Sawun Giwa

10&11

by @realeshaa

*SAWUN GIWA*

 _Ya take na Raƙumi_

        


         

_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_



*F-R-PG 10&11*

Da wani irin mamaki da al'ajabi Sir Abdallah ke kallonta idan har ba gezo idanunsa ke masa ba tabbas shi yaga ta nuna ahankali ya juya ya kalli bayansa ganin ko da wani abayansa ga mamakinsa shi kaɗai ɗin ne awajen hakan na nufin shi take nufi ba wani ba.


   Afusace Sir Auwal ya daka mata tsawa cikin fushi yace.

“Are You Mad Neenah kinsan me kike faɗa kuwa?,Kina cikin hayyacinki ko kuwa kin samu matsalar ƙwakwalwa ne?”.

Principal kuwa ido kawai ya zuba mata tare da tallafe kuncinsa yana kallonta ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗaure fuska kana yace.

“Keee Head girl!!!”.

Ahankali ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye da rauni ta kallesa muryanta na rawa tace.

“Na'am Sir”.

Cikin tsira mata ido yace.

“Ki kalle mu da kyau shin akwai tsaranki ko kuma abokin wasanki anan?”.

Batare data kallesa ba ta girgiza kai still hawaye na kwaranya daga idanunta.

Still babu walwala atare dashi yace.

“Ok menene ainihin abinda ya faru shin abinda kika faɗa farko ne gaskiya ko kuma wannan sabon da kika dawo dashi?”.

Kife kanta tayi akan cinyarta ta shiga rera kuka cike da rauni shin me zata ce.

Tsawa ya daka mata tare da cewa.

“Heyyy Am talking to you”.

Cikin shesh-sheƙan kuka tace.

“Nima ban sani ba”.

Sir Auwal da takaici ya gama cikasa ya watsa mata harara ahasale yace.

“Khadija shin akwai abokin wasan ki anan ne?badan darajar karatu ba shin kin isa ki haɗa hanya da A.A Zaman ne bare kuma har ace magana ya haɗa ku?!”.


   Cikin hargagi da borin kunya Malam Saidu ya miƙe idanunsa akan Principal yace.

“Sannu Malam Hassan agaskiya ka bani kunya da yake an taɓo ɗan masu jini awuya shine za'a tsaya ana ta jan magana amma ni lokacin data Min sharri ai babu wanda ya saurareni dan haka in dai adalci kake sonyi to kayi gaggawan daukar matakin daya dace akan ƙazafin da aka shirya min sannan aka nemi muzanta ni wasu daga sunga Allah ya basu dama sai su nemi wulaƙanta mutum”.


Cikin sauri Principal ya ɗaga masa hannu babu walwala atare dashi yace.

“Dakata!,Malam Saidu ya kamata kasan abinda zaka riƙa faɗa sannan kasan da wanda kake magana kada ka manta wanene Bundi acikin garin nan da kuma ƙasar baki ɗaya matsayin sa ya wuce ka tsaya ka ƙalubalencesa”.

Kallonsa ya mayar kan Neenah cikin tsira mata ido yace.

“Head girl Zan miki tambayar ƙarshe idan har baki bani amsar daya dace ba zan koreki daga makaranta na sannan in bawa kowacce Makaranta dake cikin garin nan Izinin ƙin ɗaukar ki idan har baki faɗa mana gaskiya ba!”.


Atsorace ta ɗago kanta still hannunta na damƙe da maranta kana idanunta na zubar da hawaye cikin rauni tace.

“A'a Dan Allah kada ka koreni ka tausaya min kaji ƙaina”.

Jinjina kai yayi kana yace.

“Ok idan ba kyaso In koreki ki faɗa mana gaskiya”.

Numfashi ta fesar tare da kallon Sir Abdallah daya tsirawa waje ɗaya ido yana girgiza ƙafarsa lumshe idanunta tayi cikin rawan murya da sarƙewan numfashi tace.

“Da...da..maaa..duk abinda yaaa faru shine ya sani ...”


Kukane yaci ƙarfin ta mai cike da kunya da karyewar zuciya sam bai cancanci haka daga gareta ba...

Ahankali Sir Abdallah ya ɗago idanunsa da suka sauya launi da tsananin ɓacin rai da zafin zuciya ya tsira mata idanunsa masu dafi da kaifi!.

Rintse Idanunta da suka sauya launi tayi tana jin wani irin zafi da tsanar kanta a ƙasan ranta.

Ajiyar zuciya Principal ya sauƙe kana yace.

“Toh amma meyesa tun farko baki faɗi haka ba hasalima sanda abin ya faru Bundi baya cikin makarantar ko dai wani ne ke ƙoƙarin tilasta miki?,”.

Saurin gyaɗa masa kai tayi hawaye na taruwa a idanunta tace.

“Eh wallahi da..ma,A'a dama-da-ma baa..bu wanda ya tilasta.min”.


Ajiyar zuciya Principal ya sauƙe cike da al'ajabi baki ɗaya ya fahimci babu gaskiya acikin maganarta cikin son tabbatar da abinda yake zargi yace.

“Kin tabbata abinda kika faɗa haka ne kada kijawa kanki matsala!?”.

Jikinta na rawa ta gyaɗa masa kai alamar hakane.

Ƙofa ya nuna mata ba musu ta miƙe da sauri har tana haɗa hanya kai tsaye ajinsu ta shiga kallon bencin su tayi taga babu kowo alamar Indu da Abeedah Sa'eed basu zoba kanta aƙasa ta nufi baya last bench ta zauna da kallo sauran ɗaliban suka bita amma babu wanda yace da ita komai kasancewar akwai Malami acikin...


Bayan fitarta Principal ya sauƙe ajiyar zuciya baki ɗaya kansa ya kulle da al'amarin yafi kowa sanin wanene Sir Abdallah da kuma abinda zai iya aikatawa ya tabbata idan har ya rantse to ba zaiyi kaffara ba akan bashi da masaniya sai dai kuma abinda ya sake sanya shi aduhu yanda yaƙi cewa komai kai ya girgiza cikin rashin sanin madafa kana cike da girmamawa yace.

“Bundi”.

Anutse Sir Abdallah ya ɗago kansa da idanunsa da suka sauya launi sai dai duk bin diddi ginka da ƙwalafaci baza ka fahimci yanayin daya ke ciki ba kallon Principal yayi batare da yace Uffan ba.

Gyara zama Principal yayi cike da dattako yace.

“Baki ɗaya kaina ya kulle da kalaman yarinyar nan sai dai zuciya ta ta kasa gaskata abinda ta faɗa duba da yanda lamarin ya faru sannan akwai rashin gaskiya atare da ita hasalima baka san komai akan abinda ya faru ba”.

Miƙewa Malam Saidu yayi cikin kumfar baki ya dafe tumbinsa tare da cewa.

“Yo ai dole zuciyarka ta kasa amincewa da abinda ta faɗa tunda kana neman gindin zama amma ni lokacin da tayi min ƙazafi ai batare da bin cike ba kuka hayayyaƙo min sai yanzu da gaskiya ya bayyana shine za'a tsaya ƙumbiya ƙumbiya”.

Cike da Izzah da ƙasaita Sir Abdallah ya miƙe tare da sanya hannunsa na dama acikin aljihu kai tsaye gaban Malam Saidu ya nufa ya tsaya wani mugun yawu Malam Saidu ya haɗiye domin ƙarfin hali kawai yake.


Kallon second Biyar zuwa bakwai Sir Abdallah ya masa tare da ya mutse fuska kana cike da tsantsar izzah da ƙasaita dake ratsa sassan jikinsa yace.

“Kana da mataki ko hukunci da zaka iya ɗauka akai na?”.

Haibarsa da ƙwarjinin sa yasa Malam Saidu kasa furta komai sai zazzare ido yake.


 Murmushin gefen baki Sir Abdallah ya saki sai kuma ya haɗe girar sama da ta ƙasa kana Ahankali ya juya ya kalli Principal tare da cewa.

“Yallaɓai duk hukuncin da kake ganin ya dace ka ɗauka akaina ka ɗauka akan abinda yarinyar ta faɗa, Amatsayin ka na shuga ba ka ɗauki matakin daya dace kada kayi la'akari da matsayi ko kimata kaƙi ɗaukar matakin daya dace ashirye nake da amsar hukunci dai-dai da laifina.

Ya ida maganar tare da ficewa daga Office ɗin kai tsaye Office dake mallakinsa ya nufa ahankali ya zauna akan kujera tare da jingina bayansa da jikin kujerar wayoyinsa dake aljihu ya cire ya ajiye agabansa kana ya lumshe idanunsa kalaman yarinyar nayi masa suwwa adodon kunnensa sam bai taɓa zaton haka daga gare ta ba shin meyesa ta canza ra'ayinta meyesa tayi ƙarya akan abinda bashi bane ko dai biyanta yayi wata zuciyar ta tambayesa.


Ahankali aka turo ƙofar aka shigo yana ji amma bai buɗe Idanunsa ba ƙara sawa kusa dashi Sir Auwal yayi tare da jan kujera ya zauna cike da takaici yace.

“A.A Zaman meke shirin faruwa ne!?,Me wannan yarinyar take nufi da kai?”.

Shiru Sir Abdallah yayi bai buɗe Idanunsa ba haka zalika baice Uffan.


Sir Auwal kuwa cike da takaici ya cigaba da cewa.

“Tabbas duk abinda ya faru da saka hannun wannan tundurƙin mutumin domin ban yarda da fitan da yayi ya kira waya ba dole akwai abinda ya ƙulla a wannan kiran da yayi shiyasa naso yayi wayar agabanmu.


Numfashi Sir Abdallah yafesar tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana ya buɗe Idanunsa dake lumshe wanda lokaci ɗaya ya sauya launi tamkar na Fusatacciyar kyanwa yace.

“Please Auwal Leave me alone bana son hayaniya”.

Sanin halinsa yasa Sir Auwal juyawa ya fita.

Sir Abdallah kuwa lumshe Idanunsa yayi sai misalin sha biyu da kwata ya miƙe kai tsaye ya nufi inda yayi parking motarsa ya shiga direct Masallacin dake cikin bariki(Barrack) ya nufa baya tunanin zai iya komawa gida yayi Sallah masallacinsu.


Yana isa bakin gate ya danna hong cikin sauri sojojin dake gate din farko suka buɗe masa bayan sun gaisa ya wuce.

Gate na biyu ya nufa suna ganinsa suka shiga,ɗaga masa hannu suna kwasar gaisuwa hannu kawai yake iya ɗaga musu shi kaɗai yasan me yake ji.


Ɗaya daga cikin sojojin dake bakin gate na biyun ne ya kalli na gefensa kana yace.

“Ikon Allah kaga irin amsawar da A.A Zaman ya mana kuwa?”.

Jinjina kai ɗayan yayi kana yace.

“Aikam na lura kamar da akwai wani abu dake damunsa dan ba haka ya saba amsa mana”.

Wanda ya fara maganar ne yace.

“Haka ne kam yau da gobe sai Allah”.

Da ganan suka rufe zancen ta hanyar ɗaukar wata hiran.

Anutse ya shiga cikin barikin dake tsare da wasu irin kayan yaƙi da gini na zamani kana ga wasu Bishiyoyi da flowes da suka ƙawata cikin kai tsaye inda babban masallacin su yake ya nufa yayi parking yashiga masallacin tare da ɗaukar Alkur'ani mai girma ya shiga karatu cikin suratul Yusuf sai da aka kira Azahar kafin ya tsagaita yayi Sallah yana zaune a masallacin har aka kira La'asar ya idar...


**

Cikin rauni Indu ta kife kanta akan damtsen hannun dattijuwar matar dake Kama da ita tamkar an tsaga ƙara wacce hannunta ke ɗauke da ƙarin ruwa fuskarta yayi fayau kana idanunta alumshe alamar bacci take.

Cikin shesh-sheƙan kuka ta ɗago kanta kana tace.

“Aunty Munah tun yaushe ciwon nata ya tashi baku faɗa mana ba dubi fa yanda ta rame ji yanda numfashinta ke fusga!,Ummu!,Ummu!!dan Allah ki tashi”.

Ta ida maganar tana jijjiga hannun Ummu.

Cikin rauni Aunty Munah ta share hawayen daya zubo mata kana tace.

“Ni kaina nayi mamakin ramarta lokaci ɗaya Autah tunda nazo na lura da akwai abinda ke damunta amma da zaran na tambayeta zata cemin bakomai yau kuma kawai gani nayi ta yanke jiki ta faɗi”.

Kai Indu ta girgiza idanunta akan Ummu tace.

“Innalillahi wa'inna ilahai rajiun me Dr yace yana damunta ko dai Deyphitis ɗin ta ne ya tashi?”.

Kai Aunty Munah ta girgiza cikin sanyi murya tace.

“Tukunna dai Dr Khameelu muke jira muji sakamako dan fitar shi babu daɗewa kuka shigo”.

Araunane Indu ta sake kallon fuskar mahaifiyarta dake sauƙe numfashi akai-akai cikin sauri ta sanya hannunta ta toshe bakinta jin kuka na neman kufce mata amma duk da haka sai da sautin ya fito.


Ahankali Imraan dake jingine da bango idanunsa akan Ummu da Indu ya fesar da numfashi mai ɗumi kana ya durkusa ya ɗago kafadarta cikin rarrashi yace.

“Is ok Indu addu'a ya kamata kiyi mata ba kuka ba In sha Allah za taji sauƙi”.

Kai ta gyaɗa tare da faɗawa jikinsa ta saki marayan kuka muryanta na fusga tace.

“Yah Imraan ina tsoron maraici biyu ina tsoron rasa Ummuh kamar yanda na rasa Abba tun ina ƙarama bazan iya juran rashin ta ba bazan iya ba”.


  Cike da rarrashi da kuma rauni ya shiga bubbuga bayanta yana jin yanda idanunsa ke tats-tsafo da ruwan hawaye...


   Aunty Munah na shirin magana Dr yashigo hannunsa riƙe da files kai tsaye jikin gadon ya nufa ya kara ƙarfin ruwan dake hannunta ahankali Imraan ya janye Indu daga jikinsa ya ƙarasa kusa da Dr ya miƙa masa hannu.

Cikin shesh-sheƙan kuka Indu tace.

“Yah Khameel ya jikin Ummu?Meke damunta meyesa meta meyesa bata farka ba har yanzu?”.

Duk alokaci ɗaya tajero masa tambayoyin.

Numfashi ya fesar tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa yace.

“Calm down Autah In sha Allah Ummuh zata farka lafiya ok”.

Anutse Imraan yayi gyaran murya yace.

“Dr. ya jikin nata Meke damunta?”.

Juyawa Dr Khameel yayi ya nufi ƙofa kana yace.

“Ka sameni a Office”.

Kai Imraan ya gyaɗa tare da bin bayansa.


Bayan Dr Khameel ya shiga Office yaja kujera ya zauna kana ya gyara zaman farin Eyeglass dake idanunsa ahankali Imraan ya zauna akujeran dake gaban deks table ɗin.

Ajiyar zuciya Dr Khameel ya sauƙe kana ya ɗauki wasu files yayi rubuce-rubuce kallon Imraan dake cikin damuwa yayi kana yace.

“Captain ya akayi ka bari jinin Ummuh ya hau sosai irin haka bayan kasan halin da take ciki tana buƙatar hutu tare da kiyaye duk wani abu da aka san bata so?”.

Cike da damuwa yace.

“Wallahi ban sani ba ko yaushe idan muka yi waya da ita lafiya lau nake jinta bansan ya akayi haka ya faru ba amma Meke damunta?”.

Kai Dr Khameel ya girgiza cikin sauƙe numfashi yace.

“Agaskiya yanzu bazan iya cewa komai ba domin komai kan iya faruwa jininta ya hau sosai wataƙil idan ta tashi zata iya Paralise ma'ana gefenta ɗaya ya zai shanye duk da ba'a fatan haka”.

Aruɗe Imraan ya rintse Idanunsa yayin da zufa yashiga wanke masa gaba ɗaya Ilahirin jikinsa cikin tsananin tashin hankali yace.

“Innalillahi wa'inna ilahai rajiun Khameel yanzu babu wani abu da zaka iyayi dan Allah katemaka min kada wani abu ya sameta”.

Numfashi Dr Khameel ya sauƙe kana yace.

“In sha Allah zamuyi iya bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto lafiyar ta da izinin Ubangiji”.

Cikin yanayin tashin hankali ya jingina bayansa da jikin kujeran idanunsa na tara ƙwalla.

Dafa kafaɗarsa Dr Khameel yayi cikin rarrashi yace.

“Be a Man Captain In sha Allah babu abinda zai sameta addu'ar mu take buƙata”.

Kai ya gyaɗa tare da fesar da numfashi kana yace.

“To amma duk me ya jefata cikin wannan hali Dr?”.

Kai tsaye Dr Khameel yace.

“Damuwa ya mata yawa arai akwai wani abu data keso ko kuma take ƙi wanda hakan ya kasa samuwa har yayi nasaran jefata acikin halin da take”.

Kai Imraan yinjina tare da lumshe idanunsa kana yashiga tunanin wani irin abu Ummu ke muradin kasancewar sa ko kin kasancewar sa har ya jefata cikin mawuyacin hali duk iya tunaninsa ya kasa hango abin...


Ummu ta kasance mace mai tsanananin haƙuri da kawaici tun Imraan na Ss2 Allah yayi wa mahaifinsu rasuwa ƴaƴa Uku Allah ya azurtasu dasu Maimunatu wacce suke kira da Aunty Munah sai Imraan da kuma Hindatu sun taso cikin ƙaunar junansu Aunty Munah tayi Aure a garin Bauchi yayin da Imraan ya kammala karatunsa yasamu damar tafiya makarantar sojoji inda ya fito amatsayin Captain alokacin da yaje wani cause a Maiduguri ne ya haɗu da Lateefa cikin ikon Allah sukayi Aure tun bayan aurensu ya ɗauki Indu ta koma gabansa wacce alokacin batafi shekara bakwai ba domin sosai yake ƙaunarta Arayuwar Lateefa babu wanda ta tsana sama da Mahaifiyar Imraan da kuma ƴan Uwansa saboda yanda yake kyautata musu musamman Indu yanaji da ita fiye da kowa arayuwarsa koda abu zaiyi wa Lateefa tare yake haɗasu wannan dalili yasa ta tsaneta fiye da kowa arayuwarta sai dai takan ɓoyewa Imraan sannan duk wajen boka da malamai babu inda bata sani ba adomin taga ta raba tsakanin su...


***

Acan makaranta kuwa tun da Neenah ta kife kanta akan deks wani wahalallen bacci ya ɗauketa ɗaya da arba'in da biyar dai-dai aka tashi ahankali ɗaliba ke tururuwan fita sannu ahankali ɗalibai suka riƙa fita daga cikin harabar makarantar kowa na tafiya har aka watse.

Bayan an gama watsewa mai gadi yazo hannunsa riƙe da kwaɗo da kuma Mukullai yana bin ko wani aji yana rufewa sannu ahankali Neenah dake bacci tafara buɗe idanunta da suka kumbura kana suka sauya launi zuwa ja tun tana ganin dishi-dishi har tafara ganin komai dai-dai atsorace tabi cikin class ɗin da kallo ganin babu kowa aciki haka zalika babu motsin kowa acikin makarantar sai ƙaran ƙofa da Window da take ji yayin da sanyayyar Iskar damina ke kada window kana yana zubo da ganyen bishiyoyin dake kaɗawa wani irin masifeffen tsoro da tashin hankali ne ya lulluɓe ta yayin da gaba ɗaya Ilahirin jikinta ya shiga rawa kana cikinta na cigaba da murɗawa da azabebben karfi yunƙura tayi da niyyar miƙewa ta yanke jiki ta faɗi kanta ya bugu da jikin bencin.

Cikin rauni ta saki wahalallen kuka Mai gadi dake ƙoƙarin rufe kofar yaji kamar sautin muryan mutum cikin sauri ya leƙa cikin ajin kasancewar ya kulle window yasa ajin yayi duhu hakan yasa bai ga kowa ba cikin sauri yaja baya yasa kwaɗo a kofar ya rufe da tunanin ko dai kukan ƴaƴan aljanu yaji.


  Cikin tsananin azaba ta dafe ƙasan maranta dake wani irin murɗawa da masifeffen karfi tana jin yanda jinin ke roshing yana zuba hannun hagu ta sanya ta dafe goshinta dake zugi kana da ƙyar ta sauƙa akan bencin ta durƙusa akan gwiwoyinta hawaye masu zafi da raɗaɗi na bin kuncinta juyi ta riƙa yi tana murƙususu duk yanda taso miƙewa ta isa ƙofan kasawa tayi.


Haka mai gadin ya riƙa bin ƙofofi da windows din cikin makarantar yana rufewa bayan ya gama rufe ko ina ya koma ɗakinsa dake bakin gate ya buɗe wani drawer ya saka mukullin kana ya rufe ya fita kasancewar yana da uzuri yasa ya nufi inda zashi.


  Acan gefen gidansu Neenah kuwa kallon agogon wayar Mamawo Maryam dake zaune tana gyara Kifi Baaka

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da juyawa ta kalli Mamawo dake tsinka musu tuwa afaranti cike da kulawa tace.

“Mamawo har yanzu fa Sister Neenah bata dawo ba gashi har ƙarfe huɗu da rabi bayan kuma tana rigani dawowa gaskiya hankali na ya fara tashi”.

Mamawo kuwa jin abinda tace yasa ta taɓe baki cikin ko in kula tace.

“Ohon mata tunda dai gaulanci da rashin hankali tasa gaba,Watanin ta rinƙa ganin ba dai-dai ba ina lura da ita kwanakin nan yawo tasa agaba idan ta fita tun safe bazata dawo ba sai ta gama gafalewa awaje”.

Cikin sauri Maryam ta katseta da cewa.

“Haba Mamawo irin wannan maganar fa bai kamata ya riƙa fitowa a baki ki kamata yayi duk wani abu da zai fito abakinki ya zama alkhairi domin uwa kike agareta”.

Afusace ta daga mata hannu tace.

“Kull Allah suƙuru bukuiy inji kishiyar mai ƙusunbi ina ni ina haihuwar Bagashariya gaula irin wannan?,Watanin Kada ki sake Kuskuren alaƙantani da wannan Kangararriyar yarinyar domin Ni dai ban haifi Kangararriya ba Ina ai *Sawun Giwa ya take na raƙumi*”.


Kallonta kawai Maryam keyi bako kyaftawa cike da takaici tace.

“Kada kice ina mayar miki da magana ko kuma na miki rashin ɗa'a amma kema ba wayonki ko kuma dabararki bace yasa Allah ya shirya miki ƴaƴa ganin damarsa ne sannan kinsan cewa duk ƙin Allah mutum bai isa ya kushe tarbiyyanta ba”.

  Ta fesar da numfashi kana ta cigaba da faɗin.

“Bayan haka kuma ahalin da Sister Neenah ke ciki bai kamata ace kin tura ta makaranta domin jinya ta kori komai hasalima sai da na faɗa mik”.

Da sauri ta ɗaga mata hannu cikin kumfar baki tace.

“Ahirrr ɗinki Maryama kada kisa ni abakin duniya ubanwa yace miki ni na tura makarantar?,Watanin kema kinsan halinta da tsinannan son makaranta kamar jikar Mango pack amma zaki goga min kashin kaza”.

Cikin taɓe baki Maryam ta furta.

“Hmmm Mamawo kenan ai koda Sister Neenah ce ta dage zataje makaranta za kiyi yunƙurin hanata saboda condition ɗin da take ciki amma sam bakiyi yunƙurin hakan ba kika barta ta tafi”.

 

Da sauri Mamawo ta miƙe da kwanon tuwon ahannunta tace.

“Khalas Asheikiya Maryama dan Allah kada kisani abakin duniya ita ɗin yarinya ce da zaki tisani gaba da ƙananun magana ko kuma dole kike so inyi mata, Watanin da zaran an fara magana zaki nunuwa mutum kinfisa sanin Allah?”.

Ta ida maganar tare da shigewa kitchen.

Cike da damuwa Maryam ta tallafe kuncinta da hannu bibbiyu to ina Neenah taje numfashi ta fesar tare da miƙewa ta shiga ɗaki ta ɗauko gyalenta ta fita kai tsaye gidansu Indu taje.


  Tsayawa tayi daga waje kana ta buga Gate leƙawa Mai gadin yayi ganinta yasa ya riƙe baki tare da cewa.

“Kiyi haƙuri wallahi saida na ganki kafin na tuna ɗazu na manta ban faɗawa Hajiya ƙarama saƙonki ba”.

Kai ta girgiza tare da faɗin.

“Bakomai amma Indu na nan?”.

“A'a itama bata dawo ba tunda ta tafi”.

Kai kawai ta gyaɗa tare da tunanin ko wani abin suke makaranta ta koma gida...


**

Anutse Ammie dake zaune cikin wani ƙayataccen falon dake ɗauke da kayan alatu na more rayuwa iri daban daban ta sauƙe numfashi tare da Kallon Sarki Aliyu Ahmad Zaman dake zaune ƙasan lallausan Carpet gabansa ɗauke da kayan marmari iri daban daban kama daga Inabi,Tuffa,Abarba,Gwanda,Forein Pia,chop-chop Ajiyar zuciya ta sauƙe ganin yanda ya ƙurawa TV ido cikin sanyin murya da nutsuwa tace.

“Abiey Abdallah Lafiya ka tsirawa TV ido batare da kasa komai acikin ka ba?”.


Numfashi ya fesar tare da kallon kayan marmarin dake gabansa lumshe idanunsa yayi kana cikin raunin murya yace.

“Hafsat kallon wannan New's ɗin ya sake kashe min jiki tare da jin tsoron Ubangiji ina tunanin halin da talakawan ƙasata ke ciki ina matukar tausaya musu abubuwa sai sake tabarɓarewa yake kayan masarufi na sake hauhawa mudun masara,Ya haura sama da dubu, Taliya guda ɗaya yakai ɗari huɗu,Mudun shin kafa ya haura dubu biyu,Shin ina talaka zai sa kansa yaji sanyi acikin wannan yanayi da ake ciki?”.


Ya sun kuyar da kansa ƙasa idanunsa cike da ruwan hawaye yace.

“Acikin wannan Ƙasa acikin wannan jaha acikin wannan garin da kewayenta akwai talakawa bila adadin dake kwana da yunwa batare da sun sanya koda ƙwayar gero a cikinsu ba suna rayuwa da iyalensu cikin ƙunci da talauci yara na kukan yunwa iyayensu na shiga cikin ƙunci”.

Ya gyara zamansa kana ya cigaba da cewa.

“Amma mu gamunan cikin Rahma da jin ƙan Ubangiji muna cin abinci kala-kala iri daban-daban har mu rage wani ma azubar Hafsat Ina tsoron ranan da Ubangiji zai tsayar dani agabansa ya tambaye Ni hakkin talakawan daya bani domin ina tsoron wannan shugabanci,Nayi magana da wasu daga cikin manyan ƙasan nan masu mulki domin aduba halin da talakawa ke ciki amma sunyi burus da maganata”.


Kai Ammie ta jinjina cikin sauƙe numfashi tace.

“Tabbas haka ne domin duk wanda aka bashi mulki ko jagoranci yana tare da babban ƙalubale agabansa kamata yayi duk wanda akace an bashi mulki ko sarauta ko kuma wani muƙami to yayi kuka domin an haɗa sa da wani irin nauyi ne da zai iya kaisa ga halaka ko kuma Ribantuwa domin mulki ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa wasu daga cikin shuwagabanni babu tausayi ko jin ƙan talakawa atare dasu amma a irin wannan yanayin da ake cikine Talaka ke tsananin buƙatar temako”.

Ta gyara zamanta kana ta cigaba da cewa.

“Sai dai wannan tsadan rayuwa da kayan Masarufi ina ganin yana da alaƙa da manyan ƙasanmu Musamman shugaban ƙasa da wasu ƙusoshi agwamnati domin aganina da ace zasu tsaya tsayin daka akan al'amuran ƙasa to tabbas da komai zai dai-dai-ta amma ka duba ka gani komai na rayuwa sake taɓarɓarewa yake duk abinda kasani ashekaru huɗu baya yanzu sun nin ka kuɗin su shin ya talaka zai yi da rayuwar sa acikin irin wannan yanayi!?”.

Cikin rauni da zubda hawaye ta ƙarasa maganar.


Nan nauyan Ajiyar zuciya Sarki Aliyu Ahmad Zaman ya sauƙe kana ya girgiza kansa tare da tsirawa rufin P.O.P idanu tare da cewa.

“Hafsat kenan bake kaɗai ba mutane da yawa koma ince Majoraty acikin mutanen wannan ƙasar suna ganin tsadar rayuwar da ake aciki laifin gwamnatin ƙasa ne da kuma sakacinsa yasa duk wasu abubuwa ke faruwa to tabbas keda masu wannan tunanin kunyi Babban kuskure”.

Ahankali Ammie ta gyara zama tana sauraron sa sai dai har yanzu bata gamsu da cewa Gwamnati bata da laifi acikin halin da talakawa ke ciki ba”.


Kallonta yayi ganin yanda ta zurfafa acikin tunani yasa yayi murmushi tare da cewa.

“Na lura kamar har yanzu baki gamsu ga magana ta ba kada kiyi tunanin dan ina mulkine nake son kare masu mulki na tabbata kinfi kowa sanin halayyata ki tuna da Aya ta (25)acikin suratul Anfal ayar da Allah yake cewa.

_“Wattaƙu Fitnatalla tusibannallazina Zhalamu minkum Khassa,Wa'alamuu Annallaha shadidul Iƙaab”_.


Jinjina kai Ammie tayi tare da faɗin.

“Tabbas na tuna ayar da Allah (S.W.A)yake cewa _Kuji tsoron wata fitina wanda idan ta taso bazata shafi waɗanda sukayi zalunci acikin ku su kaɗai ba,Lalle kusani Allah mai tsananin uƙuba ne”._

Ta gyara zamanta cikin rauni tace.

“Tabbas wannan ayar tana tsoratar wane akan irin mutanen dake kallo ana aikata ɓarna da saɓawa Ubangji sannan suce baza suyi magana ba ai be shafe suba ”.


  Numfashi mai ɗumi Sarki Aliyu Ahmad Zaman ya fesar kana yace.

“Shin awannan zamanin namu wani irin laifi da manyan kaba'ira ne ba'a aikatawa?,Zinace,Zinace sun yawaita tsakanin al'umma musamman mazan Aure da matan Aure Luwaɗi ya yawaita atsakanin al'ummar wannan zamani kada ki manta mutanen Annabi Luɗ Allah ya halaka sune akan luwaɗi wanda awannan zamanin ya zama ado acikin wannan al'ummar tamu haka zalika mata sun maida maɗigo abin ado har wasu su fito social media suna faɗin cewa su ƴan Less ne batare da kunya ko tsoron Ubangiji ba ƴan mata da Samarin su sun maida Tik-tok wajen yaɗa baɗala suna bayyanar da tsaraici da kalaman ash-sha”.

Kai Ammie ta jingina tare da jingina bayanta da jikin kushin tana sauraron sa.


Cikin rauni ya cigaba da cewa.

“Tauye mudu ya zama ado acikin al'ummar wannan ƙarni wanda akan tauye mudu Allah ya halakar da Mutanen Annabi Shu'aib,ta ko wanni fanni ana tauye mudu kama daga masu sana'ar gwari sukan sanya masu kyau asama kana su saka bage(Riɓaɓɓu)aƙasa domin me siya yayi zaton masu kyau ne masu gwada litar mai suma ba abarsu Abaya ba masu awun shinkafa masara fulawa duk tauye mudu suke alhali su idan zasu auna ba haka suke ba.


Ya lumshe idanunsa tare da gyara zamansa cikin rauni da sarƙewar murya yace.

“Zagin fiyayen halitta ya zama abin wasa acikin mutanen wannan zamanin namu dubi yanda Allah ya fifita fiyayen halitta Annabi Muhammad (S.A.W) amma wasu daga cikin kafirai sun mai da hakan abin wasa sannan wasu daga cikin musulman mu basu da kishi addini sukanyi ɓatanci ga Manzon tsira fiteyyen halitta!,Ana zubar da jinin salihan baya wanda basu jiba basu gani ana wulaƙanta marayu tare da cinye musu hakki tayaya kike tunanin Ubangiji ba zai jarabce mu ba


Numfashi Ammie ta fesar tare da jingina bayanta da jikin kushin kana tace.

“Tabbas hakane kafin naji wani bayanin naka na ɗaura laifin ne baki ɗaya akan shuwagabannin amma yanzu na fahimta sai dai fa duk da haka da akwai laifin Manyanmu na Arewa akan matsalar rashin tsaro dubi halin da akeci ga wata sabuwar fitina da take shirin Kunno kai tsakanin ƙasashen mu biyu”.


Numfashi ya fesar tare da cewa.

“Bazance babu amma muma kanmu kuna da laifi da ace zamu gyara tsakanin mu da ubangiji tabbas komai zai zo da sauƙi domin babu wanda ya isa yayi mana maganin wannan matsalar face Ubangji”.


Kai ta gyaɗa dai-dai lokacin Gimbiya Fa'izah ta shigo falon cikin shiga ta alfarma jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshi kai tsaye ta nufi kan 3sitter ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya cike da Izzah tana danna waya.

Kallonta Sarki Aliyu Ahmad Zaman yayi jin batayi sallama ba batare daya tanka taba ya cigaba da cewa.

“A irin wannan yanayi a irin wannan zamani da zalunci cin amana,cin dukiyar marayu haddasa zamba cikin aminci suka yawaita taya Ubangiji bazai jarabce mu ba!?”.


Jinjina kai Ammie tayi cikin sanyi murya tace.

“Tabbas duk abinda ka faɗa haka ne shiyasa Ubangiji ya barmu da halinmu kana ya haɗamu da wasu azzalumai daga cikin shuwagabannin domin ya hukunta mu wannan duniyar ba abakin komai take ba”.

Baki Gimbiya Fa'izah ta taɓe kana ta miƙe still idanunta nakan wayarta tace.

“Am Habibi dake naga yau kana da time yasa na shigo muyi magana but naga ba kai kaɗai ba zuwa anjima zan dawo”.

Cike da nutsuwa da Kamala Sarki Aliyu Ahmad Zaman ya kalleta kana yace.

“Zaki iya yin maganar ki ina sauraro ki domin anjima ina da baƙi daga Maiduguri da Gombe kinga bani da lokaci”.

Ya mutse fuska tayi kana tace.

“Badamuwa Aduk sanda ka samu lokaci sai muyi magana saboda tsaro bai kamata ace mutum ya saki baki ko ina yana magana ba domin baka san masu ɗiban sirrinka su yayata ba”.

Cikin sauri ya daga mata hannu kana yace.

“Ok zaki iya tafiya bana buƙatar dogon magana”.

Kai ta gyaɗa tare da juyawa ta fita cike da Izzah da ƙasaita”.


Kai Ammie ta girgiza halayyar Gimbiya Fa'izah sai ita tare tazo ta sameta da mijinta amma bata da burin daya wuce taga ta maida ita bora awajen mijinta kullum cikin abubuwa na rashin ɗa'a take mata wannan dalili yasa sam basa shiri da Sir Abdallah domin shi mutum ne mai tsananin kammamewa baya ɗaukar raini komai ƙanƙantarsa...


Cikin sanyi ya kalli Ammie kana yace.

“Hafsat kiyi haƙuri da halayyar Fa'izah Insha Allah wataran sai labari”.

Murmushi tayi tare da faɗin.

“Kada ka damu ban taɓa riƙe Fa'izah araina ba hasalima kallon ƴa nake mata domin bata wuce sa'ar Aysha ba dan haka ba zan taɓa daukar ta matsayin kishiya ba kaima ka cigaba da haƙuri da ita wataran sai labari”.

Murmushi yayi cikin jin daɗi yace.

“Nagode Hafsat daraja da kimar Yayan Fa'izah da kuma yanda kike bani ƙwarin gwiwa yasa nake zaune da ita”.

Murmushi kawai Ammie tayi aranta tace Namiji kenan sai kuma tace.

“Baƙin naka hala akan matsalar ƙasa ne”.

Kai ya gyaɗa tare da cewa.

“Eh zamu haɗa contribution ne wanda zamu tallafawa latakawa jahohin Borno,Adamawa,Gombe,Yola, Bauchi da sauran garuruwan da suke buƙatar temako ”.

Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cewa.

“Masha Allah Ubangiji Allah ya ƙara ɗaukaka Allah yasa a mizani”.

Ameen ya hayyu ya ƙayyum ya amsa gyara zama tayi ta cigaba da cewa. “Abdallah ya faɗa min cewa ya fitar da Shin kafa Traller talatin,Masara Traller talatin,taliya Traller ashirin,Macoroni Traller goma,suga da Maggi Traller goma sai kuma kuɗi miliyan Hamsin da za'a rabawa talakawa”.

Wani amintaccen murmushi Sarki Aliyu Ahmad Zaman yayi kana yace.

“Alhamdulillah tabbas nasan ko bayan raina Abdallah zai kula da talakawan ƙasar nan”.

Murmushi tayi kana suka cigaba da tattaunawa akan halin da ƙasar ke ciki...


**

Duk inda Maryam tasan zata je ta duba Neenah saida taje amma bata sameta cike da gajiya da tarin damuwa ta dawo gida akan kujera ƴar tsugunno ta zauna tana maida numfashi kallon ta Mamawo tayi cikin taɓe baki tace.

“Awahalatu ƴar kinibi-batu jikar agalima Watanin kin gaji da galantoyin kin dawo?”.

Fuska Maryam ta ɓata babu walwala atare da ita tace.

“Wallahi duk abinda ya samu Sister Neenah kece sanadi Baiwar Allah nan bata da lafiya amma saida kika turarsasa mata zuwa makaranta Fisabillah abinda kika aikata yayi dai-dai kenan?”.

Da sauri Mamawo ta dafe ƙirjinta tare da zare ido tace.

“Ahirr ɗin ki Maryama agidan ubanwa na tura ta makaranta?,Ita dai ta tafi yawon Dandinta da kuma bin maza data saba ”.

Cikin yanayin ɓacin rai Maryam ta miƙe tare da cewa.

“Wallahi Baba yana dawowa gidan nan zan sanar masa duk wani abu da kike wa Sister Neenah agidan nan”.


  Saurin kallonta Mamawo tayi kana tace.

“Anya kuwa Maryam anya?,Wallahi badan agida na haifekiba sai ince canza min ke akayi,Watanin ban taɓa ganin yarinyar dake ƙin mahaifiyarta akan wata Gafalalliya irin kiba”.

Banza Maryam tayi mata cike da takaici kamar wacce aka tsikara tayi saurin miƙewa ta shiga ɗaki kan Kabot ta duba nan taga wayar Mamawo cikin sauri ta ɗauka tashiga contact ganin sunan Yah Saidu na yawo a screen ɗin yasa tayi saurin dearling ringing ɗaya taji anyi picking.


Cikin sauri tayi sallama tare da cewa.

“Ina wuni Kawu Saidu”.

Daga ɗaya ɓangaren Malam Saidu dake ƙoƙarin tarar Napep ya tsaya yace.

“Lafiya Maryama ya karatu yasu Saude”.

Aƙage tace.

“Duk muna lafiya Kawu dama cewa nayi bari in tambayeka ko an tsare su Sister Neenah amakaranta ne Dan har yanzu bata dawo ba”.

Da mamaki ya gyara tsayuwar sa kana yace.

“Ikon Allah aikuwa tun ɗaya da arba'in da biyar aka tashesu ƙila tabi wani wajen ne ki tambayi gidan ƙawayenta”.

Cikin sauri Maryam ta girgiza masa kai tace.

“A'a wallahi Kawu babu inda taje duk da ma idan akwai inda zataje bai wuce gidan su Hindatu ba to can ɗin ma naje bata nan sannan har bakin makarantar su naje amma arufe shiyasa nace bari in kira ko Allah yasa kasan inda take”.


Shiru yayi na wasu mintuna kana ya saki wani murmushi yace.

“Kin dai tabbata duk inda take kinje bata nan ko?”.

Araunane ta gyaɗa masa kai kamar yana gabanta tace.

“Wallahi duk naje Kawu ni babu abinda yafi ɗaga min hankali kamar cewa bata da lafiya Ni tunanina ma kada arufe ta amakarantar ba asan tana ciki ba gashi ba wadatacciyar lafiya bane da ita”.


Murmushi yayi kana yace.

“Kada ki damu bari inje in duba makarantar da haraban wajen amma da wuya ace tana cikin makarantar an rufe domin sai an duba ko wani aji kafin arufe amma dai bari naje na duba”.

Ya ida maganar tare da katse kiran.

Araunane Maryam ta fita daga ɗakin ko kallon Mamawo dake aikin jiƙa gero bata yiba ta nufi bakin rijiya dai-dai lokacin aka fara kiraye kirayen Sallar Maghriba buta ta ɗauka taja ruwa kana tashiga ban ɗaki.


Cike da farin ciki Malam Saidu ya tari adaidaita ya hau wani irin tsuma jikinsa keyi tafiyar minti goma ya kaisa bakin makarantar zuwa lokacin duk anshiga Sallah yana isa bakin gate din yasa hannu acikin aljihunsa ya ciro key gate ɗin kasancewar shida mai gadine mukullin ahannunsu yana buɗewa yashiga kana ya maida gate din ya rufe.

Kallon yabi haraban makarantar dashi wanda hasken sola da glove ya haske cikin kamar rana.

Ahankali ya tsaya tare da harɗe hannunsa aƙirji yana bin ajujuwan da kallo ko wanne aji arufe da kwaɗo zuciyarsa ce ta raya masa anya kuwa tana nan domin da tana nan mai gadi ba zai rufe da ita ba.


Siririn tsaki yaja kana ya juya sai kuma yayi saurin tsayawa atake wata zuciyar tace kasani ko lokacin daya rufe tana bacci ka gwada bugawa kaji atake yabi shawaran zuciyarsa cikin sauri ya nufi Ss 3A yana zuwa jikin ajin ya manna kunnensa ajikin Ƙofar ahankali yake jin kamar sauƙan numfashi da nishi.

Bubbuga ƙofar yayi yace.

“Neenah!”.

Aruɗe Neenah ta ɗago kanta da yayi mata mugun nauyi ta kalli ƙofar jin sautin muryan da ba tayi tsammani ba yasa cikinta sake murɗawa da azabebben ciwo hannunta na hagu ta ɗauka ta toshe bakinta .

Cikin kwantar da murya yace.

“Neenah kina jina idan har kina ciki kiyi min magana nida Maryama ne gata nan atsaye”.

Still shiru tayi zuciyarta na cigaba da tsinkewa da wani irin ƙarfi.

 Malam Sa'idu kuwa jin tayi shiru yasa ya ɗan ɗaga sautin muryarsa tare da faɗin.

“Maryama kiyi mata magana gashi dai ina jin motsinta amma tayi shiru”.

Jin abinda yace yasa da ƙyar ta buɗe bakinta tace.

“Eh Kawu ina ciki”.

Wani irin tsalle ya buga cike da matsanancin farin ciki kallon ƙofar yayi yaga uban kwaɗon dake jiki saurin juyawa yayi nan yaga tarin dutsina da sauri ya nufi wajen ya ɗauka tare da cewa.

Kada ki damu yanzu zan buɗe ki”.

Kai kawai ta iya gyaɗawa hawaye na zilala daga idanunta.


Da ƙarfi ya riƙa buga dutsen ajikin kwaɗon amma bai buɗe ba ganin lokaci na tafiya yasa ya takarƙare da duka ƙarfinsa ya buga cikin sa'a kwaɗon ya ɓalle ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗewa jikin bencin ya hangota atakure ƙofar ya maida ya rufe tare da sa sakata kana ya ƙarasa gabanta ya tsugunna yana sakar mata da murmushi mai cike da ma'anoni hannu yasa tare da shafa fuskarta.

Atsorace ta bige hannun sa kana ta yunƙura da niyyar tashi.

 

Cikin sauri ya fisgota baya ta zauna daɓas acinyarsa azabure ta yunƙura da niyyar tashi saurin rungume ta yayi aƙirjinsa yana shinshina wuyanta sai kuma yayi saurin janye hijabinta ya manna kansa akan wuyanta saurin kai hannunsa kan ƙirjinta da babu Bra yayi.

Cikin tsananin tashin hankali da ruɗewa ta saki marayan kuka tare da ingijesa da ƙarfi ta nufi ƙofa.

Kansa ne ya bugu da jikin bencin atake wajen ya fashe miƙewa yayi cike da ɓacin rai taku biyu yayi alokacin da take yunkurin buɗe ƙofar ya finciko rigarta baya ya watsa mata Lafiyayyan mari afuskarta hagu da dama lokaci ɗaya taga wasu taurari sun gilma acikin ƙwayar idanunta kana jiri ya dibeta tayi baya luuuuuu cikin sauri ya tallafo ta jikinsa ya rungume tare dasa hannu akan rigarta ya yaga biyu atake Madaidaitan Brea's ɗinta suka bayyana awaje.


Wata mahaukaciyar dariya ya sheƙe dashi kafin ya ciro wayarsa acikin aljihu yayi dearling number Mamawo cikin sauri Maryam dake zaune kan sallaya ta miƙe ta ɗauki wayar tare da sallama cikin ƙasa da murya yace.

“Maryama kina jina ko?”.

Cikin sauri ta gyaɗa kai tare da cewa.

“Kawu an same tane?”.

Kai ya girgiza tare da faɗin.

“Maryama yanzu me gadi ke sanar min cewa tunda aka tashi yaga wata mota tazo ta ɗauke ta yayi zaton ma ko ɗan uwanta ne amma kada ki bari Saude ko Baban ki yaji saina gama bincike”.

Ya ida maganar tare da katse kiran da kallo Maryam tabi wayar sam bata yarda da abin da ya faɗa ba taya sister Neenah zata bi wani a mota cikin ranta tace wannan ba gaskiya bame.


Neenah kuwa zare ido tayi cike da mamakin karya da sharrin da ya mata sam bata da kuzarin yin ihu ko ƙara.

Wani mayataccen kallo me cike da shauƙi ya bita dashi Kafin ahankali ya kwantar da ita aƙasan wajen kana ya miƙe ya cire rigarsa cikin tsananin tashin hankali da ruɗu tasa hannu ta rufe ƙirjinta cikin rauni tace.

“Dan Allah ka tausaya min kada ka lalata min rayuwa kaifa matsayin Uba kake gareni meyesa kake son cutar min da rayuwata!”.

Ahantare ya gwaɓe mata baki kana yace.

“Rufe min baki shegiyar yarinya me zaƙin baki ai yanda ki kayi niyyar to zar tani saina tozar taki yanda zakiji kin tsani kanki da rayuwar sannan in ɗauki duk abinda ya faru tsakanin mu in watsa duniya muddin kika yi kuskuren sanar da wani TOH rayuwarki tana cikin hatsari”.

Bai jira cewar taba ya mike tare da ɗaukar wayarsa kiran Gionee ya ajiye kusa dashi sai kuma ya janye dogon wandan shi ya dawo tsirara haihuwar Uwarsa.


Cikin tsananin tashin hankali ta runtse idanunta shi kuwa hannunsa yasa tare da janyo ta jikinsa cikin tsananin ruɗu ɗimuwa da tashin hankali Neenah ke girgiza kai ta buɗe baki da niyyar ƙara ya ɗaga hannu ya kwaɗa mata mari da yasa numfashinta ɗaukewa kana ya janyo rigarta ya ɗaure mata baki tare da rabata da suturar jikinta cikin tsananin rashin tausayi da imani kana da mummunan ƙudiri Aransa ya toshe hancinta”...


_Sawun Giwa It's 500 hundred Via 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number ***...show ur Evidence ***._


_@Follow me on Arewabooks realeshaa_


_@Follow me on Wattpad realeshaa_



_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya..._



_Ayi shearing saboda Allah Ƴan Uwa masoya da abokan arziƙi_



*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***


     *ESHAA CE*🤙