19
by @realeshaa
*SAWUN GIWA*
_Ya take na Raƙumi_
_By_
*Aishatu Abdullahi Idris*
_REAL ESHAA_
*F-R-PG 19*
Acan Masarautar Sarki Aliyu Ahmad Zaman kuwa.
Gimbiya Faiza ce tsaye a jikin window Bedroom ɗinta ta tsirawa farfajiyar gidan ido tana kallon yanda tarin Matan gari da maza ke tsaye sunyi layi wanda a ƙalla sunfi dubu yayin da aka ƙawata cikin gidan da wasu irin jeren Balloons sky blue da fari masu masifar kyau baki ɗaya cikin gidan ciki yake da tarin mutane kala daban-daban yatsanta manuniya take ɗan bub-bugawa ajikin glass ɗin window.
Kallo ɗaya zaka yiwa fuskarta ka hango tsantsan ɓacin rai da tarin damuwa.
Wayarta dake riƙe hannun hagune ya hau ruri cikin fesar da numfashi tayi picking ganin sunan Hajiya Hassana na yawo a screen ɗin yasa tayi picking kana cikin sanyi tayi sallama daga ɗaya bangaren Hajiya Hassana cike da kulawa tace.
“Fa'iza meke faruwa kwana biyu ina kiran wayarki baya shiga tunda mukayi waya kan cewa zakuje wajen Boka Linƙinkiyas Kufr”.
Zazzafan Ajiyar zuciya mai gauraye ƙunan zuciya Gimbiya Faiza ya tasaki tare da cewa.
“Hassana na rasa ya zanyi da Meerah duk wani abu da zai kawo min cigaba ya zama silar farin ciki na sai Meerah ta ruguza muddin ya shafi Abdallah”.
Cikin rashin fahimta Hajiya Hassana tace.
“Ikon Allah ince ko wani abin ta sake yi?”.
Cikin tafarfasan zuciya Gimbiya Faiza ta kwashe duk yanda sukayi awajen boka ta faɗa mata ta ɗaura da cewa.
“A yanzu maganar da nake Miki Boka yayi fushi dani yace kada mu sake taka inda yake muddin Muna so mu tsira da ranmu da kuma lafiyarmu saboda baƙin mugunta irin na Meerah ta rabani dashi yanzu ina kike tunanin zamu sake samun Boka mai aiki kamar wannan”.
Cikin takaici Hajiya Hassana tace.
“Ke wannan yarinya akwai Sha-sha-sha wlh baki ɗaya halinsa ɗaya da Faty babu abinda suka iya sai wauta da shashanci ai ita tayiwa kanta dan haka kada ki damu akwai wani sabon Boka daya fito a Dutsen Kura aikinsa kamar yanka wuka zamu je”.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya da jin sassauci Gimbiya Faiza tace.
“Toh shikenan”.
Hira suka ci-gaba dayi kana daga bisani sukayi sallama...
Gimbiya Faiza kuwa tsayuwa ta cigaba dayi awajen tana ayyana wa aranta koda wani abu zata sakeyi bazata sake sanarwa Meerah ba bare kuma ta ɓata mata bajet.
Aɗan razane ta juya bayanta jin andafa kafaɗarta da sauri ta saki wani gauron numfashi ganin Meerah sai ta tamke fuskarta tare da ture hannunta Muryan ta cike da rauni da kuma ƙunci tace.
“Shin me kike so agareni Meerah?Bayan kin cuci rayuwata kin tarwatsa min duk wani shirina?”.
Marairece fuska Meerah tayi tare da faɗin.
“Haba Aunty Fa'i wani irin cuta kuma,Koda zan cuci kowa aduniya bazan cuceki ba”.
Alalace Gimbiya Fa'izah ta kalleta ji take tamkar ta shaƙe wuyanta badan nisan kwana da tsawon rai ba da tuni sun mutu awajen Boka Linƙinƙiyasir Kufr domin saida sukayi kwana biyu kafin suka koma cikin hayyacinsu hakan ma saida aka haɗa da roƙon Allah da addu'oi ta haɗiye wani abu mai masifar ɗaci kana tace.
“Ba yau kika fara cutata ba aduk sanda zan shirya wani abu akan Abdallah sai kin ruguza min komai bayan asarar maƙudan kuɗi da kike yimin awannan karon har rayuwata ma neman halaka min shi kika kusa yi”.
Jingina da jikin window Meerah tayi tare da sassauta Murya kana tace.
“Aunty Fa'i kiyi haƙuri nifa bada wani nufi nayi ba nayi hakane domin ceto rayuwar Abdallah bazan iya juran ganinsa cikin mawuyacin hali bare kuma hauka kina ganin shegen mutumin nan da babu Allah aransa wai so yake ya kwanta dani”...
Kallonta kawai Gimbiya Faiza keyi tana jin takaici aranta cikin rashin walwala ta cigaba da cewa.
“Sannan kuma ainihin abinda ya kai mu bashi kika faɗa ba kada fa ki manta munje ne adomin Asanya masa tsanar wannan yarinyar aransa sannan Asanya masa soyayyata amma sai kika ƙi faɗa kawai kika faɗi son ranki!”.
Hannu ta ɗaga mata afusace tace.
“Dakata Meerah kada ki sake fusata min zuciya da wa'annan kalaman naki marasa tushe da ma'ana kinsan maƙudan kuɗin dana kashe domin wannan aikin amma cikin ƙanƙanin lokaci kika lalata komai da wannan banzan ƙwaƙwalwar taki!”.
Baki ta taɓe tare da ɗage kafaɗarta kana tace.
“Oho dai kuma ai asarar kuɗin ma bake kaɗai kika yiba har dani”.
Cikin tsuke fuska Gimbiya Faiza tace.
“Ok haka kika ce kenan?,Toh shikenan tunda hakane wayonki da dabarar ki sai ya cire masa yarinyar aransa”.
Cikin rashin damuwa tace
“Wannan ba matsala bane sannan ina da ƴan daban da zan sanya su nemomin wannan tsinanniyar yarinyar ako ina take domin bani da abokiyar ƙiyayya sama da ita”.
Ta cije laɓbanta tare da cigaba da cewa.
“Na sanya neman ta aduk inda take afaɗin garin nan ida har wani kuskure ya ɗebeta tashigo wannan gidan saina illata mata rayuwar ta sai tayi dana sanin haihuwar ta da akayi tazo doron duniya”.
Dogon tsaki Gimbiya Faiza taja cike da takaici tace.
“Na daɗe banga ballagaza Sha-sha-sha irin kiba kina cusa kai babu ƙwarjini duk wannan haukan da kike yi bai san kina yiba idan har zaki nutsu ki nutsu mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin samun abinda muke muradi! Akansa”.
Ganin yanda jikin Meerah yayi sanyi yasa ta saki murmushin samu nasara kana ta cigaba da cewa.
“Kinga idan har hakan ya kasance shikenan burin mu zai cika zaki mallaki Abdallah amatsayin miji Ni kuma zan samu kujera domin na zamo sarauniyar gobe kiyi tunani akan Maganata”.
Kugunta ta riƙe tare da faɗin.
“Shikenan zanyi tunani akai amma duk wani abu da za ayi kada kiyi yunƙurin cutar da rayuwar Abdallah domin aikata hakan zaisa na fallasa sirrinki! Sannan na tarwatsa duk kan shirin ki”.
Dariya Gimbiya Faiza ta sanya tare da faɗin.
“Baki da matsala,Bari naje na shirya kada afara bamu isa wajen ba”.
Har ta kai bakin ƙofa ta juya tare da kallon Meerah data faɗa duniyar tunani kana tace.
“Kiyi taka tsantsan da Gimbiya Aysha domin kinsan bata da mutunci ko kaɗan zata iya kunyataki acikin taron mutane so duk wani abu da kika san zai haɗaki da ita ki kiyaye”.
Kai ta gyaɗa kana ita kuma ta fice.
Waya Meerah ta ɗago tare da dealing wani number bayan an ɗauka tayi magana na tsawon minti uku kafin ta ajiye wayar ta shiga toilet ranta fessss.
Acan wajen Masarautar kuwa Matan gari ne da maza sunyi layi-layi wanda aƙalla yawansu ya haura sama da dubu ɗaya koma fiye da hakan
Sosai aka ƙawata gidan da wasu irin lafiyayyun furanni farare masu kyau da ƙamshi yayin da ƙofar gidan akayi wani irin desaring na ƙofa Sky blue da fari inda aka rubuta _(HAPPY BIRTHDAY PRINCE ABDALLAH ALIYU AHMAD ZAMAN)_
Kana aka kewaye su da wasu irin balloons Fari da Sky Blue daga cikin gidan kuwa baki ɗaya an canza launin gidan da wasu irin kayan sarauta masu kyau da tsari wani irin adon ƙawa da ƙasaita aka yiwa ƙaton _KADAN_ dake tsakiyar gidan wanda wani irin ruwa mai kyau kalar dark blue ke zuba daga cikinsa...
Yayin da acan Garden aka wani irin ƙawatashi da wasu irin silver color ɗin kujeru masu kyau da tsari a jera da wasu irin flowers masu ƙawa da ɗaukar hankali sai wani ƙaton cake da ake gewayeshi da wani irin fitilu masu canza launi duk da cewa rana amma suna haskawa daga can gefe wasu kujeru ne na alfarma.
Baki ɗaya Garin cike yake da manyan manyan baƙi Kama daga Govnor jahar Borno Minister Borno Sarkin Bauchi ɗan Govnor Gombe da kuma ƴar Sarkin Yola wacce ta wakilci Mahaifinta sai manyan mutane abokan kasuwanci sa na ƙasashe da ban da ban.
Acan falon Ammie kuwa Sir Abdallah ne tsaye cikin wani farin yadi mai taushi da sulɓi sai sheƙi yake yayin da ya ɗaura Neavy blue Alkyabba mai taushi da ƙyalƙyali akansa yayi rawani da farin hirami kana kwantaccen sumar kansa zuwa sajensa yayi luf-luf sai ƙyalli da ɗaukar ido yake ta kalmin ƙafarsa kuwa fari ne ƙal mai azabar kyau yayin da hannunsa ke ɗaure da Neavy blue ɗin agogon diamond.
Anutse Ammie ta kallesa tare da cewa.
“Masha Allah _Fatabarakallahu Akhsanil khaliƙin_ tsarki ya tabbata ga Ubangiji daya ƙawa wannan halitta tasa”.
Lallausan murmushi ya sakar mata cikin tarin ƙaunarta yace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum”
Cikin yaba kyawun da yayi tace.
“ Autana kayi kyau Ubangiji Allah ya kare ka ya ƙaro maka shekaru masu tarin albarka Allah ya nuna min ranar Aurenka Ubangiji ya cika duniyarka da farin ciki ya kuma yaye maka duk kan baƙin ciki da ƙunci”.
Amintaccen murmushi ya saki wanda ke ƙara wa fuskarsa kyau kana yace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Ammie na”.
Gyaran Murya tayi tare da cewa.
“Ya kamata ka fita afara gudanar da taron tuntuni angama shirya komai kai ake jira Sannan afara rabawa bayin Allah kyautar su domin akwai rana wasu sun fito ba tare da izinin mazajensu,wasu kuma masu ciki ne sannan akwai masu ƙananun yara toh dan haka kada aɓata kowa lokaci ya janyo wasu matsala wajen Mazajensu”.
Numfashi ya fesar tare da shafa sumar kansa kana yace.
“Ok Ammie kisa a abuɗe store ɗin kafin na fito sannan ki haɗa min da takardun makarantar domin nayi Singh akai”.
Jinjina kai tayi akuma dai-dai lokacin.
Gimbiya Aysha ta fito cikin wata lafiyyar Gezner Neavy blue yayin da ta ɗaura Farin Alkyabba mai ratsin blue jikinta na fitar da sanyayyan ƙamshi mai ratsa zuciya.
Yalwataccen murmushi Ammie ta saki idanunta akan Gimbiya Aysha ta furta.
“Fatabarakallahu Akhsanul Khaliƙin Ubangiji Allah ya tsareku daga sharrin abin ƙi mutum ko Aljan Allah ya azurtaku da salihan ƴaƴa”.
Ƙayataccen murmushi ya saki tare da gyara tsayuwar sa kana ya riƙe tafin hannunta tare da langwaɓar da kai muryarsa cike da shagwaɓa yace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum but Ammie”...
Sai kuma yayi shiru yana shafa girarsa kafin Ammie tace wani abu wayarta ya ɗauki ruri ganin sunan Sarki Aliyu Ahmad Zaman yasa tayi saurin picking tare da sallama shiru tayi na tsawon minti biyu kafin tace.
“Ok”.
Katse kiran tayi tare da kallon Sir Abdallah dake gyara zaman alkyabbarsa kana tace.
Autana Abieynka yace kowa ya gama hallara kai kaɗai ake jira”.
Ahankali ya fesar da numfashi kana yace.
“Ok Ammie kuje zan zo in same ku”.
Hararansa Gimbiya Aysha tayi tare da faɗin.
“Ohhh yaron nan Allah ka fiye Lazy da son jiki me zaka tsaya yi kaje ka sallami mutane”.
Hararanta yayi kana yace.
“Kije mana ai zan biyo bayanki akwai saƙon da nake jira mai muhimmanci ne”.
“Ba wani saƙo Malam ka wuce muje bayin Allah na kan rana atsaye suna jiranka”.
Lumshe Idanunsa yayi tare da cewa.
“Please kada ki dameni ki rabu dani”.
Baki ta taɓe kana tace.
“Hmmm gwara ka ajiye wannan Miskilincin naka anan,kada kaje ka tsora ta al'umma da wannan murtuƙeƙken fuskar taka sukasa tsayawa karɓar tallafin”.
Ta ida maganar tare da bin bayan Ammie da tuni ta fice.
Zama yayi aɗaya daga cikin kujerun falon tare da fesar da da sanyayyan numfashi kana ya dafe goshinsa da hannunsa na hagu tare da ciro wayarsa number Sir Auwal yayi dealing.
Daga ɗaya ɓangaren ringing ɗaya Sir Auwal ya ɗaga cike da damuwa yayi wa motarsa key tare da cewa.
“A.A Zaman ka bani minti goma gani nan zuwa wani abu ne ya riƙeni”.
Ajiyar zuciya Sir Abdallah ya sauƙe tare da cewa.
“Ok but kayi sauri dan Allah wallahi na ƙagu”.
Kana ya katse kiran tare da miƙewa ya gyara zaman Alkyabbarsa ya fita da sauri Security biyar tsaye dake mara masa baya cike da takun ƙasaita da izzah yake tafiya yayin da baki ɗaya ilahirin jikinsa ke fitar da sihirtaccen ƙamshi.
Ahankali ya nufi wajen Idanunsa ya sauƙe akan dandazon mutanen dake gidan wanda iya kallon idon ka Al'umma Annabi yayin da busar Algaitu da kiɗan taushi ke sake yawaita acikin wajen...
Ya mutse fuska yayi sam baison wannan kiɗe-kiɗen...
Ahankali ya sauƙe Idanunsa akan Meerah dake sanye cikin wani fitet gownt Neavy blue daya matseta fuskarta yasha heavy make-up wani ɗan figigin mayafi na riƙe ahannunta yayin da wuyanta da hannunta ke maƙale da sarƙan Gwal da awarwaronsa kana kunnenta maƙale da ɗan kunnesu da zobe.
Baki ya taɓe tare da kawar da kansa gefe idanunsa suka sauƙa akan Gimbiya Khairat dake sanye cikin wani Ɗanyel boyel Blue Black da ratsin fari aciki fuskarta ɗauke da simple make-up da kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar Asalin bafulatace.
Kyakkyawa ce ajin farko ga kamewa da izzah.
Yayin da gefenta Gimbiya Aysha wacce bisa duk kan alamu ita ta faɗawa Gimbiya Khairat irin shigar da Sir Abdallah yayi yasa itama tayi wanda kayansu ya kusan zuwa kala ɗaya da Meerah dan ko wacce irin shigarsa tayi Idanunsa ya sauke ɗaya gefen wanda duk matan manya da ba zai iya gane suba Idanunsa ya ɗauke daga kansu ya cigaba da tafiya cike da nutsuwa yayin da kallo ya koma kansa kowa sai yaba kyawun sa yake musamman ƴan matan wajen.
Kai tsaye gyefen da Sarki Aliyu Ahmad Zaman ke zaune ya nufa daga gyefen damarsa ya zauna yayin da Governor ke zaune gefen damansa daga hagunsa kuma Minister Kuɗi ne
Daga ɗaya bangaren masu ruwa da tsaki na kewayen Borno sai manyan baƙi da suka zo daga wasu ƙasashe cikin su harda Larabawa, Indiya wa,Turawa da dai sauransu...
Ajiyar zuciya Sarki Aliyu Ahmad Zaman ya sauƙe ganin tilon ɗan sa fuskarsa ɗauke da ƙayataccen murmushi wanda ke nuna zallan ƙaunar daya ke masa ya miƙe tare da gyara zaman rawanin kansa cike da nutsuwa da ƙasaita ya karɓi micro phone da Security ya miƙa masa zaman Alkyabbarsa ya gyara kana yace.
_“Innal hamdulillah nahmaduhu wanasta'inuhu wanastagfir wana'uzu billahi min shururi anfusna wamin sayyi'ati a'amaluna man yahdillahu falamudillalah walam yudilil fala yahdilana wa'ashhadu la'ilahu wahdahu lasharikslahu Wa'ash'hadu Anna Muhammad Rasulullahi,Amma ba'ad Assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuhu”..._
Atare dandazon Al'ummar Annabi dake wajen suka haɗa baki da faɗin.
“Wa'alaikum Salam warahmatullah wabarkatuhu”.
Cikin nutsuwa da kamala ya kalli tarin mutanen da iya ganin idanunsa sune kana ya kalli mai girma Govnor yace.
“Da farko ina yiwa mai girma Govnor Barka da zuwa wannan taron mai albarka tare da Ministry,Da kuma sauran al'umma wanda lokaci bazai bani damar ambaton sunan suba da fatan kunzo lafiya”.
Ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cigaba da cewa.
“Agaskiya nayi matuƙar farin ciki da ganin tarin mutanen da banyi zaton ganinsu a'wannan taron ba haƙiƙa nida ɗana munyi matuƙar farin ciki mara misaltuwa abisa wannan taron da kuka halarta.
Ɗaya daga cikin jerin matan dake tsaye ne awaje ta taɓe baki tare da cewa.
“Dan Allah mu ba wannan surutun muke buƙata ba kawai ku raba mana abinda ya kawo mu tafi haba tun yaushe muke tsaye anan saboda ku kuna cikin inuwa shiyasa zaku barmu ashanye!!”.
Kallonta sauran matan dake kusa da ita sukayi kana wata ƙatuwa gajera tace.
“Haba baiwar Allah kiyi haƙuri mana ke yaushe ma kika zo da zaki ishemu da mita ina kallo fa satin layi ki kayi idan kinsan ba zaki iya haƙuri ba ai sai ki tafi haba mutane basu da haƙuri haka”.
Ganin ƙibar matar da kuma yanda take da zafi yasa ta tsuke bakinta tana ƙunƙuni...
Sarki Aliyu Ahmad Zaman kuwa cike da dattako ya cigaba da faɗin.
“Wannan itace ranan zagayowar haihuwar Bundi Abdullah duk da cewa awani ɓangaren ba murna ya kamata mu tayi shiba saboda wasu daga cikin kwanakinsa ne suka ragu kamata yayi ku taya shi jimami da baƙin ciki”.
Ya sauƙe numfashi tare da cigaba da cewa...
“Duk da cewa wannan Birthday yasha ban-ban da sauran wanda sauran Ƴan mata da samarin wannan zamanin keyi wanda za'a je akama hall ayita kiɗe-kiɗe da raye-raye da kuma aikin ashsha, tabbas Abdallah mutum ne na daban wanda nake alfaharin Kasancewarsa ɗana kuma Sarkin ku na gobe a wannan karon ma zai gudanar da kyautar kamar yanda aka saba ko wacce Shekara muna kuma fatan Ubangji ya kawo sauƙi acikin wannan rayuwar tamu”.
Jinjina kai Jama'ar dake wajen sukayi cike da gamsuwa da maganar sa suka amsa da Ameen...
Ahankali sarki Aliyu Ahmad Zaman ya miƙawa Sir Abdallah Microphone anutse Sir Abdallah ya karɓa tare da miƙewa ya gyara zaman Alkyabbarsa tare da lumshe Cat eyes ɗin sa kana ya motsa laɓɓansa tare da cewa.
“Ina yiwa baki ɗaya al'ummar da suka halarci wannan taron Barka da zuwa tabbas nayi farin cikin ganin wannan mutanen saboda ni suka halarta haƙiƙa bakina bai isa godiya agareku ba sai dai fatan Alkhairi”.
Ya fesar da numfashi tare da leƙa hanyar shigowa wajen kana ya lumshe Idanunsa tare da cigaba da cewa.
“Tabbas wannan ranan rana ce ta farin ciki kuma baƙin ciki atare dani domin kwanakin haihuwata sun ragu wasu sukan ɗauki wannan ranan amatsayin ranan farin ciki da sharholiya sai dai kash!Wannan ranan ba rana bace ta farin ciki ranace daya kamata kowa yayi kuka domin kwanakin sa na duniya ne suka ragu”...
Murmushi Meerah ta saki tare da tallafe kuncinta kana ta tsirawa idanunsa da bakinsa ido suna abinda suka fi burgeta atare dashi baki ɗaya ta shagala da kallonsa ta jiyo sautin murya cikin sauri ta ɗaga kanta.
Ɗaure fuskar tayi tare da watsawa Gimbiya Khairat dake tsaye a kanta kollon banza kana tace.
“Me kika ce?".
Cike da isa Gimbiya Khairat tayi dariyar rainin hankali tare da faɗin.
“Cewa nayi iska na wahalar da mai kayan kara wanda kike dominsa bai san kina yi ba”.
Dariyar rainin hankali Meerah tayi duk da kuwa yanda kalamanta suka daki zuciyarta kana cikin nunata da yatsa tace.
“Ke ƙaramar mara kunya ku caka ki fita idona domin ruwa ba a san kwando bane Abdallah dai mallakina ne sannan maganar iska na wahalar da mai kayan kara gaki nan babbar wahalalliya kin biyi motar haya kinzo wanda kika zo domin sa bai sani ba!”.
Cike da izzah da ƙasaita Gimbiya Khairat ta juya manyan idanunta tare da cewa.
“Kinsan cewa *Sawun Giwa ya take na raƙumi* domin Ni jinin sarauta ce zan kuma nuna miki ƙarfin sarauta tafi na mulki domin Prince Abdallah Aliyu Ahmad Zaman mallakina ne ɗan sarauta sai ƴar Sarauta”.
Cike da tsanar ta Meerah ta nunata da yatsa kana tace.
“Ni kuwa zan tabbatar miki da cewa Ubana shike da iko da gaba ɗaya Maiduguri da Arean ta da ace acikin jahar Borno kike da saina tabbatar miki da cewa tabbas _Sawun Giwa ya take na raƙumi_ domin da ƙarfin mulki zansa ajinjige ƙaramar masarautar da kuke tun ƙaho dashi”.
Afusace Gimbiya Khairat ta buɗe baki da niyyar mayar mata martani Gimbiya Aysha tayi saurin ƙarasawa wajen tare da jan hannun ta kana tace.
“Calm down Khairat akwai mutane da yawa kada kiyi abinda bai dace ba”.
Ƙwaffa Gimbiya Khairat tayi tabbas sai ta nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane.
Dogon tsaki Meerah taja bayan barinsu wajen kana ta koma ta zauna tamkar zuciyarta zai fashe...
Acan waje ma jin sautin muryan Sir Abdallah ya gigita ƴan matan dake wajen ko wacce birninta ina ma ace ya zamo mijinta data gama samun burin duniya ..
Sir Abdallah kuwa cike da rashin walwala ya kalli agogon Diamond dake ɗaure atsintsiyar hannunsa kana yace.
“In sha Allahu ba tare da ɓata lokaci ba zamu fara gabatar da abinda ya kawo mu saboda da yawa daga cikinku kuna tsayene arana muna kuma roƙon Ubangji ya kawo mana lafiya a ƙasar mu Nigeria da Niger ya kuma ɗaukaka mana musulunci a kan kafirci Allah ya bawa ƙasar Palastin Sa'a akan Israel”.
Atake wajen ya ɗauki tafi tare dayi masa addu'ar Alkhairi da kariya.
Koma wa yayi ya zauna akan kujeransa sai kuma yayi saurin ɗaga kansa hango Sir Auwal na nufo kansa sanyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da tsira masa idanu har ya ƙara sa kusa dashi...
Anutse Sir Auwal ya ƙara so tare da zagayawa gyefen da Sir Abdallah ke zaune kana ya miƙa masa jakar dake riƙe ahannunsa wanda bisa duk kan alamu kudi ne wanda za'a raba kallon Jakar Sir Abdallah yayi batare daya amsaba yace.
“Ina take?”.
Kai Sir Auwal ya girgiza cikin rashin walwala yace.
“I don't know nayi iya bakin ƙoƙarina tare da yin amfani da address ɗin daka bani but”.
Cikin sauri Sir Abdallah ya ɗaga masa hannu zuciyar sa na wani irin bugawa da Masifeffen ƙarfi cikin wani irin yanayi yace.
“Ban fahimceka ba ina ce na baka address ɗin gidan?,Auwal zuciyata na sanar dani cewa tana cikin mawuyacin hali U support to find her idan baza ka iya fita ba jillni zan fita in ne Meta ”...
Numfashi Sir Auwal ya fesar tare da cewa.
“Na bin ciki wannan address ɗin amma sam babu ita na shafe sama da awa acikin unguwar”.
Gyaran murya da Sarki Aliyu Ahmad Zaman yayi yasa Sir Abdallah kasa cigaba da faɗin abinda yayi niyya cikin mutuwar jiki da tsinkewar zuciya ya karɓi jakar dake hannun Sir Auwal sannan ya buɗe ya ciro bandir ɗin kuɗi kana ya bawa security jakar yana riƙe dashi.
Fita daga kan high table ɗin yayi ya sauƙa ƙasa kana ya umarci ɗaya daga cikin security daya kaiwa Gimbiya Aysha jakar kuɗin.
Anutse ya fara bin Layin da Mazan ke jere abakin Gate mutum na farko ya miƙawa Naira dubu Hamsin da shadda shampoo da kuma turare aciki sai kuma ya haɗa da da Security aka bashi Buhun shinkafa,Buhun Masara, Catoon ɗin taliya, Maggi.
Zubewa dattijon mutumin yayi cikin zubda hawaye yace.
“Nagode, Nagode Nagode Bundi Ubangiji Allah ya albarkanci rayuwar ka Allah ya tsareka daga sharrin mutum ko aljan”.
Kallonsa Sir Abdallah keyi cike da tausayinsa domin mutumin ya manya zai kai shekara tamanin ko saba'in da biyar.
Ckin rawan Muryan dattijon ya cigaba da cewa.
“Yau tsawon kwanaki biyu nida iyalaina bamu ci komai ba,Amma yau gashi adalilinka na samu kuɗin da zan yi jari da kuma abinci da zan ciyar da iyalaina na tsawon wani lokaci Allah ya baka zuri'a ɗayyiba ubangiji ya biya maka bukatar ka duniya da lahira”.
Lumshe idanu sir Abdallah yayi cike da tausayin Mutumin yace.
“Amin,Kada ka damu Baba Dan Allah kabar kuka gobe idan Allah ya kai mu kazo ka sameni”.
Godiya mutumin ya masa tare da fita.
Shikam cikin sanyi jiki da tausayin halin da talakawa ke ciki ya cigaba da rabawa ko wanni mutum dubu Hamsin da buhun shinkafa,Buhun Masara, Catoon ɗin taliya, Maggi,sugar...
Gimbiya Aysha, Meerah da kuma Ammie ce cikin nutsuwa suka fara bin gefen da tarin Matan ke zaune wasu na tsatstsaye Cike da tausaya wa Ammie ta karɓi Bandir ɗin dubu-Dubu tana miƙawa ko wacce mace Dubu talatin da Turmin zani da turare da Omo aciki wanda Aka rubuta _(Happy Birthday A.A.Zaman)_ kana ko wacce a haɗa ta da buhun shinkafa Buhun Masara Catoon ɗin taliya da sauransu kamar yanda aka bawa Maza. Meerah Kam sai wani yamutse fuska take cikin da isgilanci ko kaɗan bata so hannunsu ya haɗu da nata ganin abinda take yasa takaici ya cika zuciyar Gimbiya Aysha ta rasa dalilin da yasa Ammie ta sanya ta acikin rabon Ammie kuwa tayi hakane domin ta sabawa Sir Abdallah da sanya Meerah acikin al'amuran sa.
Cike da tausayawa Sir Abdallah da sir Auwal ke rabawa mutane kuɗin yayin da security uku ke tayasu.
Haka suka cigaba da rarraba kyautar cike da tausayawa saɓanin Meerah dake wulaƙantasu...
Mimmiƙewa matan dake zaune suka fara suna ɓata layin tare da ture-ture ko wacce burinta ta karɓa kada ya ƙare akanta.
Microphone Meerah ta karɓa cikin ɓacin rai ta buga musu tsawa tare da cewa.
“Ya kamata Ku nutsu kusan abinda kuke bamason ƙauyanci da Jahilci nan ba wajen siyasa bane temakon ku akeson yi idan kuka ce zakuyi hauka zan kora ku waje duka ku rasa”.
Cikin sauri Ammie ta karɓi Microphone daga hannunta tare da girgiza mata kai cikin sassauta murya tace.
“Dan Allah ku nutsu Koda ace baki ɗaya Matan Jahar Borno ne ba iya Biu ba zaku samu wannan kyautar ba sai kun tashi hankalin ku ba kunga akwai masu yara sannan akwai masu ciki da kuma tsofaffi dan Allah ku kula kada kuji ciwo In sha Allah babu wacce zata tafi batare data karɓa ba”.
Ihun murna suka sanya tare da cewa Allah yatemiki Uwar marayu sarauniyar mu Ubangiji ya ƙara miki nisan kwana.
Murmushin tayi tare da faɗin.
“Ameen”
Kana suka ci-gaba da rabo.
**
Cikin sauri Maryam ta nufi ɗakin Mamawo har tana harɗe ƙafa tare da ɗaga sautin muryarta tace.
“Mamawo”.
Cikin washe baki Mamawo dake tare da mata wanda suka fara taruwa domin ɗaurin Aure tace.
“Ya akayi Maryama?,Har yanzu ba kiyi wanka ba gashi an kusa dawowa daga ɗaura Aure?”
Cikin tashin hankali Maryam ta sharce zufan daya karyo mata sam bata damu da kallon da matan ke mata ba kana tace.
“Nifa banga Sister Neenah ba na duba ko ina?”.
Zare Idanu Mamawo tayi tare da fitowa daga cikin ɗakin kana ta furta.
“Watanin me kike nufi da wannan maganar Maryama maza kije ki duba ko ina”.
Aruɗe Maryam ta girgiza kai kana tace.
“Allah dagaske bata nan duk na duba ko ina?”
Afusace Malam Sa'idu da shigowar sa kenan ya ɗaga hannu ya kwaɗa mata mari ciki fushi da tsananin ɓaci rai yace.
“Ƙarya kike munafuka algunguma ke kinfi kowa sanin inda take”.
Kai ta girgiza hawaye na kwaranya daga Idanunta kana jikinta na rawa tace.
“Wallahi Allah bansan inda take ba tunda na fita ban sake komawa ɗakin ba sai yanzu da Baba yace in kirawo ta”.
Afusace ya ɗaga hannu tare da sharara mata mari akaro na biyu da yasa taga gilmawar taurari cikin hargowa da masifa ya tureta baya tayi taga-taga zata faɗi kana yace.
“Dan Ubanki idan har kika yi sanadiyar gudun yarinyar nan wallahi saina sabau taki”.
Cikin tsananin raɗaɗin marin daya mata ta dafe kuncinta tare da fashewa da kuka.
Mamawo kuwa kallon matan da suka tsaya cirko-cirko suna sauraronsu tayi kana tace.
“Toh mun gode zaku iya tafiya”.
Abin ka da mata tsegumi baya wuce su tun kafin su isa gidajensu magana ta bazama cewa Neenah ta gudu yayin da wasu ke cewa gwara da ta gudu saboda gallazawar Mamawo wasu kuwa cewa suke yawon karuwanci ta tafi.
Acan wajen ɗaurin Aure kuwa cirko-cirko suka tsaya jin amarya ta gudu cikin sauri tamkar zai tashi sama Baba ya nufo gida.
Cike da tijara Mamawo ta maida kallonta ga Malam Sa'idu ganin matan sun watse kafin cike da bala'i tace.
“Wannan wani irin rashin mutuncine Yah Sa'idu agaban Idanuna kake dukanta meye alaƙarta da ɓatan Wannan kangararriyar yarinyar da bata kwana agida?”.
Da ɓacin rai atare dashi yace.
“Ya isheki Saude da kunnuwa na naji wannan munafukan algungumar yarinyar naki natsara wa Neenah ta gudu kada ta tsaya alalata mata rayuwa saboda bata da mutunci!!”.
Kallon tuhuma Baba da ƙarasowarsa kenan ya bishi dashi kafin ya maida kallonsa kan Maryam da har zuwa lokacin hawaye ne ke zuba daga idanunta kana yace.
“Meke faruwa Maryama?,Ina aikan dana yi miki?”.
Kanta ta ɗago tare da share hawayen ta cikin rawan murya tace.
“Duk na duba ɗakuna da kichen da kuma ban ɗaki amma bangan taba shine nazo ina faɗa musu ko gamawa banyi ba Kawu Sa'idu ya riƙa kwaɗa min mari”.
Saurin dafe bango Baba yayi sakamakon wani jiri dake ɗibarsa kana cikin rawan murya yace.
“Toh Ina taje??”.
Jujjuya kai Maryam tayi tare da cewa.
“Nima Allah bansani ba”.
Mamawo data gama shaƙa ta finciko Maryam tare da gaura mata marin da yasa jinta na wucen gadi ya ɗauke cikin kumfar baki tace.
“Dan Kutmar Ubanki ina kika je kika ɓoyeta,Watanin dama ina lura da take-taken ki munafurci kike ƙullawa toh wallahi idan har ba aganta ba saina gana miki azaba mai raɗaɗi!”.
Ta maida kallonta kan Baba da yayi zuru-zuru hannu ta ƙyasta masa da faɗin.
“Kai kuma na dawo gareka!”.
Cikin sanyin murya da tsoro yace.
“Toh ni kuma me nayi Saude!?”.
“Watanin Kafi ɗan dako sanin tasha ai, Ni sam ban yarda da kai da Maryama ba bakin ku ɗaya duk wani munafurci da ƙulle-ƙulle tare kuke yi!”.
Kai ya girgiza tare da cewa.
“Haba Saude meyesa kike yi min mummunar zato nine fa na yanke Auren da kaina meyesa kike zaton zan canza ra'ayina”.
Dogon tsaki taja tare da tsare sa da ido kafin tace.
“Duk wani abu da kake aikatawa atafin hannu na kake dan gar nake kallon ka.
Cike da ɓacin rai malam Sa'idu ya kalli Maryam tare da faɗin.
“Keeee maza ki fita ki nemota duk inda kika turata kema Saude ki fita ki zaga maƙota dan ina da yaƙinin ba zata wuce unguwar nan ba”.
Kallonsa ya mayar kan Baba dake tsaye ya tallafe kuncinsa cikin rashin walwala yace.
“Kai kuma fa tsayuwar me kake yi anan?,Shine tsiyar temakon matsiyata yo in ba hak ba daga temakon sai araina min wayo yarinyar data gama zubar da darajarta awaje zan temaka na rufa muku asiri shine zaku raina min wayo”.
Runtse idanu Baba yayi tare da juyawa ya fita zuciyarsa tamkar zai fashe.
Ganin kowa ya fice yasa Malam Sa'idu ciro wayarsa tare da dealing wani number ana ɗagawa ya kara kunne tare da cewa.
“Jungle ka shiga What'sApp yanzu zan turo maka wani hoto ka tabbatar duk inda take kun kawo min ita”.
Daga ɗaya ɓangaren Matashin dake zaune da wasu sun kai biyar suna zukar Wiwi yace.
“Angama Oga”.
Kana ya katse wayar tare da buɗe datarsa cikin minti biyu hoton ta ya bayyana a screen ɗin wayar.
Sake kiran wayar Malam Sa'idu yayi tare da cewa. “Hoton ya shigo yanzu zamu fara neman ta” godiya malam Sa'idu ya masa tare da katse kiran...
Tafiya take acikin ciyayin da yayiwa gyefen kwaltar ƙawanya ƙafafunta babu takalmi haka zalika hijabin dake kanta ƙaramine rigar da zanin dake jikinta duk da ban suke.
Sosai take tafiya yayin da hawaye ke kwaranya daga idanunta ko kaɗan bata jin tsoron duhun ciyawar da kuma ƙwarin dake ciki burinta kawai tayi nesa da gida tafiya take batare da tasan inda take jefa ƙafarta ba wani irin zugi ƙirjinta keyi.
Cikin sauri ta juya bayanta jin alamar tafiya ganin bata ga kowa ba yasa ta cigaba da sassarfa batare data lura da inda take sanya ƙafarta ba ihu ta Ƙwalla jin ta taka wani abu kallon gyefen kwalta tayi ganin babu wasu motoci dake zirga-zirga yasa ta zauna tana mamakin abinda yasa garin yayi shiru tafin ƙafanta ta tallafo tare da kallon dogon ƙayar daya soketa lumshe idanunta tayi tare da ficikewa hawaye Masu zafin gaske suka zubo mata.
Saurin juyawa tayi jin sautin wata kakkausar murya daga bayanta na faɗin.
“Gata can wancan dake zaune itace”.
Kallon su ta tsaya yi domin sam bata sansu ba ganin sun dun faro kanta gadan-gadan yasa azabure ta miƙe tare da fallawa da gudu cikin tsawa Janglu yace.
“Ku bita kada ku barta ta gudu ku kamo min ita”.
Ihu ta ƙwalla tare da ƙara gudunta garin yayi shiru babu hayaniyar mutane hakan yasa babu wanda zai kawo mata ɗauki.
Juyawa tayi yayin da ɗaya daga cikin su yakai mata wawura tare da cafko Hijabinta tsugunnawa tayi cikin Sa'a Hijabin ya fita ta miƙe. afusace Jagwal ya sanya mata ƙafa wani irin baya tayi tare da faɗuwa da goshinta atake wajen ya fashe ihun azaba ta ƙwalla tare da cewa.
“Wayyo Allah na Baba na mutu”.
Tsugunna wa Jungle yayi akan ta tare dasa hannu ya ɗago fuskarta tare da haɗiye yawu yana lasan busassun laɓɓansa da yayi baƙi alamar shaye-shaye yace...
*My dear Fan's Free page ya kusa ƙarewa ku hanzarta wajen biya domin mu samu mu kutsa cikin labarin gadan-gadan batare da ɓata lokaci ba*
_Sawun Giwa na kuɗine 500 hundred zaki tura ta wannan account number 6030406548 Abdullahi Idris Aishatu keystone bank ko kuma katin Mtn ta wannan number *** tare da tura shedar biya ta wannan number ***._
_Ayi shearing saboda Allah ƴan Uwa Masoya da abokan arziki_
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
***
***
*ESHAA CE*