A HAKA NAKE SON SHI

2

by @saratalkasum88

~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~






Daga Alƙalamin


_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_



_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_



Littafin A HAKA NAKE SON SHI na kuɗi ne nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500.


_🥏 WhatsApp Number +966577675904_



*بسم الله الرحمن الرحيم*



Shafi na biyu (2)


Da mamaki Dattijo ke kallon Abir ganin yadda nan-da-nan jikinta ya ɗauki rawa, dawo da kallonsa ya yi kan motar yana jiran ya ga waye zai fito wanda kafin ya fito ɗin ma yarinya ta tsorata?. Direba ya fito cikin sauri ya zagayo baya ya buɗe tare da rusunawa ya ce "Oga mun iso wajan."

Yana zaune ya hakimce a gidan baya ya kwantar da kansa a jikin kujera idanunsa a lumshe, wanda in ka gan shi a haka sai ka rantse bacci yake shi kuwa yana tsaye. A hankali ya ɗago da hannunsa na hango ya bude idanunsa tare kalon agogon dake hannunsu, sai da ya sha ƙamshi ya shirya dan kasan dan har direba ya kosa da riƙe marfin motar da ya yi sannan ya fito da ƙafarsa ɗaya waje, sai da ya kai sakan arba'in sannan ya fito da ɗayar ƙafar, miƙo kansa ya yi yana wani shan ƙamshi, sai da ya shirya dan kan shi sannan ya fito daga cikin motar.

Dogo ne fari sol zubin ƙarfafa kyakyawa ajin farko wanda bai fi shekara 30 ba, fuskarsa sanye da ɓakin glass wanda ya ƙara wa fuskar tashi kyau da ƙwarjini a idanun mai kallon shi, yana da saje wanda ya ƙara ƙawata fuskar. Sanye yake da ƙananan kaya baƙaƙe har hula cap dake kansa wadda a jikin hular aka rubuta *D. S. P*, sake lumshe dara-daran idanunsa ya yi yana yatsina fuska jin iska ta kawo masa wani irin wari marar daɗin shaƙa ya buɗe su tare waro su akan Baba Dattijo, sai da ya gama ƙare wa wajan kallo sannan ya dubi Dattijo ya ce " Hey tsoho ba ka ga wata yarinya a nan ba?" Ya yi maganar yana sauke ajiyar zuciyar ya yi magana mai tsayi, kuma duk da ya ganta amma saboda hali irin nasa yake tambaya.

Dattijo ya dube shi ya ce " Kai ɗin waye? Sannan kuma wa kake nema?"


Jin muryar wanda ya yi maganar Abir dake bayan Dattijo ta leƙo kanta dan ta tabbatar ko masarrafar jinta daidai ta jiyo mata. Idanuwanta suka sauka a kan shi, sai yanzu ma ta ji ƙamshin turarensa ya kawo mata ziyara cikin wani kalar yanayi ta dan fesar sa numfashi sannan ta fito daga bayan Baba.


Wani irin waro idanu ya yi tare da yin taku biyu, ganin haka yasa ta isa gareshi tare da sakin kukan da take dannewa, shi ko saurin cire glass ɗin fuskarsa ya yi yana kallon ta fuska ɗauke da mamakin ganin ta kamar ya ga sabuwar halitta, wani irin yanayi ya shiga na ganin ta cike da al'ajabi ya gyara tsayuwa ya ce "Baby!"


Matsowa kusa da shi ta yi kamar za ta faɗa jikinsa ta ruƙo hannunsa cikin muryar kuka ta amsa.

"Yaya! Ashe zan sake ganin ku a rayuwata? Don Allah ka yi sauri ka ɗauke ni kar su kuma sace ni." Ta faɗa ta na girgiza hannunsa, farin ciki ya mamaye mata zuciya ganin Yayan nata a wannan lokacin..

Hannu ya sa ya goge mata hawayen duk da a kiɗime yake, amma bai nuna ya shiga ruɗu ba cikin kasalalliyar murya ya ce "My Babyy." Ya ƙarashe maganar yana kallon tufafin dake jikinta, jin warin dake tashi daga jikinta yasa ransa ƙara ɓaci ya buɗe mota tare da kallon ta, ganin haka ya sa ta gane me yake nufi ta nufi ƙofar da ya fito.

Har za ta shiga ta juya ta dawo wajan Dattijo ta dube shi ta ce " Baba na gode Allah ya saka da alkhairi zan ɗauki number ka a wajan Mommy, sannan in da hali tun da ka ce kai baya ce ma komai in ka kai masa abinci, ina so ka ba shi magani ko ka wanke masa wajan saboda sun sare shi da girma a wajan. Zan samu lokaci sai na zo in Allah ya ba ni iko , sai an jima Baba Allah ya sada mu da alkhairi." Ta faɗa tana kallon hanyar da ya bi.


Murmushi Dattijo ya yi yana jinjina kai, sosai ya ji yarinyar ta birge shi ya ce " Karki damu yarinya ai an jima ma zai fito waje, Allah ya kiyaye gaba ya tsare miki rayuwa." Amin ta ce tana murmushi sannan ta dawo ta shige motar shi ma ya shiga suka bar wajan..


Suna tashin motar sai ga shi ya dawo da sauri Dattijo na shirin wucewa ya ji ƙaran tafiyarsa ya juyo da sauri.

Yana muzurai ya dogare sandarsa tare da tsayuwa irin ta fulani yana dariya ya ce "Baba Anty ta kawo abinci?"

Girgiza kai kawai Dattijo ya yi ya wuce ya bar shi a bakin hanyar yana ta surutai.

Shi kuwa ɗankwalinta da ta yi famar ta ɗaura masa a kafaɗa ya kalla ya ce " Ni ne sarkin wannan rawanin ya zama naki Anty, duk wanda ya zo nan sai ya biya kuɗin mota zai tafi." Haka ya yi ta surutu yana zagaye bakin hanyar, duk wanda ya zo wucewa sai ya ce masa " Kasan Anty?"

In ka ce ba ka san ta ba zai ɓata rai ya nufe ka da rabin taɓarya ya ce 'me ya sa ka ce ba ka Anty ba?' In Allah ya taimake ka ka gudu ka tsira, idan kuma ka ce ka san ta sai ya yi ta dariya ya bar ka ka wuce yana bin ka a baya har sai kun yi ƴar tafiya sannan ya dawo..



Tun da suka shiga cikin motar ya dinga kallon ta yana jera mata sannu har suka isa gida.


A jikin gidan an rubuta

*FAMILY HOME MAITAMA*


Babban gida ne yana da ɓangarori hudu haka akwai babbar haraba a gidan inda aka yi wajan aje motoci a gaf da ɓangaran farko, harabar gidan an ƙawatata ce shukoki ko'ina ka kalla kwanan birgewa fulawowi ne a jere isar Magariba na kaɗa su.


Suna gama packing direba ya fito ya buɗe musu suka fito, hannunta ya kama suka bi wata ƙofa wadda za ta sada su da cikin gidan. A babban palon gida suka yi sallama in da yake cike da mutanen gidan maza da mata da ƙananan yara, da sauri ta fisge roƙon da ya mata ta nufi wajan wata matashiyar mata hakan yasa ita ma ta tashi da sauri suka haɗe ta faɗa jikinta tana kuka.

Kowa na palon fuskarsa ɗauke take da farin ciki sun zagaye ta suna ta taɓa jikinta duk da wari da take bai hana ɗaya bayan ɗaya sun rungume ta ba suna kukan ganin ta.



Shi kuma gefe ya samu ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon su, ganin ba za su gama ba ya sa ya daka wa wasu 'yan mata uku dake rungume ta ita tsawa .

"Ku sake ta na ce!" Ya faɗa a fusace, gabaɗaya sun sa kansa ya fara ciwo da wannan hayaniyar ta su, ga wani irin yanayi da yake jinsa da zarar ya kalle ta.

Nan-da-nan duk suka sake ta ita kuma ta dunga kallon familyn nata ɗaya bayan ɗaya, can ta hango tsohuwa zaune a kan kujera ta hakimce tana kallon ta, murmushi ta yi ta soma takawa a hankali ta ƙarasa ga tsohuwar da take farin cikin ganin ta ta ce ",Grandma wai ba ki ganni ba ne."

Wani irin kallo Grandma ta mata ta sauke ƙafafuwanta daga harɗe su da ta yi ta dubi Abir ta ce " Ke raba ni da wannan 'yan bana bakwai ɗin, so kike na tashi ni ma ina wawurar ki kamar su aje su ɓalla min ƙafa? To ni ba gantalalliya ba ce kamar su yanzu da suka gama ganin ki ba ga shi kin zo har inda nake ba?"

Yar dariya Abir ta ɗago kai suka haɗa idanu da shi, langaɓar da kai ta yi kamar za ta sa kuka shi kuma ya kifta mata idanu yana ɗage gira, alama ya mata da ido me ya faru? Cuno baki ta yi gaba ta janye idanunta daga kallon shi ta dawo kan Grandma, zama ta yi a ƙasa kan capet ta yi murmushi ta ce "Grandma kenan wai ko ba ki yi kewa ta ba?"

Kauda kai ta yi ta ce "kayya ƴar nan! In da wanda ya fi ni shiga tashin hankali a gidan nan ai sai dai mahaifiyarki, ko baccin kirki bana iya ci saboda damuwar ban san a wani hali kuke ba a mace kuke ko a raye, ina Ibrahim ɗin yake?"

Za ta yi magana suka ji an buɗe ƙofa duk suka mayar da hankalinsu kan ƙofar, wani matashin saurayi ne ya shigo yana fito ganin duk mutanen gidan a palon yasa ya yi saurin katse fiton da yake ya soma shafa kansa. Idanuwansa ne suka sauka a kan Abir da ke zaune a kusan Grandma, da sauri ya nufe ta yana faɗin "Wa nake gani kamar Baby?


Ita ma dariya ta yi tana kallon shi har ya iso, ƙoƙarin rungumar ya yi ya ji an daka masa tsawa.


"In ka taɓa jikinta sai na kakkarya ka a gidan nan!" Ya faɗa rai ɓace yana huci, a zafafe ya nufi wajan ɗaya daga cikin 'yan matan ya ce "Ke Fatima cire hijabinki ki bani."

Ba muso Fatima ta cire ta miƙa masa shi kuma ya nufi Abir ya yi saurin saka mata tare da miƙar da ita ya ce " Wuce ki je ki yi wanka ki fitar da kayan nan, duk surar jikinki ana gani shi ne kema har kika wani zauna maza suna kallon ki a haka. Kai kuma Salim ka sake bin ta da kallo za ka sani." Ya faɗa yana nuna shi da hannu..

Dariya Salim ya yi dan bai yi mamakin abin da Yayan nashi ya faɗa ba, ya miƙe tsaye ya dafa kafaɗarsa ya ce " Ni fa daɗi na da kai Yaya Abdul ba ka so a raɓi Baby sai ka ce kai kaɗai ne yayanta, Ammi ki faɗa masa ya daina shiga tsakani na da Baby tun da ni ma ɗan'uwanta ne ba bare ba ne ni a cikin gidan nan." Ya faɗa yana haɗe rai tare da kallon matar dake gefen mahaifiyar Abir..


Ko ci kanku Ammi ba ta ce musu ba sai ma harara da take aika wa Abdul har Salim ɗin, tashi ta yi ta ja tsaki ta wuce daga palon kamar za ta tashi sama. Grandma ta tofar da yawu a inda Ammi ta tashi ta ce "Mai hali dai ba zai basa ba, ni ban taɓa ganin shafaffiya da mai irin Farida ba, mace sai ɓakar zuciya kamar dangin kutare, to Wallahi ba da ni ba kai dai Salmanu ba yi dacen mata ba."

Girgiza kai wanda aka kira da Salmanu ya yi ya ce "Ai Mama mu yanzu farin ciki muke da aka samu Abir ta kubuto daga mugun hannun da ta faɗa, ita kuma ki rabu da ita ta je ta yi ɓakin halinta tun da ta saba. Kowa ya tashi ya tafi ɓangaransa Kabir an jima ina son magana da kai." Yana gama faɗin haka ya tashi ya bar wajan. Suma duk suka bar palo ya rage daga Mommy sai Grandma sai Abdul da ya zauna zaman jiran ta fito, da an yi sakan biyu zuwa biyar sai ya kalli ƙofar ɗakinta hakan yasa Grandma ta ce " Uhmm malam ai sai ka tafi ka ba mu waje ko, na ga dai uwarka ba son zaman ka take a nan ba ko da yake ma ai tasan ba ta isa ta hana ka zuwa nan ba saboda uwar ubanka Kabiru tana nan dole ka zo ka zauna a wajena."

Murmushi ya yi kawai bai ce da ita komai ba sai ma juyo da kallon shi ya yi ga Mommy da ke zaune tana danna wa, a sannan ya ce " Mommy abinci nake son ci ina jin yunwa ni da Baby." To ta ce masa sannan ta ce " Laraba ki jera abinci a kan denning Babana zai ci abinci."



Ɓata fuska ya yi jin sunan wadda ta kira, shi fa abin da ya tsana kenan ya ci abincin ƴar aiki, abinci indai ba na Mommy ba ne duk gani yake ba zai yi daɗi ba, fesar da iskar bakinsa ya yi ya ce "Haba Mom ya za ki ce waccan kucakar ƴar ƙauyen ce za ta haɗa mana abinci kuma wai har da Baby za ta ci girkin ta? Gaskiya Mommy ke muke so ki mana abinci ba mai aiki ba." Ya faɗa yana hura hanci.

Murmushi Mommy ta yi ta yunƙura za ta tashi sai ga Laraba ta fito hannayenta dauke da trey tana washe baki ta iso za ta aje.


"Ke! Maza bar wajan man."

Ba ta san lokacin da kayan hannunta suka kubce ba ji kake tass! Suna fashewa, hankalinta a tashi ta kalli Mommy ta ce "Alkur'anin Allah Hajiya hi ya tsorani har abincin ya zube, aradu tsoron hi nake ji ki faɗa masa ya daina firgita ni Hajiya wannan ai he in hiɗe Goggona ta yi asara ta." Ta yi maganar tana dawowa kusa da Mommy fuskar nan sai maiƙo take saboda man da ta narka wa fuskar...


Dariya Mommy ta yi ta ce "Don Allah Abdul ka daina tsorata yarinyar nan haka, kalli ka ga duk kasa jikinta yana rawa."

Kwafa ya yi bai ce komai ba, sai da ya gama duba jikinsa ya ga ba ta ɓata masa da ba ya ce "Wallahi ta ci sa'a ba ta ɓata min kayan jikina ba, da sai na kakkarya ta a palon nan."


"Ba shakka ɗan marassa tausayi da ka soma yin gadon bakin halin waccan mata uban naka Baraka, Wallahi Abdullahi ka guji cin zarafin ɗan'adam." Cewar Grandma tana kaɗa kai.


Cikin shigar doguwar rigar atamfa ta fito daga ɗakinta ta soma takowa a hankali cikin nutsuwa kamar mai tausayin ƙasa, sai yanzu suffarta ta fito. Ɓaka ce ba ta da tsayi har can amma ba za a kira ta da gajerar mace ba, siririya ce ba ta jiki , tana da doguwar fuska mai ɗauke da ɗan ƙaramin bakinta madaidaici, shekarunta ba su fi 18 ba amma ka ganta kamar yar shekara 15 duk da wannan ƙanƙantar amma tana da diri mai ɗaukar hankali, gashin kanta ɓaki sidik wanda ya zubo har gadon bayanta sai sheki yake, hancinta ɗan siriri wanda aka bula shi ta sa masa ƴar barina fara sai ta ƙara ƙawata fuskar.

A kusa da Grandma ta zauna ta ce "Mommy ƙafata zafi take min sabo...


Ba ta ƙarasa maganar ba sakamakon hayaƙin da ya kawo wa hancinta ziyarar bazata ta shaƙa, nan-da-nan ta soma tari tana riƙe ƙirji, kafin minti ɗaya tuni ta fita haiyacinta..







_My sister Littafin nan na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500 ne , ku hanzarta ku biya naku domin ayi tafiyar nan tare da ku._


_🥏+966577675904_







*Idan kin karanta please ki daure ki min share my sister 🙏*


_Hmm mu je zuwa_








_*Maman Nusaiba*_