SHAFI NA BIYAR
by @ummishatu
©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*
*SO DA ALAƘA....!*
_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_
*Wattpad:@Ummishatu*
Free page
5
***Driving yake amma tunaninsa na wani waje, shi gaba ɗaya lamarin mata yanzu tsoro yake bashi ba mamaki ba, banda lalacewar zamani ta yaya mace zata rinƙa ƙasƙantar da kanta tana ajiye darajar da Allah yayi mata tana cire kunyar da aka santa da ita tun tale tale tana kaiwa namiji kanta? Tsaki yaja a karo na ba adadi tun bayan da yabaro gidan Ruhaima, shi dai idan da abinda ya tsana a duniya to zina ce, yaƙi jinin zina sannan ya tsani duk wani mai aikatata amma yanzu yaga kamar tama zama ado dan idan mutum ba yayi wai gani ake bai waye ba, sannan masu yi basa kunyar bayyana kansu ya fahimci hakanne dalilin yawan kawo masa hari da mata keyi shi dai ya rasa wannan masifa ya rasa me suke gani atare dashi da suke yawan kawo masa farmaki, da zancen zucin da yake yi ya shiga unguwar su ransa a cunkushe kuma a ɓace, sallar ishah ya tsaya yayi sannan ya shiga gida, tun a hanya yaketa ganin kiran hajiya amma bai ɗaga ba.
Kamar yadda ya tafi yabarta hankali tashe yanzun ma haka ya sake dawowa ya sameta, duk bata da cikakkiyar nutsuwa, yana shiga ta miƙe daga zaunen da take bayan ta ajiye Ajmal a gefe wanda ada yake kwance a jikinta yana bacci,
"Ina Ruhaiman take? Me ya faru? Me ya hadata da ƴan sanda har ta kaisu ga zuwa police station? Yanzu ya aka ƙare?"
Duk da a cikin fushi yake sai da yayi murmushi jin irin tarin jerin tambayoyin da hajiya ta jero masa lokaci guda kuma ya san kowacce tambaya tana buƙatar amsarta,
" Sameer..... Kabani amsa mana "
" Hajiya ba wata matsala bace babba... Harma ai an kashe case ɗin, tana can gidanta na sauketa..."
Daga haka ya wuce kitchen, zama hajiya tayi a ranta tana juya wannan al'amari, kwata kwata Sameer yaƙi wayar mata da kai ya sakata a duhu yaƙi ya bata gamsasshiyar amsar da take buƙata, kiran da ya shigo wayarta ne ya katse mata tunanin da take yi,
" Umaima....."
"Hajiya kinji badaƙalar da Ruhaima tayi ko? Wallahi sai na yi mata rashin mutunci sai na nuna mata true color ɗina.... Ta rasa wa zata bi sai mijina?"
Jin abin da Umaima ke faɗi yasa hajiya zaro ido cikin duburburcewa dan sam ma sai ta kasa fahimtar inda zancen ya dosa,
" wai Umaima me kike faɗa hakane.... Meyake faruwa? "
" Hajiya Sameer bai sanar dake abinda yake faruwa ba?? "
" Bai sanar dani komai ba, kin ganshi shigowarshi kenan ya bani amsa a dunƙule yaƙi ya fayyace min komai...."
Daidai lokacin Sameer ɗin ya shigo cikin falon riƙe da filet wanda ya zubo abinci aciki, jin abin da hajiya ke faɗa a waya ya tabbatar masa da Umaima suke waya, ji yayi ransa ya kuma ɓaci, bai zauna ba ya wuce ya fita shi koma maganar fa ya tsana baya son yaji ana sake maimaitata dan hakan sake ƙona ransa yake yi, wannan wacce irin fitina ce ke damun Ruhaima? Koda yake kusan haka yanzu gaba ɗaya zamanin ya koma, wasu matan ma suna da auren amma hakan bai hanasu bibiyar wasu mazan ba a waje, shi kansa ba dan kariyar ubangiji ba matan aure nawa ne suka kawo masa hari? Kasa cin abincin yayi saboda damuwa.
In banda salati babu abinda hajiya ke yi jin labarin abinda ya faru da Umaima ta kwashe ta sanar da ita yanzu kamar yadda itama Alhaji sabo mijinta ya sanar da ita babu abinda ta ragewa hajiya ta sanar da ita komai, jiki a sanyaye kuma a mace hajiya ta kashe wayar bayan ta gama jin abinda ya faru, tabbas ta san Ruhaima tana da nutsuwa da kunya da halin ƙwarai to amma yanzu ba a shaidar mutum shine matsalar, mutum yana iya canjawa akoda yaushe sannan kowanne mutum tara yake bai cika goma ba, haka kuma wani abin ƙaddara ce wadda babu yadda mutum zai yi da ita, ita ta ɗauki Ruhaima tamkar ƴar da ta haifa ta cikinta ba wai sirika ba, duk abinda zata yiwa ɗan cikinta shi zata yiwa Ruhaima,wayarta ta sake ɗauka ta fara kiran layin Ruhaima,
Jiki a sanyaye ta ƙarasa gaban handbag ɗinta ta ciro wayar ganin hajiya ce me kiran yasata jin kunyar duniya ta lulluɓeta ta san Sameer yaje ya sanar da ita halin da ake ciki,
"Haba Ruhaima.... Ya ina yabon ki salla amma zaki kasa alwala.... Dan kina cikin wani hali Ruhaima sai ki kifara ƙoƙarin ɓata rawarki da tsalle?? Ai ko wani ne awaje Ruhaima bai dace ki kai masa kanki ba harda yunƙurin sata bare mijin Umaima....."
"Hajiya dan Allah ki fahimceni ke kadai na san zaki fahimceni akan wannan lamari wallahi yanda ake tunani ba haka abin yake ba...." ta faɗa cikin kuka,
"Wannan ai ya wuce Ruhaima sai dai a kiyaye gaba, dukkan ɗan adam ajizi ne amma ki kiyaye, dan Allah.... Ni tunda Sameer ya dawo naji yaƙi magana dama naji hankalina bai kwanta ba sai da Umaima ta kirani yanzu, Allah ya rufa asiri amma ki kiyaye dan Allah" daga haka taji hajiya ta katse wayar, take kuma wani kiran ya sake shigowa kamar dama jira ake, ganin Umaima ce sai da gabanta yai muguwar faɗuwa,
"Hello inlaw....."
"Karki fara... Karki kuskura ki sake kirana da haka Ruhaima... Ai baki ɗaukeni a hakan ba tunda har kike bibiyar mijina, dama wannan shine dalilin da yasa kika zo har gida neman sa?"
"Dan Allah ki fahimceni Umaima, kema kin san wallahi ko a mafarki bazan taɓa aikata hakan ba...."
"Daga yau sai yau wallahi babu ke babu mijina, idan kika sake yunƙurin kusantar mijina zaki gane shayi ruwa ne......"
"Umaima karki bari shaidan ya shiga tsakaninmu dan All....." ƙitt taji Umaima ta datse kiran, wasu hawayen baƙin ciki ne suka sake ɓarke mata, daman ta san yanzu babu wanda zai yarda da ita kowa kallon mai laifi yake yi mata duk da irin kokarin da hajiya ke yi a kanta ace ta aikata haka ai da ta tabbata butulu, kukan nan dai shi take ta yi har tsawon wani lokaci da ita kanta bata sani ba.
Samun kansa yayi cikin wani ƙarin ɓacin ran a duk sa'ilin da ya tuna wayar da yaji hajiya suna yi da umaima, wato Alhaji sabo sai da ya kwashe duk abinda ya faru ya fadawa umaima kenan saboda tsabar rashin kara, Meyasa bazai rufa mata asiri ba sai ya sake zubar mata da mutunci acikin family? Haushi ne ya kamashi ya ja tsaki,
"Kawai salon ta jawowa mutane magana..... Sai da ta dauko mana magana dai hankalin ta ya kwanta" ya faɗa cikin ɓacin rai yana tashi daga kwancen da yake kan madaidaicin gadonsa,
Kukan magensa ne ya sake tunzura shi, dan shi yama manta da ita, ba dan ya so ba ya miƙe ya buɗe ƙofa, yana buɗewa ta shigo tana shinshina ƙafarsa sunkuyawa yayi ya ɗauketa yana shafata, ganin tana lasar baki yasa shi dafe kai,
"am sorry pretty.... Yau ban baki abinci ba sai sau ɗaya... Wallahi kaina ne a caje daren yau ɗinnan...." Saman gadonshi yaje ya ɗorata sannan ya fita, part ɗin hajiya ya sake komawa bai jima ba ya fito riƙe da glass cup cike da madarar kwali sai abinci a wani ɗan ƙaramin filet, part ɗinsa ya koma ya ɗauki magen ya ɗora akan cinyarsa ya soma bata abincin da madara tana ci,har ta cinye tas ya kwantar da ita kusa dashi, haka dama yake rayuwa da wannan magen wadda ya sakawa suna pretty tun tana yar ƙarama da ya tsinceta a lambun gidan ya ɗaukota, tare suke kwana.
Da ƙyar ta samu bacci daren ranar dan sai bacci ɓarawo, bayan asubah ta samu ta farka, amma tana farkawa abinda yafara zuwa ranta shine abinda ya faru jiya, take ta ji wani sabon bakin ciki ya sake turnuƙeta sai da ta share hawaye sannan ta shiga bathroom ta ɗauro alwala tazo tayi salla, bayan ta idar ta ɗauki alqur'aninta dake ajiye gefe ta karanta abinda ya sawwaƙa sannan ta rufe ta soma azkhar. Wunin ranar gaba ɗaya acikin ɗaki tayi shi duk da dama hakan ɗabi'arta ce yanzu amma na yau kam kamar na dabanne, shigowar baba saude mai aikinta wadda yanzu ita kaɗai ta rage acikin ma'aikatan gidan dan duk sauran ta sallamesu tun jimawa,shigowarta ne yasa ta tashi zaune da koɗaɗɗun idanuwanta take kallon baba sauden,
"Ruhaima... Lafiya kuwa yau duk baki fito ko falo ba? Ko wani wurin ke yi miki ciwo?"
"Wallahi lafiya lau baba saude.... Kawai dai akwai abinda ke damuna"
"Hakane.... Kowa ka gani dama akwai abinda ya dameshi sai dai hakuri, duk abinda yake damun bawa idan yayi hakuri zai wuce, na san kina cikin damuwa amma ki kara haƙuri akan wanda kikayi abaya Insha Allah ubangiji Allah zai baki mafita sannan yana tare dake a koda yaushe... Allah ya fiki sanin damuwarki Ruhaima kuma zai kawo miki ɗauki Insha Allah "
Duk da bata bayyanawa baba saude damuwarta ba amma kalaman na baba saude sun samar mata da nutsuwa kuma sun sanyaya mata zuciyarta haka kuma sun rage mata wani kaso mai yawa daga cikin damuwarta, ƙwarin gwiwa taji ta sake samu akan ƙudurinta da kuma nufinta,
Bata san lokacin da ta ɗauki wayarta ta kira hajiya ba, da sallama hajiya ta ɗauki wayar tata lokacin suna tare da Sameer acikin bedroom ɗinta yana kwance kan gadonta Ajmal yana kan ruwan cikinshi yana doki dashi,
Saida ta gaida hajiya sannan cikin sanyin muryarta wanda ya gaurayu da damuwa tace "Hajiya dan Allah ina son magana da Umaima da Sameer da kuma ke harma da Alhaji sabo idan zai yuyu... Ma'ana dai ina so mu haɗu gaba ɗayanmu anan gidan ki kuma gabanki dan akwai wata sarƙaƙiya da nake son warwarewa....."
"To shikenan Ruhaima amma ni da sai nake ganin idan har akan waccar maganar ce ta abinda ya faru da kin barshi..."
"a'a hajiya a dai taimaka min a saurareni...."
"to shikenan sai mu barshi asabar ko saboda kinga suna zuwa aiki...."
"hakan yayi hajiya nagode Allah ya ƙara girma..."
Sallama suka yi, ɗan tashi zaune Sameer yayi yana kallon hajiya,
"me kuma ya faru?"
"Ruhaima ke son Magana damu gaba ɗaya.... Ina jin zata koma gida ne amma dai bata faɗi hakanba kawai hasashe na ne..."
"zata koma gida kuma? To amma hajiya ai bai kamata mu barta ta tafi ba..." ya fada cikin damuwa yana ƙarasa tashi zaune,
"to ya za ayi Sameer? Bari dai lokacin yayi sai muji me take tafe dashi"
Bai ƙara cewa komai ba ya tashi ya fita cikin damuwar dashi kansa bai san ko ta mecece ba, farfajiyar gidan ya fita ya samu ya jingina hannayensa cikin aljihun bakin trouser ɗin dake jikinsa..........✍🏻
*_Ummi Shatu_*👌🏻