A HAKA NAKE SON SHIFree

ArewaPen original

RomanceFreeCompleted

A HAKA NAKE SON SHI

  • 1views
  • 29chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

completed

No synopsis yet.

Sample · 1

~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*__🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚__Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Gargadi! Ban yarda wani ko wata su juya min labarina ba ta kowacce fuska, yadda na fara lafiya Ubangiji ka ba ni ikon gamawa lafiya, Allah ya tsaftace mana Alƙalaminmu._*بسم الله الرحمن الرحيم*Mabuɗi *(1)*Sassanyar iskar yammaci da ke kaɗawa haɗi da sanyin ƙasa suka haɗu suka bada wata kalar ni'imtacciyar iska mai daɗin shaƙa. Daidai kwanar wani layi cikin wata unguwa wata budurwa ce ta yanko layin a guje, gudu take irin na ceton rai tana yi tana waiwayen bayan ta har ta ƙaraso bakin titi. Waiwayawar da za ta yi ta hango wasu garadan maza uku suna nufo ta, cikin tashin hankali ta rasa inda za ta nufa kasancewar wajan shuru sai wata ƙatuwar bola dake gefen hanyar. Can gaba kaɗan da bolar wani kango ne wanda ba a ƙarasa ginin shi ba, hakan yasa ta kwasa a guje ta hanye kan bolar tana huci ji take kamar numfashi zai daina aiki, bakinta a manne yake da gam haka ma hannunta a ɗaure yake, amma a haka take ƙoƙarin tsira da rayuwarta. Wani kalar wari da ke fitowa daga cikin bolar ne ya kawo wa hancinta ziyara, ta taka wata leda mai ɗauke da wani abu mai kama da ruwa ai kuwa ta yi baya luu ta faɗi a cikin bolar, Kafin ta yi wani yunƙuri sai ga su sun iso bakin bolar suna kallon ta, ita kuma ban da kakarin amai babu abin da take ta sallama cewa lalle fa ruwa ya ƙare wa ɗankada, tun da har suka cin mata duk gudun da ta yi ya tashi a banza sun kama ta."Kai Dagus maza ka saro min kanta yanzu, dan na lura yarinyar nan gudun bala'i ne da ita ta gajiyar da mu sosai. Dan haka yanzu mu sassare mata gaɓoɓin jiki." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana dafa na gefen shi.Ita kuwa ta kasa tashi ballantana ta taimaki kanta sakamakon wani ɗanko mai kama da ƙara ya manne mata kafarta a kan bolar, duk da kuma iskar shaƙa ta yi mata kaɗan hakan bai sa ta daina kiciniyar tashi daga kan balar ba. Duk numfashin da za ta ja sai ta ji kamar ana yankar zuciyarta ne gaf take da rasa ɗan sauran numfashin da take kai-kawo da shi.Wanda aka ce ya je ya saro kanta ne ya nufo kan bolar a fusace, cikin tashin hankali take kallon shi har ya ƙaraso ya zaro wata wuƙa mai baki biyu ya ɗaga cikin rashin imani zai sauke mata ita a ciki aka dakatar da shi. A fusace ya juyo ya dube su, wanda ya ba shi umarnin ya ɗaga masa hannu tare da nuna masa wannan kangon da ke gaba da su, hakan yasa ya gane mai yake nufi ya sunkuya ya ɗauke ta ya nufi cikin kangon. Ihu take kurmawa wanda da shi da babu duk ɗaya, saboda bakinta da yake a manne da gam tana ji tana gani suka shigar da ita kangon har cikin wani guri wanda alamu ya nuna ɗaki ne za ayi a wajan. Jefar da ita ya yi a wajan ta runtse idanu saboda wani kalar azababben zafi da ya ziyarci kunkurinta, Dagus y...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters29
premium24
06

9/10

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
07

11/12

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
08

13/14

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
09

15/16

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
10

17/18

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
11

19/20

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
12

21/22

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
13

23/24

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
14

25/26

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
15

27/28

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
16

29/30

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
17

31/32

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
18

33/34

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
19

35/36

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
20

37/38

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
21

39/40

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
22

41/42

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
23

43/44

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
24

45/46

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
25

47/48

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
26

49/50

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
27

51/52

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
28

53/54

Premium
Updated 2 years agoAvailable now
29

55/56

Premium
Updated 2 years agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play