SO DA ALAƘA

SHAFI NA HUƊU

by @ummishatu

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*

 ( _Home of expert & perfect Writers_) 





    *SO DA ALAƘA....!*




 *_NA_*


_*UMMI A'ISHA*_



Free Book


4



*Wattpad :@Ummishatu*



***Wasu zafafan hawaye ne suka sauka akan kuncinta lokacin da ta ji irin ƙarya da ƙazafin da Alhaji Sabo yake shirya mata,


Sai da ya sake gyara zamansa sosai ya kalli DPO cikin salon yaudara da ƙarya tsantsa yace,


"Yallaɓai wannan yarinyar taci mutuncina mutuƙa, ka duba ka ga irin ɗanyen aikin da tayi min......duba goshina da kaina duk naɗe suke da bandeji sakamakon aika aikar da tayi min, so tayi ta ɗauki rayuwata ranka ya daɗe Allah bai nufa ba, jibi yanda ta illata ni da kwalbar lemo dan kawai ta zo akan in taimaka mata ni kuma nace me yasa bata sameni a gida ba wurin iyalina kamar yadda na sanar da ita tun farko, sai tace min wai bata so iyalina ta sani ni kuma babu wani abu da nake ɓoyewa iyalina komai nawa is open, yarinyar nan ta fito ƙarara ta nuna min abinda take nufi dani nace a'a yanzu dai zan bata dubu ɗari taje ta kashe matsalar gabanta domin akwai alaƙa tsakaninta da iyali na, lokacin da na bata kuɗin nace ta tafi gida muka yi sallama ashe ba tafiya tayi ba laɓewa tayi dan tayi min sata, ina shiga toilet na jiyo alamar motsin mutum, fitowar nan da zanyi sai na hangeta tana ƙoƙarin yin awon gaba da jakata wadda aciki ta ga na ɗauko waɗannan kuɗin na bata.... Yallaɓai to cut the story short wallahi daƙyar na ƙwace jakata.... Kai garin in ƙwace ɗinne ma ta ɗauko makami tayi amfani dashi ta jimin wannan ciwon da kake gani wanda sai da ta kaini ga zuwa asibiti...... "


Kallonta DPO yayi na ɗan wasu sakanni yayin da ita kuma idanuwanta ke kallon ƙasa tana zubar da hawayen baƙin ciki da ɓacin rai, wannan wacce irin ƙaddara ce? Alhaji sabo ya yaudareta ya so yaci amanarta ya keta mata rigar mutuncinta Allah ya tsallakar da ita amma yanzu kuma yazo yana yi mata sharri da ƙage,muryar DPO ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi, 


"Hajiya kin aikata laifi kan laifi.... Laifinki da yawa, ta yaya zaki nemi yiwa mutum sata, sannan dan ya kare dukiyarsa kiyi yunƙurin ɗaukar rayuwarsa? This is a very serious case.... We can take it as criminal offense....." 


"Ni banyi niyyar yi masa sata ba, asali ma shine ya gayyace ni zuwa guest house ɗinsa duk da na kawo maganar mu haɗu a gidansa amma yaƙi yace baida lokaci..... Wannan ciwon da naji masa yunƙurin keta min haddi yayi shiyasa nayi amfani da kwalbar giyar dake cikin sitting room ɗin na buga masa..... "


" sharri zaka yimin Ruhaima? Abin naki harda sharri ya koma? Saboda kin buƙaci mu ƙulla mummumar alaƙa naƙi amincewa na nuna miki wannan ba halayyar mutanen ƙwarai bace shiyasa yanzu zaki zo nan kiyi min sharri? Alhaji sabo ya faɗa cikin hayaniya kamar gaske, 


"Ya isa haka Yallaɓai... Amm Ruhaima kika ce yayi yunƙurin keta miki haddi ko?" DPO ya buƙata yana Kallonta, 


"Ehh yallabai haka nace" 


"To a lokacin me ya hana ki kiyi ihun neman taimako? Wanne yunƙuri kika yi dan ankarar da mutanen dake maƙotaka da wurin dan akawo miki ɗauki?" 


"Banyi ihu ba kawai dai nayi ƙoƙarin ganin na kare kaina...." ta bashi amsa hawaye na bin kumatunta, 


"wannan ba hujja bace.... Sannan wannan maganar taki ba wacce hankali zai ɗauka bace Ruhaima... Idan har dagaske kike abinda kika faɗa cewar yayi yunƙurin keta miki haddi to kamata yayi kiyi ihu a matsayinki na mai hankali, sannan ni sai nake ganin babu abinda zai sa ki ziyarci guest house ɗinsa mutukar abinda kike faɗa gaskiya ne, me ya hana kije gidansa? Duk wanda aka ce mace taje guest house abinda zai fara zuwa ransa shine kinje taya shi hutawa ne..... Yanzu dai duk ba wannan ba, Alhaji sabo babu buƙatar mu fitar da maganar nan waje ko mu tura court, kamata yayi kuje gida kuyi sulhu, zamu bada belinta sannan dole zamuyi rubutu saboda gaba, domin case irin wannan bama ɗaukarsa da wasa..... "


Har suka yi suka gama bata sake furta koda kalma guda ɗaya ba saboda tama rasa me zata ce, binsu kawai take da ido har zuwa lokacin da DPO yace ta bada no wanda za a kira yazo yayi belinta, bata da zaɓi wanda ya wuce ta bada no din hajiya. Hajiya aka kira lokacin tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallar magrib tana azkhar, tana jiyo hayaniyar su Ajmal wanda ke ta ƙiriniya dasu Abid wanda suka zo weekend, 


A gigice hajiya ta fita da wayar a hannunta bayan ta saurari bayanin da aka yi mata a wayar wai daga police station ne aje ayi belin Ruhaima, part din da ke kusa da nata ta nufa a kiɗime dan ƙafarta ko takalmi babu tana tafe tana cin tuntuɓe, 


Fitowarshi daga wanka kenan yana goge jikinsa da towel yaji shigowar hajiya tana ƙwala masa kira cikin tashin hankali, 


"Sameer..... Sameer..... Kana ina ne? Wai ko baka ciki?" 


Jin kiran da take yi masa kamar bana lafiya bane yasashi saurin fitowa a yanda yake daga shi sai gajeren wando da towel a hannunsa, 


"Hajiya lafiya......?" 


"Babu maganar lafiya Sameer.... Yi maza ka shirya ka tafi police station Ruhaima aka kama.... Sauri kaje ka jiyo me ya faru...." 


Saida yaji gabansa ya tsinke ya faɗi amma sai ya dake bai bari hajiya ta fahimta ba, 


"Hajiya..... Kuma ni zan je?" 


"To wa kake so yaje? Ni zanje ko wa?" 


Shiru yayi bai amsa ba, sannan cikin halin ko in kula ya kawar da kai, 


"kayi maza ka shirya nace maka kaje, ko baka ji?" hajiya ta fada cikin faɗa, 


"Naji" 


Daga haka ya juya ciki, tsaki ya ja ya wuce gaban mirror ya fesa body spray sannan ya wuce gaban closet dinsa, farar jallabiya kar ya ciro yasaka yana jan tsaki, gefen gadonsa yaje ya ɗauki wayar shi da key ɗin mota ya fita yana ta faman ciccin magani, 


Part ɗin hajiya ya shiga, bai bi ta kan yaran dake ta faman guje guje ba a cikin babban falon gidan sannan da alama suma ɗin babu wanda ya ankara da shigowar tashi, 


Samun hajiya yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye sai faman safa da marwa take ta faman yi tana ta kaiwa da kawowa a falonta, 


"Hajiya wanne division ne?" ya fada fuska ba fara'a, faɗa masa tayi ya juya ya fita yana ta ɓaɓɓata rai, tafiyar mintuna 30 ce ta kai shi division ɗin, 


Lokacin da yaje iya DPO kaɗai da Alhaji sabo ya samu bai ga Ruhaima ba, kamar yadda Alhaji sabo ya tsare dpo ƙarya da gaskiya haka ya tsare Sameer wanda kusan gaba ɗaya ma zancensa ƙarya ne,


Sai da suka yi rubutu kowa yasa hannu daga ƙarshe aka shigo da Ruhaima dan itama ta saka hannu, kawar da kai Sameer yayi lokacin da take shigowa, fuskar ta jajur da idanuwanta saboda taci kuka har ta gaji, ɗankwalinta a hannu sai ko gyalenta dake kanta wanda ta yafa, hannu tasa Sameer yayi sallama dasu ya fita tabi bayansa, handbag ɗinta aka bata da takalminta, a hannu ta riƙe su dan tsabar baƙin ciki ko takalmin bata saka ba, tana biye dashi har gaban motarsa, ko Kallonta baiyi ba ya buɗe ya shiga itama ta shiga ranta a cunkushe kuma a dagule me yafi wannan tozarci da kunya? Ayi mata ƙazafin sata da bin maza? Yanzu ta san bata da wata hanya wacce zata wanke kanta sai abinda hali yayi, amma dai abinda ta yarda dashi shine Allah baya zalunci sannan baya bacci, ta san komai daren daɗewa Allah zai tona asirin alhaji sabo, 


Tunda suka fito daga police station ɗin bata yi gigin kallon ko inda yake ba sai yanzu da suka hau titi sannan ta saci kallonsa ta gefen ido, sai da tayi danasanin kallonsa saboda yadda taga ya haɗe girar sama da ƙasa ya cika fam kaɗan yake jira ya fashe, 


Tuƙi kawai yake yi gaba ɗaya ya tattara nutsuwarsa akai kamar babu wata halitta acikin motar sai shi ɗaya, ransa a ɓace yake tuƙin cikin tsananin baƙin ciki, kai tsaye gidanta ya wuce da ita, har cikin gidan ya tura hancin motarsa lokacin da mai gadi ya buɗe musu ƙofa, birki yaci da ƙarfi wanda sanadiyyar hakan har sai da ta buge kanta amma bai ko kalleta ba, buɗe ƙofa tayi ta fita dan jikinta ya bata hakan kawai yake buƙata ahalin yanzu, tafiya kawai take bata ko sake marmarin juyowa ba taji alamun fitowarsa daga cikin motar shima, tana dab da hawa barandar falonta tajiyo amon muryarsa cikin kaushi yake yi mata magana, 


"Be kamata ba sannan kuma ba daidai bane ki rinƙa bin mazajen mutane awaje ciki harda mijin ƙawarki, mijin ƙanwar mijinki dan kawai mijinki ya rasu, sannan saboda tsabar rashin tunani da toshewar basira harda sata..... Tirr.... Akwai mata da yawa da suka rasa mazajensu kuma suka daure suka yi hakuri suka kame kansu suka killace mutuncinsu, idan ba zaki iya haƙuri ba ki rungumi azumi a matsayin magani..... " daga haka ya juya ya nufi motarsa cikin tsananin fushi da ɓacin rai, tana tsaye tana kallonsa takalminta da jakarta da ɗankwalinta duk sun zame sun faɗi awurin saboda jinta take kamar ba ita ba, waɗannan baƙaƙen maganganun da Sameer ya faɗa mata su suka fi yi mata ciwo fiye da abinda Alhaji sabo yayi mata, yanzu ta san ba iya Sameer kaɗai ba kusan kowa kallon da zai rinƙa yi mata kenan, jarababbiya marar haƙuri ta kasa jure rashin mijinta tana neman wasu mazan, mai halin ɓera wadda Allah Allah take taga wasarere ta sata, tana nan tsaye kamar an dasata tana zubar da hawaye har motar Sameer ta fita, tafi mintuna 20 tsaye bayan tafiyarsa dan baƙin ciki dan har ƙafafuwanta saida suka yi tsami suka ƙage, daƙyar ta jasu ta shiga ciki sauran kayanta da ta zubar kuwa nan ta barsu ko bi ta kai bata yiba sai maigadi ne ya shigo mata dasu, zaman dirshan tayi a tsakiyar bedroom ɗinta tana kuka wiwi saboda baƙin ciki, daƙyar ta rarrashi zuciyarta bayan taci kuka ta ƙoshi, tana ƙoƙarin yin shirin bacci lokacin misalin ƙarfe 9:30 na dare taji wayar ta dake cikin jaka tana faman neman agaji sakamakon ƙarajinta da ya karade ko ina na cikin dakin.......✍🏻






*_Ummi Shatu_*👌🏻