005
by @jeeddah3256
KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels
005
A tsorace AB ya ɗago idanunsa ya kalli Daddy zuciyarshi tana wani kalar bugawa sai da ya maida kanshi ƙasa kafin ya ce "Ka gafarce ni Daddy ba wai inaso bijrewa umarninka bane ko kaɗan bana fatar zuwan ranar da ni Abba za ka bani umarni na bijire maka. Kawai dai ina rokon alfarma da ka janye zance neman min aure, a halin yanzu na fi so na ƙarashe rayuwata babu aure.
"Zance banza kenan Abba taya ina raye tare da shaƙar numfashi a duniya na barka, babu aure? Burina shine ka yi aure Abba ka haifa min jikoki shiyasa a lokaci da Alhaji Bello Madawaki ya fasa aura maka 'yarsa Rumaisa a bisa hujja da kai kanka bakasan da wanzuwar ta ba. A lokaci raina ya ɓaci kalar ɓaci da bai taɓa yi ba, shiyasa idanuwana suka rufe ruff ba tare da na yi duba da irin abunda zai je ya komu ba na aura maka 'yar uwarka wacce nake gani na isa da ita amma ta watsa min ƙasa a ido.
Abba bansan waye ya bankaɗo daɗaɗɗen sirri da na ɓoye tsawon shekaru wanda daga ni sai margayiya Maryam muka san dashi. Abba kai ba shege bane ɗan gaba da fatiha kamar yadda mahaifin Rumaisa ya faɗa ba. Ina da cikakken yaƙini akan cewa ta hanyar aure aka same ka sai dai babban takaicina da ya kasance bansan komai ba akan iyayenka ba. Kuma banida wata gamsasshiyar hujja da zan faɗa maka akan dalili da yasa ka kasance ɗana. Kuma banaso ka sake yi min wata tambaya akan asali iyayenka domin kafin na mallake ka, ka zama ɗana sai da na cika wasu sharuddan koda ace yau iyayenka na asali suka bayyana, ba zan taɓa basu kai ba, domin kai ɗin rayuwata ne Abba ina sonka fiye da 'ya'ya da na haifa.
Daddy ya ƙarashe magana tare da ƙoƙarin hanawa hawayen cikin idanuwansa zubowa.
Kowacce kalma dake fita daga bakin Daddy tana shiga jikin Abba tare da kassara masa dukkan wani ƙudurinsa saboda haka ba zai iya ja-in-ja da Daddy ba.
Tun sanda AB ya baro Parlorn Daddy ya dawo ɓangarensa ya kwanta akan sofa tunani ya yi masa yawa, zuciyarsa tana cike da alhini abunda zai faru dashi anan gaba. Ƙarar wayarsa dake kan centre table ce ta dawo dashi daga natsuwarsa da ta kaurace masa suna Rumaisa Madawaki ya gani, sai da gabansa ya faɗi yana matuƙar ƙaunar Rumaisa ita ce mace ta farko da ya fara soyayya da ita, sai kuma ga wannan ƙaddarar ta raba su. Sai da ta jera masa kira huɗu ana biyar ya yi picking, yana ɗaura wayar a kunnensa tun kafin ya yi magana ya ji shesshakar kukan Rumaisa bata yi magana ba sai faman gunji kukanta take yi, shi kuma bashi da kuzari da zai iya rarrashinta, shi kansa yana bukatar wanda zai rarrashe shi. Tsawon lokaci suka dauka a haka ita tana kuka shi kuma yana sauraren kukan nata, daga bisani ya kashe wayar tare da blocking dukkan numbers ɗin Rumaisa, saboda komai ya zo ƙarshe a tsakaninsu, soyayyarsu ta zama tarihi dukkan alƙawarruka da suka yiwa junansu sun bi ruwa, saboda haka bai ga amfani ci-gaba da ajiye numbernta a wayarsa ba.
Bayan fitar su AB daga parlorn Daddy Mami ta kalli Daddy a natse cikin sanyi murya gami da mutuwar jiki ta ce "Alhaji nima da za ka ɗauki shawara ta da nace ka haƙura da zance nemawa Abba aure da kayi haƙuri ka ɗan jinkirta zuwa wani ɗan lokaci. Musamman idan ka yi duba da hali da yake ciki.
"Kin ga Mariya ki yi min shiru ki adana shawararki banaso idan ma shawara kike so badawa ki ba 'yarki domin idan lokaci da na ɗiba mata ya cika ba tare da ta kawo mijin aure ba tabbas za ta sha mamakin kalar hukunci da zan yanke akanta.
"Amm....
"Ya isa Mariya na gama magana karki dawo min da hannu agogo baya.
Ba yadda Mami ta iya dole ta ja bakinta ta tsuke duk da a can ƙasan zuciyarta tana jin zafin abinda Daddy ya aikata taya zai dauƙo ɗan wasu, wasu ma da bai da cikakken sani akansu ka mayar dashi naka sannan kuma ka ɓoye hakan ba tare da ka sanar da makusantan ka ba. Wato nufinsa koda mutuwa yayi Abba zai yi gadonsa ita kam wannan fallasuwar sirrin nasa gaba ta kaita da haka kawai za a cuce ta a dauko ɗan shege a gauraya shi da 'ya'yan halas. Da shikenan Abba zai mamaye dukiyar da batasa ba.
Murmushin gefen baki tayi tare da miƙewa ta koma nata parlor.
Tun sanda Sadiya ta baro Parlorn Daddy take kwance a ɗakinta tana kuka ta rasa dalili da yasa take jin ƙunci can ƙasan zuciyarta, duk lokaci ta dubi takardar sakinta da Daddy ya damƙa mata a hannu sai sautin kukanta ya daɗa ƙaruwa.
Siyama ce ta turo ƙofa ta shigo ta daɗe tsaye rungume da hannuwanta a ƙirji tana kallon Sadiya dake rare kuka kafin ta girgiza kai tare da sauke hannayenta, ta taka a hankali ta nemi kusa da ita ta zauna cikin sanyi murya ta kira sunanta "Yaya Sadiya!
Sadiya bata iya amsawa ba saboda kukan da take yi kawai dai ta ɗago ta kalli Siyama, kana ta sake maida kanta ta cigaba da kukanta, a wurinta yin kuka shi kaɗai ne mafita da yai mata saura.
"Ni wannan kukan naki yaya Sadiya na rasa da wane suna zan kira shi kukan farin ciki, kukan rashin cimma buri ko kuma kukan raini wayau?
Cike da madaukakin mamaki Sadiya ta ɗago tana kallon Siyama da farko batada niyar kulata koda kuwa ta zo ne da zimmar rarrashinta, amma kuma wannan furunci da tayi yasa ta haɗiye kukanta har ta kai da furta "Me kike nufi Siyama??"
"Abinda nake nufi ki ware guda daga cikin dalillai dana lissafa da yake da nasaba da wannan kukan da kike yi.
"Bai zama dole sai nayi abinda kike so ba Siyama na fahimci dukkanku gidanan bakwa tausaya min yaya Abba shi kaɗai ne damuwarku.
"Dole mu ɗura damuwar mu akan yaya Abba domin ya cancanci a tausaya masa saɓani ke ɗin da nake ji haushi da takaicinki yaya Sadiya, ina tabbatar miki da cewa kin yi baƙar asara na rasa gwarzo kuma jarumin namiji irin Ya Abba, ba kuma za ki san da ingancin magana ta ba sai ana gaba. Wallahi yaya Sadiya sai kin yi nadamar abinda kika yiwa Ya Abba sai ki yi danasani tozarta Daddy da kika yi.
Siyama tana ƙarashe magana ta tashi ta fice abinta ta bar Sadiya da rusar kuka.
Sannu a hankali Aydah ta kama handle ɗin ƙofar parlorn AB lokaci da Aydah ta shigo parlorn ta hango shi kwance wasu hawaye masu mugun ɗumi ke ta sintiri akan tattausan kumatunsa da wani kalan sauri Aydah ta isa gabanshi ta zube guiwayoyinta abu na farko da ta fara yi shine ɗaura tafin hannunta akan kamatunsa ta shiga goge masa hawaye tun sanda ta zube a gabansa natsuwarsa ta dawo jikinsa bai yi yunƙuri hana ta goge masa hawaye ba, sai ma kallon innocent face ɗinta yake idan aka cire Daddy to Aidah ita ce mutum ta biyu dake bala'in sonshi ko rashin lafiya yake yi Aydah ta dinga kuka kenan har sai ya sami sauki. Shiyasa sometime idan yana rashin lafiya yake ɓoyewa, ko kaɗan bata so ta ganshi cikin damuwa yanzu nan za ta rikice. AB yana gani ta fara kuka ya zabura ya tashi zaune ya yi ƙoƙari ɓoye damuwarsa ta hanyar, kama hannayenta ta miƙe tsaye kusa dashi ya zaunar da ita kafin ya kai da yi magana har ta riga shi "Ya Abba kuka kake yi ko wuri yana maka ciwo ne na kira Daddy ya maida ka asibiti?"
Ta yi magana tana kama t-shirt ɗin jikinsa ta ɗage ta sama tana kallon gun da Sadiya ta caka masa wuƙa, sai dai wurin har ya fara baƙi-baƙi alamar warkewa hannunta ta kai ta shafa tabon dinkin da aka yi masa yadda take lailaya fatar cikinsa ya ji tsigar jikinsa ta mimmiƙe babu shiri ya ture hannunta tare da gyara rigarsa ada fiye da wannan yana shiga tsakaninsa da Aydah bai taɓa ji komai ba. Sai gashi yau da yasan babu wata alaƙa ta jini a tsakaninsu tana taɓa shi ya fara ji feeling shi kan har gobe kallo su Aydah yake a matsayin ƙannansa na jini. Idan ma ya ce ya sauya masu matsayi ina yaga wasu da zai bugi kirji yace 'yan uwansa ne shi kan iyayensa sun cuce shi da sun san cewa basa farin ciki haifarsa miyasa tun yana gudan jini ba su zubar dashi ba, gashi nan sun haife shi sun jifar dashi sun barshi da fuskanta ƙalubale irin daban-daban.
"Ya Abba please talk to me.
Muryar Aydah ya tsikayi a dodon kunnensa cikin shagwaɓar nan nata da ya zama jini jikinta.
"I'm fine Baby Aydah kawai dai ina cikin damuwa na rashin sani su waye iyayena taya aka yi na zo hannun Daddy jefar dani suka yi ya tsinta ko kuma a gidan marayu ya yi adopting ɗina??" Baby Aydah ina so nasan amsoshin waɗannan tambayoyi sai dai kuma Daddy ya yi min gargaɗi akan kada na sake yi mishi zancensu kuma ba zan iya take umarnin Daddy ba.
Sai da Aydah ta sauke numfashi kafin ta gyara zamanta ƙugunta ya ƙara mannewa dana AB "Ya Abba ka yi haƙuri ka ɗaure ka cire duk wata damuwa aranka Allah yana sane da hali da kake ciki a sannu zai warware maka dukka damuwarka, wannan abin zai zo ya wuce kamar ba a yi ba.
"Haka ne Baby Aydah in-sha-Allah zan yi kokari na bi shawararki.
"Thank you Yaya Abbana tashi mu tafi sport field mu yi wasa kwana biyu nayi missing buga wasa dakai, yaya Siyama bata iya komai ba a table tennis.
Murmushi ya yi wanda bai wuce iya fatar bakinsa ba yasan Aydah tana yi haka domin ta kawar masa da damuwar da yake ciki, shiyasa bai mata musu ba ya ce ta je ta canza kaya ta sami shi a field, da gudu ta fice Siyama ta biyo ta zuwa field ɗin suna wasa tana musu tafi da sowa yayin da ihunsu ya kai kunne Sadiya da sauri ta taso daga kan gado ta nufi window ta leƙa ta hango yadda AB yake ta zabgar fara'a ga walwala akan fuskarsa, tun ba a je ko'ina ba farin ciki da walwalarsa sun fara dawowa jikinsa saɓani ita da take ji wani kalar ƙunci haɗe da baƙin ciki yana nuƙurƙusar zuciyarta. Sai da aka fara kiran sallar magarib kana suka dawo cikin gida.
A washegari Daddy ya umarci AB ya koma bakin aikinsa wanda shine ceo na Kamfanin Daddy na siyarda motoci moon light Automobile industry, ba wai iya motoci kamfani yake siyarwa ba, suna sai da cars accessories da kuma abubuwan gyaranta Moon light Automobile industry kamfani ne da ya shahara saboda haɗin gwiwa ne da kamfanin whitepaper Automotive industry Germany, shiyasa motoci da suke kamfani suka fita daban da na sauran kamfanoni. Kaitsaye AB ya wuce ofishin sa dake hawa na huɗu secretary shi ta shigo ta kawo mishi schedule ɗinsa na yau ya duba firstly yana da meeting da team members (employees)na kamfani kana akwai online meeting da zai yi da whitepaper Automotive industry throughout bai huta ba saboda akwai sabuwar mota da kamfanonin nasu za su yi lunching sai around ten na dare ya dawo gida.
#Love story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye novels
#kurman Allo