BAQEER

Page 2

by @ayushermuhd

BAQEER

   *NA*

*AYUSHER MUHD*

      *DA*

*UMM ASGHAR*


*RUBUTUN ƳAN TAGWAYE BIYAR KARO NA BIYU.*

*TAFIYAR BIYU TAFI ƊAYA*




*2*

Yau tunda ta tashi take jin jikinta babu daɗi gabaki ɗaya yayi mata nauyi ga wani irin ƙunci da ya lulluɓe kirjinta lokaci zuwa lokaci sai taji gabanta ya faɗi, komai take yi tana yin shi ne cikin rashin karsashi tunda tasan ba rashin lafiya take yi ba sai dai yanayin data samu kanta a ciki sam baya yi mata daɗi. A kasalance ta yunƙura daga inda take kwance a tsakar ɗakinta ta tashi, tsakar gidansu ta fito ta hau tattare wajen da suke yin girki don itace da girkin ranar, haka nan cikin dauriya ta samu ta haɗa wutar ta ɗora tukunya, aikin take yi salalaf-salalaf kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki don sam jikinta baya da wani ƙwari.


Tana lura da abokan zamanta da suke ƴan maganganu ƙasa-ƙasa a gefe da sun ganta sai suyi shiru suna zunɗenta da baki abinda yasa ta ƙara tunanin tabbas akwai abinda ya faru da suke ɓoye mata duk kuwa da ba yau ne karon farko da suka taɓa yi mata irin hakan ba sai dai na yau ɗin yayi tsanani ga kuma yanayin data tashi dashi tun safe yasa tayi tunanin tabbas ba lafiya ba, gashi ma maigidan tunda ya fita bai dawo ba haka nan Baqeer yau yayi nisan kiwo abinda ba halin shi ba ya fice waje yayi zamanshi in har ba wani muhimmin uzuri ne ya riƙe shi ba ba tare da ya leƙo yaga a halin da take ciki ba don duk inda ya tafi hankalinshi yana kanta sanin irin zaman da take yi a cikin gidansu yasa baya son yin nesa yana barin gidan don kaɗan da aikin mutanen gidan suyi mata wani abun na cutarwa ita kuma ba iya kare kanta take yi ba.


Har ta gama girkin ta raba kamar dai yadda suka saba Baqeer bai shigo gidan ba abinda ya ƙara ɗaga hankalinta don baya taɓa kaiwa magriba a waje duk inda yaje yana ƙoƙarin dawowa gida kafin ayi sallar magriba idan kuma ya zama lallai sai ya daɗe a wajen to tabbas zai kirata a waya ya faɗa mata. Sai da ta kawar da komai ta tsaftace wurin kafin ta tashi ta koma ɗakinta, wayarta ta ƙara ɗauka ta kira number Baqeer sai dai har yanzu a kashe ake ce mata, juya akalar kiran tayi zuwa ga wayar maigidan sai dai har ta ƙari ɓurarinta ta gama bai ɗauka ba, ƙara kiran wayar tayi amma har yanzu bai ɗaga ba. Tunani tayi watakila sallah yake yi don haka ta ajiye wayar da zummar ta sake kiranshi in anjima, tashi tayi ta fita don ta ɗauro alwalar ita ma tayi sallah sai dai abinda taji a tsakar gidan yasa ta sakin butar dake hannunta ta faɗi sauran ruwan dake cikin butar ya tsiyaye akan simintin tsakar gidan nasu.


Kamar wacce aka jeho sai ganinta suka yi a gabansu tana cewa "Me ya samu Baqeer ɗin kuke ɓoye mini? Ni dama nasan shirun nan nashi bana lafiya bane tabbas akwai abinda ya faru dashi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙare da ɗora hannayenta bibbiyu a kanta tana kuka.

"Ke dallah kada ki cikawa mutane kunne da kwakwazo a cikin gida, wani abu kika ji ance ya samu Baqeer ɗin da zaki cika mu da iface-ifacen kuka," Uwargidansu Jamila tayi maganar cikin yi mata tsawa.


Duk da faɗan da ta rufeta dashi bata saduda ba sai da ta ƙara cewa "Amma sai naji kamar kun ce Baqeer yana asibiti, dan Allah ku taimake ni ku faɗa mini ba hakan bane ko hankalina ya kwanta, yau tunda Baqeer ya fita bai dawo ba bayan hakan ba sabon shi bane." ta ƙare maganar cikin rawar muryar da tashin hankali ya gama kassarawa.

Har Jamila ta buɗe baki zata cigaba da zazzaga mata masifa sai Abu ɗaya kishiyar tasu ta ɗaga mata hannu alamar tayi shiru don haka Jamilar taja bakinta ta tsuke sai dai ranta fal ƙuna taso Abu ta ƙyaleta yau ta zazzaga mata rashin arziƙi saboda yadda tafi jin haushinta da kishinta akan Abu ganin yadda mai gidan ya ɗauki dukkanin wata soyayya ya ɗora akanta da tilon ɗanta sai kace fin nasu ƴaƴan yayi.


Muryar tausayi Abu tayi ta wani kwakkwaɓe fuska kamar zata yi kuka tace "Ashe baki ji ba ai da baza mu fara yin maganar nan har taje kunnenki ba amma tunda kin riga kin ji babu amfanin ɓoye miki," ta ɗan yi jim kamar tana juya ta yadda zata fara faɗa mata wannan mummunan labarin bare yadda taga duk ta matsu taji a wane hali ɗan nata yake ciki. Sai data gyara tsayuwarta sannan tace "Baqeer ne Allah ya aikowa da tsautsayi mota ta buge shi, yanzu haka su Alhaji na can asibitin Mallam Aminu Kano inda aka kai shi shi da Bashir, sai fatan Allah ya kiyaye gaba dai amma ga yadda nake ji kamar ance bai ma san a inda kanshi yake ba."


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" ta ƙara ambata tana mai fashewa da wani irin kuka duk da tunda Abu ta fara maganar take tsiyayar da ruwan hawaye dama "Yanzu Baqeer ɗin yana asibiti tun ɗazu aka rasa mai faɗa mini? Wayyo ni Allah ka tashi kafaɗun yarona alfarmar Annabi da Alqur'ani" ta ƙare maganar tana nufar hanyar waje da nufin tafiya asibitin taje taga halin da ɗan nata yake ciki, tsabar ruɗewa tama mance da ko mayafi babu a jikinta bare kuɗin motar da zata hau ta kaita asibitin.


Abu ce tayi hanzarin janyota ta dawo da ita tsakar gidan tace "Malama ina zaki? Yanzu da daren nan daga faɗa miki magana? Salon Alhaji yace waya faɗa miki kice mune bayan ya hanemu da yin hakan?" Kallon Abu tayi da kumburarriyar fuskarta data koɗe saboda kuka tace "Wallahi bazan iya zama ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan har ba zuwa nayi naga a wane hali yake ciki ba, don Allah kuyi haƙuri ku barni na tafi wallahi bazan faɗawa Alhaji a wajenku naji ba." 

Sai sannan Jamila ta saka musu baki don duk abinda suke yi kallonsu kawai take yi tunda Abu ta haneta da yin magana, cewa tayi "Idan dai kin tabbatar da baza ki faɗa mishi mu muka gaya miki ba sai kiyi tafiyarki don ko nice hakan ta faru da yarona nasan hankalina ba zai taɓa kwanciya ba idan ba zuwa nayi naje naga a halin da yake ciki ba, sai dai kuma kada ki manta ko mayafi babu a jikinki bare kuɗin mota ko kina tunanin akwai wanda zai yi miki kallon hankali a hakan da kike".


Sai sannan ma ta tuna ai ko sallar magriba bata yi ba ashe fa alwala ta fito zata yi taci karo da wannan mummunan labarin da yayi fatali da dukkanin wata nutsuwarta. Ɗakinta ta shiga ta fara zarya kafin ta ɗau ki hijab, zurawa kawai tayi ta tada sallah sai dai sam ba ka jiyo karatunta sai sautin kukanta, da tazo sujjadar karshe kuwa kasa miƙewa tayi kawai ta cigaba da kuka tana neman Allah ya tausaya musu ya tsagaita wahalar Baqeer. Da ƙyar ta iya sallame sallah, ko hijab ɗin bata cire ba ta jawo jakarta ta nufi hanyar waje kai tsaye, ba komai take ganewa ba, hakan yasa ta zura takalmin da take aiki dashi a tsakar gida kawai ta fita titi.

Abu da Jamila suna hangota ta tagar window ɗin dakunansu, a tare suka saki wata dariya ta jin dadi dan tabbas sun san yau akwai kura a gidan nan, su dai iya kacinsu su buɗe ido su kwashi kallo. 

Mai adaidaita ta tare sannan ta shiga ciki tana tafe tana lazimi, har saida yace gasu a Aminu Kano. Idanunta ta sauƙe kan asibitin tana jin gabanta na faɗuwa, haka ta fito ta kira Bashir akan ya sanar da ita inda aka kwantar da Baqeer ɗin, a lokacin yana kwance dan ba'a daɗe da gama ɗaukar jininshi ba, hakan yasa yace ta kira Bello shima bai sani ba ya kashe wayar tare da jan wani tsaki haka kawai shi ba da hatsari ba an kwashe mishi jinin jikinshi, shi yasa sam baya kaunar Baqeer saboda a komai sai Baban ya nuna fifiko a kanshi.

Bello ta kira cikin sauri, nan ya sanar mata zai zo ya ɗauketa daga inda take kasancewar asibitin da girma yake, sannan Baba ya hanashi komawa cikin ɗakin.


****

Zaune Baba yake gaban Baqeer wanda kallo ɗaya za kayi wa fuskarshi ka fahimci tsantsar damuwar dake ɗauke da ita, idanunshi na kan Baqeer yana kallon yadda yake kwance kawai baya ko motsi, numfashi kawai yake yi, hannayenshi ya riƙo zuciyarshi na sake karyewa yake magana “Baqeer ka taimakeni ka tashi, ka sani kai kaɗai ne burina, da kai kaɗai nake taƙama a duniyar nan, kaine wanda in na gani nake jin sanyi a raina nake kuma kyautata zaton nayi abin arziki na kawoka duniya da nayi, ka taimakeni ka farka kafin wannan taron naku, kada ka bari abinda muka daɗe muna shiryawa ni da kai ya tafi a banza……” Maganarshi ce ta maƙale jin sako ya shigo cikin wayarshi, duba wayar yai yaga sakon secretary na Gomna ne wanda yake sanar dashi sun turawa Baqeer kuɗi akan yayi siyayyar abinda zai buƙata in yaje Abuja yin gasar. Wayar ya maida aljihu ya sake damke hannun Baqeer yana ji kamar ranshi zai fito.

Ƙofar da yaji an buɗe ne yasa ya kalli ƙofar tare da sakin hannun Baqeer, nan da nan idanunshi suka canza fuskarshi ta murtuke, rai a ɓace yake kallinta, sai dai ko bi takan shi ba tayi ba ta ƙarasa shigowa ciki da gudu tana cewa “Na shiga uku, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Baqeer?”

Cike da tsawa Baba yace “Fatima ashe baki da hankali?”

Cak ta tsaya daga inda take tana kallonshi a tsorace “Banda hauka da rashin tunani uban wa ya baki izinin zuwa asibitin nan?”

Hawaye ne suka gangaro mata tace “Haba Alhaji, yanzu ta ina kake tunanin zan iya zama bayan naji ɗana yayi hatsari? Sannan kalli yadda aka nannaɗeshi da bandage wanda kana gani kasan……”Kuka ne ya kwace mata wanda ya hanata ci gaba da magana, nan ta ƙarasa jikin gadon tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, Baba yana tsaye yana saurarenta na wasu mintina kafin yace “Kin ganshi ai ko? To tattara ki koma ni bana son shirmen banza, ɗana ba abinda zai sameshi kuma bana so wasu mutane su sani balle a mana hassada da baƙin cikin da aka saba, kuma wallahi karna sake ganin ƙafarki anan in har ba ni nace miki kizo ba.” Ɗago jajjayen idanunta tayi ta kalleshi cike da tausayi tace “Alhaji kar kayi min haka na rokeka da Allah ka barni na zauna kusa da ɗana dan Allah ka dubi wannan mahaifiyar.”

Hannu ya ɗaga mata alamar tayi mishi shiru dan Baba kowa ya sanshi akwai zafi, sam bashi da sakin fuska shi yasa yaranshi da matanshi kowa ke shakkarsa, “Wallahi kika bari na sake magana sai ranki ya ɓaci ni bana san shirmen banza, ce miki aka yi Baqeer rago ne irinki da zaki zauna kina kuka yana saurara? To ni bana son shirme ki koma can gida kiyi ta kukanki kina sharewa, yarona da izinin Allah ba abinda zai sameshi ki koma na miki alƙawari yana farkawa zan sa a kawoki.”

Hawaye kawai take yi kamar wanda ake zuba mata ruwa a cikin idanuwanta saboda yawan hawaye, da ƙyar take jan ƙafafunta ta fito daga ɗakin. Bashir wanda ya taso dan ya ga mai zai faru yana jikin ƙofa yana kunshe dariyarshi, jin alamun ana toshe baki yasa Fatima ta juya ta kalli Bashir, cike da raini ya nuna mata hannunshi yace “Jinina aka ɗauka aka sakawaa ɗanki.”

Hannun ta kalla ta juya ta kalli ɗakin inda jinin ke shiga jikin Baqeer, tace “Nagode Allah ya kara haɗa kanku.”

Juyawa tayi suka fara tafiya da Bello. Baba kuwa a ɗaki zirya ya shiga yi don a yanzu abin yafi ɗaga mishi hankali, “Kai Bashir shigo.”

Bashir dake waje abinda yaji Baban nashi ya faɗa kenan, da sauri ya shiga ciki yana sosa bayan ƙeyarshi.

“Ka zauna da Baqeer duk wani abu daya faru kayi mini waya ka sanar dani dole zanje gidan Sulaiman Karaye bazan taɓa yadda da wannan iskancin ba, ni muna nan asibiti shi yana kwance a gida hankali kwance.”

Yana kaiwa nan ya juya bai ma tsaya ya jira mai Bashir zai ce ba, da sauri ya fito daga waje ya hango Fatima, nan ya ƙarasa inda take jiran adaidaita a mota ya tsaya kusa da ita.

Ganinshi yasa ta buɗe gaban motar tana share kwalla ta zauna zuciyarta duk babu daɗi, “Kema yanzu kin fara daina jin magana ta ko? A wani dalili da zaki fito bada izinina ba?”

Ta share kwalla tace “haba Alhaji kayi mini adalci mana, wacce uwa ce zata zauna a gida bayan taji halin da ɗanta yake ciki ba tare da taje ta ganshi ba? Sannan ka duba yadda Baqeer yake kamar wanda bashi da rai?” Hawaye kawai take yi tana jin zuciyarta na wani irin zafi, ya fahimceta sarai amma ɓacin rai da halin da yake ciki bazai barshi ya sauƙa daga fushin da yake ba.

A ƙofar gidansu yai parking nan ta fita bai ko ce mata komai ba, tana sauka yaja mota ya nufi gidan Sulaiman Karaye.


*****

Katon gida ne wanda a unguwar yana daga cikin manyan gidajen masu kuɗi, tun daga waje zaka gane kyan gidan saboda fitulu da aka saka suke haska layin gidan, ba wai kato bane gidan wanda baza’a iya kwatantawa ba, ba kuma cinye rabin layin yayi ba, gida ne dai babba daidai misali wanda za’a iya gina gida uku ko hudu na mai ƙaramin ƙarfi, kasancewar gidan sabo ne yasa yake sake ɗaukan ido. Alhaji Sulaiman Karaye ba wai bakon mutum bane don sun san juna shekaru masu yawa a baya. A gaban gidan yayi parking tare da sanar da mai gadi yana son magana da mai gidan.

Kamar mai gadin zai musa sai ya fasa dan Alhaji Sulaiman ya sha sanar dashi duk wani dattijon dake son ganinshi to fa a sanar mishi kome yake yi zai bari ya saurareshi tunda bai san uzurin dake tafe dashi ba.







#BAQEER

#AYUSHERMUHD

#UMMASGHAR