007
by @jeeddah3256
KURMAN ALLO*
(A beautiful Love story)
NA
JEEDDAH ALIYU
&
ASMY B ALIYU
#Love Story
#Gwagwarmaya
#Team Tagwaye novels
007.
*MOON LIGHT AUTOMOBILE INDUSTRY*
AB yana zaune a office ɗinsa yana duba wasu car design da whitepaper Automotive industry suka tura masa yana selected ɗin wanda suke buƙata a kamfani nasu, secretary shi ce ta shigo tare da sanar dashi yana da baƙuwa amma ta duba bata da appointment dashi. Sai da ya kwaɓe fuska kafin ya tambaye sunanta "Rumaisa Madawaki!
Secretary tasa ta faɗa.
"Let her in.
Ya yi magana kaman mai ciwon haƙora jim kaɗan da fitar secretary tasa Rumaisa Madawaki ta turo ƙofa tashigo tana sanye da turkish Abaya maroon in color tayi rolling da veil ɗin rigar sosai rigar ta karɓi fatar jikinta kasancewar fara duk da fari nata ta ɗan sirka shi da mayukan nan na zamani shiyasa skin ɗinta ya yi wani ɓauuu farinta har ci idanuwa yake. Tun kafin ta ƙaraso AB ya fara shigar ƙamshin turarenta a hankali ta tako yayin da idanuwansu suka sarƙe sosai ya hango ramar da tayi, nan take ya ji zuciyarsa ta karye amma sai ya yi kokari basarwa baya so ta silarsa su dawo da hannun agogo baya. Sai da ta iso gaban desk ɗinsa ta tsaya tare da rungume hannuwanta a ƙirji kallo-kallo suke wa juna shine ya fara janye ganinsa, gami da kawar da kansa gefe ɗaya.
"Ban taɓa tsammani akwai wani dalili da zai zama sanadi rabuwar mu a faɗin duniya nan. Abba idan kai ka shirya haƙura da soyayyarta ni kan yanzu ma na ɗaura ɗamarar yaƙi da duk wanda zai kawo min cikass a soyayyarka.
Ta ƙarasa magana tare da zama akan kujerar dake gaban desk ɗin tana kuma facing ɗinsa, ɗan bazawari murmushi AB ya yi shi kaɗai yasan irin raɗaɗi da yake ciki na soyayyarta sai dai bai ga amfani soyayyar ba tun da ba za ta kai su da mallakar juna a karkashin inuwar aure.
"Ka haƙura dani ko Abba?
Tayi magana hawaye na fitowa daga kwarmin idanunta.
Sai da ya ɗan wargaza
Sumar kansa kafin cikin raunatatciya murya ya ce "Ba zan taɓa iya daina sonki ba Rumaisa sai dai ya zama mana dole da haƙura da juna, duk wata soyayya da muke wa junan mu bata da wani amfani tun da mahaifinki ba zai iya mallaka min ke a matsayin matata, ta sunnah ba.
"AB idan har da gaske ba ka haƙura dani ba to ka bani wani ɗan lokaci in-sha-Allah zan daidaita al'amurranan zan nemi hanyar da Dad zai amince da aurenmu.
"Idan ma nace na jira ki Rumaisa ni kuma nawa mahaifin ya zan yi dashi domin na daukar masa alƙawari nisanta daga gare ki.
"Wacce irin magana ce kake faɗa Abba? Ko dai dama ba ka ji soyayyata kwatankwacin yadda nake jin taka?"
Rumaisa ta faɗa cikin muryar kuka.
"Ba haka bane Rumaisa ke kanki shaida ce akan matsananci son da nake miki you're my first love how do you think zan daina sonki faratt ɗaya??
"Dole nayi wannan tunani Abba saboda hali da ka nuna min ka daina picking calls ɗina daga ƙarshe ma sai blocking ɗina ka yi, Abba wallahi ba zan iya rayuwa idan babu kai. Ka bani haɗin kai mu yi yaƙi kwatar soyayyarmu.
Da girar ido ɗage yake kallonta yana ɗan shasshafa kwatatce sajensa, kafin ya ce "Rumaisa bana so mu yi abunda zai saɓa ra'ayin iyayenmu, mu yi haƙuri mu bi su yadda suke so a rayuwa ba komai kake so kuma ka same shi ba. After all this time Daddy yana ƙoƙarin ganin ya faranta min saboda haka ba zan iya abunda zai ɓata mishi rai ba.
"Nima ban ce ka yi abunda za ka ɓata wa mahaifinka ba kawai i want my love back ka dawo da soyayyar da kake min Abba ka ɗaukar min alƙawari za ka jirani har zuwa lokaci da Dad ɗina zai amince da aurenmu.
Girgiza kai ya yi tare da faɗin "hakan ba zai yiwuwa ba Rumaisa mu haƙura da juna kawai.
"Ba zan iya ba Abba idan ban same ka ba mutuwa zan yi wallahi zuciyana zai buga..
Ta ƙarashe magana tare da saukowa daga kujera ta durƙusa on her knees ta haɗe hannayenta guri ɗaya cikin muryar kuka take faɗin "Dan girman Allah Abba karka bar ni rabuwa da kai zai iya cutar dani ka tausayawa rayuwata.
Da wani kalan sauri AB ya taso ya kama kafanɗunta ya tashe ta tsaye hakan ya bata damar faɗawa ƙirjinsa hugging ɗinta ya yi tana kuka yana rarrashinta da daddaɗan maganganu hakan yasa ta daina kuka, ya ja ta zuwa kan ɗaya daga cikin cushion ɗin da ke cikin ofishin nasa ya ci-gaba da rarrashinta da kalaman soyayya masu sanyayya zuciya.
"Da gaske nake yi AB idan babu kai ba zan iya rayuwa ba dan Allah karka sake juya min baya. Ka duba yadda na lalace tun daga ranar da aka fasa auren mu har kawo yau ɗinan rabon da na zauna naci abincin kirki iyakacina nasha tea shima sai naga yunwa za ta min illah nake ɗan kurɓawa sama-sama.
Rumaisa ta faɗa tana ɗauke hawaye da suka sake silalo mata a kumatu.
Sai lokaci da tai wannan magana AB ya ƙare mata kallon tsaf da gaske kuwa ta rame irin muguwar rama nan wacce da an ganka sai an tambaya ba za a shaida kana ciki damuwa, da sauri ya miƙe tare da nufar desk ya ɗauke car key gami da wayoyinsa yana faɗin "Tashi mu je mu ci abinci dama lokaci tashi na lunch ya yi.
Rumaisa tayi murmushi tare da miƙewa ta ɗauki handbag ɗinta yana gaba tana bin sa a baya yayin da AB ke ci-gaba da faɗin "Daga yau duk abunda zai faru Rumaisa kada ki sake bari kanki da yunwa ina sonki sosai ba zan iya jurewa ba idan wani abu ya same ki.
Ya ƙarashe magana daidai suna isowa parking lot kowanne su ya shiga motarsa suka fice daga kamfani.
Alhaji Sanusi dake tsaye jikin window ofishinsa idanuwansa akan AB da Rumaisa wani kololon baƙin ciki ne ya dunƙule masa a kahon zuciya a fusace ya baro jikin window ɗin ya ɗauki wayarsa ya yi dialling numbern abokin ci mushe sa "Alhaji Umar kaga abinda naga ni kuwa??
"Me ka gani Alhajin Allah?
Alhaji Umar ya faɗa har yana haɗawa da wata 'yar bazawarar dariya.
"Alh Umar wannan shegen yaro tsintatce yanzu nan naga ya fita daga kamfani tare da 'yar gidan Bello madawaki?"
"What??
"Wallahi nake gayamaka ai na zaci ka ga fitar su hankalina ya yi mugun tashi Alh Umar kada waɗannan shegun yara su mayar mana da aiki baya.
"in-sha-Allah hakan ba za ta taɓa faruwa ba bari nayi gaggawar kiran Alh Bello madawaki na ƙara rura wutar al'amari.
"Haka nake so mutumina.
Alh Sanusi ya faɗa tare da hanging up yana saki murmushin mugunta, alƙawari ne ya ɗaukar wa kansa ba zai taɓa bari Alhaji Bashir da shegen ɗansa AB su sake farin ciki a rayuwarsa, shekaru 15 da kafa wannan kamfani shine silar hasassa shi duk wani cigaban kamfani shine ya kawo shi burinsa a ce yafi kowa damawa a wannan kamfani a matsayin sa na ƙani Alhaji Bashir da suke uwa ɗaya amma abin takaici sai da ya gama shan wahala kamfani ya haɓaka ya zama lamba ɗaya, Alhaji Bashir ya ɗauki babban matsayin da yake hari ya ba wa ɗansa AB duk da haka ya danne zuciyarsa ya ci-gaba da aiki a kamfani daga hawan AB kujerar CEO (Chief Executive officer) shegen yaro nan ya dinga bincike da bin diddigi shige da fice kuɗaɗen Kamfani har yai nasarar gano irin almudahana da suka dinga yi shi da financial director, AB bai bar su ba har sai da suka dawowa da kamfani kuɗaɗen da suka sata wannan abin da yai musu shine silar da yasa account ɗinsu yai ƙasa har yau basu farfaɗo ba. Sannan kuma ya bi ya tare gaba ya tare musu baya duk wani motsinsu akan idanuwanshi. Wannan shine silar da ya haifar da zazzafar ƙiyayya tsakanin AB dasu Alh Sanusi daga wannan lokaci suka shiga bincike hanyar da za su kawo ƙarshen AB a kamfani. Alh Sanusi ya yi nisa da tunani ƙarar buɗe ƙofa da Alh Umar ya yi ya dawo dashi natsuwarsa ba tare da ya ƙarasa tunano irin gada zare da suka ɗannawa AB da mahaifinsa.
*GUSTO RESTAURANT*
AB da Rumaisa suna fita kai tsaye
Gusto restaurant suka nufa AB yana gaba tana bin sa a baya AB ya zaɓi Gusto restaurant a dalili yaba da daɗin abincinsu ga kuma wurin babu haniya, bayan an kawo musu menu kowanne su ya zaɓi abunda yake so yaci koda suka kammala ci abinci ƙarfe 3:00pm AB yana duba wristwatch ɗinsa sai da gabansa ya faɗi kasancewa da Rumaisa ya manta da Aydah da ya yiwa alƙawari zai je ya yi picking ɗinta a school agaggauce ya sha ruwa ko ta kai juice ɗin da aka kawo masa bai bi ba ya miƙe tare da kallon Rumaisa yana faɗin "Habibty I have to go bansan cewa lokaci ya tafi sosai har haka ba.
Cike da zallan mamaki ta dire spoon ɗin hannunta ta ɗago "Habibi ina za ka tafi kake wannan saurin??
"Zan je nayi picking Aydah a school kinga lokaci ya tafi sosai sai mu yi waya.
Yana ƙarashe magana bai jira jin ta bakinta ba ya nufar entrance ɗin fita da sauri ta bishi da kallo wannan hali na AB dangane da irin wannan kulawar da yake ba wa ƙannansa yana bala'in ƙona mata rai duk wani abu da ya shafe su sai ya dinga wani rawar ƙafa more especially wannan brat girl Aydah, yanzu da tasan babu alaƙa ta jini a tsakanin shi da Aydah sai ta wani irin mugun kishi ya lulluɓe ciki da wajen zuciyarta, tsabar takaici sai ture abinci tayi ba don ta ƙoshi ba ta ɗauki handbag ɗinta a fusace ta bar restaurant ɗin.
*CRESCENT INTERNATIONAL SCHOOL*
Tun kafin AB ya yi parking ya hango Aydah tana ta faman kumbure fuska murmushi ya yi yasan yau sai sun yi daru da ita Aydah ba dai rigima ba har ta siyarwa tana dashi. Sai da ya yi mata horn kusan sau uku kafin ta nufo wurinsa duk da yasan ta ganshi tun ma kafin ya yi parking ita a dole fushi tayi fushi, tana zuwa buɗe backseat ta jefa backpack ɗinta kana ta zagaya ta buɗe front seat ta zauna, lulu eyes ɗinsa ya watsa mata yana sakar mata da tsadadden murmushinsa. Turo baki tayi gami da kauda fuska tana ci-gaba da kumbure-kumburenta cike da tsokana ya fara yi mata waƙar da yake mata sanda tana yarinya muddin yana so saka ta kuka a wancan lokaci ita yake mata "Aididi, Aididin ya Abba mai majina a hanci tayi k....
"Ya Abbaaaaa! Please stop that horrible song of yours na tsani wannan waƙa bana sonta.
Aydah ta faɗa tamkar cikin muryar kuka, yadda ta kwabe fuska yai masifar ba wa AB dariya sosai ya dinga yi mata dariya ita kuma ta ƙara hasale wa sai kawai ta kwaɓar da seat ta kwanta tare da lumshe idanuwanta "okay I'm sorry my little baby gayamin me kike so na siya miki kafin mu isa gida?"
Taƙi ta tanka masa sai rarrashinta yake tai biris dashi "Shikenan tun da ba za ki kula ni ba nima nayi fushi daga yau mun bata karki sake yi min magana.
Ya yi magana shima yana turo baki kaman ita. Aydah tana ji abunda ya faɗa tai sauri tashi daga kwance da take ta mayar da seat ɗin daidai fuskarta ya bayyanar da irin razanarwa da tayi na ji furuncinsa zuciyarta har wani kalar bugawa yake yi ba abunda ke sauri tayar mata da hankali irin Ya Abba ya ce ya yi fushi da ita "Ya Abba dan Allah karka yi fushi dani.
Tayi magana yayin da idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, a natse AB ya juyo ya kalleta yaga yadda take danne hawayenta murmushi ya sakar mata yana faɗin "who touch my Baby??
"Ya Abba ne.
Ya faɗa sounding so childishness har wani kalar turo ƙaramin bakinta take yi wanda hakan ya daɗa ƙarawa fuskarta kyau, a daidai wani super store ya tsaya ya siya mata tarkace chocolate da biscuits, a bakin gate ya ajiye ta bai shiga gida ba yana kara jaddada mata ta tabbata taje islamiyya idan ya bincika bata je ba zai yi fushi da ita. Hakan yasa tana shiga gida ta wuce bathroom tayi wanka ta shirya cikin uniform ɗinta na islamiyya da yake Siyama bata dawo daga school ba dole ita kaɗai za ta tafi ko abinci bata tsaya ci ba ta fice direban dake kai su school ya kaita.
#Love Story 2023)2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#team tagwaye Novels
#Kurman Allo