16
by @realeshaa
*SAWUN GIWA*
_Ya take na Raƙumi_
_By_
*Aishatu Abdullahi Idris*
_REAL ESHAA_
*F-R-PG 16*
Kasancewar tsakanin su da rata yasa sam bata tsinkayo muryarsa ba Hasalima bata yi zaton jin sautin muryarsa ba a irin wannan lokacin kasancewar koda ya idar da sallar maghariba ya kan zauna acikin masallacin har sai anyi Isha'i kafin ya fito...
Sanyayyar ajiyar zuciya gami da samun nutsuwa Baba ya sauƙe tare da kallon Malam Sallau dake gefensa cike da dattako da kuma samun sassauci azuciyarsa yace.
“Ka gani ko Malam Sallau na faɗa maka cewa sam wannan ba Kyauta bace amma sai da ka fito dani ina addu'oi ina nafi kowa sanin irin tarbiyyar dana bawa Kyauta!ba farayi nake ba,da itace da tuni ta juya dana kirata itama wannan ina yini addu'a shiriya tare da sauran ƴaƴan Musulmai”.
Cike da mamaki Malam Sallau ke kallonsa kafin ya taɓe baki tare da faɗin.
“Haba!,haba!!,Malam Audu na tabbatar idanuna ba za suyi min ƙarya ba wallahi wannan ƴar kace Neenah da kake ikararin ta ɓata domin saida na tabbatar itace kafin na faɗa maka sannan idan har ba ƴar kaba ce me zaisa su tsaya kofar gidan ka ko kuma fentin gidan ka yafi na kowa ne! da zasu tsallake duk gidajen unguwanni suzo naka su tsaya?”.
Kai Baba ya girgiza cikin son tabbatar masa da gaskiyar cewa wannan ba ƴarsa bace ya nufi jikin motar ba tare daya tanka saba yayin da zuciyarsa ke wani irin bugawa da masifeffen ƙarfi har zuwa wannan lokacin Neenah na rungume jikin Sir Abdallah yana bubbuga bayanta.
Ahankali Neenah ta janye jikinta daga nasa amma still hannunta na riƙe anasa cikin muryan kuka tace.
“Nagode Sir Ubangiji Allah ya saka maka da mafificin Alkhairi ka taimake ni alokacin da nake tsananin buƙatar temako bazan manta da Alkhairin ka agareni ba”.
“Kanta ya shafa tare da sakar mata da lallausan murmushi kana yace.
“Ki daina yimin godiya duk abinda nayi na miki ne saboda Allah bayan haka ina daraja duk wata ɗiya mace domin mata abin girmamawa ne”.
Ya ida maganar yana share hawayen dake kwaranya daga idanunta.
Kai ta Jinjina tana jin sassauci aƙasan zuciyarta ahankali ta furta.
“Zan tafi ka gaishe da Mama Asabe kace ina matuƙar godiya abisa Alkhairinta agareni”.
“Ok,Ki riƙe sirrinmu kada kiyi yunƙurin sanar da kowa abinda ya faru dake domin sirrine mai girma atare damu kiyi min alƙawari komai zai faru babu wanda zaiji”.
Lumshe idanunta tayi cikin sanyi da rauni tace.
“In sha Allahu babu wanda zai ji koda mahaifina ne nayi maka alƙawari”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Ok muje ko?”.
Saurin kallonsa tayi bakinta na rawa tace.
“Ina?”.
Kai tsaye yace.
“Gida sai nayi musu bayanin abinda ya faru”.
Zare idanu tayi lokaci ɗaya jikinta ya ɗauki rawa tuno Mamawo da tayi cikin zubda hawaye tace.
“A'a ba sai ka shiga ba idan har Mamawo taji abinda ya faru wallahi na shiga Uku! Kasheni zatayi”.
“Shittttttt”.
Ya faɗa yana ɗaura ya tsarsa akan lips ɗinsa...
Shiru tayi hawaye na taruwa akwarmin idanunta.
Numfashi ya fesar kafin ya lumshe Idanunsa kana ya buɗe su a kanta yace.
“Tsawon kwanaki takwas bakya gida idan har ba muje tare nayi musu bayani ba zasu iya zargan wani abu ko kuma ayi miki wata mummunan fassara wanda hakan bazai min daɗi ba,Koda namiji ne ya ɗebi irin wannan tsawon lokacin baya gida idan ta koma dole za'a zargesa bare kuma mace”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da cewa.
“A'a nasan ta hanyar da zan fahimtar dasu amma dan Allah kada ka shiga”.
Numfashi ya fesar kana yace.
“Bana zaton bayanin ki zai gamsar dasu yana da kyau ace nayi musu cikekken bayani batare dana faɗa musu ainihin abinda ya faru ba”.
Kuka ta fashe dashi hadda shesh-sheƙa cikin rawan murya da tarin tsoro tace.
“Ni dai dan Allah kada ka shiga wallahi tsoro nake ji”.
Hannu ya sanya tare da share mata hawayen kana ya janyo hannunta na dama tare da bata feck cikin sauri ta lumshe idanunta jin wani irin yanayi atare da ita.
Yatsun hannunta ya riƙe yana kallon Zoben azurfan da yayi masifar amsar yatsanta ahankali ya furta.
“A ina kika samu wannan zoben?”.
Idanunta alumshe jin yanda yake matsa hannunta tace.
“Babane ya bani”.
Kai ya gyaɗa yana cigaba da murza zoben hannunta.
Numfashi ta fesar tare da janye jikinta daga nasa kana ta cire hannunta ahankali tace.
“Nagode da Alkhairinka agareni Yaya Ubangji ya yalwata duniyarka da farin ciki”.
Batare data jira jin abinda zaice ba ta juya ta nufi gida tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki yayin da zuciyarta ya ci-gaba da bugawa da masifeffen ƙarfi fiye da ko yaushe haka nan ta tsinci kanta cikin mummunan tsinkewar zuciya da faɗuwar gaba.
Numfashi ya fesar har ta shiga ciki kafin ya buɗe motar ya shiga yana jin wani iri atare dashi...
Baba kuwa mutuwar tsaye yayi tun sa'ilin da yayi arba da fuskarta duk wata gaɓa da magudanan jinin jikinsa ya tsaya idanunsa sun kasa yarda da abinda suka gani ji yake tamkar yanace ta yane masa idanu baya kallo ko kuma mafarki yake sam zuciyarsa ta kasa yarda Neenah ce yayin da idanunsa ke tabbatar masa da cewa tabbas itace...
Jiri ne ya ɗibesa yayi taga-taga zai faɗi cikin sauri Malam Sallau ya tare sa tare da faɗin.
“Kaga abinda nake faɗa maka ko Malam Audu? ƴarka maza take bi ko ince yawon karuwanci ta tafi amma alokacin kaƙi jin Maganata,Shawarar da zan baka yanzu tun kafin ta jawo maka abin kunya ka aurar da ita idan acikin abokanan sheɗan cin nata akwai mai aurenta In ba haka ba fita Masallaci ma sai ya gagareka”.
Kallonsa kawai Baba keyi batare da iya tanka saba ya janye jikinsa kana
Cikin ficewar hayyaci ya nufi gida batare daya sake furta koda kalma ɗaya ba.
Neenah kuwa cikin tsananin tsinkewar zuciya da masifeffen tsoro ta tura jemem'men ƙauren langa-langa kana ta sanya ƙafarta na dama tare da furta.
_“Bismillahi walajna,Wa Bismillahi kharajna,Wal'alallahi rabbina tawakallalna”_.
Kana tashiga tana mai dafe saitin ƙahon zuciyarta.
Mamawo da ta fito daga banɗaki hannunta riƙe da buta da tochlight ta tsaya cak tare da tsira mata ido kafin tace.
“Sannu da zuwa Baiwar Allah wa kike nema!?”.
Kai Neenah ta girgiza tare da nufar inda take atsorace taja baya tare da faɗin.
“Lafiya wa kike nema?, Watanin kiyi haƙuri dan Darajar Muhammada Rasulullahi kada kiyi Kidmashin ɗina (Kidnapped) bamu da komai acikin gidan nan sai ƙarago(Ƙuli-ƙuli)mai suga da kamu sai bushesh-shen gauta”.
Da kyar Neenah ta aro jarumta tare da cewa.
“Nice fa Mamawo”.
Zare ido Mamawo tayi duk da kuwa taso gane Muryanta amma bata yarda ita bace da mamaki ta sake kallon ta kafin tace.
“Kece wa!? Watanin banji da kyauba,Nace kece wa?”.
Ta haɗiye wani yawu mai masifar ɗaci tare da faɗin.
“Neenah”.
Sake butar Mamawo tayi tare da cewa.
_“Laha’ila ha'illallahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama_, Neenah kece wannan!? Watanin bariki tayi amfani kinga ma yawon ta zubar ɗin kenan kin dawo!?,Ina Malam yazo yaga abin da na daɗe ina faɗa masa yayi burus dani”.
Akuma dai-dai lokacin Baba ya shigo kallonsa Mamawo tayi tare da faɗin.
“Malam zoka ga ikon Allah Watanin yau dai Neenah ta dawo da kanta toh Allah ya rabamu da abin kunya”.
Kai kawai ya iya gyaɗa mata tare da faɗin.
“Ta kyauta”.
Sheƙeƙe Mamawo ke kallonsa kafin ta gyara ɗaurin zaninta da faɗin.
“Au ta kyauta ma zaka ce?,Watanin kaga Ainihin yanda fatar ta murje tayi luwai alamar ta saba da maza”.
Shiru Baba yayi batare daya tanka taba ya kalli Neenah dake durkushe akan gwiwoyinta murya can ƙasan maƙoshi yace.
“Ki sameni aɗaki”.
Cikin sauri ta gyaɗa kai tare da miƙewa yayin da zuciyarta ke cigaba da bugawa da kaso Cassa'in cikin ɗari.
Sheƙeƙe Mamawo tabi bayanta da kallo kafin taja tsaki Mai sautin gaske kana tace.
“Kin dai ji kunya Karuwar banza in Sha Allahu sai kin wulaƙanta alade da karnuka ma sai sunfi ki daraja!karuwar banza ƴar dandi”.
Cikin sassarfa Neenah ta ida shiga ɗakin bakinta dauke da sallama kana ta durƙusa agefen yar yalolon katifar da yake zaune akai.
Muryarta cike da rauni tace.
“Baba gani!,Baba!!Baba!!!”.
Sai da tayi baki uku kafin ahankali ya ɗago kansa tare da cewa.
“Daga ina kike duk tsawon wannan kwanaki!?”.
Kallonsa tayi sai taga ya tsirawa silink idanu hawayen dake ƙoƙarin zubowa tayi saurin mayarwa kana tace.
“Baba labarin yana da tsayi domin abubuwa marasa daɗi...”.
Cikin sauri ya ɗaga mata hannu tare da buga mata wata razananniyar tsawa da bata taɓa jin yayi wa wani mahaluki irinsa ba bare kuma ita kana yace.
“Ba wannan na tambayeki ba so nake ki faɗa min daga ina kike?”.
Atsorace ta kallesa jin tsawan daya buga mata Muryanta na rawa tace.
“Malamin mune ya temakeni,”.
Da wani irin fushi da tafarfasan zuciya yace.
“Wanene wannan mutumin daya ajiyeki A mota har kika rungumesa atsakiyar titi??”.
Atsorace ta kallesa akaro na biyu bakinta na rawa tace.
“Temakona yayi Baba badan shiba da yanzu bana raye shine mutumin daya”...
Azabure ta dafe kuncinta yayin da hawaye masu masifar zafi suka kwafce mata kana wani Abu Mai nauyi ya toshe mata Maƙoshi sakamaon marin daya zuba mata.
Cikin ƙaraji da tsananin ɓacin rai yace.
“Yaushe kika koyi ƙarya Neenah?”.
Saurin girgiza Masa kai tayi bakinta na rawa tace.
“Wallahi,Wallahi,Wallahi ba ƙarya nake yi maka ba Baba Kawu Saidu shine wanda ya cutar da rayuwata!shine yake neman ruguza min farin ciki”.
Cikin wata razananniyar tsawa me firgitarwa ya zuba mata ido tare da faɗin.
“Karya kike ke makaryaciya shin yaushe kika zama makaryaci Kuma fasiƙa!?”
Kai take girgiza still hawaye na kwaranya daga idanunta amma ta gaza furta koda kalma ɗaya.
Murmushi me ciwo yayi kana ya cigaba da cewa. “Koda yake ba laifinki bane dan kinyi rantsuwa akan ƙarya dama duk wani mazinaci makaryaci ne kuma fajiri”.
Kukan da take ƙoƙarin riƙewa ne yayi nasaran kwace mata cikin tsananin tashin hankali kana murya na rawa tace.
“Wallahi ni ba mazinaciya bace ban taɓa aikata zinaba”.
Afusace ya miƙe ya fita har yana take mata ƙafa kichen ya shiga zuciyarsa na wani irin zafi.
Da sauri mamawo dake rakuɓe ta miƙe ta,tare sa cikin sassauta murya tace.
“Malam lafiya me zaka yi da Injin Belt?”.
Cikin matsanancin baƙin ciki da karyewar zuciya kana da rauni yace.
“Rabu dani Saude Ni Kyauta zata tozarta!?, Ni takeson wulaƙantawa a idon duniya wallahi gwara in kasheta in huta!da wannan baƙin cikin da zata sanyani a idanun duniya”.
Ya ida maganar tare da shiga ɗakin batare da tunanin komai ba ya ɗaga Injin Belt ya shauɗa mata agadon bayanta wani azabebben ihu mai cike da rauni da rashin madafa ta saki tare da rintse idanunta cike da baƙin ciki ya ɗaga Injin Belt ɗin ya cigaba da dukanta tako ina ajikinta tsaban azaba da rauni kasa kukan fili Neenah tayi ta koma na zuci...
Da gudu Maryam dake Sallah ta fito bayan ta sallame rungume Neenah tayi cikin tsananin tashin hankali tace.
“Dan Allah Baba ka daina du kanta amaimakon kayi farin ciki da dawowarta sai ka hau du kanta!”.
Mamawo dake kallon ikon Allah ta saki murmushi kafin tace.
“Toh nima dai abinda na gani kenan Maryama yau kyauta guda ake duka Kyautafa wohoho Lallai Alwalar kifi ta karye”.
Banza ya musu tare da ficewa daga gidan zuciyarsa na ƙuna.
Zama yayi adakalin ƙofar gida kalaman Malam Sallau nayi masa suwwa adodon kunne ƙirjinsa dake zafi ya dafe dole yasan abun yi...
Maryam kuwa cike da tausaya wa ta ɗago Neenah tare da riƙe hannunta suka shiga ɗaki tana rarrashin ta kamar za tayi kuka tace.
“Dan Allah Sister Neenah kiyi shiru ki daina kuka ki cigaba da addu'a Allah yana tare da mai gaskiya”.
Ahankali ta ɗago idanunta da suka kumbura sukayi luhu-luhu dasu saboda kuka kana tace.
“Maryama Baba yaƙi saurarona,yaƙi ya bani dama inyi masa bayani, Wallahi ban aikata abin da ake zargina dashi ba ban aikata,Ban aikata ba”.
Kife kanta tayi atsakanin tafin hannunta tare da cigaba da cewa.
“Baba ya kasa fahimtar damuwata Sister Maryama ina cikin tashin hankali rayuwata bata da wani amfani ji nake kamar in mutu in huta da wannan rayuwar mai cike da ƙalubale”.
Cikin sauri Maryam ta rufe mata baki tare da cewa.
“Kiyi shiru kada kiyi saɓo ki riƙa maimaita kalmar _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun_ za kiji sassauci azuciyarki”.
Kai kawai ta gyaɗa Allah ne kaɗai yasan zafi da raɗaɗin da take ji azuciyarta.
**
Kallon Indu Imraan yayi babu walwala atare dashi yace.
“Kada ki bari In sake maimaita maganata”.
Kwaɓe fuska Indu tayi tare da kallon Ummu dake murmushi tace.
“Ayyah Ummu kice ya bari sai anjima zan tafi dubi fa duka² karfe 8:00am ne yaushe ma garin ya waye kuma fa ina son zuwa school”.
Harara ya galla mata kana yace.
“Yaushe na fara Wasa da ke Ina ce tun jiya nace ki shirya ki koma kafin na dawo aiki,Amma dana kira Lateefa take sheda min cewa baki koma ba muddin Baki so mu samu matsala ki tashi ki shirya”.
Cike da dattako Ummu ta kalli Zonbi dake murmushi tace.
“Maza tashi ki ɗauko mata hijabinta su tafi”.
Ashagwabe Indu ta fashe da kukan sangarta kana tace.
“Ayyah Ummu idan na tafi waye zai ta yaki hira”.
Dariya Ummu tayi kana tace.
“Ga Munah sannan ga Zonbi dama can ba tare muke dake ba”.
Baki ta tura tare da karɓan Hijabinta da Zonbi ke miƙa mata kana tace.
“Ai Aunty Munah gobe zata tafi itama Aunty Zonbi ba mai zama bace”.
Kallonta ta mayar kan Imraan dake kaɗa key mota kana ta furta.
“Yah Imraan mu tafi tunda dai korata Ummu keyi dama can Kaine nawa dama neman gwaninta ne yasa nace zan zauna”.
Murmushi yayi kana ya riƙe tafin hannunta tare da cewa.
“Yawwa Autanmu”.
Dariya Zonbi tayi cike da tsokana tace.
“To shalelen Yah Imraan agaishe da Aunty Lateefa”.
Hararanta Indu tayi kana tace.
“Baza afaɗa ba idan kina so kije da kanki”.
Ranƙwashinta Imraan yayi tare da cewa.
“Auntyki kike mayarwa magana”.
Saurin kallonsa Zonbi tayi ido ɗaya ya kashe mata.
Cikin sauri Ummu ta kawar da kanta Indu kuwa dariya ta fashe dashi tare da cewa.
“Abin ɓoye zai fito fili”.
Ƙeyarta ya talle fa tare da ranƙwashinta.
Baki ta tura kana ta fice yana biye da ita.
Zonbi kuwa wani irin farin ciki ne ya ratsa zuciyarta wanda har sai da Ummu ta fahimta...
Ajiyar zuciya Indu ta sauƙe tare da kallon Imraan dake driving cikin yanayin damuwa tace.
“Yah Imraan na damu da Blue eyes jikina na bani kamar ba lafiya ba”.
Saurin kallonta yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa ta buga adake ya tsirawa titin idanu tare da faɗin.
“Kada ki damu In Sha Allahu tana cikin ƙoshin lafiya bari mu fara biyawa gidansu kafin ”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da faɗin.
“Toh Allah yasa gwara muje dai In kalleta zanfi samun nutsuwa”.
Kafin yace wani abu wayarsa ta ɗauki ruri picking yayi tare da mannawa akunnensa.
“Ok,Ok Sir amcoming”.
Ya faɗa tare da katse kiran.
Kallon Indu data zuba masa ido yayi tare da faɗin.
“Bazan samu biyawa ta can ba saboda ana nema na wajen aiki but zuwa dare zamuje”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Allah ya kaimu”.
A ƙofar gida ya ajiye ta kana ya wuce.
Anutse ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama aya mutse Lateefa ta kalleta cike da gadara tace.
“Sannu jarababbiya an sake dawowa atakura min ne toh bari kiji wallahi na wucewa sharrin ku duk wani munafurci da kini bibin ku atafin hannuna kuke dangin miji dangin jaraba”.
Azuciye Indu ta buɗe baki da niyyar magana sai kuma ta fasa ta wuce bedroom tare da banko ƙofar.
Sam ba zata kulata su zama ɗaya ba ta lura fitina take nema.
Ahankali Maryam ta shiga kitchen Bahon da suke kife kwanikan wanke-wanke ta stuguna ta ɗauki kwanon silba kana ta buɗe tukunyar dake ɗauke da ɗumame ta zuba musu kari uku(gundure).
Ledar dake ɗauke da gauta ta buɗe har sun fara ja ta ɗauki Uku.
Da sauri Mamawo ta tari gabanta babu walwala atare da ita tace.
“Ina Zaki kai wannan Uban Tuwon da kika ɗiba?”.
Kallon kwanan tuwon tayi kana ta kalli Mamawo data tsareta da ido kafin tace.
“Wannan ne uban ɗumame Mamawo duka-duka nawa yake?”.
Cikin zare mata idanu tace.
“Ke ki fita Idona zaki bani amsar tambayar dana miki ko kuma zaki tsaya yimin rashin kunya kamar yanda kika saba?”?.
Kai ta girgiza tare da cewa.
“Allah ya tsareni daga yi Miki rashin kunya,Tuwo kuma nida Sister Neenah ce”.
Wani banzan kallo ta watsa mata kafin ta wafce kwanon daga hannunta cike da masifa tace.
“Buhun Ubanki keda Neenah Ina dai da kunnenki kika ji, Watanin Uban dake riƙe da ita yace kada abata ko lomar abinci taje Karuwanta nata su Bata”.
Shiru Maryam tayi cike da takaici kana tace.
“Wannan wani irin abune fisabilillah taya Baba zaice kada abata abinci?,idan ba'a bata ba ina zata samu taci?”.
Cikin kumfar baki ta ɗage ka faɗa tare da faɗin.
“Data ɗauki kwanaki bata nan uban wa yake bata?kaji min muna furci!,Watanin Maryama idan zaki fita sabgar yarinyar gwara ki fita maza zauna muci”.
Kai ta girgiza tare da faɗin.
“A'a tunda baza ki bata ba nima bazan ciba”.
Bata jira cewarta ba ta wuce ɗaki.
Murmushi Neenah dake sanye cikin Uniform tayi idanunta cike da ruwan hawaye ta riƙe hannun Maryam kasancewar taji komai kana tace.
“Kada ki damu sisters Maryam bana jin yunwa”.
“Taya zakice bakya jin yunwa bayan ba kici komai ba gashi kuma zaki tafi makaranta”.
Murmushin ƙarfin hali Neenah tayi tare da faɗin.
“Allah dagaske bana jin yunwa na tafi”?
Bata jira cewarta ba ta fice tana share hawayen da suka kasa tsayawa afuskarta.
Ƙofar Mamawo ta nufa cike da ladabi tace.
“Mamawo na tafi”
Labulen Mamawo ta ɗaga tare da ƙare mata kallo tace.
“Watanin yau idan kika tafi sai yaushe zaki dawo?”.
Cikin rashin fahimta tace.
“Idan aka tashi”
Taɓe baki tayi tare da fadin.
“Watanin nayi zaton ko yauma sai kinje kin gama raba musu banɗashen gurasar zaki dawo ai wawuya jakar Maza inde maza zaki biyewa kin shiga uku”.
Cikin sassarfa ta miƙe ta fita zuciyarta na ƙuna wasu hawaye masu masifar zafi ne suka shiga bin kuncinta yayin da wani tsoro da fargaban haduwarta da Malam Saidu ya mamaye zuciyarta har ta biya kofar gidansu Indu zata shiga sai Kuma ta fasa ta wuce tuno irin cin mutuncin da Lateefa tayi mata.
Misalin goma da rabi na safe Baba na shirin fita Mamawo ta shiga ɗakin batare daya tanka taba ya ratsa ta zai wuce.
“Malam magana fa nazo muyi naga kuma kana ƙoƙarin wuceni ka fita”.
Ta faɗa cikin sanyi da ladabi.
Komawa yayi ya zauna tare da faɗin.
“Ina sauraren ki,maganar menene?ɗan sauri nake zanje Sarar ƙashi”.
Ɗan murmushi tayi tare da dai-daita nutsuwarta kana tace.
“Kasan ance ta tsuniyar gizo bata wuce na ƙoƙi,duk wani abu daya shafeka nima ya shafeni akan dai maganar Neenah ne”.
Sai kuma tayi shiru
Kai ya jinjina tare da faɗin.
“Ina sauraren ki”.
Cikin sassauta murya tace.
“Kayi haƙuri da abinda zan faɗa amma aganina ya kamata ka aurar da Neenah gudun abin kunya da zai je yazo Malam ina jiye maka ranar da wannan yarinyar zata ɗauko cikin shege ko shegiya akawo maka ka raina”.
Kallonsa tayi ganin ita yake kallo yasa ta sake sassauta murya ta cigaba da cewa.
“Bawai ina faɗar haka saboda bana son Neenah bane a'a, Watanin sai dai dan mu samu maslaha ga Yah Sa'idu yana sonta dagaske aganina gwara mu rufawa juna asiri ya Aureta tunda yaji ya gani”.
Shiru yayi na tsawon minti uku kafin ya sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.
“Saude duk abinda kike ganin ya dace akai toh kiyi na baki dama”.
Ta ɗan buɗe Idanunta tare da karkace kunnunwanta kana tace.
“Ban fahimci me kake nufi ba Malam”.
Kallonta yayi kamar bazai ce komai ba sai.kuma yace.
“Ina nufin kiyi duk abinda ya dace kawai”.
Ya ida maganar tare da ficewa.
Wani miskilin murmushi tayi tare da ciro wayarta Number Malam Sa'idu ta kira amma har ya gama ringing sa bai ɗauka ba tsaki tayi tare da ajiye wa ta cigaba da sabgoginta yayin da ƙasan zuciyarta ke cike da farin ciki zata tura Neenah ta rabu da ƙaya cikin sauri ta gama aikinta tashiga gidan Uwani ƙawarta dan bata labari...
Acan ɓangaren Sir Abdallah kuwa Anutse ya fito daga sashensa Security dake tsaye yayi saurin risinawa tare da faɗin.
“Barka da Safiya Ranka ya daɗe”.
Cikin yanayin sa kamar ko yaushe yace.
“Barka dai”.
Anutse ya nufi sashe Ammie cikin wata bugaggiyar Gezner sky blue yayin da ƙafarsa ke sanye cikin wata baƙar halcover na maza Mai masifar kyau kana kansa na sanye cikin baƙar hula Dara siririn sajensa shi ya sake ƙawata kyawun fuskarsa yayin da wani fitinennen ƙamshi mai sanya nutsuwa da shauƙi ke fita ajikinsa.
Bayi da kuyangi sai zubewa suke suna kwasar gaisuwa hannu yake ɗaga musu yayin da fuskarsa ke ɗaure kamar ko yaushe.
Tun kafin ya ida shiga ɗakin yake jin hayaniya da surutai yayin da hadimai ke ta faman kai komo Anutse ya Sanya tafin hannunsa dake ɗauke da wani zoben azurfa baƙi Mai masifar kyau ya murɗa handle ɗin ƙofar kana ya shiga.
Ware manyan idanunsa yayi fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi ganin wacce ke hakimce ya sanya sa cewa.
“Laaa-laaa wa nike gani kamar kamar dai?”.
Baki Matashiyar matar dake zaune cikin wani Rantsat-tsen Abaya Blueblack ta taɓe hannunta dake dauke da wasu manyan Bangols da zoben azurfa ta ɗago tare da gyara rufin mayafin Abaya tana Mai kawar da kai gefe.
Sir Abdallah kuwa lallausan murmushi ya saki tare da riƙe tafin hannunta kana ya zauna agefenta ƙoƙarin fisge hannunta take yayi Saurin damƙewa da ƙarfi yana cewa.
“Iyeeeee wato kinyi karfi har zaki ƙwace riƙon dana miki”.
Idanunta akan Ammie tace.
“Ammie ki cewa wannan yaron ya fita sabgata babu ruwansa dani”.
Ware manyan idanunsa yayi cike da zolaya yace.
“See me see this girl Woooo Wanene yaron”.
Mintsininsa tayi tare da cewa.
“Aini babu ruwana da kai tunda baka da kirki”.
Langwaɓar da kai yayi kana cikin sassauta murya ya lumshe Cat eyes ɗinsa tare da cewa.
“Allah ya huci zuciyar Auntyna shin lefin me nayi?”.
“Cikin kawar da kai tace.
“Tun yaushe nake faman kiran wayarka kaƙi ɗagawa sannan nace da Ammie tace ka kirani Amma still ka share saboda baka so inzo”.
Kansa ya langwaɓar tare da faɗin.
“Ya Salam kin san dai cewa babu wacce nake burin tazo wajen wannan taron nan irinki sannan sabgogine suka yimin yawa shiyasa amma kaina bisa wuya ayimin afuwa”.
“Jishi kamar gaske zaiyi min daɗin baki”.
Ta faɗa tana hararansa.
Murmushin yayi kana yace.
“Kin san dai babu daɗin baki tsakanin mu kuma naga Birthday ma da sauran lokaci”.
“Toh koh in koma sai lokacin yayi nazo”.
Tayi maganar tana mai hararansa.
Murmushi yayi kana ya buɗe baki zai yi Magana Ammie data tsira musu ido cike da so ta tari numfashinsa ta hanyar cewa.
“Tashi kuje kuyi breakfast Dan na lura Mujadalarku baya ƙarewa kullum kuna nan kamar yara bayan haka kuma sai ka fita ba kaci komai ba”.
Dariya Gimbiya Aysha tayi tare da miƙewa hannunta na cikin nasa kana tace.
“Aikuwa dai Ammie kinsan har yanzu a yaro yake tunda yaƙi yin Aure”.
Baki ya taɓe tare da ja musu kujera suka zauna
Kana yace.
“Har yanzu banga wacce ta dace da tsarina bane”.
Miƙewa tayi ta koma bayansa kana ta sanya hannunta aka faɗarsa tace.
“Amma ai akwai ƴan matan dake masifar sonka ka bawa ɗaya daga cikinsu dama kuyi Aure”.
Baki ya taɓe tare da janyo Cup gabansa yace.
“Sam basu yimin ba domin basu da qualities da nake buƙata awajen mace ba Hasalima sauran badan Allah suke sona ba”.
Still hannunta na kafaɗarsa tace.
“Ga Gimbiya Khairat tana da wayewa,Ilimi,kyau,dukiya,Uwa uba mulki sannan tana masifar sonka ƙafanta biyu A Sudan tana zuwa wajena kuma duk akan kane”.
Ɓata fuska yayi ya tsiyayi tea kana ya kai bakinsa kafin ya kalleta da faɗin.
“Please dan Allah ki rabani da maganar wannan shashashar yarinyar”.
Zata sake magana Ammie ta ɗaga mata hannu alamar kada tace komai. Kai ta gyaɗa
Kana ta miƙe ta buɗe soyayyen cheaps ta zuba masa sai ɗayan wainar shin kafa da kuma perper soup ɗin kayan ciki ta turawa Sir Abdallah gabansa
Anutse ya kai hannunsa kan Cheaps ɗin akuma daidai lokacin wayarsa ta ɗauki ruri kallon screen ɗin wayar yayi ganin sunan Sir Auwal na yawo a screen ɗin yasa yayi picking.
Shiru yayi na tsawon minti biyu kafin cike da izzah ya motsa laɓɓansa tare da faɗin.
“Ok”.
Kana ya miƙe saurin kallonsa Gimbiya Aysha tayi cike da kulawa tace.
“Ina kuma zaka Auta ba tare daka karya ba?”.
Kallon Agogon diamond ɗin dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi kana yace.
“Akwai important meeting da zamu shiga yanzu kuma Ni kaɗai ake jira”.
Bai jira cewarta ba ya fice cikin sauri Ammie ta ƙwalawa ɗaya daga cikin Ma'aikatan kiran kana ta Umarceta data haɗa breakfast ta kai masa mota. Cikin gaggawa hadimar ta haɗa kana ta kai masa...
Kai Gimbiya Aysha ta girgiza cike da Izzah da kuma ƙasaita irin na jin sarauta ta motsa laɓɓanta ta kana tace.
“Wai Ammie har yanzu Autah bai daina wannan aikin wahalar ba?”.
Kallonta Ammie tayi tare da ajiye Cup din dake riƙe hannunta tace.
“Wani irin aikin wahala kuma Aysha?”.
Cikin taɓe baki tace.
“Wannan teaching ɗin da yake”
Sanyayyan murmushi Ammie ta sake tare da faɗin.
“Aysha kenan shi aikin temako da neman lada ai babu wahala acikinsa sai dai ɗumbin nasara,Lada da kuma tarin Alkhairi”.
Gauron numfashi ta fesar tana muskutawa tace.
“Hakane Ammie amma matsayinsa ya wuce wannan kada fa ki manta wanene shi a ƙasar nan da kuma faɗin Afrika baki ɗaya ina ganin idan har hakan yake so yana da wanda zai wakiltasu suyi hakan basai shi da kan sa ba”.
Ta fesar da numfashi tare da cigaba da cewa.
“Amma saboda wani dalili nashi mara tushe baki ɗaya ya rabu da ragamar aikinsa ya tsaya shirme”.
Fuska Ammie ta ɓata kana tace.
“Kinga Ni kuwa ina alfahari da wannan koyar da yake domin zai tai maki al'ummar garinsa da kuma ƙasarsa sannan zai sake fuskantar halin da talakawa ke ciki”.
Shiru tayi tare da cigaba da cin abincinta tasan komai zata faɗa Ammie ba zata yarda ba kamar yanda shima baya, yarda da maganar.
Canza hirar tayi ta hanyar cewa.
“Ammie wai ni ina wannan Bagashariyar matar?”.
Cikin rashin fahimta Ammie tace.
“Wa kenan?”.
Kai tsaye tace.
“Fa'iza da ƴar riƙon ta tunda nazo ban sanya su a ido ba”.
Cikin rashin walwala Ammie ta kalleta tare da faɗin.
“Hala ta fita dan duk safiya tana zuwa mugaisa yau kuma bata shigoba”.
Cike da isa da kuma ƙasaita tace.
“Shin bata san nazo bane? da bazata tayi min sannu da zuwa ba?, nifa wallahi yanda na tsani mutuwa ta haka na tsani in buɗe ido in gansu sam”...
Atausashe Ammie ta ɗaga mata hannu babu walwala atare da ita tace.
“Dakata!Aysha bana son rashin kunya ki iya kalaman ki ko Faiza ba taci darajar komai ba zata ci darajar Auren Mahaifin ki da take ina mamakin ƴaƴan miji da suke aibanta matan Ubansu toni bazan ɗauki wannan rashin tarbiyyan ba kinfi kowa sanin halina”.
Miƙewa Gimbiya Aysha tayi tare da barin wajen tamkar zata tashi sama sam Ammie bazata taɓa canzawa ba.
**
Wani baƙin dajine dake ɗauke da guntayen bishiyoyin tsamiya da kuma na kuka wanda duk tsawon su dai-dai yayin da bishiyar tumfafafiya ya masa ƙawanya daga can tsakiyarsu wata ƴar bukka ce dake kewaye da manya-manyan shuri guda huɗu wani irin shuɗiyar hayaƙi Mai masifar wari da ƙarni ne ke fita daga cikinsa baka jin sautin komai sai haushin karnika da kukan Jakuna...
Cike da bushewar Zuciya Gimbiya Faiza dake tsugunne kan ƙafarta na hagu ta kalli bokan cikin rashin tsoron Ubangiji da bushewar zuciya tace.
“Barakam-Barakam Liƙinƙiyas-kufur Munzo da buƙatar mu wajenka tare da yaƙinin zamu samu biyan buƙata”.
Cikin Wata razananniyar murya mai tarwatsa lissafi da firgitarwa yace.
“Nasan abinda ke tafe daku ba sai kun faɗa ba za'a biya muku buƙatar ku”.
Zare ido Meerah tayi cike da matsanancin tsoro lokaci ɗaya jikinta ya shiga ɓari tunda take bata taɓa zuwa irin wannan wajen ba..
Cikin ƙalƙyala dariya irin na matsafa yace.
“Tabbas buƙatar ku zata biya akan Abdallah amma da sharaɗi ɗaya”.
Murmushin samun nasara Gimbiya Fa'izah tayi kana tace.
“Mun amince menene sharaɗin?”.
Bakinsa ya lashe tare da kallon Meerah dake yatsine fuska tana toshe baki Allah ya sani tana da ƙyanƙami da ƙyama cikin Muryansa mara daɗin amo da sauti yace.
“Zan kwanta da wannan domin da Sparm ɗin ta za'a yi aikin da zai kama acikin kanƙanin lokaci.
Da sauri Meerah ta miƙe tana binsa da mugun kallo mai cike da ƙyama tace.
“Kutmar Uba dawa zaka kwanta?”.
Ya wani ɗaure fuska yana kallonta
Cikin Sauri Gimbiya Fa'iza ta janyo hannunta cikin ƙasa da murya tace.
“Kee ki nutsu mana ko shima rashin kunyar da kika saba yi mana zaki masa to wallahi wannan yanzu sai ya mai daki Kwaɗo”.
Tsorono ya kama Meerah cikin sanyi tace.
“To ai shine yake neman zuwa da maganar da ko amafarki bazan lamunta ba kawai ki faɗa masa ko nawa ne za'a bashi amma wallahi banda ni”.
Ta sake kallon mummunan halittar sa cike da jin haushi tace.
“Ina Ai _Sawun Giwa ya take na raƙumi_ wallahi wannan da ace mutum ne Kamar sauran mutane da saina sa anyi masa mummunan hukunci tare da tsarkin Baki da hypoh da Jick”.
Cikin Fushi Linƙin-ƙiyas Kufru ya daka musu tsawa tare da faɗin.
“Ku tashi ku ɓace min da kallo kafin insa ƴaƴan tururuwa su fitar min daku”
Da wani irin sauri Gimbiya Fa'iza ta zube gaban ƙafafunsa kana tace.
“Tuba muke Linƙin-Ƙiyasi Kufru idan ka koremu babu inda zamuje kasan cewa kaine kaɗai kake temakona a yau ma ina neman temakon ka kada ka juya mana baya ita ɗin yarinya ce”.
Banza ya mata saima kawar da kansa gefe da yayi ganin haka yasa Gimbiya Fa'iza cigaba da bashi hakuri ta ɗauki kimanin minti 10 kafin ya haƙura...
Meerah kam kallonta take cike da mamaki ganin duk wannan izzah da kasaitar nata ta ajiyesa gefa tana bashi haƙuri...
Wata ƙwarya mai dabbara² ya ɗauko tare da kafa bakinsa akai ya shiga wasu surkulle atake fuskar Sir Abdallah ya fito aciki.
Atsorace Meerah taja baya tare da zare ido cikin gurɓatacciyar hausarsa yace.
“Me kike so ayi masa so kuke ahalakasa ko kuma ahaukata shi ko kuwa amai dashi mata maza?”.
Cikin sauri Gimbiya Faiza tace.
“So nake Ahaukata shi cikin gaggawa Hauka na har abada sannan aɓatar dashi yanda zaiyi nesa da garin dama ƙasar baki ɗaya!”.
Kai Meerah ke girgizawa cikin tsananin tashin hankali da tsoro kallon Gimbiya Fa'iza tayi amma ta ɗauke kai. Saurin maida kallonta garesa tayi.
Kafin ta furta komai wani baƙin hayaƙi mai sauti ya fita miƙewa yayi cikin ɗaga sautin da bushewar zuciya yace.
“Maza ku tafi ga Abdallah! Maza ku halaka Abdallah!! Maza ku tafi dashi inda ba'a da wowa!!!”.
Atake wasu irin halittu masu mummunan siffa suka riƙa fita yayin da Jejin ya ka came da wasu irin sauti marasa daɗin amo....
*My dear Fan's Free page ya kusa ƙarewa ku hanzarta wajen biya domin mu kai Limit da ake buƙata mu cigaba da posting batare da ɗaukar lokaci ba anuna min soyayya ta hanyar biyan kuɗin littafin...*
_Sawun Giwa It's 500 hundred Via 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank or Mtn card ,*** show ur Evidence ***..._
@Follow me on Arewabooks Realeshaa
Follow me on Wattpad Realeshaa
_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani_
_Ayi shearing ƴan Uwa masoya da Abokan arziƙi._
*ESHAA CE*