FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Trailer
“Baqeer! Baqeer! Baqeer” Kalaman da kunnuwansa kawai suke juyo wa kenan, a hankali wasu hawaye suka gangaro gefen fuskarshi, shi kenan yanzu ƙafafunshi sun tafi? Shi kenan haka zai karashi rayuwarsa a keken guragun? Runtse ido yayi babu abinda yake gani sai babban amininshi tsaye gefen matar da yake shirin aura kafin wannan ibtila’in ya faɗa mishi, gasu nan tsaye suna murmushin soyayya. Shikenan shi yanzu komai nashi ya ruguje? Sake maida idon yayi ya rufe, me zai kuma gani? Ƴan uwanshi ya gani da matan mahaifinshi suna kallonshi suna yi mishi dariya “Yau ina son da aka daɗe ana nuna maka Baqeer? Ina bambanta ka da aka daɗe ana yi?”Wani zazzafan kwalla ce suka sake zubo mai, yayinda ya sake maida idanunshi ya rufe, tsaye ya hangota cikin idanuwanshi tana sakar mishi wani ƙayataccen murmushi wanda ya sagar da duk wata gaɓa dake jikinshi.“Baqer! Kada ka kuskura zuciyarka ta mutu dan ka zam...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.