SHAFI NA BIYU (ƊANƊANO)
by @ummishatu
*2*
BAYAN SHEKARA SHIDA
***
~~~*K* wance yake kan lafiyayyen gadonshi yana lullube cikin duvet yana sharar bacci kasancewar yau tunda sanyin asuba ake kwarara ruwa,
Da gudu yashigo cikin dakin ya haye saman gadon ya fada kansa yana janye duvet din da yake lafe aciki yana shan dumin da na'urar dumama daki ke bayarwa,
"Daddy katashi....., Papa.... Papa katashi....uncle tashi..."
Ahankali yabude idonshi guda daya ya kalli yaron wanda yake dan kimanin shekara shida jajur dashi ma'abocin kyau da daukar hankali,ganin yaron sanye da kayan bacci masu nauyi sakamakon dan sanyin dake shigar mutum yasashi yaye duvet din da yake ciki gaba daya yatashi zaune yana mai sake kallon yaron,
"Aryan ya bakayi shirin school ba? Yaufa akwai makaranta ka manta ne?"
Turo baki yaron yayi ya haye cinyar baban nashi yana fadin,
"Papa ni yau bazanje school ba...ni awurinka zan zauna"
Rikeshi yayi ya sassauta murya alamar rarrashi,
"Abba na idan bakaje school ba ka zauna agida me zakayi?"
"Daddy ni tare dakai zan zauna..."
"A'a Aryan makaranta zakaje kaji,kaga ka kusa yin latti...zo muje ashiryaka maza kaje PA ya kaika...Nima ba agida zan zauna ba gombe zanje anjima"
"Daddy zan bika...zanje wurin hajiya.."
"No, makaranta zaka tafi,da wuri nima zanje nadawo"
Makale kafada yayi zai fara kuka dan har ya muncine ido,
"No sweetheart kar kayi kuka,ba nafada maka anayin hutu zamuje inkaika duk k'asar da kakeso ba kayi spending holiday dinka acan ba? Tell me wacce k'asa zamuje lokacin hutunka?"
Sake turo baki Aryan din yayi yana kokarin yin kuka,
"Come on lovely son,fada min mana..."
Wayarshi ya dauka dake ajiye akan bedside drawer ya kunna sannan yamika masa,
"Ungo duba,zabi k'asar da zan kaika hutu..."
Karbar wayar yayi yana dubawa yana yi yana turo dan karamin bakinsa mai dauke da pink lips,sai dariya yake yi yana duba pics din zuwa can ya nunawa Abban nashi,
"Daddy wannan...."
"New York kake so musake zuwa...? No problem zan kaika to,yanzu maza tashi muje in shiryaka.."
Sauka sukayi daga kan gadon gaba dayansu Khalil na sanye cikin kayan bacci masu kama da na sanyi kalar ruwan toka dogon wando da rigarshi mai gajeren hannu gaban rigar da hoton Ball guda uku,
Cikin toilet dinshi suka shiga yayi masa wanka da ruwa mai dumi sannan ya dauro masa towel suka fito,mai ya dan shafa masa sannan suka nufi dakin Aryan din, uniform dinshi na makaranta ya dauko yasaka masa dark purple din wando da light purple din riga da kuma dark purple din rigar sanyi mai dauke da sunan makarantar su ajiki sai necktie da farar safa da farin combos,cumb ya dauka ya taje masa sumarshi mai dan yalwa sannan yakama hannunshi bayan ya daukar mishi school bag dinshi yakuma fesheshi da turare,
Yana rike da hannunshi har dan karamin sashen umma barira wanda wani dan kyakkyawan corridor zai sadaka dashi,tana zaune falonta da lunchbox din Aryan agabanta da kuma breakfast dinshi wanda kuku yadafa,
"Dan nema dama nasan wurin babanka ka tafi maimakon ka zauna inshiryaka shine ka tada rigima ka gudu ko...."
Makale kafada yayi yasake rike Khalil yana dan turo baki irin yanda shagwababbun yara keyi,
"Kanaji umma na yimaka magana shine kayi mata shiru ko..."
Sakinshi yayi ya tsugunna yagaida umma barira nan ta amsa tana cewa,
"Rabu dashi zai dawo ya sameni.... Zo nan ka karya katafi makaranta"
Sake makale kafada yayi ya makale Khalil dole sai shi ne ya bashi breakfast din yaci yasha tea suka fita domin akaishi makaranta inda Nura PA ke jiransu amma fafur yaki yace shi Daddyn shi ne zai kaishi,gaban mota Khalil yabude musu suka shiga Nura yajasu suka nufi bright future Academy,acikin motar ma sai rikici yake dakyar ya yarda yafita lokacin da suka karasa cikin makarantar sai da uban ya lallabashi tare da yimasa dabaru kala kala sannan ya yarda yatafi class yana ta faman kyalkyala dariya yana yiwa uban bye bye,dariyar shima yakeyi yana daga masa hannu ta glass din da yasauke wanda ke jikin motar,basu bar makarantar ba har saida suka ga shigarshi cikin class, murmushi Nura PA yayi aransa yana jinjina wannan soyayya dake tsakanin Khalil da danshi Aryan shidai yasan akwai soyayya mai girma da karfi tsakanin iyaye da yaransu to amma bai taba ganin soyayya irin wannan ba domin tasu soyayyar daban take.
***
"Youth obey the Clarion call,let us lift our nation high,under the sun or in the rain,with dedication and selflessness, Nigeria ours Nigeria we serve......"
Wata matashiyar budurwa keta faman rera wannan wakar daga inda take zaune cikin wani dan madaidaicin falo tana goge wasu fararen kaya kimanin set goma sha biyu,
"Tirkashi..... tabdijam lallai Hanan kin baiwa wannan hidimar k'asar muhimmanci, yanzu har kin haddace wannan NYSC national anthem din tun kafin kije camp din?"
Dariya tayi ta dago ta kalleshi,wani saurayine wanda ahaife zai iya bata kimanin shekaru uku zuwa hudu,
"Yaya shamsu kenan kana wasa dani....kasan kuwa yanda nake son NYSC? Nifa babban burina inganni da wannan uniform din ajikina ina takawa das das,wallahi Allah ma yasani ni badan inyi aiki nayi karatun nanba sai dan kawai inyi bautar k'asa inganni cikin kaki ina watayawa...."
Dariya shamsu yayi wanda tuni yanemi wuri ya zauna ya ciro wayarshi daga aljihun gaban rigarsa,
"Yaro yarone,yaro man kaza,wai fa ke kin zaci service dinnan dadi gareshi ko baki san wahalar dake cikinsa ba,hmmm zaki bani labari ne yarinya bari su turaki kudu zaki yi bayani...."
"Allah amin....,kamar kuwa kasan nafi son akaini can,ai gara inje inga duniya amma kawai malam ina zaune a kano rai da rai kamar wata wannan...ni wallahi a kudu har akwa ibom na saka da ebonyi ko enugu ban saka ba saboda tayi min kusa....."
"Yayi kyau to yanzu wadannan uban tulin white din da kike gogewa na menene?"
"Ahhh kaji yaya shamsu da wani zance,na tafiya ta camp ne mana,ba ance a camp rai da rai acikin white akeba? Ai ni komai nawa wadatacce zanyi,bazan tafi da kaya kadan ba bare inzo ina neman kari a kurarren lokaci....."
"Hmmm Allah dai ya kaimu ranar...on nawa ma zaku shiga?"
"On 11 yau kuma muna first kaga saura kwana goma kenan...."
Shamsu bai kara magana ba mahaifiyar su tashigo rike da food flask wanda abisa dukkan alamu daga kitchen tafito,zama tayi gefen shamsu tana cewa,
"Ohh su Hanan dai abin nema yasamu kamar yaune za ashiga camp dinnan ko gobe duk kinbi kin hana kanki da kowa sukuni akan shirye shiryen tafiya camp dinnan,hala sun kiraki sun sanar dake garin da zasu turaki?"
"Haba mamaye ai sai kisa ayi miki dariya da dawasu akusa,sai ana saura kwana biyu ko uku sannan zasu yimana posting kowa yaje yaduba inda aka turashi kin manta lokacin da yaya shamsu yayi nasa ne?"
"Au toh ai kin san abunda baka san kanshi ba,to nidai Allah ubangiji yasa subar min ke akusa kamar katsina ko bauchi inda yayanki shamsu yaje...."
"Tab ai mama ita bata son kusa kiyi mata addu'ar nesa kawai...."
Mamaye bata kai ga kara yin wata maganar ba sukaji sallamar malam mustapha wanda shine mahaifinsu,yana rike da wata leda baka,
"Uwar masu gida.....,zo ungo wannan takalmin yanzu naganshi nasiyo miki zo ki gwada idan baiyi ba amayar acanjo..."
"To Abba..."
Da sauri tafita bayan ta kashe iron din da take guga dashi,wani farin takalmi ne mai kyau kamar combos yana da igiyoyi ajiki sannan baida nauyi sakawa tayi tana murmushi,
"Abba yayi min daidai nagode madallah..."
"Ai naga kece kike neman farin takalmi shiyasa nasiyo miki"
"Ehh Abba nagode" tasake fada bayan ta dan russuna,ciki ta sake komawa wurinsu mamaye inda ta iskesu suna cigaba da maganar ta na mutukar kaunar da take yiwa service.
Dagowa mamaye tayi tana kallonta ganinta rike da combos yasata fadin,
"Ikon Allah wani takalmin aka sake siyowa ni fatsima?? Naga kin siyo takalman nan ba daya ba ba biyu ba...."
"Mamaye kenan to ai wannan farin takalmin kullum fa shi ake sakawa acan kinga ai dole atanada dayawa...."
"To ai shikenan Allah yabada sa'a..."
"Uhmmm Hanan yar hidimar k'asa.." inji shamsu wanda ke yar dariya,
K'arar wayarta da ta jiyo daga uwar daki yasanya ta mikewa ta shiga ta dauki wayar tana rayawa aranta dama tasan shine,mujahid sam baida hakuri yafiya naci da takura,zama tayi gefen gado sannan ta daga wayar,
"Hanan yau ina kika shigane jinki da ganinki online yayi min wahala...?"
"Mujahid kenan,kamanta da asubah munyi waya dakai? Ina nan kawai dai aiki nake yine...."
"Ayya....to yanzu da yaushe zanzo inganki?"
"Uhmmm to zuwa gobe dai saboda ina son zuwa kurna gidan anty salaha kaga sai ka kaini ko...."
"Babu damuwa amma ni da son samuna inzo anjima"
"A'a kadai yi hakuri sai goben"
"Ok to ya na iya..."
Saida suka taba yar hira sannan yayi mata sallama ta katse wayar tana jin wani sabon tunani yana bijiro mata aciki zuciya,mujahid yajima yana binta akan tabashi dama ya turo gidansu ayi maganar aure amma taki tace ita sai tagama karatu kuma tagama service,kusan koda yaushe maganarshi kenan idan ma sunyi aure bafa hanata karatu da service zaiyi ba amma ta kafe kai da fata tace ita kam sai ta gama komai na karatu sannan zata yi aure to duk lokacin da ta fadi haka sai yace mata "idan kuma na mutu fa kafin lokacin?"
Ta kanji faduwar gaba aduk lokacin da ya furta wannan kalmar domin harga Allah tasan yana mutuwar sonta duk da kasancewar shi yaro dan ba wani babba bane kawai auren gata yake son ayi masa dan koda zai girme mata baifi yabata shekaru biyu ba idanma sun kai shiyasa takance masa shi fa sa'anta ne dame yafita? Idan tafadi haka shi kuma sai yayi murmushi yace ai koda watanni biyu yafita yadai fitan balle har shekaru biyu wanda yafika da shekara biyu kuwa ai yafika, murmushi tayi ta mike tafita acikin zuciyarta tana fadin "mujahid manya".......................✍️