Mutum Mugu Ne

24

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*

           24

....... Lagos.....

Washegari bai tashi da wuri ba, sai shida saura ya farka, ya lek'a Zaytunah ta na nad'e kan gado tana sharan bacci, a yadda ya ganta itama d'in ko tashi bata yi ba, a gurguje ya shiga band'aki yai alwala ya fito, tashin Zaytunah yai dan ta tashi ta yi sallah, sannan ya wuce ya gabatar da tasa sallar Asubahin. Bayan ya idar ya ga Zaytunah komawa bacci tayi ba ta tashi d'inba. Daga inda yake zaune yace "Zaytunah ki tashi kiyi sallah, lokaci ya wuce" 

Bata tashi ba sai da ya sake nanata maganar, ta tashi ta zauna tana goge ido, kafin daga bisani ta shige band'akin.

Yana karanta Qur'ani ta fito, ta saka hijab ta tada sallah. Bayan ta idar ta kwantar da kanta k'irjinsa tace "My one jiya banji dad'in abin da kayi ba, kawai sai ka kwanta a k'asa, it's an insult to me fah"

Bai ce uffan ba ya cigaba da karatun da yake.

" Dan Allah kadena horona ta wannan hanyar, na kan ji bak'in ciki sosai idan ka raba makwanci dani"

Sallamar Azra ya kat'seta.

"Dad, may I come in?"

Abin mamaki, Azra ce da sallama tana neman izinin shigowa. Ya sani shi ba mai tsananta wa yaransa bane, kusan rainon turawa ya ke musu abu d'aya da ya san baya wasa dashi shine sallarsu, matuk'ar yana gida tare suke zuwa Sallah da yaransa ZunNurain da Aamir idan kuwa baya nan to da ya dawo zai bincika ko sun yi Sallah. Wani batun neman izini kafin su shiga d'aki babu shi, study room ɗinsa ne kawai yake kullewa a gida saboda baya so su mai wasa da mahimman takardunsa. Hakanan idan ba wai sun ke'be da Zaytunah bane baya kulle bedroom ɗinsa. Yaranshi suna shiga duk inda suka ga dama agidan akowani lokaci ba tare da neman izini ba.

Dukkansu suka juya suna kallon k'ofar amma Azra bata shigo ba. Ganin bata da niyyar shigowa Sajid yace "come in princess" sai a lokacin ta bud'e k'ofar ta shigo ta k'arasa wajensu ta tsugunna tace "Good morning Dad, Good morning Mommy"

Sajid ya jawota jikinshi yana shafa fiskarta yace "Good morning princess, how's your night?"

"It's beautiful Dad, I had a wonderful dream"

"Who gave you this stinking rag you are wearing, Azra? Zaytunah ta fad'i tana nuna zanin da Azra ke d'aure dashi.

Wani kallo Sajid ya wurga mata yasa ta had'iye masifarta.

Azra tace " Mommy this is not a rag, and it's not stinking either"

Ta kamo kunnen Sajid ta rad'a masa magana a kunne " Dad, Nazzy gave me this, she said it's called Iyo in yoyba(Yoruba)" (Iro- meaning zani).

Yasan Azra nada matsalar fitar da harafin 'R' yanzu ne ma harshenta ke k'ok'arin iya fad'i, yawanci lokuta takan kira harafin 'y' ko 'l' a wajen 'r'. Har yau ba ta iya fad'in sunan yayanta da kyau sai tace 'Nuyen' a maimakon 'Nurain'. Sunanta ma yanzun take iya fad'i da sai dai tace sunanta ' Azla'.

Ya kissing kumatunta sannan ya tambayeta ko ta yi sallah, ta amsa da cewa ta yi sallah kuma Nazzy ta mata wanka yanzu ma ta zo d'aukan kaya ne.

"And who told you to ask for permission before you enter this room?"

"Nazzy, Dad. She told me whenever Dad and mommy are alone in the room, I should seek permission before I enter"

"Why?" Zaytunah ta fad'i da sauri dan dama kunnenta na kan maganar da suke yi.

"She said it's good to ask for permission because Allah will give you reward and you'll enter Jannah" ta k'are maganar tana dariya.

Wani dad'i ya ji ya ziyarci zuciyarsa tabbas Ziha ta koya masa darasi. Dole ya fara lura da tarbiyan yaransa sosai tun yanzu da suke k'ananu.

"Ni kam maganar Nazzy Nazzy nan ya isheni, je ki d'au kaya ki saka"

Sajid ya rufe Qur'ani ya ajiye gefe ya tashi rik'e da hannun Azra ya je ya bud'e jakar tasu ya ciro mata riga da wando kalar sky blue neman hula ko d'an kwali yake yi bai gani ba. Sai yanzu abin yazo masa asalima Zaytunah bata fiye rufewa Azran gashi ba, sai yanzu yake ganin rashin kwa'bar Zaytunah ka iya sawa yaransu su tashi da halin ko oho. At least Azra is 5yrs tun yanzu ya kamata a saba mata da shigar musulunci saboda ta taso da son abun.

Ya dai ga wani siririn gyalen Zaytunah ya d'auko ya had'a dashi, hanyar fita daga d'akin suka yi.

Zaytunah tace " My Sajid muna magana ne fa, ka bata taje wancan yarinyar ta sa mata"

Juyowa yayi ya kalleta yace " we have alot to talk about Zaytunah, amma ba yanzu ba, not today and not here. Ko ma minene complain ɗinki ki ajiyeshi idan Allah ya sa mun koma Abuja zamu zauna muyi maganar"

Daga haka shi da Azra suka fita daga ɗakin.

A falo ya tarar da Tim, Gbenga da Ziha suna zaune da yare suke magana dan haka bai san mi suke cewa ba. Azra ta sake hannunshi ta nufi wajen Ziha da gudu ta mik'a mata kayan da Sajid ya fitar mata tace ta sa mata. Ta k'ar'ba kayan tace suje d'aki ba a chanja kaya a gaban mutane.

Da yare Gbenga ke ce mata kuma mi zasu gani ajikin 'yar wannan yarinyar.

Ziha ta wani rolling idonta alamar eh d'in.

Tana d'aga kai suka yi ido hud'u da Sajid da ke tsaye yana kallonta. Ta yi saurin sunkuyar da kai tareda cewa "Good morning Uncle"

Murmushi ya sake mata kafin yace "morning Ziha, sannu da k'ok'ari fah nasan kin sha rigimar Azra'

"Lah ba komai fa"

Yana gaisawa da su Gbenga ta wuce da Azra d'akinsu. Ya bita da ido for the first time daya mata kallon k'urilla kenan, sai yanzu ya ga yadda shape d'in hips d'inta ya fita sosai, kodan kayan da ta sa ne. Lace ne milk me flowers green d'inkin buba aka yi da plain zani, ta d'aura zani akan rigar, d'an kwalin kayan ta d'aura ba ta saka gyale ko hijab ba.

Gbenga da Tim suka kalli juna kowa da abinda yake tunani aransa.

Daddy ya fito daga d'akinsu, suka gaisa ya tambayi lafiyar iyalinsa Sajid yace suna lafiya. maimakon ya koma nasu d'akin sai ya zauna a falon ya fake da jiran Azra.

"Funmilayo, Funmi" Daddy ya k'wala sunanta

"Yes, Daddy"

Daga d'akinsu take amsa masa.

Da sauri ta fito tareda Azra ta yane kanta da k'aramin gyale green. 

Ta tsugunna gaban Daddy. Ya ciro kud'i a aljihunsa ya mik'a mata yana mata bayani da yare daga k'arshe ya koma addu'a. Sajid ya gane hakan ne lokacin da ya ji a k'arshen maganar Daddy yana cewa"in the mighty name of Jesus" Timothy da Gbenga suka amsa da Amen.

Naziha ta mishi godiya sannan ta tashi, Gbenga da Tim ma suka miƙe.

Ido Sajid ya zare lokacin da ya ga Gbenga ya sak'ala hannunsa a kafad'ar Ziha a haka kuma suka fita daga gidan, ya na ji Azra na faɗin "Nazzy please come back soon" amma shi bai iya cewa komai ba.

Muryan Daddy ya farfad'o da shi daya ji yace " I pray she gets good points"

Sajid yai saurin tambayar sa inda zasu je.

Daddy yace "Funmilayo za ta je rubuta Jamb ne, su kuma zasu rakata"

Wato ma zata je rubuta Jamb amma shi bata iya fad'a masa ba. Wata zuciyar tace tunda issues d'in Zaytunah suka taso ai baka samu zaman magana da ita bama balle har ta gaya maka.

Farar spaghetti da sauce d'in manja aka kawo musu wanda ya ji kifi sai kayan tea.

Shi da Azra kad'ai suka ci musamman da ya ta'ba ya ji girkin Naziha ne, Allah Sarki ashe tun da sassafe ta had'a breakfast kafin ta fita. Zaytunah kam cewa tayi bazata iya cin abincinsu ba, sai dai ya mata order ko ya je ya siyo mata abinda za taci.

"Zaytunah kince su Arna ne ba za ki ci girkinsu ba, restaurant da za a siyo miki abincin an ce miki musulmai ne a wajen? Ko kuma lokacin da muke abroad turawan da ki ke cin girkinsu su d'in musulmai ne?"

" Ni dai ba zan ci ba, zuciyata bata yadda da su ba, inba sun shanyeka ba ta ya za'ayi ka iya zama dasu anan all this time. Four bedroom flat ne fah, suma bai ishesu ba balle su ajiye bak'o agida. Munafurci dai irin na Yarabawa sun ga kana da kud'i zasu mak'ale ka su yagi rabonsu, to ba zai yiwu ba"

Ya girgiza kai kawai ya cigaba da cin abinci, tunda ya zo gidan nan basu ta'ba yin girki ya raina ba, kuma har ga Allah suna dai dai k'ok'arin su wajen girki mai kyau, ranar da suka fara yin Amala ma shi rice suka dafa masa, da Ziha tace masa Amala suka yi yace ta kawo masa kad'an ya gwada ci dan bai ta'ba ci ba, da kuwa ya ci ya ji dad'insa tun daga nan shi kenan ya fara ci.

"My one dan Allah na tambayeka mana. Wai miye had'in ka da mutanen gidan nan ne? Daka nace musu har kasa dole sai mun zauna a nan"

"Ki shirya Ishola na zuwa zamu fita tare zai sauke ki a inda za ki ci abinci, zanje na ga barrister" amsar da ya bata kenan.

Sun bar Azra a gida saboda tace zata jira Nazzy. Ganin Zaytunah browsing expensive restaurant na Lagos da za ta ci abinci take yi a waya, yasa Sajid yace Ishola ya fara kai shi gidan Barrister tukunna kafin ya kaita inda zata je.

Suna zuwa kai tsaye Asibiti suka wuce inda aka kwantar da Nickolas.

Irene suka samu tana jinyarsa, suka tambayeta abinda ya faru ta gaya musu.

Sajid ya tambayeta abinda ta sani gameda mutuwar d'an uwansa Alhaji Aliyu.

Kuka ta fashe musu da shi da k'yar suka samu ta yi shiru. Ce musu tayi ba za ta iya gaya musu ba har sai idan an kama Uncle Joe, amma matuk'ar ba a kama Joseph ba, ba za ta iya gaya musu ba.

Haka suka hak'ura suka bar Asibitin a hanya Sajid ke tambayar Barrister yadda aka yi Ziha ta iya samun audio d'in maganansa da Joseph.

Barrister ya sanar mishi ranar Alhamis ta zo ta sameshi har gida tace tana da plan yadda za'ayi ka bada evidence ɗinka a kotu ba tareda iyalinka sun shiga had'ari ba, so bayan ta gama bada bayanin nima na gamsu sai muka je muka samu wani abokin Uncle d'inta dake aiki da MTN so, shine ya bamu audio na conversation d'in.

Sajid ya jinjina hankali irin na Naziha.

Police station suka wuce, Dan jin bayanai gameda Joseph amma basu samu labari mai dad'i ba, har lokacin ba a san inda yake ba.

Daga police station Sajid ya kira Ishola ya ji ko ya kusa isowa ko kuma su wuce da Barrister in yaso ya samesu a gidansa. Da mamaki yake sauraron Ishola dake ce mishi ai yanzu haka suna Banana island wai Zaytunah tazo gidan wata k'awarta so yana jira ta fitone su tafi idan ma bata nemi ya kaita wani wajen ba kenan.

Yana kashe kiran ya kira Zaytunah bata d'auka ba sai a kira na biyu ta d'auka.

"Kina da hankali kuwa Zaytunah? Nace driver ya kaiki wajen cin abinci kin wuce gidan k'awa"

"Haba my one minene aciki na riga nazo ta wajen nefa shine na tuna akwai wata k'awata da muka yi karatu da ita tace anan take aure shine na shiga mata fah, besides rabona da Lagos shekara nawa Ina kallon yadda Lagos ya sake chanjawa ne over the years"

Takaici ya kamashi, koda shike laifinsa ne da ya ke nuna halin ko in kula a baya ga shi yanzu ya zama mata jiki da jini.

"Shikenan idan kin gama kallon yadda Lagos ya chanja ki nemi taxi ko wani driver da zai mai dake gida amma ba Ishola ba"

Yana kashe wayar ya sake kiran Ishola yace maza maza yazo ya d'aukeshi yanzu...