MIJIN MATACCIYA

SHAFI NA HUƊU

by @ummishatu

  *4*



   ~~~Koda tafito daga office din senior master bayan yagama accepting dinsu bata ga wannan yaron ba na dazu amma kuma maganganun yaron nata kai kawo acikin kwakwalwarta musamman ma maganar da yayi da yanda yazo ya riketa kamar dama can yasanta,


Da tunanin yaron da bata san ko waye ba tabar makarantar ta nufi zonal office domin taje tayi documentation zuwa gobe kuma sai ta nufi gida kanon dabo domin anbasu hutun sati biyu kowa yaje gida ya kintso sai yadawo da shirin zama,duk da bata son koyarwa kuma bata sha'awarta amma wannan kam tana jin zataji dadin aiki dasu domin makarantar ta azo agani ce kuma class biyu kacal aka bata wato JSS 2 da JSS 3 inda zata rinka koyar dasu darasin turanci dama abinda ta karanta kenan wato BSC English.


Aranar ta gama harhada kayanta domin da safe sammako take son yi zuwa gida bata son takai rana ahanya,mujahid kuwa kamar sun shekara basu ga juna ba yadda yabi ya rikice mata ya dameta da waya ba dare ba rana yana tambayar yaushe zata tafi idan babu dama shifa sai yazo da kanshi dan yaganta. Sassafe ta fita ta samu taxi yakaita tasha inda zata shiga motar kano kuma cikin nasara tana zuwa motar ta cika dama mutum daya ake jira babu bata lokaci suka dauki hanyar kanon dabo tumbin giwa.

***

 A guje yashiga cikin babban falon gidan yana kiran "Daddy.... Uncle..... Papa..."


"Kai Aryan menene haka kake gudu sai ka yanke jiki ka fadi ko?..."


"Umma Ina Daddy na?"


Dariya umma barira tayi ta mika hannu ta jawoshi jikinta,


"Banda abinka dan jikalle na ina zaka samu ganin babanka yanzu? Tun fa kafin ka tashi daga bacci yafita yace zaije waccan kasar arnan ni banma rike sunan garin ba,ai ko zai shigo gidan nan to ba yanzu ba...., Maza muje acire kaya ayi wanka azo aci abinci ayi shirin islamiyya malam yana nan zuwa"


Bata fuska yayi kamar zai saka kuka jin abinda umma barira tace,shi Daddyn sa yake son gani,shi yake son fadawa abinda yagani yau,da gudu ya shige dakinsa ya dauki kantamemiyar wayarshi ya zauna akan gado yana neman layin baban nashi amma bai samu ba ahaka umma barira tazo ta iskeshi nan ta karbe wayar ta ajiye asama sannan tajashi zuwa toilet tayi masa wanka ta shiryashi sai rakwarkwabe fuska yake yi irin baya so dinnan.


Misalin karfe 1 na dare ya shigo gidan tare da mukarrabansa, direct sashensa yashiga yayi wanka yasaka kayan baccinshi masu silbi riga da wando maroon colour,ga abinci nan akan table kala daban daban wanda duk aciki baya jin akwai wanda zai iya ci, da kanshi yashiga kitchen ya hada coffee sannan yafita ya nufi dakin Aryan,


A gefen gadon Aryan din ya zauna yana dan kurbar coffee din dake hannunshi yana yi yana nazarin d'akin,ga littattafai nan acan k'asa kan center carpet da alama home work yayi yagama kuma shine ba adebe littattafan ba yabarsu awurin,


Da kanshi ya tattarasu yasaka masa cikin school bag dinshi sannan yasake komawa gefenshi ya zauna tare da kunna yar karamar fitilar dake girke gefen gadon Aryan wato bedside lamp.


Cikin magagin bacci yaron yafarka ganin Khalil zaune kusa dashi yasashi kokarin tashi zaune,mayar dashi Khalil yayi ya kwantar tare da dan rungumoshi jikinsa cikin sanyin murya yana fadin,


"Koma kayi baccinka Aryan...., Nazo ne inganka dama,yi bacci kaji yaron kirki"


"Daddy naganta yau..... Kace min ta mutu ashe bata mutu ba Allah naganta"


Duk a tunanin Khalil magagin bacci ne yasa Aryan wadannan surutan na shirme shiyasa yayi gaggawar dakatar dashi ta hanyar fadin,


"Shhhhhh,Nace kayi bacci ko? Kar nasake jin bakinka awurin"


Maida idanuwanshi yayi ya rufe yana motsa baki alamun yana son yin magana amma babu damar yi,shafar kanshi Khalil yafara yi tun daga sumarshi har zuwa fuskarshi alamar so da kulawa mintuna kadan yasake komawa bacci,sai da yaga yayi nisa acikin baccin sannan yayi masa addu'a ya shafe masa jikinsa dashi sannan yakashe masa bed side lamp din da ya kunna yatashi ya fita bayan ya lullube shi ya rufe masa kofar dakin,


Bedroom ya wuce direct ya nemi wuri ya zauna saman kujerar dake can girke gefe daya da center table a gabanta,lumshe idanuwanshi yayi take tunanin da yasaba bijiro masa ya fara bijirowa kwakwalwarshi kamar koda yaushe wato tunanin matarshi Ramlat margayiya,


"Allah sarki Ramlat kin tafi kin barmu da kewarki da tunanin ki da kaunarki da kuma begenki da kishirwar ganinki..... Sai dai kash nasan bazan sake ganinki ba sai a darus salam,Allah ya jikanki,yaron mu ma da bai sanki ba kullum cikin mafarkinki da begenki yake...."


Daurewa yayi ya hadiye hawayen dake barazanar zubo masa,ahankali ya jingina da jikin kujerar ya kwanta sannan ya lumshe idanuwanshi yana tunani aranshi. Tsawon mintuna masu yawa ya dauka yana tunanin daga karshe dai ya tashi yashiga bathroom duk zufa ta jikeshi tamkar yana gaban wuta,ruwan sanyi ya sakarwa kansa bayan ya kunna na'urar dake bada ruwa. Ruwa yayita kwararawa kansa sai da yaji dan dama dama sannan yafito bayan ya daura alawala,


Wani kayan yasake sakawa sannan ya tsaya gaban mahaliccinsa kamar yanda yasaba akoda yaushe,sallah yayita yi har karfe 3 na dare tayi sai lokacin ya kwanta bacci amma kuma baccin ya gagreshi sai tunani dake ta addabar ruhinsa daga karshe dai yayi nasara baccin ya daukeshi bashi ya farka ba sai asubah. Bacci yasake komawa bayan yayi sallar asubah,yana cikin bacci yaji Aryan yana tashinsa,


"Daddy kace min mommy na ta mutu kuma jiya naganta a school..... Papa naga mommy jiya katashi kaji..."


Cike da bacci a idonshi ya bude idanuwansa yatashi zaune yana kallon Aryan wanda ke sanye cikin uniform din makaranta sai kamshin turaren silver boy yake yi idanuwanshi sunsha kwalli baki, murmushi Khalil yayi sannan yajawoshi jikinsa ya rungume,


"Good morning lovely son...."


"Daddy naga mommy jiya a...."


"Mu fara gaisawa first sai ka fada min,ko baza ka gaida ni ba yau?"


"No Daddy zan gaida ka, Good morning"


"Morning my love,how was your night? Wa kace kagani jiya?"


"Uncle mommy na mana wadda kake nuna min a hoto har kace min ta mutu lokacin da za a haifeni..."


Dan jimm Khalil yayi yana nazarin maganar da Aryan yafada,lumshe idanuwanshi yayi ya shafi sumar Aryan,


"To naji Aryan...ai idan aka mutu ba a dawowa ita kuma mommy dinka ta mutu"


Bude baki Aryan yayi zai sake magana Khalil ya dakatar dashi sakamakon kaiwar da idonshi yayi kan agogon dake ajiye kan bed side drawer,karfe 7:40 agogon ya nuna,


"Aryan ya isa maza jeka ka tafi school kaga ka kusa makara"


Kiss yayi ma yaron a kumatu sannan ya saukar dashi daga kan gadon yana tambayar shi yaci abinci? Daga masa kai yayi alamar ehh,


"Me kaci?" Yasake tambayarshi yana son kawar da damuwar dake saman fuskar yaron,


"Potatoes smiley & egg muffin"


"Good boy,umma ta hada maka da chocolate ko?"


Kai ya daga masa,kumatunshi yaja sannan ya rakashi ya koma ya kwanta bayan ya rufe kofar d'akin nashi,wani baccin yake son yi amma yasan ba mai yuyuwa bane domin yau yanada commitments da yawa gashi yana son ya je gombe ayau yadawo duk da dama yasaba hakan, hakura da baccin yayi yatashi yayi wanka ya shirya cikin fararen kaya yafita dama already table ashirye yake amma iya ruwan tea kadai ya iya sha yafita yaje ya gaida umma barira daga nan yafita office,a office dinma babu abinda yaci duk da ankawo abinci conference room din nasu,bashi yabar office ba sai 6 na yamma wato dab da magriba,daga can wani uzurin yasake wucewa bai fito ba sai misalin karfe 8 da kusan rabi kai tsaye kuma gobe suka nufa.


Lokacin da yashiga family house dinsu a gombe tuni wasu ma har sunyi bacci agidan amma dai hajiya Zaitun wato mahaifiyar su bata kai ga yin baccin ba hakama sauran yanmatan gidan duk suna tare a falonta suna hira,


Zama yayi agefen yanmatan gidan wato mufida da zarah da Sarah wadanda duk yan riko ne hajiya ke rikesu amma ita Zaid ne dan autanta,


"Mufida ku kawo min abinci inci wallahi rabona da abinci har na manta....."


Tashi suka yi dukansu suka fita ita kuma hajiya tasamu wuri ta zauna tana kallon d'an nata wanda aganinta yanzu duk ya lalace yaki yin kiba amma da ba haka yakeba,


"To ba dole kayita zama da yunwa ba mu'azzam tunda ka ki yin aure ka zabi yin rayuwa kai kadai babu mace... Yanzu da kana da aure yaushe matarka zata barka da yunwa wuni guda..."


Bai kai ga yin magana ba su mufida suka shigo kowaccensu rike da food flask,tuwon shinkafa suka kawo masa miyar taushe sai gasasshen nama da kunun aya mai sanyi wanda yaji kwakwa da madara da dabino sosai,saida yaran suka fita sannan ya kalli hajiya bayan yafara kwasar girkin dake gabansa,


"Wallahi hajiya ba rashin aure ne ke hanani cin abinci ba, lokacin cin abincin ne ma babu kwata kwata, rabona da gida fa tun karfe 8 nasafe ahakanma dan dai ina daurewa ne bana son yin nesa da Aryan amma da wallahi sai inyi kwana biyu banje gidanba...., Ni yanzu ma banida lokacin aurenne gaba daya"


"To koma dai yaya ne ai gara ace kana da matar akan ace babu Khalil,kai kaine babba kuma kana nema ka zama babban kwabo...... Ko tafiye tafiyen k'asashen wajen nan da kake yi acan kake aikata son ranka?"


Cak ya tsaya daga cin abincin da yake yi sannan cikin sanyin murya yace,


"Wallahi tallahi hajiya ni harkokin aikina ke fitar dani waje bawai wani abuba,haba hajiya ai ko dan Ramlat bazan iya aikata mummunan laifi kwatankwacin wannan ba..."


"Nima bance kana aikatawa ba amma dai yadace kayiwa kanka fada,mutum ya radi kansa tun kafin duniya ta radeshi, mutane suna ganin kana da kudi da komai na rayuwa amma baka da mata to gani zasuyi kamar wani abu kake aikatawa agefe..."


"Hajiya wallahi duk lokacin da kika yimin maganar auren nan jinina ne yake hawa saboda bana sonta..."


"Ai shikenan,to Lubnah ta haihu yau da safe ta samu yarta mace,sai ka samu lokaci kaje kayi mata barka"


"To insha Allah, Allah yaraya,zan dawo inyi mata barka idan nasamu lokaci, Ina zaid kuma"


"Ai yatafi Abuja tunda rana,baku hadu bane?"


"Bamu haduba ai rabona da gidan tun 8 nasafe"


Hira ya zauna suka sha da hajiya sosai kai idan ba sani kayi ba sai kace agarin zai kwana,karfe 1 da yan mintuna suka kama hanyar Abuja,


Lokacin da yashiga part dinsa a mutukar wahale yake ga gajiya ga kuma damuwar dake addabar mararsa,cire rigar jikinshi yayi yarage daga shi sai iya singilet da dogon wando,wayarshi ya dauka ya kira number nura PA,mintuna kadan sai ga nuran yashigo,


Cikin mawuyacin hali ya kalli nura, "Nura ina zaka samo min kanwa ko lemon tsami?"


"Ranka yadade kanwa kuma? A wannan daren? Ai yanzu babu inda za asamu kanwa acikin garin Abuja,dama dama lemon tsamin ma"


"Je kasamo min lemon tsamin"


Sake gyara kwanciyar shi yayi bayan nura yafita yana dafe da mararsa wacce ke murda masa wannan yana daya daga cikin dalilin da yasa baya son yaci abinci ya koshi domin duk ranar da ya koshi to sai ahankali.......✍️