15
by @realeshaa
*SAWUN GIWA*
_Ya take na Raƙumi_
_By_
*Aishatu Abdullahi Idris*
_REAL ESHAA_
*F-R-PG 15*
Acan Masarautar Sarki Aliyu Ahmad Zaman kuwa adake Meerah dake kwance kan makeken gadonta hannunta riƙe da waya ta ɗago kanta jin yanda aka banko ƙofar kallo ɗaya ta yiwa Gimbiya Fa'izah dake huci tamkar kububuwa ta kawar da kai gefe tare da cigaba da latsa wayarta.
Gimbiya Fa'izah kuwa afusace ta tsaya akanta cikin ɗaga sautin murya da hargowa ta kira sunanta da faɗin.
“Meerah”.
Alalace Meerah ta ɗago kanta ganin yanda take huci yasa ta sake tamke fuskarta babu walwala atare da ita tace.
“Ina ji”.
Cikin kumfar baki da tarin takaici Gimbiya Faiza ta girgiza kai tare da faɗin.
“Akan mai zaki min ƙarya?,sannan ki ɓata min lokaci?”.
Zaman Bluetooth dake kunnenta ta gyara tare da watsa mata kallon raini kana tace.
“Dan Allah ki fita sabgata in shaƙi iskar ƴanci Yaudara da ƙaryar me na miki?”.
Ta haɗiye wani abu mai ɗaci tare da cewa.
“Meyesa zakiyi min ƙarya kisa inyi asarar maƙudan kuɗaɗena kina zaton wannan video kaɗai zai wadatar da abinda muke so ne?”.
Miƙewa Meerah tayi tare da watsa mata wani kallo babu walwala atare da ita tace.
“Kinga Aunty Fa'i ki fita sabgata dan Allah dan wallahi koda sama da ƙasa zai haɗu Bazan aikata abinda kike soba sannan maganar video shima ina nazarin zamansa ko akasin haka”.
Ta wani ɗaure fuska tare da cigaba da faɗin.
“Muddin wani abu ya sami Abdallah zuciyata ba zata iya jura ba shi ɗin rayuwata ne kuma zan iya aikata komai sannan inyi faɗa da kowa dan ganin na karesa mutuncin sa koda kuwa ace kece”.
Da hannu Gimbiya Fa'izah ta nuna kanta kana tace.
“Meerah Ni kike faɗawa Maganar da ranki yake so aka ɗa namiji?,Ɗa namiji ma ba kowa ba sai Abdallah?,Mutumin dake da banza ɗaya ne?,Mutumin dake da babu duk ɗaya ya ɗauka?,Akan ina son ƙwato miki ƴan ci kike son wulaƙantani?”.
Sake tamke fuska Meerah tayi tacem
“Dakata Aunty Fa'i kada ki fusata min zuciya,koda yake bazan damu ba saboda kin jefeni da wa'annan kalaman domin tarihi ne yake son maimaita kansa”.
Kasa furta komai Gimbiya Fa'izah tayi sai kallonta da take cike da mamaki Meerah kuwa cikin rufe idanu ta cigaba da cewa.
“Ko kin manta cewa haka kema kika yi ta ɗawainiya da son Mai Martaba yana wulaƙanta ki domin bakya cikin irin jerin matan da yake so Hasalima bashi da niyyar auren”.
Ta gyara tsayuwar ta cike da rashin kunya ta cigaba da faɗin.
“Ko kin manta mahaifina shi yayi ruwa yayi tsaki har akayi wannan auren amma saboda butulci shine zaki nemi wulaƙanta abinda nake so,Saboda bakisan darajar haihuwa Ba shekara da shekaru kina zaune babu wani result sai dai kici ki kwanta dole ki kasa sanin menene So tunda mafiya mijin da kike Aure ba auren soyayya kuka yiba?”.
Atsorace ta ɗago idanunta da lokaci ɗaya suka canza launi cikin rawan Murya tace.
“Akan na faɗa miki gaskiya Meerah kike yimin gorin haihuwa?”.
Banza Meerah ta bawa ajiyarta tare da zama agefen gadon kana tace.
“Ai dama gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata taya kike tunanin zan yarda ki cutar da abinda shine farin cikina kuma jin daɗina”.
Kai Gimbiya Fa'izah ta girgiza tare da jingina bayanta da jiki Siff tace.
“Bakomai da farko naso nayi surprised ɗinki ne da baki tilasta min na faɗa miki gaskiya ba da ace kin shafawa Abdallah wannan maganin kamar yanda na umarce ki da yanzu ahaka kina matsayin matarsa sai dai ayanzu kin lalata komai atunaninki Ni kika yiwa mugunta toh ki sani kanki kika yiwa domin Ni na riga na wuce tunanin ki”.
Cikin sauri Meerah ta diro daga gadon tare da riƙe hannunta ganin tana ƙoƙarin fita tace.
“Ban fahimce kiba Aunty Fa'i me kike nufi da cewa da yanzu ina matsayin matar Abdallah?”.
Wani miskilin murmushi Gimbiya Fa'izah ta saki sai kuma ta ɗaure fuska tare da cewa.
“Abinda kika ji na faɗa shine gaskiya domin a wancan ranan da kin shafawa Abdallah wannan maganin dana baki da yanzu kina matsayin matarsa domin Boka ya jadda damin cewa da zaran kin shafa masa maganin aƙasan Marasansa zai birkice dole awannan daren ko kuma washe gari a ɗaura muku Aure amma sai ki kayi fatali da abinda na faɗa miki”.
Wani irin zufa ne ke karyowa Meerah agaba ɗaya ilahirin jikinta cike da alhini da tarin dana sanin tabbatas tayi wasa da damarta sam bata yi tsammanin haka bane...
Gimbiya Fa'izah kuwa cikin rashin walwala ta cigaba da cewa.
“Kada ki manta irin wannan aikin Boka yamin har nayi nasaran mallakar Sarki Aliyu Ahmad Zaman amatsayin miji sannan na zama matarso a idanunsa amma ke saboda gidadanci da rashin wayo dana baki saiki kaƙi amfani dashi.
Cikin rawan Murya da tarin dana sani tace.
“Kiyi haƙuri nayi zaton cutar dashi zakiyi wannan dalili yasa banyi amfani dashi ba amma dan Allah ki tausayawa rayuwata”.
Kai Gimbiya Fa'izah ta girgiza kana tace.
“Is too late Meerah bazan riƙa kashe kuɗi na ina ɓata lokaci akan ki ba amma bakya gani na barki da Abdallah”.
Ta Ida maganar tare da ficewa kai tsaye bedroom ɗinta ta shiga.
Da gudu Meerah tabi bayanta tare da zubewa aƙasan ƙafafunta tace.
“Dan girman Allah Aunty Fa'i kiyi haƙuri kada ki biyewa halina Kinga ni yarinya ce”.
Gira ɗaya Gimbiya Fa'izah ta ɗaga dariya ce taso ƙwace mata amma sai ta masge.
Cikin zubda hawaye Meerah ta cigaba da faɗin.
“Kefa tamkar uwa kike agareni kuma ko wacce Uwa burinta taga ƴaƴanta acikin farin ciki kinsan bani da burin daya wuce in mallaki Abdallah amatsayin mijina ban damu da kota wacce hanya zanbi ba Ni dai burina in kasance ƙarƙashin Inuwar Aurensa”.
“Ok Ina da sharaɗi idan har kin amince zaki bi ashirye nake da samo miki wata hanyar domin kin lalata wannan”.
Cikin rawan jiki Meerah ta gyaɗa kai tare da cewa.
“Wallahi na amince in dai zan mallakesa acikin kwana biyu zanyi duk abinda kike so”.
Wani miskilin murmushi Gimbiya Fa'izah ta saki aranta tace anzo wajen afili kuwa cewa tayi.
“Ok kije zan ne meki”.
Jiki asaɓule Meerah ta miƙe har ta kai ƙofa tace.
“Dan Allah ki tausaya min kinga Ni yarinya ce duk abinda na faɗa Miki tuntuɓen harshene”.
Kai kawai Gimbiya Faiza ta gyaɗa Akasalance ta nufi Bedroom ɗin ta cike da tarin danasani.
**
Cikin sanyi da tausayawa Mama Asabe ta kalli Neenah dake kuka kamar ranta zai fita ahankali ta miƙe ta koma kusa da ita kana tace.
“Ayyah Khadijah kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara yanda tazo miki wannan kukan da kike yi Babu abinda zai Miki face ciwo da zai ja Miki na san cewa abin da ciwo ga duk ɗiya mace amma kiyi haƙuri”.
Araunane Neenah ke girgiza kai sai kuma ta zube akan cinyar Mama Asabe tace.
“Ya cutar da rayuwata ya jefa rayuwata acikin ƙangin wuya ya rabani da burbushin farin cikin da nake ciki shin ya Babana zai ji idan har wannan mummunar labarin ya riski kunnensa”.
Tana murza fuskarta akan cinyarta ta cigaba da cewa.
“Shin da wani ido zan kalli mijin da zan aura alokacin daya tabbatar da cewa Ni ba cikakkiyar budurwa bace?,Shin wace amsa zan bashi da zai sa ya gamsu da cewa Ni ba mazinaciya bace?”.
Kanta mama Asabe ke shafawa cike da tarin tausayinta cikin kuka tace.
“Kiyi haƙuri Khadijah Allah yana kallo tabbas zai sa dangana da haƙuri azuciyar Mahaifinki sannan zai baki miji na gari wanda zai soki dan Allah badan wani abu ba kiyi haƙuri ki share hawayenki sannan ki rungumi ƙaddararki hannu biyu”.
Kai ta gyada Mana Asabe kuwa haka ta riƙa rarrashinta tare dayi mata nasiyyar.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kwanan Neenah uku agidansu Sir Abdallah kuma har zuwa yanzu Ammie ko wani daga cikin gidan baisan da zamanta ba Mama Asabe na bata kulawar data dace bata haɗuwa dashi in ba safiya ba yazo gaida Mama Asabe sannan ya duba jikinta.
Acan gefen Baba da Maryam kuwa sosai suke cikin tashin hankali musamman Baba ya sake ramewa ga jarabar Mamawo dake addabar sa kullum yana cikin kaiwa Ubangiji kukansa ya bayyanar masa da ƴarsa sannan ta kasance a hannu na gari...
Cike da ƙasaita Sir Abdallah dake zaune kan 2sitter ya ɗaga kansa tare da tsirawa Corridor da zai sa daka da kichen Ido dai-dai lokacin da Neenah ta fito jikinta sanye da wata doguwar riga fari mai hannun Spaghetti kanta sanye da hular net rigar robace tabi jikinta yayin da hannunta ke riƙe da wani madaidaicin bowl pinch colour mai masifar kyau ahankali take tafiya tunda abin ta faru da ita ta sake zama so silent ko falon baya fita yanzu ma Mama Asabe ce ta sanya ta ta kawo masa Fruit sakamakon kiran gaggawa da Ammie ta mata shine ta fito cikin sanyi ta durƙusa q gabansa tare da risinar da ƙwayar idanunta ƙasa cikin sanyayyar murya me cike da rauni tace.
“Sir gashi”.
Idanunsa na kan System dake kan cinyarsa ya motsa laɓaɓansa cike da Izzah dake ratsa sassan jikinsa kana yace.
“Taso ki zauna anan”.
Saurin kallonsa tayi tare da kallon gefen ƙafafunsa daga ƙasa daya nuna mata kai ta girgiza still hannunta na riƙe da bowl ɗin fruits Salat tace.
“A'a nagode nan ma yayi”.
Kallon daya mata ne yasa tayi saurin miƙewa ta zauna har yatsun ƙafarsa na gugan nata.
Hannu ya ƙyasta mata atsorace ta ɗago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta kallesa sake ɗaure fuska yayi tare da miƙa mata hannu.
Kallon rashin fahimta tayi masa da ido ya nuna mata bowl ɗin kana ya nuna mata hannunsa
Kai ta gyaɗa hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa ne sukayi nasaran zubo mata akan kuncinsa.
Manyan idanunsa dake kanta ya lumshe alamar ke nake sauraro.
Ahankali ta ɗan matsa ta miƙa masa.
Karɓa yayi ya fara sha still hankalinsa na kan System ɗin sa wanda bisa duk kan alamu saƙo mai muhimmanci yake turawa.
Neenah kam kanta na ƙasa sai hawaye dake cigaba da zubo mata tun daga ranar da Malam Sa'idu ya hakke mata ta rabu da duk wani farin ciki da jin daɗi..
Anutse ya riƙa sha sai da yaji ya ishe da kafin ya mika mata bowl ɗin da faɗin.
”
Kai ta girgiza idanunta na tara ƙwalla tace.
“Um-um na ƙoshi”.
Haɗe fuska yayi tare da faɗin.
“Shanye nace”.
Lokaci ɗaya ƙwarjini da haibarsa ya cika mata ido jikinta na rawa ta zame ta zauna ƙasa.
Bai hanata ba jikinta na rawa takai spoon din bakinta tare da satan kallonsa gani tayi baki ɗaya hankalinsa na kan wayarsa ajiyar zuciya ta sauƙe ta cigaba dasha ahankali.
Baifi rabi tasha ba ta miƙe tare da nufar kitchen har taje ƙofa ta tsinkayo muryarsa na cewa.
“Kada ki kuskura ki ajiye sauran ki tabbatar kin shanye”.
Kai ta gyaɗa tare da ƙarasawa tsarerren kichen ɗin da yaji komai na more rayuwa tamkar da mace aciki ajikin sink ta tsaye ta shanye tasss dan sosai ya mata daɗi kana ta wanke bowl ɗin ta fito.
Kai tsaye bedroom ta nufa bayan ta fito.
“Waya baki izinin shiga?”.
Ta tsinkayo muryarsa mai cike da Izzah da ƙasaita.
Kafin ya sake furta komai ta isa gabansa ta durƙusa akan gwiwoyinta Allah ya sani tana masifar tsoronsa musamman idanunsa ta tsani ya tsareta dasu bare kuma yanzu ta sake zama so silent...
Anutse ya ajiye wayarsa tare da tsira mata ido na minti biyu zuwa uku kafin yace.
“Ya jikin ki”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa idanunta cike da hawaye tace.
“Da sauƙi”.
Numfashi ya fesar tare da tsira mata idanu kana yace.
“Ina yake miki ciwo yanzu?”.
Hawayen daya zubo mata ta sanya bayan hannu ta goge tare da cewa.
“Babu ko ina”.
“Kin tabbatar?babu inda ke Miki ciwo tako ina!?”.
Ya faɗa yana kawar da kai gefe.
Jinjina masa kai tayi tayi kana cike da kunya tace.
“Eh”.
Shirune ya wanzu na tsawon minti goma kafin ya ɗago kai anutse yace.
“Ki nada number Mahaifinki akan ki?”.
Kanta ta gyaɗa ganin kallon mamaki da take masa yasa yace.
“Ina so za muyi magana mai muhimmanci dashi akan karatun ki”.
Ya ƙare maganar yana miƙa mata wayarsa.
Kanta a ƙasa ta karɓi wayar kana ta saka masa number dearlin yayi amma cikin rashin Sa'a wannan Baturiyar tace Switch Off.
Numfashi ya fesar kana ya daidaita nutsuwarsa akanta tare da cewa.
“Ina kike son cigaba da karatunki?”.
Kallonsa tayi cikin rashin fahimta ta maimaita.
Ina kike son cigaba da karatu.
Aranta.
Ahankali ta ɗago kanta tare da cewa.
“Bangane me kake nufi ba”.
Ido ya tsira mata tare da cewa.
“Menene baki fahimta ba ko kuma dai Hausar ce bakya ji inyi miki da Babur,Barbarci ko Shuwa?”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Suma ban iya ba”.
Sai ga hawaye shar-shar-shar
“Ya Salam.
Ya furta asaman laɓɓansa ya lura abin kuka baya mata wuya cikin tsira mata idanu yace.
“Toh ki share hawayen ki sai nayi miki yanda zaki fahimta ki daina kuka”.
Har Kasan ransa yake jin tausayinta baya son ganin hawayenta na zuba.
Ba musu tashiga goge hawayen still wasu na fitowa.
Ƙasa ya sauƙa tare da zama dab da ita har kafaɗansa na gugan bata kana yace.
“Na yanke shawarar zaki cigaba da karatunki a abroad naso ace wayar Mahaifinki ya shiga muyi magana amma idan kika sake samun sauƙi zamuje tare sai inyi musu bayani tare da Maganar karatunki”.
Hawaye na zuba daga Idanunta tace.
“Ina so inga mahaifina Nasan zuwa yanzu yana cikin damuwa da tashin hankali”.
Numfashi ya fesar yace.
“Na sani kuma in Sha Allahu zan kai ki?,Amma yanzu wace ƙasa kike da sha'awar cigaba da karatu?”.
Saurin kallonsa tayi tana mamakin furucinsa Muryanta na rawa tace.
“Ko wanne ina so?”.
Kai ya Jinjina tare da faɗin.
“Ok zan miki Veazer sai ki tafi ƙasar Sudan acan zaki rubuta Private Weac sannan ki cigaba da jami'a domin kema hankalin ki zaifi kwanciya”.
Zare ido tayi cike da mamaki ta furta.
“Sudan!?”.
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Eh Sudan ko baiyi miki ba sai ki canza ƙasar da kike so?”
Ya ida maganar yana mai tsareta da ido.
Lumshe idanunta tayi kana ta buɗe su akansa sai kuma ta motsa laɓɓanta ahankali.
Kafin tace wani abu aka turo ƙofar falon atare suka kalli Ƙofar
Cike da tsananin mamaki Meerah ke kallon Neenah dake zaune gab da Sir Abdallah wani irin kallo take binta dashi me nuni da zallan kishi da ta tashin hankali cikin ɗaga sautin murya da hargagi ta mulmulo wani Uban ashar tare da cewa.
“Kutumar Uba!,wacce tsinanniya karuwa Ƴar dandi nake gani anan!?”.
Ware idanu Neenah tayi tare da juya bayanta sai kuma ta kalli Meerah dake wani irin huci atsiwace Neenah ke cigaba da kallon kayan dake jikin Meerah wanda marabansa da babu kaɗan kana cikin taɓe baki da yanayin sanyi tace.
“Nide ba tsinanniya bace!, Sannan ba ƴar dandi ba!, kuma ba karuwa ba!, sai dai kece karuwa!,dan ko shigarki beyi kama dana ƴaƴan musulmai ba bare kuma ace masu tarbiyya”.
Afusace Meerah ta nufi kanta tana wani irin huci tana isa kanta ta ɗaga hannu da niyyar yarfa mata mari azabure Neenah ta miƙe tsaye tana zazzare ido.
Sir Abdallah dake zaune yayi saurin miƙewa tare da riƙe hannunta kana ya yarfar yana bin ta da mugun kallo
Zazzafan ajiyar zuciya Neenah ta sauƙe tare da komawa bayan Sir Abdallah zuciyarta na bugawa da masifeffen ƙarfi.
Cike da Izzah da isa ya nuna mata ƙofa kana yace.
“Fita kada ki tada min hankali banza mara nutsuwa!”.
Meerah kuwa wani kallon tsana take bin Neenah dashi sam bata damu da kalamansa ba tace.
“Don uwarta waya bata daman shiga gonata me take a muhallina!?”.
Zare Idanu Neenah tayi tare da faɗin.
“Ni dai ba Uwata gaskiya,Muhalli kuwa ba sakarya irinki ke Mallakar wannan muhalli mai cike da kima da daraja ba”.
Afusace Meerah ta kalleta cikin jin zafin kalamanta ta ɗaga sautin murya tamkar zautacciya tace.
“Sai dai uwar wa!?”.
Kai tsaye Neenah ta saci kallon Sir Abdallah daya harɗe hannunsa a ƙirji kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta galla mata harara muryanta can kasan maƙoshi tace.
“Sai dai naki”.
Zare ido Meerah tayi tare da kukan kura ta nufi kanta cikin ƙaraji tace. “Lalle yau zanci Ubanki la'ada waje ƙaryar rashin kunya kike!”.
Cikin shammata ta fisgota tare da cukume wuyanta ta zabga mata Lafiyayyan mari.
Ihu Neenah ta ƙwalla tare da cukunkume rigar Sir Abdallah kana ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya tare da faɗin.
“Wayyo Allah na!, Wayyo Baba Idona!,ta makantar dani Wayyo Yah Abdallah idona bana kallo shikenan na zama makauniya”.
Atsorace ya cirota daga jikinsa kana ya tallafo fuskarta yashiga hura mata sanyayyar iskan bakinsa tare da cewa.
“Buɗe idonki In gani!?,Meyasa mu idon!?,”.
Ƙin tankasa tayi sai hawaye da idanunta ke tsiyayar wa afusace ya juya ya kalli Meerah dake jijjiga cike da takaicin Abinda tayi masa ya ɗaga hannu ya kifa mata mari da yasa taga giftawar taurari masu wutsiya cike da isa da Izzah yace.
“Ke wacce irin jahila da ƙiƙiyace!?kinsan wacece ita!?, kinsan lalurar dake damunta zaki ɗaga hannu ki daketa!?,toh wallahi idan wani abu ya sameta saina ɗaureki?”.
Hawayen dake kwaranya daga idanunta ta share cike da baƙin ciki da tsanar Neenah tace.
“My Prince Ni ka mara akan wannan figigiyar yarinya ƴar matsiyata karuwa kake kirana da jahila da ƙiƙiya wallahi saina zama ajalinta sai na salwantar da rayuwar ta!?”.
Ido ɗaya Neenah ta buɗe still hawaye na zubo mata sai kuma ta zato harcenta ta kaɗa kana arsiwa tace.
“Oho dai ai ido ba mudu bane amma yasan kima kuma dai kinsan ko makaho ne ya laluma tsakanina dake yasan karuwa!?,Sannan Ni babu wanda ya isa yayi ajalina sai Ubangijin daya busa min numfashi”.
Sir Abdallah kuwa kallonta kawai yake cike da mamaki tsiwarta ashe dai haka take abinda ya sameta ne yasa tayi sanyi don tunda abin ya faru ba tayi magana mai tsayi irin na yau ba.
Ihun data ƙwalla ne yasa yayi saurin kallon Meerah data shaƙeta tana ƙoƙarin kai mata duka.
Afusace ya ɗaga hannu ya kifa mata mari akaro na biyu kana yace.
“Fita min aɗaki tunda bana ki bane wallahi idan kika yiwa yarinyar nan lahani saina miki abinda bakya zato shashasha mara lissafi”.
Cikin zubda hawaye da baƙin kishi tace.
“Ni kake kora har kana zagina saboda wannan ƴar talakawan!?”
Cikin yanayin fusata da takaici yace.
“Ok bazaki fita ba kenan ko?”.
Cikin zubda hawaye tace.
“Wallahi saina faɗawa Mai martaba”.
Janye Neenah daga jikinsa yayi kana yace.
“Wallahi wa Rabbul ka'aba idan kika yarda wannan maganar takai kunnen mai martaba sai kinji kin tsani rayuwar ki sai na Miki abinda bakya zato”.
Da gudu ta juya ta fita tana wani irin kuka me gunji tasan zai aikata duk abinda ya faɗa.
Tsaki yaja tare da bin bayanta yasawa kofar key shaf mancewa yayi bayan fitar Mama Asabe bai sawa ƙofar key ba har tasamu damar shiga tayi masa hauka...
Sum-sum Neenah tabi bayansa tare da nufar bedroom ɗin da take a corridor da zai sadata da bedroom ɗin ta tsaya cak.
“Dawo nan”.
Muryarsa da babu wasa ya ratsa dodon kunnenta.
Kanta aƙasa ta dawo ta zauna kusa da ƙafarsa bata yarda ta kallesa ba.
Ido ya tsira mata babu walwala atare dashi yace.
“Baki da kunya ko!?”.
Saurin kallonsa tayi cikin tura baki tace.
“Um-um me nayi”.
Ware idanunsa yayi sai kuma ya ɓata fuska tare da faɗin.
“Shin Meerah sa'arki ce da zaki yi mata rashin kunya!?”.
Amaimakon ta bashi amsa sai ta fashe da kuka hadda shesh-sheƙan.
Kallon mamaki ya mata tare da cewa.
“Kukan me kike min!?,Ko kuma saboda ban bari ta dake ki bane kika samu bakin yimin kukan banza!?”.
Cikin tura baki da rauni ta ɗan kallesa tare da cewa.
“Ba ita bace ta zagi Mamana ba bayan bata raye kuma tace min karuwa Ni dai wallahi ba karuwa bace”.
Baki ya taɓe kana yace.
“Rufe min baki,Matsiwaciya dana bari Meerah ta lilli saki sai kiyi kukan ne dalili?”.
Zare idanunta dake cike da ruwan hawaye tayi kana tace.
“Lallai kam Allah bata isa ba kawai taci darajar kane amma da sai na mata duka!?”.
Kallonta yayi sama da ƙasa tare da sakin murmushin da bai shirya ba lallai ma wannan yarinyar cikin tsare gida yace.
“Sannu Iliya ƴar mai ƙarfi”.
Ta gyara zamanta muryanta cike da rauni da kuma ɗan sakewa data fara tace.
“Nifa wallahi badan faɗa babu kyau ba yau da kaga kalata baka san kirarin da ake mana bako”.
Kai ya gyaɗa alamar eh.
Ta gyara zamanta har jikinta na gugan Gwiwoyinsa tace.
“Hmmm Dija ƙaya bakisan na gida ba duk inda mai suna Khadijah take to bata ɗaukar raini sannan ƙarfi ne das'mu”.
Murmushi yayi wanda ya ƙara ƙawata kyawun fuskarsa sosai ta bashi dariya amma baiyi ba cikin tsare gida yace.
“Oya jeki shirya minti goma na baki ki fito saura kuma ki tsaya shirme”.
Kai ta gyaɗa kana ta tura baki tare da miƙe wa.
Da kallo yabi bayanta kafin ya sauƙe ajiyar ya lumshe idanunsa dai-dai lokacin da wayarsa ya hau ruri ahankali ya duba ganin sunan Gimbiya Fa'izah na yawo a screen ɗin yasa yaja siririn tsaki tare da kawar da kansa gefe yasan ba zai wuce kan maganar Meerah bace.
Neenah kuwa tana shiga bedroom din kai tsaye toilet ta wuce ta watsa ruwa kana ta fito ɗaure da towel ɗinsa da tsawonsa yakai gwiwarta gaban dressing mirrow ta zauna tare da buɗe mayukansa masu daɗin ƙamshi ta shafa tulin body spray dinsa ta ɗauka ta riƙa fesawa tana lumshe idanunta yayin da take sakin murmushi akai-akai wani kwalban turare mai masifar kyau da tsari na Company _A.A Zaman_ ta sauƙe idanunta akai wanda ta taɓa kallo a wani Indian film sak banu abinda ya rabasu miƙewa tayi tare da lumshe idanunta ta riƙa fesawa kamar yanda jarumar cikin Film ɗin keyi tana juyawa.
Ahankali Sir Abdallah ya harɗe hannunsa aƙirji tare da jingina bayansa da jikin ƙofa yana kallon ikon Allah ganin abin nata bamai ƙarewa bane yasa shi Faɗin.
“To ajiye min turare tunda suma bada na aro suke ba kuma ki tabbata saina zaneki adadin ƙamshin da kika yimin asarsa”.
Cak ta tsaya Tamkar gunki yayin da gaba ɗaya ilahirin jikinta ya hau rawa cikin tsananin tsoro ta juya zata gudu santsin ruwan ya jata baya yayi luuu yayi saurin sanya tafin hannunsa ya taro ta jikinsa tare da kawar da ido atsorace ta kulle idanunta gam yayin da jikinta ya hau ɓari.
Shikam kallo ɗaya ya mata nan yaga yanda gashin idanunta suka kwanta luf-luf sunji dam shin ruwa yayin da cikin minti ɗaya ya ƙare mata kallo.
Kuka ta fashe dashi tare da cewa.
“Dan girman Allah kayi haƙuri bazan sake ba”.
Gira ya ɗage muryarsa can ƙasan maƙoshi ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Minti nawa na baki!?”.
Still Idanunta na lumshe suna tsiyayar da hawaye tace.
“Ayyah Yayana na tuba dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba”.
Ya tsansa ya buga abakinta kana kana yace.
“Baki bani amsar tambayar dana yi miki ba”.
Ahankali ta dafe bakinta tare da turasa gaba cikin shagwaɓa da tsoro tace.
“Goma”.
Tana ƙoƙarin gyara daurin towel ɗinta dake ƙoƙarin sin cewa yayin da take mutsu-mutsun janye jikinta daga nasa jin yanda baki ɗaya tsikan jikinta ke tashi.
Kallon yanayin ta yayi yana ayyana abubuwa da dama akanta kafin ahankali ya janye ta daga jikinsa kana yace.
“Minti ɗaya na baki kisa kayan ki ki fito.
Cikin sanyin murya da kunya tace.
“Toh ka fita insa kayana”.
Saurin kallonta yayi babu walwala atare dashi yace.
“Aɗauri kashi ko aɓata igiya ke har kin kai wata macece common wuce ki shirya”
Juyawa tayi ta bar wajen Trolley daya mata Order kaya ta buɗe ta dauko Italy Abaya maroon me adon duwatsu daga sama yayin da ƙasan ke ɗauke da manyan flowers kallonsa tayi yana tsaye inda yake baki ta tura kana ta zira rigar tare da janye towel din.
Wani boxes na mata mai kyau ta sanya kana ta yane kanta da veil ɗin ajiyar zuciya ya sauƙe sosai rigar ya mata kyau kallon ƙirjinta yayi kana ya kawar da kansa gefe tare da buɗesu ahankali ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Ina wannan abin naku da kuke sawa?”.
Kallonsa tayi kana ta kalli jikinta tcikin rashin fahimta tace.
“Wani abu”.
Sumar kansa ya shafa tare da cewa.
“Is ok muje kawai”.
Kai ta gyaɗa tare da yin gaba shi kuma ya biyi bayanta zuciyarta cike da tsoro da kuma fargaban ko mawa gida yayin da wani sashen ya ci ka da farin cikin zata koma gida ta haɗu da Indunta da Maryam da Kuma Baba.
Tsayawa tayi tana wasa da yatsun hannunta tace.
“Ina Mama Asabe ba kada in tafi ba muyi sallama ba”.
Batare daya tsaya ba yace.
“Bata kusa”.
Ya ƙare maganar yana fita. Bayansa tabi.
Suna fita farfajiyar gidan tashiga gaban motar yayin da Ma'aikata da masu tsawon ƙofar keta kwasan gaisuwa da kallo tabi haraban gidan sosai ya mata kyau ashe duk yanda ake bada labarin gidan Sarki ya wuce tunani sai yanzu data gani da idonta ta tabbatar.
Anutse ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key kana ya danna Hong cikin sauri fadawa suka buɗe masa tangamemen gate ɗin ya cinna hancin motarsa waje tare da daidaitawa akan Kwaltan
Ganin ya ɗauki hanyar Borno road yasa tayi saurin kallonsa muryanta na rawa tace.
“Yah Abdallah ina za muje!?ba gida zaka kai niba!?”.
Wani kallo ya watsa mata kafin yace.
“Sayar dake zanyi”.
Zare ido tayi kafin ta kife kanta atsakanin cinyoyinta ta fashe da kuka.
Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da driving ɗin sa har suka shiga Buratai tana kuka agidan mai ya tsaya tare da saka faceMaks dinsa kasancewar baison hayaniya kana aka zuba masa.
Lokaci ɗaya Neenah da bacci ya fara ɗaukarta zuciyarta ya fara tashi cikin sauri ta buɗe idanunta tare da ƙaƙarin amai kallonta yayi tare da faɗin.
“Lafiya!?”.
Idanunta dake cike da ruwan hawaye ta lumshe kana tace.
“Amai zanyi”.
Baice komai ba ya buɗe mata murfin motar da gudu ta fita can gefe inda ba mutane ta tsugunna ta dinga kela amai duk friut Salad data Sha sai data amayar kafin ta ɗago kanta ahankali Swan water ya miƙa mata ta karɓa ta wanke bakinta da fuskarta.
Ahankali ya ɗagota tare da riƙe hannunta acikin nasa suka nufi mota key ya yiwa motar tare da cewa.
“Ƴar ƙauye kawai daga tafiyar minti kaɗan zaki yiwa mutane amai dama ki haɗiye abinki ko kina ji dan wannan hanyar ba kyau bane dashi kika yi sake kuwa sai dai ki zama ƴar aiken boko Haram”.
Zare ido tayi tare da riƙe hannunsa tace.
“Allah bazan yiba”.
Kai ya gyaɗa kana ya cigaba da driving ɗinsa sosai sukayi tafiya tare da wuce ƙauyuka da dama wasu ba mutane Boko Haram sun Kora wasu kuma duk akone cikin awa biyu da rabi suka shiga Maiduguri kasancewar ta Dambuwa suka bi.
Kai tsaye inda za ayi mata password suka nufi cikin wasu awanni ya gama yi mata duk abinda ya kamata tare da cewa nan da wasu kwanaki zata samu vearzer.
Ba ɓata lokaci suka ɗauko hanya yamma liƙis suka shigo cikin Biu zuwa lokacin jikinta yayi lugus abinka da wacce bata saba tafiya ba duk tayi zuru-zuru da ita ƙafafunta sun kumbura.
Kai tsaye Unguwar su ya nufa har kusan ƙofar gidansu tana masa kwatance suna isa yayi parking lokacin har anshiga sallar Maghriba.
Anutse ya kalleta tare da cewa.
“In sha Allah nan da wasu kwanaki Vearzer ki zai fito zaki tafi Sudan acan zaki rubuta Private Weac/Neco ki kafin ki cigaba da karatu akwai Aunty na zaki zauna agidanta idan lokacin tafiyar ku yayi zan faɗa miki duk abinda ya kamata da kuma ma wanda zakiyi amma dole saina sanar da Baba sannan in bashi haƙuri akan abinda ya faru”.
Kallonsa kawai take tabbas ya cika ɗan halak sai dai sam bata tunanin zata iya zuwa wani ƙasa yin karatun tafi so tayi karatu aƙasarta na gado.
Muryarsa ya katseta cikin sauri ta kallesa jin yana cewa.
“Ki kula da kanki nayi alƙawarin In sha Allah za kiyi karatu mai zurfi domin cikon burinki sannan ki temaki na ƙasa dake”.
Hawaye ne suka zubo mata kai ya girgiza tare da faɗin.
“Yanzu ba lokacin kuka bane!?, Lokacine da zaki maida hankali akan abinda kika sa gaba sannan ki cire damuwa aranki!”.
Kai ta gyaɗa cikin sanyi murya mai cike da tarin nutsuwa yace.
“Me kike burin karanta?".
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Ka zaɓa min ko wani abu”.
Numfashi ya fesar tare da tsirawa glass ɗin motar idanu kana yace.
“No wannan Choice ɗin kine ki zaba da kanki”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa tare da cewa.
“Ka zaɓa min duk abinda kake ganin ya dace”.
Kansa ya jingina da jikin Kujerar motar tare da lumshe idanunsa alamar tunanin kusan minti uku kafin ya kalleta kana yace .
“Na zaba miki Law”.
Saurin kallonsa tayi tare da maimaita.
“Law?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh,Nan da wasu kwanaki zanyi Birthday awajen Birthday zan haɗa ki da Aunty na da Zaki zauna awajenta akwai waya awajen ki!?”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“A'a.
Shiru yayi sai kuma yace.
“Ok gobe idan kinje makaranta ki sameni a office".
Kai ta gyaɗa yayin da hawaye ya wanke mata fuska lokaci ɗaya abinda ya faru ya dawo Mata sabo da sauri ta buɗe murfin motar ta fita tare da kife kanta da jikin motar ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya.
Ahankali ya buɗe murfin motar ya fito tare da zagayawa gefen da take tsaye kallon Unguwar yayi ganin babu hayaniyar mutane yasa ya janyota jikinsa ya rungumeta kanta ya manna a faffaɗan ƙirjinsa.
Yayin data sanya hannu ta zagaye ƙugunsa cikin sanyin murya da tausayawa yace.
“Ki daina kuka nayi alƙawarin bin hakkin ki nayi alƙawarin bazan taɓa bari kima da mutuncinki ya tafi abanza ba sannan kiyi ƙoƙarin ɓoye min wannan sirrin kada ki bari kowa yaji”.
Kai ta gyaɗa still hawaye na zuba daga idanunta wani irin zafi zuciyarta keyi sake manna kanta tayi shi kuma yana bubbuga bayanta.
Alamar rarrashi yayin da yake jin zafi da ɗacin zuban hawayenta.
Cikin tsananin kaɗuwa gami da matsanancin tashin hankali mai gauraye mamaki Baba daya fito daga masallaci lokaci ɗaya jikinsa ya hau rawa cikin tsananin kaɗuwa da tashin hankali yake kallonta muryarsa cike da rauni da tarin ɗimuwa ya daga murya tare da faɗin.
“Kyauta!”...
_Sawun Giwa na kuɗine 500 hundred zaki tura ta wannan account number 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number *** tare da tura shedar biya ta wannan number ***_
_@Follow me on Arewabooks Realeshaa_
_@Follow me On Wattpad Realeshaa_
_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafarta masa zunubansu ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani._
_Ayi Shearing saboda Allah Ƴan Uwa masoya da abokan arziki_.
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
***
***
*ESHAA CE*🤙🏻