wanketa tun daga kanta har tafin ƙafarta duk da kuwa Ac dake aiki haka zalika zuciyarta ke wani irin tafarfasa yana kai komo.

Meenah kuwa baki ta saki tana kallon ikon Allah ganin yanda Neenah ke kwance aƙirjin Imraan hannunsa na dama na tallafe da ƙugunta yayin da hannunsa na hagu ke ƙasan Breast ɗin ta ya tallafe.


Cikin sauri Indu ta zuba ruwan atafin hannunta na dama sannan ta yayyafawa Neenah asaman fuskarta amma ko da wasa bata motsa ba duk da sanyin ruwan cikin sauri Imraan ya karɓi goran ruwan da hannunsa na dama kana ya cire Hijabin dake jikinta.

Atake yalwataccen sumar Kanta dake ɗauke da kitson kalaba manya-manya ya zubo akafaɗarta cikin sauri ya zuba mata ruwan tun daga tsakiyar kanta ya sauƙa har zuwa fuskarta da ƙirjinta kana ya cigaba da bubbuga fuskarta yana faɗin.

“Neeraan!Neeraan!! Neeraan!!!,Open your eyes please!Wake Up ³”.


Wani irin numfashi Neenah taja tare da motsa eyeball ɗin ta dake lumshe kana tashiga girgiza kanta tana motsa yatsun ƙafarta sai kuma ta fashe da matsanancin kuka muryarta na rawa tace.

“Aunty Lateefa niba shegiya bace kuma ni ba tsintacciya bace ina da Mahaifi sannan ina da Mahaifiya, Mahaifiyata kuma Allah ya mata rasuwa dan Allah kada ki sake muzuntata,tun da bata cikin wannan duniyar ki barta ta samu salama amakwancinta”.

Ta damƙe hannun Imraan dake cikin nata still Idanunta na lumshe suna zubar da ruwan hawaye ta cigaba da cewa.

“Ni ba shegiya bace ina da Iyaye sannan talauci da wadata duk Ubangiji ke bawa wanda yaso kana ya hana wanda yaso asanda ya so kuma hakan ba yana nufin sani yafi wani bane a'a babu wanda yafi wani kima da daraja a wajen Ubangiji face wanda yafi tsoronsa”.

Wani irin kuka Indu keyi cike da tausayin Aminiyar nata.

Cike da rauni Neenah ta cigaba da faɗin.

“Sannan bawai ina tare da Indu dan kwaɗayin dukiyar su bane ƙawance na da Indu daga Allah ne bawai wata manufa ba kada ki sake muzanta Iyayena bazan iya juran hakan ba iyayane sune rayuwata!”.

Cikin matsanancin kuka Indu ke girgiza mata kai muryanta na rawa tace.

“A'a Blue eyes ni nasan cewa ƙawance mu saboda Allah ne duk wanda zai faɗi wani abu saɓanin haka ya faɗi son ransa ne amma nafi kowa sanin wacece ke ni nasan cewa saboda Allah kike tare dani”.

Girgiza kai Neenah tayi still Idanunta alumshe kana suna zubar da hawaye tace.

“A'a Indu kowa kallon kwaɗayayya mai son abin duniya yake min, Aunty Lateefa da ƙawarta na yimin gori cewa na maƙale miki saboda ina cutar ki sannan ina saki ki amshi kuɗi wajen Yah Imraan ki bani sannan ya ɗauki nauyin karatuna kuma sai tasa ya daina biya min”.

Ta wani irin ja dogon numfashi kana ta cigaba da cewa.

“Nayi alƙawari koda Yah Imraan bai daina biya min ba bazan cigaba da karatu da kuɗin sa ba ɗawainiyar da kuka min nagode bazan manta da alkhairinku agare ni ba”.


Lokaci ɗaya idanun Imraan suka kaɗa sukayi Jawur dasu cikin tsananin ɓacin rai da fushi yake kallon fuskar Neenah da har zuwa lokacin bata gama dawowa hayyacinta ba maganar na fitowa daga ainihin zuciyarta ne ya fesar da wani numfashi mai masifar zafi kana ya miƙe da Neenah ajikinsa kan 3sitter ya kwantar da ita cikin wani irin fushi da ɓacin rai ya juya kan Lateefa da lokaci ɗaya wani masifaffen tsoro ya lulluɓeta ta haɗiye wani yawu mai masifar ɗaci kana tayi ƙasa da kanta ganin kallon da yake jifanta dashi.

Cikin tsareta da ido ya gyara tsayuwar sa tare da cewa.

“Lateefa Mekika aikata?,Shin menene damuwar ki shin kin taɓa bada Naira biyar contribution acikin abinda nake mata shin idan na ɗauki duk dukiya ta nayi temako dashi menene matsalarki?”.

Ya kalli Neenah da still hawaye ke zuba a Idanunta kana har zuwa lokacin bata gama dawowa hayyacinta ba yace.

“Lateefa kin bani kunya atunanina duk abinda zan yiwa Indu da Neeraan idan baki ce min Allah sanya alkhairi ba Toh ba zaki kushe ba this is first and last da zaki sake kuskuren aikata irin wannan abin!?”.

Wani irin kallo Lateefa ke binsa dashi zuciyarta na sake yin baƙi da zugi ta tsani jin ya kira Neenah da Neeraan...


Imraan kuwa cikin fushi ya cigaba da cewa.

“Neeraan na da babban matsayi awajena wanda bazan juri ganinta cikin wani hali ko kuma ci mata mutunci in jura ba dan haka kiyi gaggawar shiga nutsuwar ki”.

Cikin sauri Lateefa ta kalli Imraan Muryanta na rawa kana ta kalli Neenah tare da faɗin.

“Soja na me kake nufi?,Kana nufin wannan tsintacciyar yarinyar mara galihu talaka har ta na da wani matsayi awajenka?”.

Cikin zubda hawaye ta cigaba da cewa.

“Kana nufin har wani matsayine da ita acikin rayuwar ka?,Kada fa kamanta matsayina awajenka sannan kada zafin zuciya yasa ka manta waceceni!”.

Wani Banzan kallo ya watsa mata tare da jan dogon tsaki kana cikin nunata da yatsa yace.

“Enoght is enough Lateefa bana buƙatar wannan shirmen naki is better kiyi gaggawan gyara kuskurenki in ba haka ba zaki ga Other side of Me akan Neeraan”.


Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tare da nuna kanta da yatsa tace.

“Sojana ni matarka kake ƙoƙarin tozartawa agaban duniya akan wannan Shegiyar yarinyar ƴar zina karuwa!.

Da ƙarfi ya rintse idanunsa tare da cije lips ɗinsa na ƙasa atake yanayin yinsa ya sauya.

Cikin nunata da yatsa ya buga mata wani irin tsawa yace.

“Enought Lateefa kada kisa nayi loosing temper na kada kisa in miki abinda bakya zato”.

Sosai ta tsorata da ganin yana yinsa Amma saboda yanda zuciyarsa ke wani irin ƙuna na tsananin kishi da ɓacin rai tace.

“And so what Sojana me zaka min kana nufin zaka dake nine?ko kuma zaka sakeni?,Ko kuma kasheni zakayi?”.

Kallon Indu dake jijjiga Neenah tana kuka yayi numfashi me zafi ya fesar kana yace.

“Ki ɓace min da kallo Lateefa kada kisa in miki abinda banyi niyya ba kada ki fusata min zuciya”.

Hannu ta tafa cikin ɗaga sautin murya tace.

“Dan Allah Sojana kayi duk abinda kaga dama bazan fasa faɗan gaskiya ba koda kuwa zaka feɗe naman jikina da rai na in de akan wannan tsintacciya ƴar zina karuwa me bin mazan ne”...


Be bata damar ƙarasa fadar sauran maganar ba ya sauƙe mata Lafiyayyan mari akuncinta cikin nunata da yatsa kana da gargaɗi kana da fusata faɗin.

“Ya isa!,Wallahi idan kika sake kuskuren aibantata ko kuma kiran ta da sunan da bai dace ba saina shayar dake mamaki banza mara hankali kullum kina girma kina da ɗa shiga jeji”.

Mutuwar tsaye tayi jin sauƙan hannunsa akuncinta wasu hawaye masu masifar zafi ne suka shiga bin kuncinta Shar-shar-shar.

Cikin rauni ta buɗe baki da niyyar magana.

Afusace ya ɗaga mata hannu tare da girgiza kai yace.

“Ki bar nan kafin in tattaki idan har ki kayi Kuskuren sake magana wallahi zan shayar dake mamaki”. 

Da gudu ta juya ta nufi Bedroom ɗinta zuciyarta tamkar zai fashe da zaran tace za tayi magana komai zai iya faruwa.

Meenah dake tsaye ta haɗiye wani yawu da ƙyar kana cikin sanyin jiki ta nufi Bedroom din Lateefa da Harara ya bita kana ya kalli Neenah da har zuwa lokacin numfashinta ke fusga alamar yana daf da ɗauke wa kana hawaye na cigaba da bin kuncinta.


Cikin rawan murya Indu tace.

“Yah Imraan mu kaita asibiti numfashinta ɗauke wa yake yi kada wani abu ya sameta Ina tsoro”.

Bata ƙarasa maganar ba hannun Neenah dake cikin nata ya zame ƙasa kana numfashinta ya cigaba da fusga yana kai komo cikin sauri Imraan ya durƙusa akanta tare da kallon Indu da duk ta burkice tana cewa.

“Yah Imraan mu kaita asibiti kada wani abu ya sameta!Kallifa yanda numfashinta yake ɗaukewa”.

Numfashi ya fesar tare da shafa sumar kansa kana ya lumshe idanunsa tare da tsirawa Neenah Ido cikin sanyin murya yace.

“Jeki ki cire Uniform ɗinki kizo mu tafi”.


Kai Indu ta girgiza hawaye na kwaranya daga Idanunta kana Muryanta ta kalli Neenah tare da cewa.

“A'a ba sai na canza kaya ba mu tafi haka Yah Imraan Ina tsoro kada numfashinta ya ɗauke duka!”.

Ahankali ya fesar da numfashi mai zafi kana ya ɗago idanunsa ya kalleta tare da faɗin.

“Oya wuce ki cire wannan kayan kizo”.

Kai Indu ta gyaɗa jikinta na rawa ta miƙe ta nufi Bedroom ɗinta jin babu alamar wasa a muryansa.


Ahankali Imraan ya sauƙe Ajiyar zuciya tare da sanya Lallausan tafin hannunsa ya ɗaura akan hancinta sauran rabin hannunsa na ƙirjinta tamkar mai tsoro ko shakkar wani abu ya kai bakinsa dake rawa kan nata lokaci ɗaya ya lumshe idanunsa tsikar jikinsa na tashi cikin tsinkewar zuciya da fargaba ya shiga hura mata Sanyayyar iskar bakinsa acikin nata yana danna ƙirjinta kana yana shafa sumar kanta.


Sannu ahankali numfashinta ya fara dai-dai ta Imraan kuwa ahankali ya cigaba da hura mata Sanyayyar iskar bakinsa dake ƙamshi yana shaƙar nata yayin da gaba ɗaya rabin jikinsa ke manne da nata.


Sannu ahankali Neenah ta fara buɗe Idanunta dake lumshe har tayi nasaran buɗe su gaba ɗaya akan Imraan da har zuwa lokacin bakinsa ke kan nata sai dai dishi-dishi take ganin komai duk da cewa idanunta abuɗe amma bata fahimtar abinda ke faruwa motsa sassan jikinta tashiga ƙoƙarin yi amma baki ɗaya takasa saboda yanda ya sake mata nauyinsa ga kuma jikinta da babu ƙarfi.


Ahankali Imraan ya cigaba da hura mata sanyayyar Iskar bakinsa kana ya ɗan gatsa Lips ɗinta na ƙasa kaɗan-kaɗan tare da ja..

Neenah kuwa wani irin matsanancin tsoro da fargaba ne ya lullubeta jin nauyi akanta yasa ta ɗaga hannunta ta motsa tare da ɗaura akan yalwataccen sumar kansa me laushi da santsi ga kuma sanyayyan ƙamshin turarensa dake ratsa hancinta ko kaɗan takasa taɓuka komai sannu ahankali ta fara buɗe idanunta da har zuwa lokacin bata iya gane komai sai dishi-dishi haka zalika bata dawo cikin hayyacinta ba Aruɗe tashiga ƙoƙarin buɗe baki da niyyar magana amma ta kasa sakamakon numfashinta dake cigaba da fusga cikin ƙanƙanin lokaci numfashinta ya cigaba da kai komo bugun zuciyarta ya cigaba da karuwa fiye da kaso Cassa'in cikin ɗari lokaci ɗaya Idanunta sukayi sama kana hannunta ya zame ƙasa ta alamar ta sake suma har zuwa lokacin kuma Imraan bai janye bakinsa daga nata ba..


  Da gudu Indu ta fito bayan ta canza kayan jikinta zuwa Saudi Abaya ta yane kanta da veil.

Tashin hankali da ɗimuwar da take ciki bai sa ta fahimci kusancin dake tsakanin Neenah da Imraan ba.

Cikin muryan kuka tace.

“Yah Imraan.

Wani irin bugawa zuciyarsa yayi da masifar ƙarfi kasa ɗago kansa ya kalleta yayi saboda matsanancin kunya.

Indu kuwa araunane ta dafa kafaɗarsa tare da cewa.

“Yah Imraan mu tafi dan Allah kayi sauri mu kaita asibiti ta har yanzu bata numfashi!”.

Cikin sauri da kyarma ya janye jikinsa daga na Neenah tare da fesar da numfashi mai sanyi ahankali ya miƙe kana ya tallafota jikinsa kallon Indu da takasa tsayawa yayi ya nuna mata ƙasan center table da ido asaman laɓɓansa ya furta.

“Ɗauko key motar gashi can”.

Ya ida maganar tare da ficewa da Neenah dake rungume aƙirjinsa.

Cikin sauri Indu ta ɗauki Car key tabi bayansa gidan baya ya buɗe ya saka Neenah cikin sauri Indu ta buɗe bayan ta shiga kana ta ɗaura kan Neenah acinyarta tana hawaye da ƙarfi ya danna hong cikin sauri mai gadi ya buɗe masa da mugun gudu yaja motar zuwa wani private hospital dake gaba dasu minti minti yake kallon Neenah ta madubi wacce babu alamar numfashi atare da ita.


Cikin tsanananin tashin hankali Lateefa ta sake labulen Window tare da jingina bayanta da jikin bango ta zame ƙasa ganin ficewar motar hawaye masu masifar zafi da ƙuna suka shiga bin kuncinta Shar-shar-shar tamkar an buɗe Famfo.

Cikin sanyi Meenah ta tsugunna gefenta kana ta Marerece fuska cike da damuwa ta dafa kafaɗarta muryanta na rawa tace.

“Haba Lateefa shin Kukan me kikeyi!?, Dan Allah kada ki karya min zuciya sam kuka akan ɗa Namiji bai cancance kiba nawa akayi Imraan da har zaisa ki zubda hawayen ki kada fa ki manta wacece ke?”.

Cikin rauni da ƙunan zuciya ta ɗago kanta ta kalleta kana ta girgiza Kai batare da tace Uffan ba tafi kowa sanin wanene mijinta ta tabbata mijinta da ban yake da sauran maza jarumine sannan kuma miskiline baya ɗaukar raini komai ƙanƙantarsa.


Jinjina mata kai Meenah tayi cike da bata ƙwarin gwiwa tace.

“Kada fa kimanta kece Lateefa maganin maza!, Lateefa Virus!, Lateefa shu'uma!Wacce ke juyawa tamkar hawainiya wacce ke firgita gungun maza sam kuka bai dace da wannan fuskarta ki me cike da Jarumtaka ba”!.


Wani gauron numfashi Lateefa ta sake tare da yin murmushi still hawaye na bin kuncinta tace.

“Hmm Meenah har yanzu baki san wanene Mijina ba Imraan da kike gani ya zarce tunani duk kan me tunani Imraan da kike gani shu'umin namiji ne kallo ɗaya zai yiwa mace ta fita hayyacinta”.

Ta lumshe idanunta cikin tsira mata ido tace.

“I think akan idonki akayi komai saboda wancan ƴar matsiyatan!, ƴar talakawa!,Ƴar zina!,tsintacciya ya tozarta ni!”.

Ƙwaffa tayi tare da kallon Meenah da itama ita ɗin take kallo tace.

“Akan wata Bagashariyar banza gaula mara tushe da asali ya mare ni, wallahi³ sai sun ɗanɗani kuɗarsu saina tabbatar musu da bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane saina tarwatsa duk kan farin cikinta”.


 Murmushi Meenah tayi kana tace.

“Haka nake son ji Lateefa ki zama jaruma ni wallahi nayi mamaki yanda kika bar Imraan yake juya ki son ranshi shin nawa Imraan yake!?Awajenki da har zai wulaƙantaki!?”.

Ƙwaffa Lateefa tayi tare da miƙewa ta harɗe hannunta aƙirji kana tajuya tayi taku biyu zuwa uku cike da isa ta juya tace.

“Wallahi wa rabbul ka'aba sai Imraan yasan ya ɗaga hannu ya mareni agaban karuwar yarinyar nan,Bayan haka saboda son ya tozartani yasa hannunsa dake mallakina ya ɗauketa agaban idanuna ya fita da ita Hmmm!”.

Ta ida Maganar cikin ƙunan zuciya da tarin takaici.

Murmushi Meenah tayi kana tace.

“Haka nake son Jin Lateefa Virus kinci dubu sai ceto maƙiyanki fadawanki ba Imraan da Indu ba har Uwar data haifesa Ki nuna musu cewa su ƙananun ƴan bariki ne!.

Wani miskilin murmushi ta saki mai cike da ma'anoni masu tarin yawa tace.

“Just Wait and See Meenah zan shayar dasu mamaki”.

Zama Meenah ta gyara kana tace.

“Haka nake sonji kada ki ɗaga musu ƙafa”.


****

Acan ɓangaren Meerah kuwa tunda tashiga bedroom ta kife kanta akan katifa take wani irin kuka me mai gunji da gurnani buɗe ƙofar Bedroom din da taji yasa ta ƙara sautin Kukanta.

Cikin sauri Gimbiya Fa'izah ta ƙarasa shiga ɗakin kana ta zauna gefen gadon cike da damuwa ta dafa kafaɗarta tace.

“Tun ɗazu nayi niyyar shigowa TOH sai kiran Hajiya Hassana ya tsaidani hope dai lafiya?”.

Jin shiru yasa tayi saurin ƙara sawa kusa da ita tare da cewa.

“Innalillahi Wa'inna ilahi rajiu'n Meerah lafiya kuwa Meyesa meki?,Me aka miki?,Ko wani wajen ke miki ciwo kada fa kisa damuwar Abdallah aranki ya janyo miki wata Cutar!?”.

Duk alokaci ɗaya ta jero mata tambayar tana tattaɓa jikinta.

Uffan Meerah bata ceba sai ƙara sautin kukanta da tayi tana birgima tare da shush-shura ƙafarta akan bedsheet din da duk ta tuƙui-ƙuye kana Atake jikinta ya fara tsuma yana wani irin ɓari da har gadon ke motsawa kana lokaci ɗaya gashin kanta suka miƙe suka tsaya tamkar wacce shorking yaja kana ƙwayar Idanunta suka sauya launi zuwa kore shar yayin da faratun hannunta(Ƙumba) suka ƙara tsawo fatar jikinta ya fara sauya kala izuwa Shuɗi kalar tsaka.

Aruɗe Gimbiya Fa'izah dake gefenta ta miƙe tare da ja baya cikin rawan murya da tsananin tashin hankali take kallon ta baki ɗaya yanayin halittar ta ya sauya Aruɗe ta miƙe taja baya zuciyarta na bugawa da masifar ƙarfi cikin tsanananin tsoro da fargaban

ganin abinda bata taɓa gani ba a iya tsawon rayuwarta.


Cikin rawan jiki ta cire wayar dake hannunta a key ta shiga contact ta fito da Number data serving da mai Mai martaba tayi dearling amma har ya katse ba'a ɗauka ba sake dearling tayi still ba response cikin tsananin tashin hankali tayi dearling Number da tayi serving da Hajiya Babba amma shima har ya katse ba response aƙalla sai da ta kira sau bakwai bakwai ba dauka ka kafin ta haƙura.


Wani irin kallo Meerah data sunkuyar da kanta ƙasa tayi mata kana tana wani irin girgiza da gurnani.

Cikin tsinkewar zuciya Gimbiya Fa'izah ta haɗiye wani yawu me masifar daci batasan lokacin da tayi dearling Number da tayi serving da Bundi amma har ya katse ba ayi picking ba wayarce ta suɓce ahannunta yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ke tsuma zufa na tsats-tsafo mata.

Meerah kuwa kanta ta ɗago tare da miƙewa ta tsaya Atsakiyar gadon kana ta tsirawa Gimbiya Fa'izah dake tsaye ido da wani irin ƙarfi ta fincike bedsheet dake kan gado ta nufi Gimbiya Fa'izah cikin wata murya tamkar na kukan Jaki ta fara cewa.

“Meya kawo ki sansanin mu!?,Shin meyasa kika shigo inda ba agayyace kiba lallai zaki ɗanɗani ku ɗarki bama son shish-shigi da azarɓaɓi acikin lamarin mu!”.

Aruɗe Gimbiya Fa'izah ke Girgiza kai batare data iya furta koda kalma ɗaya ba saboda tsanananin firgici da ɗimuwar abinda Idanunta suka gane mata.

Tamkar Butter fly haka Meerah ta tashi sama tana yawo har ta isa saitin kan Gimbiya Fa'izah tana zuwa ta shaƙe wuyanta kana ta ɗagata da hannu ɗaya tayi sama da ita tana jujju yata tamkar wacce ta ɗauki ƴar tsana.

Cikin sarƙewar murya Gimbiya Fa'izah tace.

“Dan Allah Meerah ki sauƙeni wallahi jiri(Juwa)nake gani kada kisa hawan jinina ya tashi dan Allah ki daina”.

Wata mahaukaciyar dariya mara daɗin amo Meerah ta sheƙe dashi kana tace.

“Kul kada ki sake haɗamu da Allah idan ba so kike ku cire miki Autan hanji da kuma zululin wuya ba”.

Arazane ta toshe bakinta yayinda zufa ya shiga sauƙa ajikinta lokaci ɗaya dakin ya fara sauya launi zuwa ja da baƙi me fatsi-fatsi wani irin wuta na kawowa da ɗauke wa


**

Acan ɓangaren Imraan kuwa awani madaidaicin Private hospital me kyau yayi parking asibitin bashi da girma sosai haka zalika babu hayaniya komai akimtse yake suna shiga aka karɓi Neenah kai tsaye Emargancy aka Kaita tare da bata temakon gaggawa cikin ikon Allah aka samu numfashinta ya dai-dai ta Alluran bacci likitocin suka mata saboda yanda take kuka da surutai yasa Imraan yace amata saboda ta samu wadatacciyar hutu.

Cikin sanyi Indu dake riƙe da hannu Neenah ta ɗago Idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kalli Imraan daya tsirawa gadon ido ajiyar zuciya ta sauƙe kana cikin sanyi murya tace.

“Yah Imraan ka koma gida zan kula da ita In sha Allah kawai ka bamu kuɗin adaidaita idan ta tashi zamu dawo tunda Dr yace idan ta farka zata dawo dai-dai”.

Imraan kuwa baki ɗaya nutsuwar sa nakan Neenah dake kwance dogon hancinta da ya sake tsayi shi yafi komai ɗaukar hankalinsa kana fuskarta tayi fayau yayin da manyan idanunta suka sake girma eyelashes ɗinta ya sake tsayi kana siririn billen ta dake gefen hagu ya fito madaidaicin bakinta na motsi duk da kuwa bacci take amma kallo ɗaya zaka mata kasan cewa akwai damuwa mai yawa atare da ita.


Ahankali Indu ta sake cewa.

“Yah Imraan!,Yah Imraan!!,Yah Imraan!!!”.

Jin Bai amsa ba yasa ta juya ta kalli saitin inda yabi da kallo gani tayi baki ɗaya idanunsa da nutsuwarsa yana kan Neenah zare Ido tayi sai kuma ta miƙe ta riƙe tafin hannunsa tare da jijjigawa tace.

“Yah Imraan!”.

Aɗan firgice ya juya kana ya sauƙe Ajiyar zuciya cikin sanyi murya yace.

“Ya akayi Indu,Me kika ce?”.

Kallonsa tayi har zuwa lokacin idanunsa na kan Neenah.

Numfashi ta fesar kana tace.

“Yah Imraan ka koma gida ka huta sai ka canza kayan ka idan yaso idan ta farka tunda Dr yace Insha Allah lafiya zata farka sai mu tari adaidaita mu taho ko?”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da shafa sumar kansa kana yace.

“Kada ki damu zan jira ku har ta farka sai mutafi tare bana tunanin zan tafi ina barku”.

Kai ta gyaɗa kana ta zuba ta gumi tare da tsirawa Neenah ido cike da tausayinta.

Ahankali Imraan ya juya ya nufi ƙofa ya fita jin ana kiraye-kirayen sallar maghariba kai tsaye masallacin dake cikin asibitin ya nufa ajikin tap dake maƙale da masallacin ya ɗaura alwala kana ya shiga cikin jam'u...


Ajiyar zuciya Indu ta sauƙe tare da janye hannunta dake cikin na Neenah ta nufi toillet dake maƙale da ɗakin ta buɗe numfashi ta fesar ganin komai atsaftace alwala ta ɗaura kana ta ɗauki hijabi Neenah ta sanya tare da shimfida veil ɗinta ta tada Sallah.


**

Akuma dai-dai lokacin anutse Sir Abdallah ya shiga coumpund ɗin su bayan an idar da Sallah Isha'i hannunsa maƙale da counter kamar ko yaushe yana istigfari da tasbihi.

Direct sashensa ya nufa daidai lokacin wayarsa ta ɗauki ruri kallon wayar yayi tare da ƙarasawa akuma dai-dai lokacin kiran ya katse zare ido yayi ganin 20miss call zama yayi agefen gadon ya buɗe miss call ɗin Sir Auwal ya gani guda uku sai kuma na Gimbiya Fa'izah guda sha bakwai.

Jingina kansa da jikin gadon yayi kana afili ya furta.

“Auwal bazai bari na huta ba but ita kuma wannan kiran me take min har Miss call 17?”.

 

Number ta ya danna kafin ya shiga kiran Sir Auwal ya shigo.

Dafe kai yayi tare da picking call din batare da yace komai ba.

Daga ɗaya ɓangaren Sir Auwal yace.

“Wannan wani sabon wulaƙanci ka koya A.A Zaman?tun safe nake aikin kiran ka amma sai yanzu kaga damar ɗauka”.

Lumshe idanunsa yayi kana cike da Izzah da kuma ƙasaita daya zama ɗabi'arsa yace.

“Ohhh Auwal wallahi ka fiye mita kamar mace kasan uzurin daya hanani picking call ɗin ka ne any way ai gashi na ɗauka Meke faruwa?”.

Hararan wayar Sir Auwal yayi kana yace.

“To ai banji ka faɗi abinda ya dace bane kafin mu fara maganar.

Murmushi Sir Abdallah yayi tare da shafa sumar sa yace.

“Ok Am sorry³ yanzu ya akayi”.


Anutse Sir Auwal yace.

“Dama akan maganar wannan mutumin nan wani mataki kake tunanin za'a ɗauka akansa?”.

Atake yanayin fuskar Sir Abdallah ya sauya cike da takaici ya furta.

“Auwal ku ɗauki duk matakin daya dace dan wallahi idan har ni zan ɗauki mataki saina sa an dandaƙesa🙆🏻‍♀️🤣 dan babu amfanin irinsu adoron ƙasa.

Murmushi Sir Auwal yayi cikin sigar zolaya yace.

“Haba ranka shi daɗe sai kace Taure adan daƙesa!?”.

Dogon tsaki yaja kana yace.

“Toh meye amfanin irinsu adoron ƙasa basu da aiki sai lalatawa ƴaƴan mutane rayuwa ba abinda yafi ƙona min rai kamar riƙe mata hannu da ƙugu da yayi akan me zai taɓa jikinta toh wallahi saina sa an tsire min shi”.

Zare ido Sir Auwal yayi tare da cewa.

“A'a duk ba za ayi haka ba A.A Zaman kamar yanda ka faɗa zamu ɗauki hukuncin daya dace”.

Baki Sir Abdallah ya taɓe kana yace.

“Allah yasa hukuncin yazo dai-dai da ra'ayina domin bazai taɓa jikinta abanza ba”.

Murmushi Sir Auwal yayi kana yace.

“In sha Allah za'a yi yanda kace sannan kuma an gama ƙera Motoci guda ɗari uku da jirgi Hamsin wanda za'a fita dasu”.

Lallausan sumar kansa ya shafa kana yace.

“Masha Allah aiki na tafiya za'a kai motoci guda Ɗari da jirage goma Libya,Sannan za'a bar motoci ɗari da jirage ashirin anan gida Nigeria,Sai kuma sauran motoci ɗari da hamsin da jirage Ashirin za'a kaisu Itally”.

Kai Sir Auwal ya jinjina tare da faɗin.

“Ok In sha Allah nan da jibi za'a yi hakan amma ya za'a yi da Ƴan Pakistan da sukayi booking”.

Cikin sauƙe numfashi ya furta.

“In sha Allah nan da next week zasuji mu”.

Ya ida maganar tare da katse kiran yayin da zuciyarsa ke saƙe-saƙe.


Number Gimbiya Fa'izah yayi dearling amma har ya katse ba ayi picking ba sake dearling yayi still ba response.

Ahankali ya miƙe ya fita tsakar gidan haske tamkar rana sai Iska dake kaɗawa da kuma Bishiyoyin dake rangaji ga hadari daya taso sai walƙiya dake haskawa gari yayi sanyi ni'ima Ubangiji na ratsawa tako ina.


Ma'aikatan gidan da bayi sai durƙusa wa suke suna kwasan gaisuwa hannu kawai yake ɗaga musu Yana isa sashen Ammie ya buɗe ƙofar falon yashiga dai-dai lokacin da take ƙoƙarin fita.

Ganinsa yasa taja baya kallonta yayi cike da kulawa yace.

“Ammie ina zakije awannan hadarin?”.

Cikin yanayin damuwa tace.

“Ɗazun ina sallah aka ta kiran wayata toh ko dana idar nace bari na duba ashe Fa'izah ce na sake kira kuma yafi sau nawa ba aɗauka ba shi yasa nace bari naje na duba ko Lafiya”.

Jinjina kai yayi kana yace.

“Ikon Allah nima bayan na dawo daga masallaci naga miss call ɗinta sannan na sake kiranta bata ɗaga”.

Zare ido Ammie tayi cikin yanayin damuwa tace.

“Subhanallah amma lafiya kuwa bari dai naje na duba”.

Saurin riƙe hannunta yayi ganin tana ƙoƙarin fita yace.

“Ina zakije haka Ammie?”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Autah Fa'izah baza tayi mana wannan kira abanza ba kasan halinta tunda kaga wannan kiran akwai dalili”.


Har ya buɗe baki da niyyar magana wayarsa ta hau ruri ganin number dake yawo a screen ɗin yasa yayi sauri ɗauka cike da ladabi yace.

“Assalamu Alaikum Abiey Barka da warhaka”.

Daga ɗaya ɓangaren Sarki Aliyu Ahmad Zaman ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Babana kana gida ne?”.

Kai Sir Abdallah ya gyaɗa cike da ladabi ya furta.

“Eh Abiey ina nan”.

Ajiyar zuciya mai martaba ya sauƙe kana yace.

“Ok kaje sashen Fa'izah ka duba ko lafiya naga miss call ɗinta da yawa sannan na kira bata daga ba kuma ina da baƙi”.

Kallon Ammie Sir Abdallah yayi ganin yanda ta tsira masa ido yasa ya ƙirƙiro murmushi kana yace.

“Toh Abiey Allah yaƙara girma da daukaka atashi lafiya”.

Cikin sauri Ammie tace.

“Shima ta kirasa ko na faɗa maka ba lafiya ba wataƙil bata da lafiya ne”.

Numfashi ya fesar zuciyar Ammie daban yake duk irin yanda matar ke nuna mata ƙiyayya bata gani ya tabbata da cewa da miss Call ɗin Ammie Gimbiya Fa'izah tagani ba zata damu ba.

Cikin son kwantar mata da hankali yace.

“Dan Allah Ammie ki kwantar da hankali bari naje na duba”.

Ya ida maganar tare da barin wajen yana ƙoƙarin shiga falon yaga hadimanta biyu atsaye ganin sa yasa sukayi saurin durƙusa wa suka gaisa amsawa yayi tare da cewa.

“Lafiya kuke tsaye anan?”

 cikin rawan murya ɗayar tace.

“Yallaɓai da alama babu lafiya tun ɗazu muke jin wani irin kuka da gurnani aciki”.

Bai jira ta ƙarasa ba ya buɗe Kofar falon yashiga.

Anutse yabi tsarerren falon da kallo komai Ash&Blak ne duk kayan ciki na sarauta ne sai ƙamshin Roomfreshner dake tashi numfashi ya fesar kana Ahankali ya nufi wani siririn Corrido dake wajen bakinsa ɗauke Sallama ahankali yaji wani irin gurnani da kururuwa ke tashi cikin sauri yaja baya cike da mamaki.


Daidai lokacin da Gimbiya Fa'izah ta faɗo gabansa da kallo ya bita cikin yanayin tashin hankali ya tsugunna akanta tare da jijjigata yace.

“Aunty Fa'izah!,Aunty Fa'izah!!Aunty Fa'izah!!!”.

Amma koda wasa bata motsa ba kana babu alamar numfashi atare da ita sai goshinta dake tsirtar da jini tsit-tsit-tsit da kuma gefen bakinta daya kumbura.

Cikin sauri ya miƙe da niyyar ɗaukar ta daidai lokacin da Meerah ta fito tamkar wacce aka jefota jikinta sanye da wani dogon riga ja daga gaba zuwa gwiwa a ɗangale daga bayansa kuma yana Jan ƙasa kana hannayen nada faɗi da tsawo still gashinta na tsaye kamar yanda yake haka zalika halittar ta bai sauya ba cikin sauri Sir Abdallah ya kawar da kansa tare da ɗaukar Gimbiya Fa'izah ya nufi ƙofa da ita tsalle Meerah tayi ta bugi bayansa da ƙarfi da tafin ƙafarta taga² yayi zai faɗi yayi saurin ajiye ta akan 3sitter ya juya Afusace ya miƙa hannu da niyyar riketa ta sake buga wani uban tsalle ta naushesa akuncinsa na dama wanda yasa ya durƙusa akan gwiwoyinsa.


Azuciye Sir Abdallah ya miƙe tare da tsira mata idanu baki ɗaya halittar ta ta sauya haƙoranta sunyi zaƙo-zaƙo tamkar horuwa babu ken gani cikin shanmata Meerah ta sake kawo masa wani dukan asaitin maƙogoransa cikin sauri ya tsugunna ƙasa tare da kauce mata yana kallonta cike da mamaki da al'ajabi sam baison kai hannunsa jikinta domin yasan zai mata Illah miƙewa yayi da sauri ganin ta nufo kansa gadan-gadan wani naushi ta kawo masa yayi saurin kaucewa ta samu Tv Plasmer dake manne jikin bango Atake ya fashe tare da tarwatsewa sai ƙarfensa ya rage Gotv dake wajen ta ɗauka ta cilla masa.

Cikin yanayin ɓacin rai da zuciya ya miƙe ya nufeta Afusace ya kai mata mari wani irin zare ido tayi Atake ƙwayar Idanunta suka koma Jajawur tamkar wuta cikin sauri ya janye hannunsa da yaji tamkar anjona masa shocking baya yayi cike da tsananin mamaki da al'ajabi baki ɗaya tunaninsa ya kulle anya wannan Meerah ce kuwa.


Anutse Ammie dake tsaye a balcony riƙe da wuyarta tayi saurin cewa.

“Zan Kira ki anjima”.

Tana Ida faɗar haka ta katse kiran kana ta janye wayar daga kunnenta.

Ahankali tabi Balcony da kallo tun ɗazu hankalin ta yaƙi kwanciya ga suna sautin ƙaran fashe-fashe da taji.

Cikin sassarfa ta nufi sashen lokacin data je tuni bayin suka bar wajen tana isa tasa hannu ta buɗe Kofar falon.

Kallon kallo aka shiga yi tsananin Sir Abdallah da Meerah azabure ya nufeta daidai lokacin idanunsa suka sauƙa akan Ammie dake tsaye jikin ƙofa duk idanunta awaje tana kallon Meerah.

Cikin yanayin tashin hankalin ya shiga Girgiza mata kai alamar ta koma kada ta karaso.

Ammie kuwa cikin tsananin tashin hankali da ruɗu take kallon Gimbiya Fa'iza dake kwance asaman kujera babu alamar numfashi atare da ita kana ta kalli yanda falon ya hargitse tamkar Wanda akayi yaƙi kallonta ta mayar kan Meerah dake wani irin gurnani Aruɗe ta furta.

_“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal wakin Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahlifli khairan minha_,Meerah Meyesa meki me akayi miki?”.

Cikin dakewar zuciya Sir Abdallah ya juya ya kalleta kana yace.

“Ammie ki tafi ki bar wajen nan kada ki tsaya dan Allah ki tafi tsayuwar ki akwai matsala!”.

Wata mahaukaciyar dariya Meerah ta fashe dashi da yasa Ammie kasa ƙwaƙƙwaran motsi ƙaramin wuƙar dake kan Fruit din Center table ta shammace su ta dauƙa kana ta nufi kan Ammie.

Wani irin kukan Kura Sir Abdallah yayi kana ya nufi kanta kafin ya isa tuni ta rigasa isa kan Ammie ta zauna ruwan cikinta tare da ɗaga wuƙar ta saita tsakiyar Idonta yayin da ta saita gefen cikinsa na dama ta buga masa naushi wanda ya kaisa ƙasa.


Aruɗe ya Miƙe ya isa kanta cikin dakewar zuciya da jarumtaka ya kai hannunsa na dama kan hannunta dake riƙe da wuƙar wani masifaffen Shorking ya jasa runtse Idanunsa yayi da ƙarfi kana ya ƙanƙame hannunsa cikin tsananin azaba da raɗaɗi ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukayi Ja ya kalleta.

Meerah kuwa wata mahaukaciyar dariya ta sheƙe dashi kana ta juya ƙotar wuƙan ta bugawa Ammie adai-dai saitin kanta kana ta sanya hannunta ta shaƙe wuyanta da ƙarfi tana danna yatsun ta ciki.

Cike da azaba Ammie ke fitar da wani irin numfashi me wuya jin tamkar wacce aka jona ajikin transformer yayin da Idanunta suka fiffito waje suna sauya kala numfashinta na fusga daga gangar jikinta...


_@Follow me on Arewabooks realeshaa_


_@Follow me on Wattpad realeshaa_



_Ya Allah Ubangijin kajiƙan mahaifina ya Allah kagafarta masa zunubansu ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mu cika da imani..._


_Ayi shearing saboda Allah Ƴan Uwa masoya da abokan arziƙi_


      *👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***


          *ESHAA CE*🤙🏻