SO DA ALAƘA

SHAFI NA SHIDA

by @ummishatu

©️ *HASKE WRITERS ASSOCIATION*





 *SO DA ALAƘA...!*




  _*NA*_


_*UMMI A'ISHA*_




*Wattpad:@Ummishatu*




Free page 



6



****Rasa abinda zai yi yayi sai faman zancen zuci yake ta yi shi kaɗai,


"to ko maganar da na fada mata ne ta ɓata mata rai? Na faɗa mata wani abu mai zafi ne?" ya tambayi kansa yana kallon harabar gidan, 


"amma ni a iya sanina ai gaskiya na faɗa mata, bai kamata ta rinƙa ɗauko mana magana ba dan kawai tana missing mijinta...." ya sake bawa kansa amsa, "oho dai..." daga haka ya fita daga ma gidan baki ɗaya a ƙafa batare da ya ɗauki motar shi ba, sai dai duk da ya zurfafa tunaninsa ya kasa gano dalilin da yasa Ruhaima tace tana son ganinsu gaba ɗaya, tafiya yayi sosai acikin unguwar yana zagayawa daga ƙarshe ya yada zango a masallacin wani ƙofar gida dake da maƙotaka da unguwar tasu ganin lokacin sallar magariba yayi.


Sai da yayi salla sannan ya koma gida, sashensa ya wuce kai tsaye yayi wanka sannan ya fito riƙe da magensa pretty, lokacin da ya koma part ɗin hajiya samu yayi Ajmal yana tv game a falon hajiya nan ya biyeshi suka yita yi tare kamar wani sa'ansa har saida Ajmal ɗin yayi bacci. Washe gari itace ta kama ranar da Ruhaima zata zo domin ganawa dasu kamar yadda ta roƙa, duk da tana cikin tsananin fargaba da da tsoro amma ta dake ta daure tana ta addu'a da haka ta shirya, navy blue color na leshi ta saka mai duwatsu ɗinkin riga da skirt, turare kaɗan ta ɗan fesa sama sama sannan ta kawo blue ɗin mayafi ta yafa, sam bata ɓatawa kanta lokaci ba wurin yin kwalliya domin ko mai bata shafa ba saboda a haƙiƙanin gaskiya bata cikin nutsuwa da farin ciki tun daga ranar da Alhaji sabo yayi mata wannan sharrin,


Misalin ƙarfe 12 na rana ta isa gidan hajiya duk da dai gabanta sai faman faɗuwa yake, a falo ta tarar da hajiya da umaima wadda ko kallo bata isheta ba, duk sai ta sake jin babu daɗi ga kuma yaransu nan suna wasa tare wato su Abid tare da ɗanta Ajmal, daurewa tayi bayan ta gaisar da hajiya ta saki fuska tace,


"umaima ina wuni?"


Kamar ba zata amsa ba dan aciki ciki ta amsa gaisuwa, duk da hakan yayiwa Ruhaima ciwo amma sai ta basar ta danni zuciyarta, itama hajiya ganin haka yasata kiran Sameer awaya aganinta gara yazo su yi su yi abinda ya tarasu kowa ya koma gidansa bata son irin wannan zaman na doya da manja,


Ita dai Ruhaima a ranta tunani take to ya taga umaima ita kaɗai? Ina mijin nata ko dai ba zai zo bane? Tana son ta sani amma babu damar tambaya, jin horn acikin gidan ya tabbatar musu da zuwan wani baƙon,


"yawwa ga abbansu Abid ɗin nan ma ya ƙaraso hajiya" inji umaima, Wani sanyi Ruhaima taji acikin ranta,


Zuwan Alhaji sabo yayi daidai da fitowar Sameer daga part ɗinsa, sanye yake cikin ƙananan kaya farar t shirt ta polo sai blue ɗin wando jeans, gaisawa suka yi da Alhaji sabo sannan ya jagoranceshi zuwa ciki,


Bayan gaishe gaishe Sameer ya dubi hajiya wadda ke zaune ɗan gaba dashi kaɗan,


"Hajiya Nifa inada uzuri.... Dan Allah ayi abinda za ayi"


Kallonsa Ruhaima tayi ta ƙasan ido ita dai a rayuwa ta rasa me tayiwa bawan Allahn nan da bata burgeshi tsakaninta dashi ko yaushe sai harara sai ɗaure fuska sannan babu wata magana mai daɗi da take shiga tsakaninsu dan ko gaishe shi tayi tun lokacin da yayansa yana nan a ciki ciki yake amsawa kai kamar ma a dole yake amsawar dama kuma bama zuwa gidan nata yake yiba sai da ƙwaƙƙwaran dalili,


"to ai Ruhaima ce ta taramu dan haka ita muke saurara...." maganar hajiya ta ratsa kunnuwanta nan ta dawo cikin hankalinta daga tunanin da take yi, gaba ɗaya kowa ita yake kallo kuma yake saurare banda Sameer wanda ko kallo bata isheshi ba dan wayar shi ma yake dannawa, shi kuwa alhaji sabo ido ya ƙura mata acikin ransa yana bakin ciki da takaicin rashin cikar burinsa yaso ya ɗanɗana kayannan yaji dan ya san zai samu cikakkiyar nutsuwar da yake so, amma yanzun ma bai haƙura ba kuma bai sare ba zai sake jarraba wata hanyar har sai ya dace,


"Kamar yadda kowa ya sani, ni marainiya ce na taso cikin maraici, cikin babu......"


"To sai me? Kowa ya san wannan, idan dan shi kika taramu muna da abin yi..." Sameer ya faɗa ta hanyar ɗaga mata hannu alamar dakatarwa, bata kula shi ba taci gaba da faɗin abinda take da niyyar faɗa,


"Duk da na taso cikin babu, babu cin yau babu na gobe, babu suttura babu kayan ƙyale ƙyale ko more rayuwa hakan bai taɓa sani tunanin inyi sata ko in ɗauki abin wani ba, ban taɓa ji araina zan saci kayan wani ko in bada mutuncina dan in mallaki wani abu ba.... A koda yaushe kakata tana faɗa min cewa wadatar zuciya itace babban arziƙi koda mutum baida cin yau baida na gobe, nasha wahalar rayuwa iri iri a lokacin da nake tasowa saboda babu, amma haka na jure nayi hakuri har zuwa girmana, wallahi tallahi kayan wani ko dukiyar wani bata taɓa burgeni ba bare har inji araina zan iya ɗauka da sunan sata..... Abban Ajmal ya taɓa sanar dani sunyi haɗin gwiwa da Alhaji sabo wurin gina wani kasuwanci, nikuma a halin yanzu inada buƙatar kuɗi dan in gina rayuwar ɗana, lokacin da naje gida nemansa umaima tace yayi tafiya, ganin maganar ko a waya zan iya yi masa shiyasa na buƙaci da ta bani no wayarsa, shi da kansa yace bazan iya ganinsa ba a gida saboda yana da meeting amma zan iya samun ganinsa a guest house ɗinsa dan kusan gaba ɗaya harkokinsa yanzu acan yake gudanar dasu, wallahi zuciyata ɗaya na shirya naje ban taɓa tunanin wai da wata manufa ya gayyaceni can ba, lokacin da naje ya fito min da ƙudurinsa ban amince ba dan aganina wannan cin amana ne amma sai ya nemi da yayi min ta ƙarfi..... " wani kuka ne yaci ƙarfinta dama kuma tun lokacin da ta fara maganar hawaye ke bin kuncinta, duk jikin kowa yayi sanyi da kalamanta duk da wai basu gaskata cewa alhaji sabo yayi yunkurin yi mata fyaɗe ba,


" Ta yaya zamu yarda da abinda kike faɗa? Kina da wata shaida?" umaima ta faɗa a kufule saboda jin abin da ake faɗa akan mijinta, yayin da shi kuma alhaji sabo kallon Ruhaima kawai yake yana tunanin ta inda yakamata ya soma wanke kansa ya sake ɗaureta sannan ya ɓatata a idon kowa,


Handbag ɗinta ta buɗe ta ciro wayarta tana goge hawaye,


"wannan itace maganar da muka yi awaya...." ta faɗa tana kunna recording ɗin da tayi, bayan duk an gama saurara ta sake kunna wani tana cewa "wannan shine abinda ya faru a guest house ɗinsa"


Kowa nutsuwa yayi yana sauraren maganganun alhaji sabo wanda suke fita tar kamar yanzu yake yi, duk abinda ya faru tun daga zuwanta har lokacin da suka yi magana da mai gadi ya kirashi awaya har shigarta da yadda ya rinƙa hilatarta tana ƙi da kokawar da suka gwabza da komai kai har zuwan ƴansanda duk sai da kowa yaji, kunya ce ta lulluɓe alhaji sabo yaji kamar ƙasa ta buɗe ya shige dan tsabar kunya, bai taɓa jin kunya irin ta yau ba, da ya san wannan ranar zata zo tabbas da bai aikata abinda ya aikata ba, ita kuwa umaima kuka ta fashe dashi, babu wanda ya iya magana daga hajiya har Sameer, itama Ruhaima kukan take yi duk da bata so ta tona masa asiri ba amma bata da wani zaɓi illa hakan ko dan ta wanke kanta daga kallon da kowa ke yi mata, miƙewa tayi ta ciro kuɗin da ya bata dubu ɗari, ta ajiye a gabansa tace,


"waɗannan sune kuɗin da ka bani.... Bani da buƙatarsu a yanzu, gashi na dawo maka dashi...."


Shi dai alhaji sabo kansa na sunkuye a ƙasa gumi sai yanko masa yake tako ina saboda tashin hankali,ganin ta juya tana ƙoƙarin barin falon tana kuka umaima tace, 


" Ruhaima dan Allah ki yafe min.... Nabi daɗin bakin namiji na biyewa kishi idanuwana sun rufe na kasa fahimtarki... Wallahi koda wasa ban san mijina yana da irin wannan halin ba" tsayawa tayi cak tana sauraren maganganun umaima, kai kawai ta ɗaga mata alamun gamsuwa amma daga haka bata iya cewa komai ba ta fita daga falon tana share hawaye......✍🏻




*_Ummi Shatu_*👌🏻