FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
Nutsastiyar yarinya ce take tafiya gefan titi tana sanye da kayan makaranta Wanda kana ganin su kasan na isilamiya ne yadin toyobo blue black Riga doguwa da dogon hijab har 'kasa kafarta cikin safa fara da takalmi plate baka ganin komai a jikinta sai 'kwayar idonta cikin nutsuwa take bin gefan titi domin isa gidan su dake cikin unguwar Shagari Qutears tafiya take a tsarge! Domin tasan kallon da jama'ar gari suke wa masu irin shigar su mussaman matasan unguwar su in suka zo shigewa har ihu! Suke musu suna fad'in"Allah a baki fir'auna a zuci! Sam basa tanka musu sanin da suka yi cewar yin hakan zubewar mutumci ne, to shiyasa take tafiya tana hard'ewa kasancewar a bokiyar tafiyar ta bata zo ba, anyi musu mutuwa a cikin gari sun tafi gaisuwa ita da 'yan gidan su. Aikuwa tana shigowa cikin layin su matansa da suke zaman kashe wando suka fara yi mata d'an kira! "...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.