SO DA ALAƘA

SHAFI NA BIYU

by @ummishatu

©️ *H.W.A*


Paid Book



*SO DA ALAƘA!*



  *_NA_*


*_UMMI A'ISHA_*




*Wattpad:@ummishatu*




  2



~~~Tun bayan ɓatan Imran rayuwarta ta shiga cikin mawuyacin hali da ƙunci gaba ɗaya an kasa gane kanta, kusan kowa ita yafi tausayawa ko hajiya da take mahaifiyarsa kamar ta fita dauriya akan lamarin. 


Yau ma kamar kullum tana kwance saman gado da Ajmal kwance a jikinta, wayarta ce a hannunta ta tsura mata ido ko kiftawa bata yi, hoton Imran take kallo wanda suka ɗauka tare ranar sunan Ajmal, hawayene ya soma bin kumatunta babu ƙaƙƙautawa, har aka buɗe ƙofa hajiya ta shigo bata sani ba kuka kawai take yi sautin sansanyar muryarta yana fita a hankali, zama hajiya tayi a gefen gadon ta dafa kafaɗarta itama tana jin kanta kamar zata fashe da kukan, 


"Ruhaima..... Kiyi haƙuri kiyi haƙuri..... Lokaci yayi da zaki daina zubar da hawayenki haka, addu'ar nan dai da muke yi ita zamu cigaba da yi ba zamu fasa ba, insha Allah duk inda Imran yake yana cikin tsarewar ubangiji..... Kiyi haƙuri ki share hawayenki ga Umaima can tazo tare da baƙi tace dama kin san da zuwansu..... "


Da ƙyar ta iya tsayar da hawayen ta ɗauki tissue ta goge fuskarta ta tashi, karɓar Ajmal hajiya tayi ita kuma ta gyara zaman dogon hijabinta wanda yake har ƙasa ta fita tana goge hawaye hajiya na biye da ita, Umaima ta hango zaune a cikin babban falonta, tun daga nesa ta fahimci cewa itama Umaima kukan take yi dan gashi nan idanuwanta sunyi ja baya da luhu luhu da suka yi, kusa da ita taje ta zauna kasancewar kujerar da take kai mai mazaunin mutum uku ce, 


Rungume juna suka yi suna sake yin wani sabon kukan a haka hajiya tazo ta iskesu, 


"Assha..... Nan ɗinma wani kukan kuke yi Ruhaima? Haba Umaima, wai shin wannan kukan da kuke yi zai ba mu mafita ne? Kuka fa baya magani...... Addu'a zaku yi masa" 


Daga haka hajiya ta wuce bedroom wanda yake mazaunin nata a halin yanzu tun bayan da aka samu labarin ɓatan Imran tana tafe tana share nata hawayen itama. Sai da su Ruhaima suka ci kukan su suka more sannan suka haƙura, 


"ga baƙin can na zo dasu..." Umaima ta faɗa tana kallon Ruhaiman, 


"kunyi magana dasu?" ta buƙata tana kallonta da jajayen idanuwanta, 


"Ehh sunce insha Allahu tsawon watanni biyu zasu kwashe suna gudanar da saukar alqur'ani da addu'o'i..... Kuma anan gidan zasu zauna, idan sun kammala za a basu abin sadaka dubu ɗari biyu" 


Ɗaga kai tayi alamun gamsuwa da bayanin da umaiman ta gama yi mata, 


"Wannan ba matsala bace sai akaisu can B/Q a saukesu, ni dai dama abinda bana so shirka da kauce hanya.... Amma tunda su karatun alqur'ani ne da addu'a hakan yayi min" 


"Nima wannan dalilin ne yasa na kawo su, ubangiji Allah ya wuce mana gaba yasa mu dace" 


"Amin Inlaw" ta faɗa tana murmushin yaƙe saboda halin da zuciyarta ke ciki, Umaima ƙanwar Imran ce kuma Allah ya haɗa jininsu da Ruhaima, tashi suka yi gaba ɗaya suke je wurin baƙin Ruhaima ta gaisa dasu sannan suka ɗan tattauna tasa aka rakasu B/Q, jin hayaniyar almajirai a ƙofar gida ya sanyata komawa cikin bedroom ɗinta ta buɗe drawer ɗin jikin mudubinta ta ɗauko kuɗi ƴan dari bibbiyu rafa biyu ta fito, da kanta ta fita ta rarrabawa almajiran sadaka kamar yadda ta saba kullum ta Allah, sai da ta tabbatar almajiran sun ƙare babu wani sauran wanda ya rage bai zo ya karɓa ba sannan ta koma ciki tana tafe tana tasbihi da carbin dake makale a yatsanta, 


Hajiya ta iske a falo tare da Umaima wadda ke ƙoƙarin haɗawa Ajmal abincinshi,zama tayi gefen umaima tana kallon yanda suke kokawa da Ajmal yanata zillo yana miƙa hannu zai kamo ɗan ƙaramin vowel ɗin da take dama masa kunun madara, 


"wait mana my dear... Yunwa kake ji ne haka?" umaima ta faɗa tana dariya, 


"Ba dole yaji yunwa ba..... Uwa bata ci ta ƙoshi ba bare shima ya samu.... Ni yau sam sam ma banga ta ci wani abu ba a cikin nan nata ko ruwa banga ta sha ba...." 


Juyawa umaima tayi ga Ruhaima ta kalle ta idanuwanta a lumshe tana istigfari sai dai tana sauraren duk abubuwan da suke faɗa, 


" inlaw bakya cin abinci why? Dan Allah ki rinƙa daurewa komai ƙanƙantarshi ko dan Ajmal.... Yanzu me zaki ci? Sai in dafa miki" 


"Azumi nake yi" ta faɗa cikin taushin murya idanuwanta a lumshe, 


"Hajiya kinji wai azumi take yi" 


"Ni na kasa gane kan wannan azumi na wannan yarinya, kullum azumi babu hutawa? Wannan wanne irin azumi ne?" 


Jin abinda hajiya tace ya sata buɗe idonta tana murmushi, 


"Hajiya jiya fa banyi ba,irin azumin Annabi Dawud nake yi, yau kayi azumi gobe ka huta, jibi kayi gata ka huta.... Jiya banyi ba dan har kika sa Mama Saude ta dafa min zogale naci ko kin manta?" 


"Eh anyi haka.... Ban manta ba" 


"Inlaw adai yi ta haƙuri dan Allah, a cigaba da haƙuri da rayuwa... Haka Allah ya ƙaddaro mana" 


Bata sake cewa komai ba ta miƙe ta fita ta ƙofar kitchen ta nufi babban kitchen wanda su mama Saude ke kwarafniyar girke girke, 


Aiki ta samesu suna yi na abincin sadaka da ake kaiwa gidan marayu da gidan yari kullum ta Allah, ɗan dafe kanta tayi wanda ke yi mata ciwo koda yaushe sanadiyyar kukan da take yi a kai akai shiyasa kowanne lokaci bata rabo dashi, 


"mama Saude idan kun kammala dan Allah akwai baƙi a B/Q mutum huɗu sai akai musu abinci da dukkan abinda ya kamata, zan ɗan shiga in kwanta daren jiya ban samu bacci ba watakila shiyasa kaina ke ciwo" 


"To shikenan hajiya... Babu komai, Allah ya sauwaƙe, a fito lafiya" 


Juyawa tayi ta nufi hanyar komawa ciki mama Saude ta bita da kallo tare da girgiza kai alamun tausayawa, ita dai tana tausayin wannan baiwar Allah domin tana cikin babbar jarrabawa, 


Sai da ta ɗan zauna wurin su hajiya sannan ta tashi ta shiga ciki ta kwanta wai ko za ta ɗan samu baccin amma ƙyamas yaƙi zuwa a madadin haka ma sai faman tunane tunane iri iri da ke bijirowa cikin zuciyarta, ita abinda yafi tsaya mata arai shine baka san halin da mutum ke ciki ba, ya mutu ko yana raye? Idan yana raye to a wanne yanayi yake? Wanne hali yake ciki? Wannan shine abinda ke sakata zubar da hawaye koda yaushe wanda ta kasa dainawa. Tana nan kwance tana ta faman juye juye ahaka umaima ta shigo ɗauke da Ajmal a kafadarta wanda ke bacci,duk a tunaninta bacci take yi shiyasa ta kwantar da Ajmal ɗin a gefenta ta fita, a hankali ta buɗe idanuwanta bayan taji fitar umaima ta zubawa Ajmal ido wanda sai yanzu ne take hango tsantsar kamanninsa da Imran wanda ada bata gani ba amma a ƴan watannin nan gaba ɗaya yaron ya juye kamar ubansa fitik, ajiyar zuciya ta ajiye a hankali tana jin ƙwalla tana ciko mata ido,


"Allah ya bayyanaka Imran.... Allah ya tsareka a duk inda kake kuma ya kareka..... Jikina yana bani cewa kana raye.... Ban taɓa ji ajikina ka mutu ba....." hawayen ta goge kafin ta tashi ta shiga toilet, alwala tayi tazo ta fara jera salloli kamar yadda ta saba dan hakanne kaɗai ke ɗauke mata hankali daga halin da zuciyarta ke ciki,


Sosai taji ta samu nutsuwa sannan zuciyarta tayi sanyi, nan inda tayi sallar wani bacci ya ɗauketa wanda ta wuni tana yi sai la'asar ta farka, ba ƙaramin daɗin baccin da ta samu taji ba saboda ta tashi zuciyarta wasai kuma nauyin da yake cikinta ma ya ragu, wanka tayi tai salla ta fita wurin hajiya, babu kowa atare da ita sai Ajmal dan da alama umaima ta tafi nan ta zauna wurin hajiya suna hira jefi jefi har zuwa lokacin da suka ji horn alamun mota zata shigo cikin gidan,


Tana ta nazari acikin ranta tana tambayar kanta to kuma ko waye yazo mai gadi ya shigo cikin rissinawa da girmamawa yace,


"Ranki ya daɗe baƙone yazo, zai iya shigowa?"


"Ehh ya shigo baba" ta faɗa a taƙaice, juyawa yayi ya fita bayan fitarshi babu jimawa baƙon ya shigo kallo ɗaya tayi masa ta gane cewa daga cikin abokan Imran ne domin ba zai fishi ba ko a haife,da sallama a bakinsa ya shiga suka amsa atare ita da hajiya, 


"Ya abunda ya faru kuma? Ubangiji Allah ya bayyana shi, ai Imran mutumina ne sosai akwai kyakkyawar alaƙa tsakanina dashi..." 


"Allah sarki, mun gode madalla Allah ya bada lada" hajiya ta faɗa kuma kusan ma da hajiyan suke hira duk da gaba ɗaya hankalinsa yana kan Ruhaima wacce ke can duniyar tunani bata ma san yana yi ba, ita kanta hajiya ta fahimci hankalinsa yana ga Ruhaima amma dai bata nuna komai ba, kudi ya ajiye musu dami guda yayiwa hajiya sallama ya fita yana sake jaddada musu wai idan suna buƙatar wani abu a gaggauta sanar dashi...................... . ✍🏻






*_Ummi Shatu_*👌🏻