MASHAHURI

3

by @bintaumarabbale

A nutse Abbu yace." Duk wanda yace muku ina koyar da ilimin jima'i to babu shakka yayi min 'karya alal ha'kika shi jima'i wani abu ne da Allah ya halasta shi a tsakanin mace da namiji anan gurin ina so in fahimtar dake cewar ina nufin miji da mata wanda aka d'aura musu aure da juna a gaban shaidu sannan shi namijin ya biya sadaki kamar yanda addini ya tana da, to babu shakka wannan mata ta zama mallakin sa ta bar hannun iyayen ta ta dawo nasa shike da iko da ita kuma a ko ina ne zai biyawa kansa 'bukata ta aure kamar yanda musulunci ya nuna mana, bayan wannan 'kofa da aka halasta mana ba a yadda mu bi wata kafar dake jikin matayen mu mu biya kan mu bu'kata ba, mutukar muka sa'bi Allah muka bi son zuciyar mu to babu shakka zamu shiga fushin ubangijin mu damu da zuri'ar mu, Wannan shine kawai abunda zan fad'a muku game da maganar da kuka zo min da ita." 

Abbu ya 'karashe maganar tashi cikin nutsuwa da kamala.


Khalid ya zakud'a kafad'ar sa yana Sosa kansa cikin sha'kiyan ci yace." Ya sheik wannan tambihin naka bai samu guri ba domin kayi mana k'wange a cikinsa ka'ki ga fayyace mana karatu yanda ya kamata ta'be bakinsa yayi cikin izgili ya zura hannu cikin wandon jins din da yake jikin shi ya zaro kud'i dami ya zube gaban Abbu ya mi'ke tare da fad'in "Guys ku tashi muje ko."



Abbu ya bisu da kallo cikin mamaki! Ya mai da ganinsa kan kud'in da suke gaban shi, kamar Wanda Khalid din yayi masa d'aurin baki sam ya kasa yi musu magana suzo su d'auki kud'in su, babu abunda zaiyi da kud'in da suke bashi domin kwata-kwata bai yarda da tarbiyar yaran ba mussaman shi mai maganar cikin su. Ya san shi farin sani yaron da yayi masa abunda bazai ta'ba mantawa dashi ba.


 Yana zaune a gurin yana tunanin yanda rayuwa ta duniya ta lalace da yanda 'yayan da aka haife su cikin musulunci gaba da baya amma suna kokarin mai da Kansu kafurai shi a ganinsa duk mutumin da ya bujerewa fad'ar Allah da manzon sa ta ya kafurta Kuma yazo duniya a banza zai koma a hofi shiyasa yake tsaye akan iyalinsa da su bi sinnar Annabi Muhammad (slw) yasan dai shiriya ta Allah ce duk tsantsenin sa da takatsantsan d'insa shima bai wuce Allah ya jarrabe shi ba, ala kullu halin dai yana addu'ar Allah ya tsallakar dashi da iyalinsa ga fad'awa ga halaka




Sai bayan ya gama sauraran tambihi daga malam Umar Sani fagge a tashar express redio sannan ya nad'e daddumar shi ya shiga gida, a lokacin suka matasan layin suka saki kid'a na wa'kokin Hausa iri-iri sai ihu! Suke yi kamar ba dare ba.



Abbu ya gyada kansa yana musu addu'a shiriya cikin zuciyar sa 'kofar gidan ya kulle yayi addu'a kana ya shiga cikin gidan yana haska torchlight din hannun sa.


Shiru Ammi da Hanifa sun yi bacci ya bude dakin shi ya shiga cikin nutsuwa yake yin komai Abbu kenan kamilin mutum mai ri'ko da addini da bin sinnar Annabi muhammadu (Slw)


*****


'Karfe bakwai na Safiya Hanifa ta gama shirin ta tana makaranta boko dake tana ajin 'karshe na kammala secondary school a nutse ta zauna kusa da mahaifiyar ta tana turo baki kamar yanda ta saba cikin shagwaba tace"Ammi ina kwana."



Ammi dake had'a mata abun karyawa tace"Lafiya lau Hanifa kin tashi lafiya."? Tace"Lafiya lau na tashi Ammi sai dai ke wayar Yayana." Ammi tayi murmushi tace"Yau zaki ganshi ya dawo ai yau juma'a." Cike da farin ciki Hanifa tace" Aikuwa wallahi na manta Allah ya dawo dashi lafiya." Ammi tace"Amin.



Bayan ta gama karyawa ta mi'ke da niyyar tafiya tana gyara ni'kaf din fuskarta tace"Ammi Abbu kuwa ya kammala azakar din da yake bamu gaisa ba kuma idan na tsaya zan makara." Ammi tace"Ai kuwa sai dai ki shige ki tafi domin Abbu bazai futo ba sai kusan sha biyu na rana lokacin zai shirya domin zuwa masallaci."



Hanifa tayi wa Ammi sallama ta futa tana gyara jakarta da take rataye a kafad'ar ta.



Gidan su Asalamiyya na gaba dasu kad'an Hanifa bata ta'ba tafiya ita kad'ai ba tare da ta biya mata ba Asalamiyya 'kawar Hanifa ce tun ta 'kuruciya halinsu yazo d'aya haka ma d'abiun su yazo d'aya bayan nan kuma Abbu ya yarda da tarbiyyar ta sannan mahaifin Asalamiyyar Abokin sa ne d'abi'un su sun zo d'aya shine yasa har ya aminta da 'kanwancen su Abbu yana sanya ido kan irin 'kawayen Hanifa sosai shiyasa itama take taka tsan_tsan bata fiye sakewa da jama'a ba


Tun daga nesa ta hango cincirin don matasan samarin da suke ji da kansu a unguwar sun ke waye shi kamar ko da yaushe shi kuma yana tsakiyar su hannunsa ri'ke da 'katuwar some times tana ganin shi a unguwar amma bata san sunan shi ba ita dai haka kurrum yake burgeta duk ganin da zata yi masa da ni'kaf a fuskarta hakan baya hanata ta 'kare masa kallo sosai guy yake burgeta da irin dressing d'inshi kuma ta lura duk masu yi masa fadanci suna kwaikwayar sa ne da irin dressing din shi, gabanta ya cigaba da fad'uwa har ta iso kusa dasu, kanta a 'kasa tazo shiga cikin gidan su Asalamiyya taji Muryar d'aya daga cikinsu yana fad'in"Wannan munafukar yarinyar watarana sai mun yage ta Wallahi kullum jiki a rufe shegiya ko don tasan tana da kyau ne yasa take rufe jikinta oho."! Dariya suka saka d'ayan yace." Kai 'yar gidan Shaik ce fa."! A slow ya d'ago kanshi yana kallonta lokacin da ke 'kokarin shiga cikin gidan suka ci karo da Ya Abbakar yayan Asalamiyya ne ya futo yana wata irin tafiya irin ta manyan 'kwari yana ganinta ya gane ta ita kuma ta ja da baya da sauri cikin ladabi ta tsuguna har 'kasa ta gaishe shi." Abbakar ya shafa fuskarsa cike da jin dad'i ya amsa mata shi kam ladabin yarinyar yana burge shi babban abunda yake bashi haushi da ita yanda take rufe jikinta sai kace matar Liman. Yace." Hanifa yau ma sai dai ki tafi ke kad'ai don basu dawo ba amma dai mybe yau su dawo."


Jiki a sanyaye Hanifa ta juya tana fad'in to Ya Abbakar." Juyawar da zata yi suka had'a ido dashi, tayi saurin yin 'kasa da kanta a salu'be ta bar gurun. Shi kuma Abbakar ya 'karasa dabar tasu kamar yanda suka saba gaisuwar su yau ma haka suka yi suna dariyar sha'kiyan ci Salis yace." Kai d'an iska naga waccan me ni'kaf din ta gaishe ka har da tsuguna maka kai kuma sai was he baki kake hahahahaha." Ya k'arashe maganar yana dariyar shakiyanci.



Abbakar ya sosa kansa yana kallon hanyar da Hanifa ta wuce yace." Hanny kenan kasan nifa kamar 'kanwata take a gurina tunda 'kawar Asalamiyya ce shiyasa take bani girma."


A hankali ya d'ago kanshi yana kallon Abbakar din cikin yanayin maganar shi kamar ta mata yace." Kome baka girman da take sai mun tu'be ta mun ga abunda yake rufe kusan sau biyar kenan ina ganinta cikin wannan bakin abun sai na yaye ta Wallahi tun da yanzu na gano 'yar babban ma'kiyina ne."