Sawun Giwa

17

by @realeshaa

*SAWUN GIWA*

_Ya take na Raƙumi_





_By_

*Aishatu Abdullahi Idris*

_REAL ESHAA_




*F-R-PG 17*

Anutse Sir Abdallah ya fito daga wani tsarerren Hall dake cikin makarantar wanda aka tanadar domin taro bayan sun gama meeting.


Yayin da hannunsa ke riƙe da wayarsa Fuskarsa babu walwala kona misƙala zarratin.

Daga gefen daman sa kuwa Sir Auwal ne dake riƙe da goran Swan water yayin daga gefen hagunsa Principal ne ya kasance sun saka sa atsakiyarsu daga can Baya kuma sauran malamai ne.


Tsayawa Sir Auwal yayi tare da kallon Sir Abdallah kana yace.

“A.A.Zaman zan shiga S.S.3.A muna da darasi gashi har lokaci ya gauta”.

Kai Sir Abdallah ya ji jinjina aƙasan maƙoshi yace.

”Ok”.

Har Sir Auwal ya juya da niyyar tafiya sai kuma ya tsaya jin Sir Abdallah na cewa.

“Kira min wancan yarinyar”

Cikin rashin fahimta Sir Auwal ya kalli agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa tare da faɗin.

“Which Girl?kasan fa yaran nada yawa ko kuma ko wacce na kira maka?”

Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya motsa laɓɓansa yace.

“Head Girl”.

Kai Sir Auwal ya gyaɗa tare da faɗin.

“Ok amma kwana biyu bata zuwa”.

Ahankali yace.

“Tazo ɗazu muna meeting naga wucewar ta ta bayan Hall”.

Baki Sir Auwal ya taɓe kana yace.

“But me zata yi maka yarinyar da tayi maka ƙazafi acikin mutane!,Ta nemi ta tozar taka!,Gashi tun ba aje ko ina ba Allah ya tona masa asiri tunda ya taɓa yarinyar da basu da alaƙa asirinsa ya tonu”

Kansa ya dafe cikin gajiya yace.

“Please kira min ita nima abinda nake son tambayarta kenan meyesa ta ɓoye gaskiya?”

Ya faɗi hakane dan ya rabu da tambayar Sir Auwal...


“Ok In sha Allah”.

Ya ida maganar tare da nufar ajin kana ya shiga cike da girmamawa Class Captain ta miƙe tare da cewa.

“Stand Up, Greet”.

Yayin da sauran ɗalibai suka miƙe da faɗin.

“Good Morning Sir”.

Cike da kamun kai ya amsa da.

“Morning Class How are U?”.

“Am fine Sir”.

Suka haɗa baki wajen faɗa.

Daga haka yai musu alama su zauna.

Zama sukayi yayin da baki ɗaya ajin ya ɗauki shiru Neenah kuwa kanta na ƙasa ta sun kuyar aƙasan benci yayin da Baret ɗinta ke kan deks.

Gyara Murya Sir Auwal yayi wanda yasa tayi saurin ɗago kanta da hannu ya mata alamar tazo.

Cikin sanyi jiki ta miƙe ta isa inda yake cikin yanayin maganar sa yace.

“Sir Abdallah na kiranki”.

Atake taji hanjin cikinta da yunwa ya gama ƙwa-ƙwulewa ya sake kaɗawa cikin mutuwar jiki tace.

“Toh yana ina”.

Ataƙaice ya bata amsa da faɗin.

“Office ɗin sa”.

Numfashi ta fesar kana ta fice.


Akuma dai-dai lokacin Principal ya tsaya dai-dai kofar Office ɗin Sir Abdallah cike da girmamawa yace.

“Bundi Ina mai sake baka haƙuri akan abinda Malam Sa'idu ya aikatawa wancan ɗalibar bansan haka halinsa yake ba shiyasa na ɗauke sa Matsayin Displine Master amma In Sha Allah da kaina zan koresa makamancin haka bazai sake faruwa ba”.


Kai Sir Abdallah ya jinjina kafin cike da izza ya motsa laɓɓansa tare da cewa.

“Yarda da kai da nayi yasa na baka zaɓin nemo masu kula da makarantar tunda mata ne kaɗai amma dubi irin mutumin daka kawo min cikin Makaranta da Farko yayi wa Head Girl ganin bata da galihu sannan ba'a ɗauki mataki ba ya koma kan wata”.

Ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa kana ya cigaba da cewa.

“Gashi har ta sanar wa iyayenta shin wani irin kallo kake tunanin za'a yiwa makaranta na da kuma Malamanta?”.


Ya lumshe Cat eyes ɗin sa kana ya cigaba da cewa.

“Idan har ya sake tako bakin Makaranta na ko kuma shiga Area da nake sai ya ƙare baki ɗaya rayuwarsa a prison”.


 Ajiyar zuciya Principal ya sauƙe kana yace.

“Kayi haƙuri Bundi In Sha Allah ba zai sake zuwa ba kuma za'a hukunta shi abisa zunubin daya aikata”. 

Kai kawai Sir Abdallah ya gyaɗa tare da wucewa office ɗin sa ya zauna yana mamakin halin Malam Sa'idu baki ɗaya mutumin babu Allah aransa yana nema ya lalata wa yara tarbiyya tare da gurɓata masa makaranta.


   Zaman sa ba daɗewa yaji knowking ɗin ƙofa muryarsa aƙasan Maƙoshi yace.

“Come In”.

Ahankali ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga tamkar kazar da ƙwai ya fashewa aciki agaban Deks ɗin ta tsugunna tare da faɗin.

“Ina kwana Sir”..

Batare daya ɗago kai ya kalleta ba ya cigaba da latsa wayarsa sai dai ko kaɗan hankalin sa bai kan wayar ya tafi wani tunani da ban.

Tsawon minti uku tana tsugunne akan ƙafarta batare daya tanka taba.


Cikin rawan murya da gajiyawa tace.

“Sir gani”.

Still idanunsa na kan wayarsa kana murya aƙasan moƙoshi yace.

“Ni kurma ne?,ko kuma makaho?,da zaki sani gaba da maimaita magana ɗaya”.

Kai ta girgiza murya na rawa tace.

“Kayi haƙuri”


“Laifin me kika yimin kike bani haƙuri?”.

Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tana wasa da yatsun hannunta.

Numfashi ya fesar tare da tsira mata idanunsa dake tsoratata kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa.

“Save me”


Cikin sauri ta gyaɗa masa kai Aɗan zaman da tayi dashi na kwanaki ta fahimci halinsa shi mutum ne da maganar bakinsa bai ishesaba Uwa Uba izzah da ƙasaita dake ratsa sassan jininsa.

Anutse ta miƙe ta isa gaban deks ɗin kana ta ɗauko Basket ɗin ta buɗe tare da yin serving ɗinsa.

Amsa yayi ya ajiye kana yace.

“Save Ur self”.

Batare data kallesa ba tace.

“Naƙoshi”.

Banza ya mata ya cigaba da cin nasa murya na rawa tace.

“In tafi”.

Afusace ya juya da niyyar yi mata magana idanunsa suka sauƙa akan shatin bulalar da yayi mata bille daga gefen bakinta miƙewa yayi tare da nufota.


Ganin haka yasa tayi saurin miƙewa cike da tsoro tana ja baya yayin da take girgiza masa kai idanunta cike da ruwan hawaye baki ɗaya idanunsa na kan bakinta ahaka ta isa jikin bango ƙara sawa yayi tare da kai hannunsa gefen bakinta ya shafa.


Runtse idanunta tayi tare da ƙanƙame jikinta waje ɗaya zuciyarta na bugawa yayin da wani irin sanyi ke ratsa tun daga tafin ƙafarta har ƙwaƙwalwar kanta cikin rawan murya da rauni tace.

“Dan Allah kayi haƙuri”.


  Batare daya tanka taba ya sanya hannunsa na dama tare da janye hijabin kana ya tsira wa dokin wuyarta zuwa ƙirjinta idanun kana ya maida idanunsa kan fuskarta da shatin bulalar ya kwanta.


Lokaci ɗaya idanunsa suka kaɗa suka sake zamewa tamkar na fusatacciyar kyanwa cikin wata kakkausar murya mai cike da kaushi yace.

“Waya miki wannan dukar?Laifin me kika yi aka yi miki irin wannan duka tamkar wacce ta aikata Zina?”.

Shiru tayi hawaye na kwaranya daga idanunta.

Wata razananniyar tsawa ya buga mata tare da faɗin.

“Nace waya miki wannan dukan?”.


Cikin muryan kuka da shesh'sheƙa tace.

“Baba ne?!”.

Cike da matsanancin mamaki ya maimaita sunan kana can ƙasan maƙoshi yace.

“Baba?”.

Kai ta gyaɗa masa kana jikinta na rawa tace.

“Eh”.

Kai ya jinjina still idanunsa na wajen yace.

“Laifin me kika masa?”.

Kai ta girgiza cikin gunjin kuka ta lumshe idanunta tare da faɗin.

“Banyi masa komai ba”.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

“Babu ta yanda za ayi yayi miki irin wannan dukar babu dalili dole akwai dalili,Menene dalilin?”.


Kai ta Jinjina cikin rauni da tashin hankali tace.

“Yace wai na tafi yawon karuwanci ni karuwa ce babu amfanina awajen sa!,Babanaaa..na da yafi kowa yarda dani shine ya kirani da Karuwaaaaa Mazinaciya!”.

Ta ida maganar tana zamewa ƙasa tare da sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta zuciyar ta na wani irin ƙuna.

Cikin shesh-sheƙan ta cigaba da cewa.

“Saboda yaga ka rungume ni yasa yake yi mana mummunar zato!”.


Durƙusawa yayi tare da ɗagota jikinsa tafin hannunsa yasa yashiga share mata hawaye yana jin wani irin ƙuna da baƙin ciki azuciyarsa...


Tafin hannunta ta ɗaura akan nasa tana wani irin kuka mai ratsa zuciya.

Zazzafar ajiyar zuciya ya sauƙe still hannunsa na riƙe da nata yace.

“Saboda tsoron guje miki Irin wannan matsalar, yasa naso mushiga in yi musu bayani amma kika ce a'a atunaninki zaki iya fahimtar dasu Nasan duk abinda zaki faɗa ba zasu yarda dake ba ke ɗin yarinya ce koda yake nima nayi kuskuren barin ki”.

Kasa furta komai tayi sai hawaye dake kwaranya daga idanunta tabbas ita kanta tayi wauta data bari yayi wa Baba bayani ba tasan kima da muhimmancinsa zai sa Baba ya fahimcesa...


Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.

“Ok kukan ya isa haka kiyi shiru in Sha Allah zanje da kaina na fahimtar dashi abinda ya faru da kuma maganar tafiyarki domin wanke zargin da ake miki hope dai kina son tafiyar?”.


Tsintar kanta tayi da son tafiyar wanda ada Sam Bata buƙata amma ayanzu tana buƙatar nesanta kanta daga gida ko zata samu salama kumburarrun idanunta ta ɗago kana tace.

“Yaushe ne tafiyar?”.

“Kina son tafiyar kenan?”.

Ya jefo mata tambayar yana mai tsareta da Cat eyes ɗinsa

Kai ta gyaɗa tana lumshe idanunta acikin nasa

Numfashi ya fesar kana yace.

“Kada ki damu In Sha Allah Nan da wasu satin nai za Birthday na da kuma buɗe makarantar dana gina,Sannan da tallafin da zan bayar so aranan ko washe gari zaki tafi sannan kizo da wuri ina so da hannunki zaki bawa wasu tallafi.

Be jira cewar taba ya miƙe tare da faɗin.

“Maza zo kiyi breakfast domin yanayin ki baiyi kama dana wacce taci abinci ba dubi cikinki kamar ba hanji”.

Kallonsa tayi idanunta cike da ruwan hawaye tace.

“Koda abinci Baba ya hanani yace bazai ciyar da karuwa ba Mamawo tace sai dai inje wajen Karuwaina su ciyar dani koda Maryama zata bani sai ta hanani”.

Cikin tarin tausayinta ya buɗe da niyyar magana kafin ya furta wata kalma.

 Wani irin duhu mai masifar duhuwa ne ya fara mamaye baki ɗaya ilahirin cikin Office ɗin yayin da kayan ciki ke wani irin rawa tamkar zasu rushe.

Akiɗime Neenah ta miƙe tare da faɗawa jikinsa ta ƙanƙamesa zuciyar ta na bugawa da sauri-sauri tamkar zai fasa ƙirjinta ya fito...


Wani irin abu mai siffar alade da ƙaho ɗaya agoshi baƙiƙƙirine ya fara fitowa daga ƙasan tiles hanunsa ɗaya cike da gashi kana idanunsa Ja-jawur babu ɗigon fari kansu ya dumfaru gadan-gadan yana wani irin haushi mai tarwatsa lissafi.

Yayin da wani farin halitta mai siffar Raƙumi ke fitowa daga Sama cikin rufin P.o.p kana ya nufi kan wannan mummunar baƙin halittar nan take suka fara faɗa cikin tsananin tsoro Neenah ta ƙanƙame Sir Abdallah tana karanto duk wata addu'ar da tazo bakinta tun da take arayuwarta bata taɓa kallon irin wannan baƙar halitta mai firgitarwa ba.


Acan ɓangaren Boka Linƙinƙiyas-Kufur kuwa wasu irin addu'oin matsafa yake yayin da yake cigaba da kiran sunan Sir Abdallah atake dajin ya ɗauki rawa wasu baƙaƙen halittu masu muguwar suffa suka riƙa sauƙowa suna wani irin kuka mara daɗin Amo da sauti.

Aruɗe Meerah tayi kukan kura tare da ingije Boka Linƙinƙiyas-Kufur ƙwaryar dake hannunsa ya ɓare wani irin suwwan kuka mai siffar kukan Jakunane ya karaɗe dajin yayin da Boka Linƙinƙiyas-Kufur ya fashe da wani razananniyar ihu.

Wanda yayi sanadiyar ɗaukewar numfashin duk wani abu mai rai a wajen ciki kuwa harda Meerah da Gimbiya Faiza.

Kana ko wanne ya baje acikin jejin...


Acan Office ɗin Sir Abdallah kuwa cikin tsananin tsoro da kiɗima Neenah ke kallon wannan halittu dake ta artabu agabansu yayin da Sir Abdallah ya zubawa sarautar Allah ido yana mai cigaba da karanto duk wasu addu'oin da suka zo bakinsa Wannan farin halitta mai siffar Raƙumin ne yayi nasaran jefo baƙi mai siffar Alade ƙasa wani ƙara wannan halittar ta sake kafin ta faɗo ƙasa wuta ya kama jikinsa suna kallo ya ƙone agaban idanunsa ga mamakin su sai wannan farar halitta ta sakar musu da murmushi abinda ya daɗe yana basu mamaki kafin daga bisani ya ɓace.

Nan take hasken ɗakin ya dawo kana komai ya dawo yanda yake tamkar babu abinda ya faru.

Ahankali ya miƙe tare da ɓanɓare Neenah daga jikinsa saurin ja baya tayi tare da sun kuyar da kanta ƙasa cike da kunya da tarin tsoro.


Tafin hannunta ya riƙe ganin kamar har zuwa lokacin Akwai firgici atare da ita kana ya jata zuwa kan kujeran ya zaunar da ita akan kujera abinci ya ɗiba ya bata cikin yanayin tsoro da damuwar da take ciki yasa tace.

“Na ƙoshi”.

Wani kallo ya mata tare da ɗaure fuskar ya kai mata kofin dake ɗauke da tea bakinta kana yace.

“Shanye”.

Ganin yanayin fuskarsa babu wasa ko kaɗan yasa ta buɗe bakinta ya riƙa bata tea tana sha kana yana haɗa mata da Cheaps.

Sai da ya tabbatar ta ƙoshi kafin ya janye kofin daga bakinta ya miƙe ya koma wajen zamansa.


Cikin sanyi murya tace.

“Nagode Ubangiji Allah ya ƙara girma da ɗaukaka”.

“Kada ki yarda koda wasa naji Abinda Ya faru abakin wasu”.

Kai ta gyaɗa kana tace.

“In sha Allahu zan iya tafiya?”.

Kai ya gyaɗa mata kana yace.

“Hope dai kina shan maganin ki?”.

Kai ta gyaɗa alamar eh.

“Good ki kula daka kiyi wasa dasu idan ya ƙare ki faɗa min”.

“Toh In Sha Allah”.

Ta faɗa.

Kafin ta juya cikin mutuwar jiki ta fita tare da nufar ajinsu da kallo yabita kafin ya jingina bayansa da jikin bango yana sakin ajiyar zuciya tabbas zai je yayi magana da iyayenta akan abinda ya faru da kuma maganar tafiyanta yana so ya inganta rayuwar yarinyar yana so ta zama Babbar mace wacce zata iya tsayuwa akan ƙafafunta...


A gefen Neenah kuwa tana shiga Class ta nemi gefen Abeeda ta zauna malamin Religion ne ya shigo bayan ya gama ya fita ya zama suna Free.

Baki ɗaya Class din sun kafa Camber kowa da hirar da suke.

Abeeda ce ta kalli ƙawarta data zuba tagumi dafa kafaɗarta tayi kana tace.

“Hawwa meke damunki naga kinyi shiru ko kema kin fara shiga sahun Neenah ne?”.

Kallonta Neenah tayi amma ba tace komai ba.

Hawwa kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe cikin yanayin damuwa tace.

“Wallahi ba haka bane ina cikin tashin hankali Abeeda baki ɗaya Acikin kwanakin nan ko karatu bana fahimta”.

Cike da kulawa Abeeda tace.

“Ai ina lura dake Shiyasa kikaji nace ko kin fara shiga sahun su Neenah ne”.

Cikin sauƙe ajiyar zuciya Hawwa tace.

“Hmmm ko ɗaya wallahi ai ita Neenah baka gane abinda ke damunta ta fiye zurfin ciki”.

Ita dai Neenah kallonsu take Allah ne kaɗai yasan me take ji aranta.

Cikin sauƙe ajiyar zuciya Abeedah tace.

“To amma Hawwa Meyafaru haka kada fa Kice zaki sawa ranki damuwar samarin wannan zamanin dan sai wata ciwo ta kamaki abanza babu abinda ya shafesu suna can suna rayuwarsu cikin farin ciki kai sun Barka da tarin ƙunci a zuciya”.


   Zazzafan ajiyar zuciya Hawwa ta sauƙe tare da faɗin.

“Kayya dama wannan ne da sauƙi wallahi,Kinsan akwai Ƙanwar Mamana wacce muke sa'anni yanzu watan ta biyu da Aure amma kada kiga yanda ta dawo tayi baƙi ta rame wallahi idan kika ganta baza ki gane ta saboda tashin hankalin da take ciki”.


Cikin jimami abeeda tace.

“Kayya Hawwa rayuwar Auren yanzu sai addu'a ko wacce mace da kike gani da kalar matsalar da take fuskanta agidan mijinta babu wata mace yau da zata ce miki tana jin daɗin gidan mijinta 💯 ko wacce da irin ƙalubalen da take fuskanta sai dai haƙuri kuma na wata yafi na wata amma wacce bata da sirrine take yaɗa sirrin gidan Auranta Shiyasa nake mamakin wasu matan dake zuwa social media suna baza sirrin mazajensu”.

Fatima Mustapha dake bencin gefensu tace.

“Ke dai Abeedah Sa'eed ki bari Babu abinda yake ƙona min rai kamar naga mace tana baza sirrin Mijinta musamman idan na hau Facebook na shiga group ɗin _SIRRIN ƳA MACE_ naga wasu mata na baza sirrin su cikin rashin wayewa abin na ƙona min rai”.

Murmushi Abeedah Sa'eed tayi kana tace.

“Zancenki dutse Sai dai _Sirrin ƴa mace_ yana da daɗin zama akwai ɗebe kewa sannan akwai masu bada shawarar data dace haka zalika akwai masu bada na banza uwa uba kuma akwai Ni shaɗantuwa”.

Murmushi Fatimah Mustapha tayi tare da cewa.

“Aikam”.

Abeedah Sa'eed kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da cigaba da cewa.

“Hmmm hallayar wasu Mazan na bani mamaki a waje sai kiga ana nunawa mace soyayya tamkar za acinye juna amma da Zaran anyi Aure sai kiga tamkar Auren ƙiyayya sukayi bana soyayya ba kuma hakan baya rasa nasaba da irin hanyar da akabi wajen Auren su mata son abin duniya samari kuma ƙarya da latse-latse kafin ayi Aure sai sun gama latse yarinya ana Aure zargi ya shiga tsakani kenan!”.


Kai Hawwa ta jinjina tare da ɗauke hawayen daya zubo mata kana tace.

“Hakane kam rayuwar Auren yanzu ya zama abinda ya zama shiyasa kika ga sam Aure baya gabana.

Shifa saboda kawai anyi Auren bai sameta da budurci ba shine yake wulaƙantata wallahi kar kiso ki ganta yanda ta dawo”.


 Zare idanu Abeedah Sa'eed tayi kana tace.

“Cabɗi jam Hawwa aikuwa ya zama dole tayi haƙuri domin wallahi a yanzu duk wata budurwa daba takai budurcinta gidan mijiba dole tayi haƙuri da duk abinda zata gani domin Mazan yanzu ka kai musu budurci ma ya ka ƙare bare kuma kaje a fanko wanda yake masifar sonki ne idan kika je masa afanko zaiyi haƙuri Amma wani ɗan iska kam tuni zai sakeki”.

Lokaci ɗaya Neenah ta dafe ƙirjinta daya buga da Masifeffen ƙarfi wasu hawaye ne masu masifar ɗumi suka zubo akuncinta cikin ranta ta furta.

_“Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan minhaa”_


Maganar Abeeda Sa'eed ne ya dawo da ita duniyar tunanin data ta tafi lokacin da take cewa.

“Hawwa agaskiya shawarar da zan baki ki faɗa mata tabi duk wata hanya da zai janyo hankalin mijinta wajenta sannan tayi ƙoƙarin fahimtar dashi amma ya zama dole ta jure duk wani wulaƙanci daga garesa saboda itace ta siya ta kuma biya Shiyasa ko yaushe ake wayarwar wa da ƴan mata kai su guji sharrin bakar yaudarar samarin wannan zamanin”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.

Shine kalmar da Neenah ke maimaita wa aƙasan ranta cikin tsananin tsoro da kiɗima...

Cikin sanyi Murya Hawwa tace.

“Bare ita Saurayine ma ya yaudareta sannan ya gudu tun lokacin naso ta faɗawa mijin da zata Aura gaskiya saboda gudun irin wannan matsalar kinga da ace ya sani yanzu bazu mata wulaƙancin ba”.

Ta gumi Abeedah Sa'eed tayi tare da faɗin.

“Kayya wani ma idan ka faɗa masa ai baka tsira ba wallahi dan gudunki zaiyi wani kuma zai soki ahaka sannan kuma babu wani abu da zakiyi amfani dashi wajen dawo da budurcinki idan kika rasa kin rasa abu mai muhimmanci da zai siya Miki kima da iyayenki awajen miji har abada ...

Haka suka cigaba da tattauna maganar har aka tashi batare da Neenah ta tanka suba...


   Kallon Neenah Abeeda Sa'eed tayi bayan sun fita cike da kulawa tace.

“Neenah kwana biyu shiru keda Indu baku zuwa kuma yau tunda kika zo na lura da yana yinki kamar baki da lafiya gashi tunda kika fita aji baki sake dawowa ba sai daf za a tashi meke damunki?”.

Kawar da kai Neenah tayi kamar ba zata ce komai ba sai kuma tace.

“Babu komai Kawai dai kaina ke ciwo”.

Baki Abeeda Sa'eed ta taɓe

Daga haka ta shiga Motar daya zo ɗaukar ta ita kuma Neenah ta kama hanyar gida da kafa zuciyarta cike da tsoro da kuma fargaban abinda Abeeda suke magana akai.


**

  Da mamaki Ummu ke kallon Imraan dake durƙushe gabanta.

Zazzafar ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta gama sauraro sa kana tace.

“Imraan ban fahimci me kake nufi ba”.

Sake sun kuyar da kansa ƙasa yayi kana yace.

“Ummu abinda kika ji na faɗa Wlh har cikin raina haka nake nufi dan Allah ki taimaka kisa baki kada kice a'a”.

Kai Ummu ta girgiza tare da kallonsa kana ta furta.

“A'a babu dalilin da zai sa in Sanya bakina acikin maganarka ka kunyata ni domin har yau ka kasa fahimtar halin matar ka ka kasa fahimtar wacece ita dan haka bazan baka amanar yarinya kuje ku wulaƙantata ba ku lalata mana zumunci”.

Saurin girgiza mata kai yayi tare da faɗin.

“In sha Allahu hakan bazai kasance ba ki yarda dani sannan ki cigaba da min addu'a”.

Nannauyar ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe tare da cewa.

“Badamuwa kaje zanyi tunani akan Maganar duk abinda na yanke zan faɗa maka amma kada ka yarda kuci amanar yarinya koda Allah yayi”.

Cike da farin ciki yace.

“Nagode Ummu In Sha Allah bazan baki kunya ba zan riƙe miki ita da Amana!”.

Sallama ya mata kana ya fita cike farin ciki kai tsaye gida ya nufa bakinsa ɗauke da sallama yashiga falon. Indu dake kallo ta miƙe da sauri tare da cewa.

“Sannu da zuwa Yah Imraan”.

Fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi ya furta.

“Yawwa Autah Albishir”.

Ya faɗa asanda yake zama kusa da ita

“Goro fari soll Yaya”.

Zama ya gyara kana yace.

“Yau nayi Wa Ummu maganar Auren Zonbi kuma tace zata yi tunani akai”.

Ware idanu Indu tayi cike da mamaki tace.

“Auren Aunty Zonbi wa Ummu kuma?”.

Kai ya gyaɗa alamar eh.

Baki a sake tace.

“Dama kasan tana son ka kenan?”.


Nan ma kai ya gyaɗa mata still da murmushi afuskarsa.

Cike da mamaki da yaƙi barinta ta sake cewa.

“Toh Amma har yaushe soyayyar taku tayi ƙarfi yaje maganar Aure”.

Hanci ya lakace mata kana yace.

_“Wala tajassasu”_


Murmushi tayi kana tace.

“Masha Allah nayi farin ciki Ubangiji Allah ya sanya Alkhairi”.

“Ameen ya hayyu ya ƙayyum but ya naga kamar ba kiyi farin ciki da maganar ba ko?”.


Kai ta girgiza tare da faɗin.

“Nayi farin ciki sosai kawai dai damuwata Blue eyes Yah Imraan Blue eyes na cikin wani hali azotana kana sonta ne kuma zaka Aureta domin ceto rayuwar ta ashe kuskuren fahimta nayi”.

Zama ya gyara tare da fuskantarta da kyau yace.

“Indu!,Tabbas Neeraan nada matsayi mai girma azuciyata wanda zan iya sadaukar mata da duk wani farin ciki na sannan zanyi yaƙi da duk wani abu da zai sata cikin damuwa akwai shiri da nake da Zaran kunyi Candy”.

Ya fesar da numfashi kana ya cigaba da cewa.

“Sai dai zan Auri Zonbi ne saboda farin cikin Ummu da kuma cika mata burinta sannan kuma da wani burina,Ita kuwa Neeraan ina so na inganta rayuwar ta ta dawo cikakkiyar mace mai ƴanci”.

Da mamaki tace.

“Kenan duk tausayin Neenah kake ji babu soyayyarta atare da kai sannan kuma Zaka Auri Zonbi saboda farin cikin Ummu ba wai dan kana sonta ba?”.


Kallon agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa yayi kana ya miƙe tare da faɗin.

“Dare yayi kije ki kwanta sannan zan baki amsar tambayoyinki amma ki sani Neeraan nada matsayi mai girma acikin zuciyata”.

Ya ida maganar tare da sakar mata murmushi kana ya nufi bedroom ɗin Lateefa.

Da kallo Indu tabi bayansa tana auna kalamansa ganin ba zata samu amsar daya dace ba yasa ta miƙe tare da kashe kayan kallon ta nufi bedroom cike da tunanin cin mutuncin da Lateefa tayi mata alokacin da ta dawo gidan koba komai zata so Imraan ya auri Zonbi domin tana da tarbiyya da nutsuwa...


Zaune ya samu Lateefa gefen gado cikin wasu Sky Blue rigar bacci yayin da ƙamshi mai sanyi ke tashi kallo ɗaya ya mata ya kawar da kai.

Da gudu ta tashi tare da faɗa wa jikinsa cikin shesh'sheƙa tace.

“Dan Allah My Soja kayi haƙuri nasan nayi kuskure amma bazan sake aikata makamancin saba kaine farin cikina kuma Allah In Sha Allah bazan sake yin wani abu makamancin sa”.

Ajiyar zuciya ya sauƙe babu walwala atare dashi ya ɓanɓareta daga jikinsa kana yace.

“Na gaji, Lateefa na gaji da jin wannan tatsuniyar taki kullum cikin maimaita magana ɗaya muke baki da Abokan gaba da wulaƙantawa sai ƴan Uwa na da mahaifiyata kin ɗauki Zonbi tamkar kishiyar ki shin mai ta tsare miki saboda tsabar wauta da jahilci acikin mutane kima cukumeta kuna faɗa?”.

Cikin tsawa ya ida maganar.


Zubewa tayi akan gwiwoyinta cikin shesh'sheƙan kuka tace.

“Dan Allah kayi haƙuri bazan sake ba tabbas ni malaifi ce awajenka amma idan har ina da laifi Zonbi ma dashi meyesa zata rungumeka agaban idanuna kada ka manta nifa matarka ce ya zama dole nayi kishi akan ka”.

Ɗaure fuska yayi tare da faɗin.

“Wannan sakarci da rashin tunani kinsan dai Zonbi ƴar uwata ce sannan wannan haukar da kike yi bazai hanani Aurenta ba idan har nayi niyyar haka”.


Hanci ta shaƙa tare da girgiza kanta kana tace.

“Ni kam na shiga Uku shin laifin me nayiwa ubangiji da yake jarrabata da iftila'in mata masu bibiyar rayuwar mijina suke son rusa min farin cikina”.


Siririn tsaki taja sam bata bashi tausayi baki ɗaya ta gama fita aransa cikin kawar da kai yace.

“Ki iya kalamanki kada kiyi saɓo babu abinda Ubangiji yake ɗaurawa bawan sa wanda bazai iya ba sai dai bawa ya ɗaurawa kansa abinda yafi ƙarfinsa ku mata mafi yawanku baku da hankali da Zaran wata ta raɓi mijinku zaku dawo tamkar wasu zautattu bakwa la'akari da alaƙar dake tsakanin su!”.

Ta ɗago idanunta da suka rine da tsantsan tashin hankali kana tace.

“Sojana na sani kallon mara hankali kake min amma kasani zuciyata baza ta taɓa juran alaƙarka da ko wacce mace ba saboda ina masifar sonka ina zaton soyayyar kace Ajalina”.

Ta ida maganar tare da kife kanta akan tiles tana wani irin kuka mai tsuma zuciya...


Ganin yanda take kukan yasa yaji tausayinta sunkuya wa yayi tare da ɗagota jikinsa.

Cikin tsare gida da nuna mata kuskurenta yace.

“Lateefa ki kiyaye gaba bansan me ƴan Uwana suka tsare miki ba musamman Indu da kike yiwa kallon kishiya, sannan kina jifan mahaifiyata da mugun magana bayan kinsan duk duniya bani da kamarta”.

Cikin Muryan kuka tace.

“Na tuba in Sha Allahu bazan sake ba zan kiyaye”.

Kai ya jinjina tare da sake kafaɗarta ya shiga Bathroom...


Acan ɓangaren Ummu kuwa ba tayi ƙasa agwiwaba bayan kwanaki da kanta ta shirya taje ta samu Aminan Mahaifin Imraan ta sanar dasu abinda ke tafe da ita a matsayin ta Wakiltasu suje gidansu Zonbi neman Aurenta..

  

 Kasancewar mahaifiyar Zonbi ce Ƙanwarta

Lokacin da Aminan mahaifin Imraan suka je tambayar Auren Zonbi sosai mahaifin Zonbi yayi farin ciki da zuwansu inda aka tsaida lokacin biki Makonni biyu masu zuwa.

Sosai Ummu taji daɗin lamarin tare da sake jaddada masa ya riƙe ta da alkawari.

Lokacin da Imraan ke sanar da Zonbi an sanya ranar bikinsu tsawon sati biyu baƙaramin farin ciki tashiga ba wanda ta kasa ɓoyewa shikam sosai yayi mamakin farin cikin data kasance aciki koda yake ba abin mamaki bane duba da soyayyar da take masa.


  Kallon Imraan daya tsira mata idanu Lateefa tayi kafin cikin damuwa tace.

“Sojana wai dan Allah meke damunka ka sanar dani wallahi duk kasa na shiga damuwa”.

Numfashi ya fesar tare da riƙe tsintsiyar hannunta kana yace.

“Lateefa ina so ki fahimceni sannan kiyi wa maganata kyakkyawar zato komai arayuwa muƙaddarine sannan Allah yakan tsarawa bawa ƙaddararsa ta inda baiyi zato ba”.

Zuciyarta ne ya shiga bugawa da Masifeffen ƙarfi ahankali tace.

“Ka sanar dani amma wannan jawabin naka na kashe min gwiwa”.

Jinjina kai yayi tare da share zufa daya zubo masa yakai kimanin minti biyu kafin ya aro jarumta kana yace.

“An sanya bikina da Zonbi nan da sati biyu”.

Atake taji jinta da ganinta ya ɗauke sosai ta shiga cikin tashin hankali da damuwa jin wai zai ƙara Aure.

Danne damuwarta tayi tare da faɗin.

“Allah ya sanya Alkhairi”.

Numfashi ya fesar sam baiyi zaton haka ba cikin sauƙe numfashi ya furta.

“Ameen ya Allah amma ina so kisa aranki cewa banyi auren nan saboda In wulaƙantaki ba ko kuma bana sonki zanyi wannan auren ne saboda raya sunnah”.

“Hmmmm”

Kawai tace daga haka ta juya ta kwanta wasu irin hawaye Masu ƙuna suka riƙa zubo mata akuncinta ya rasa wacce zai Aura sai Zonbi yarinyar data fi tsana arayuwarta.

Duk maganar da yake banza tayi masa har ya gaji ya haƙura...


Washe gari da safe ta kira Meenah awaya ta sanar Mata daga ɗaya ɓangaren Meenah ta mulmulo wani Uban ashar tare da cewa.

“Aikuwa sai dai bayan ranmu tashigo gidanki amma muddin muna da rai da lafiya bata isa ba”.

Lateefa ta share hawayen daya zubo mata kana tace.

“Shikenan Meenah idan har ya Aureta wallahi mutuwa zanyi bazan iya juran ganin na haɗa shimfiɗar mijina da wata banza ba”.

Aƙage Meenah tace.

“Ki kwantar da hankalin ki gani nan zuwa”.

Ta faɗa tare da katse kiran cikin minti ashirin ta isa gidan Lateefa daga lokacin suka fara bin bokaye da Malaman tsibbu adomin su tsaida Auren kuma duk inda sukaje kuɗi suke zubarwa


***

Acan ɓangaren Neenah kuwa sosai tashi ga cikin damuwa da tashin hankali baki ɗaya rayuwa tayi mata ƙunci abubuwa sun cukurkuɗe mata har zuwa wannan lokaci Baba baya amsa gaisuwarta sannan ya hanata zuwa makaranta koda fita ƙofar gidane ya hana gashi har zuwa wannan lokaci basu haɗu da Indu ba duk da cewa sau biyu tana jin zuwan Indu amma Mamawo ta hanata shiga.

Kullum cikin zullumi da hantara take awajen Mamawo bata da sukuni ko wani kataɓus abinci sai dai Maryam ta ɗebo asace ta kawo mata tanaso ta haɗu da Sir Abdallah amma sam babu dama baki ɗaya ta sake baƙi ta rame rayuwar tayi mata ƙunci.


**

Acan ɓangaren Imraan da Ummu kuwa shirye-shiryen biki ya kankama sosai yau ya rage saura kwan Uku ɗaurin Aure wani irin rawan jiki Imraan keyi.

Dr Khameel dake driving ya kalli Imraan dake maƙale da waya akunnensa da murmushi afuskarsa yace.

“Kai Captain anya ko lokacin auren Lateefa kayi wannan zumuɗin?”.

Murmushi Imraan yayi tare da janye wayar daga kunnensa kana ya sauƙe ajiyar zuciya tare da faɗin.

“Kasan wani abu?”.

Kai Dr Khameel ya girgiza.

Imraan kuwa numfashi ya fesar tare da cewa.

“Ina so inyi Auren nan ne saboda kwanciyar hankalin Mahaifiyata sam Lateefa bata da mutunci ta ɗauki ƴan uwana tamkar kishiyoyinta ina bukatar macen da zata kula min da ƴan Uwa na ta riƙe su da mutunci”.

Ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cigaba da faɗin.

“Wallahi da ace Lateefa zata gyara alaƙanta da ƴan uwana da kuma mutanen dake zagaye dani babu dalilin da zaisa in kara Aure, amma saboda Wauta gani take hakan shine mafita gashi yanzu soyayyar Zonbi ya samu kyakkyawan muhalli azuciyata”.

Kai Dr Khameel ya jinjina asanda yake parking din Motar kana yace.

“Abinda mata da yawa suka kasa fahimtar kenan su atunaninsu miji kaɗai suka Aura ba ƴan uwansa ba wanda da zasu riƙe ƴan Uwan miji amatsayin nasu da sun more zamantakewar Aure amma basu da burin daya wuce suga sun raba tsakanin ɗa da Uwa bayan basu san yanda akayi Uwa ta rayu da ɗanta har yazama mutum ba”.

Ƙwaffa kawai Imraan yayi tare da buɗe murfin motar ya fita zuwa inda zasu karbi katin bikin...


**

Lateefa ce zaune awani ƙaramin ƙauye yayin da Meenah ke gefenta daga can gefe su kuwa wasu mata ne sun kai goma da alama layi suke bi ɗaya daga cikin matan ne ta kalli na gefenta kana tace.

“Ke dai Uwani ki kwantar da hankalin ki na faɗa miki aikin Mutumin nan kamar yankan wuƙa yake”.

Wacce ta kira da Uwani na share hawaye tace.

“Hmmm magajiya babu abinda yake ƙona min rai da Sagiru kamar kuɗin Tumakaina dana sayar na bashi akan zai gara mana gida mubar gidan gandu ashe Sagiru kansa yake gyarawa gida toh kwaran kwaso dubu ko zanyi yawo tsirara sai an fasa wannan Auren”.

Kafaɗarta Uwani ta dafa kana tace.

“Bare ma ba zakiyi yawo tsirara ba tun da kika zo nan Aure sai dai yayi alahira”.

Dariya ce takama Meenah lalle wasu Mazan halinsu sai Allah.

Zunguranta Lateefa tayi hakan yasa ta daina dariyar tana cigaba da jin yanda Magajiya ke tsinewa Sagiru.


Sun kai kimanin minti arba'in da zama kafin layin dake gabansu ya ƙare.

Suna ganin matar dake ciki ta fito sukayi saurin miƙewa suka shiga ɗakin bakin su ɗauke da sallama.


*My dear Fan's Free page ya kusa ƙarewa ku hanzarta wajen biya domin mu kai yawan Limit da ake buƙata mu cigaba da posting ba tare da ɓata lokaci ba...*


_Sawun Giwa It's 500 hundred Via 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number ***...Show ur Evidence ***_


_@Follow me On Arewabooks Realeshaa_


_@Follow me on Wattpad Realeshaa_


_Ya Allah Ubangiji kajiƙan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarinsa ya Allah kajiƙan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani..._


    _Ayi shearing saboda Allah ƴan Uwa Masoya da abokan arziki_


*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka  kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

***

***


   *ESHAA CE*